← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 128

Sashe 14

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Mutumin ya k'araso gun Zaid tare da fadin "Ya Salam" waigawa yayi gefe ya ga kowa na ta kanshi don dare ya soma yi, da sauri ya cicibe Zaid ya saka a mota, ya shiga ya Motar shi sai wani Asibiti mai suna Garkuwa Clinic.
Nurses suka shiga da Zaid, nan da nan aka soma taimaka mai,bayan wasu lokkutta, Dr ya fito ya samu Mutumin zaune daga waje, yace "ka kwantar da hankalin ka, stress ne ya ma yaron yawa, mun saka mishi drip. Alhajin ya sauke naunayar Ajiyar zuciya, yace "Alhamdulilah".
*
Lura yayi da Wallet dinshi a bude kuma a k'asa, da mamaki ya karasa ya dauka, wayam ba ko sisi, yana da tabbacin akwai kudi a cikin Wallet dinnan, kudi ne ko da suka zarce dubu bakwai, abun da mamaki,gun Mairo ya nufa yace "Maryam, waya shigo min daki? Banga kudina ba" tace "ka dai duba, wa zai shigar maka daki? Duk muna nan" sharewa kawai yayi, don ya san kudin na cikin wallet, definitely daukan kudin akayi, to wa ya dauka? Share magaanar kawai yayi. AbdulMajid zaune kamar dan maraya, ba uhm ba uhm uhm, Abba ya dan rausayar da kai yace "Maryam,wai har yanzu Zaid na cikin dakin nan, ya ki fitowa?" baki ta ya6e tace "Yo ya fito? Tunda mu din ne bai san gani? Ga dai Abdul nan yanda kasan ni na mutu be da wani walwala saboda Zaid" Baba Abbs ya mike ya nufi k'ofar yana mita "Haan anyi yaro da taurin kan tsiya, ya fi awa hudu ciki fa, ni yunwan nan nake jiye mai kar ta mai lahani" cikin hali na ko in kula, Mairo tace "Yo ai Yunwa ba k'anwar uwa bace bare na uba, da yaji yunwa zai fito yaci Abinci". Alhaji Abba yace "bari dai inje in gani, ya shiga k'wank'wasa dakin, ji yayi kamar k'ofar bude take, yana turawa kuwa kofa ta bude, da sauri ya kutsa kai, ya na neman Zaid, shiru, haka ya lalube har toilet ba Zaid ba alamunshi, da sauri ya fito, yace " Mairo be ciki, wallahi baya nan" Dam gabanta ya fadi, to ina yaron nan zaije? Kar dai ya tafi tona mata asiri ne?" da sauri ta mik'e suka shiga nemanshi duk gidan ba shi ba alamunshi, hankalin Baba Abba ya tashi matuk'a, Mairo ma ta dan tsorata, Baba Abba ya fita k'ofar Gida yana tambayar masu Gadin gidaje ko sunga gilmawar Zaid, duk sukace ba su ganshi ba, Da sauri ya tari taxi yayi gidan Hajjo yana mai rok'on Allah ya sa yana chan.

Hajjo ta ji zance bambarak'wai, "Abba ba kai kace min yau zaka dauko su a Makaranta ba?name zaka zo kana tambaya na in Zaid yazo" Cikin rudewa yace "ba a ganshi bane, ba wanda ya san da fitar shi" zumbur ta mik'e tana tafa hannu gami da salati, tun daga nan suke ta baza neman Zaid, har police stations sunje sun bada report anma shiru.
**
A hankali ya bude idonshi ya sauke su a kan Agogon da ke mak'ale a bangon dakin Asibitin k'arfe 6:45am, tab wani irin bacci yayi haka? Ina ne nan? Daga hannu yayi yaji alamun drip, da sauri ya kalli hannun ya ga cannula, sai ya sa Kuka, Zaid ya ga tashin hankali, yayi kuka har ya gaji, sai wurin 7:50am nurse ta shigo, da Murmushi a fuskarta, tace "Good Morning" kai ya rausayar zuwa wani gefe, don kanshi na matuk'ar ciwo, nurse ta kara cewa "ya jikin naka? What do you want?" Zaid yace "I want my Mummy" nurse ta murmusa tace "kar ka damu zasu zo yanzu kaji?" Kuka Zaid ya fashe dashi, irin kuka mai hade da ihu, da sauri nurse ta fita ta kira Alhaji a waya, dama jiya da daddare ya bata mobile dinshi.
*
Bayan zuwan Mutumin ya zauna gaban Gadon yana mai kallon Zaid cike da shauk'i, ya gyara a Zaid zama yaci Abinci, sai bayan da ya gama cin Abinci suke kallon Junansu. Mutumin yayi murmushi yace "Ya Sunanka?" sai da ya maimata so biyu kafin Zaid yace "Zaid Sada Abu" da mamaki Mutumin ya kalleshi, yace "Sada Abu?" Zaid ya gyada kai, Mutumin ya tausaya ma Zaid, don ya san Labarin Sada Abu da Matarshi sun mutu a hatsarin Mota watanni biyu da suka wuce, irin be sanshi ba personally, amma Sada Abu mutum ne mai jamaa in kai baka sanshi ba, wani wanda ka sani ya sanshi, kuma dai labaran mutuwansu da ya dinga zaga k'afafan yada labarai, kama daga Jaridu, Mujallu d.s.

Mutumin yace "Sorry, Allah ya ji k'ansu" da sauri Zaid yace "Kasan Baba na?" Mutumin ya gyada kai yace "Mutumin kirki ne, mai kamala, Allah yayi har ya mutu bamu hadu ba". Zaid ya fara hawaye, Mutumin yace "kayi hakuri kaji? Kowa zai mutu" chan ya nisa yace "Ni zan koma Kaduna yanzu, zan bar note idan an sallameka a kai ka gun danginka" da sauri Zaid yace "Aa, ni ba zan koma gurinsu ba" da mamaki Mutumin yace "don me?" yace "Saboda su suka kashe min Baba da Maama, nima sunce zasu kasheni" Mutumin yace "Aa Zaidu, Babanka Accident sukayi, suka k'one suka mutu, ba wanda ya kashe su" ido tsaye yace "Wallahi maman majeed ce, ai ta gaya min, kuma ta gaya ma k'awarta zata kasheni" nan Zaid ya kwashe komai ya gaya ma Mutumin iya abunda ya sani, da Mamaki ya ke kallon Zaid yana raratabo zance, ya gasgata maganar shi, yayi amanna yaro kamar Zaid ba zai iya k'irk'iro zancen nan ba, Mutumin ya hadiye miyau yae "how old aee you?" Zaid yace "Eleven" "to Mallam Zaid ya zanyi da kai?" "ka tafi dani donAllah, zan bika" da mamaki Mutumin ya ke kallon Zaid, chan yace "No, you can come with me, ba zan iya tafiya dakai haka ba ba tare da sanin kowa ba, zai yi kama da na sace ka, hakuri zakayi ka koma Gida" ido k'ek'esha yace "Ba zan koma gidan ba, in tafiya zakayi ka tafi barni, nima inyi tafiyata" chan kuma ya fashe da kuka yace "ka taimaka min Baba, ni yaro ne" a hankali Mutumin nan ya fara hawaye, 'Baba' Zaid ke ce mai, abunda yafi mai dadi, anya zuwan Zaid gareshi ba dalili? Tabbas akwai dalili, kallo daya da ya ma Zaid yaron ya shiga ranshi, maybe Zaid was sent to him to be the son he never had, amma kar Selfish intrest dinshi ya sa shi cikin matsala, hakan zai yi affecting reputation da status dinshi, baya son abun yayi kama da ya ya sato Yaro, amma ya zaiyi da yaron nan? In ya barshi be son hannun wa zai fada ba, ya dade ya na tunani chan yace;
"Zaid, yanzu sauri nakeyi gobe Monday, ina da report din da zanyi a Abuja, a yau nake son zuwa Kaduna har in wuce Abuja, banda time a Kano, yanzu zan tafi da kai Kaduna, Bayan na gama aiki, Zuwa Friday zan dawo Kano, zanyi Bincike na, idan naga abun da ka fadamin k'arya ne, in ka sake ka yarda na kama da k'arya zaka ga abunda da zan maka, da kaina zan kaika gun Mairon ta kasheka, Ido tsaye Zaid yace "na yarda" Mutumin yace "shikenan, barin je in karbo takardan Sallama". Bayan Likita ya rubuta ma Zaid Magunguna, aka sallamesu, suka kamo hanyar Kaduna. Duk a tsorace Alhajin yake.
*
Bacewar Zaid ya zaga ko ina a cikin unguwarsu, ba ma kowa ya sanshi, ba inda ba a je nemanshi ba, AbdulMajid yayi kuka kamar ranshi zai fita, Daren Jiya sam Hajjo da Abba ba su runtsa ba, Mairo ko da yamma ta faki idanuwa ta fita gun Mallam danliti na Marmara don ya mata aiki, "kar Zaid ya sake dawowa,ko a batar dashi, kai ya ma tura Aljannu su kashe shi,don in ya dawo akwai Matsala" Mallam dan liti yayi daria yace "kar ki damu, gwara a kashe shi a huta, zama ki fi kwanciyar hankali" nan take ta amince, haka ta cika dhi da kudi ta koma Gida, harda ita aka bazama neman Zaid.
Ikon Allah ya hana Mallam dan liti ganin komai game da Zaid,ko menene ke hanashi ganin Zaid ba karamin garkuwa bane, to yanzu in yace da Mairo akwai matsala, zata ga gazawarshi, shi ko be so ya samu matsala da aikinshi, abun Mamaki wai Mallam da Addua Allah kar ya sa a ga Zaid, ko an ganshi to sai dai gawanshi. Hmm Muje dai zuwa...
聽 聽 聽 聽 聽 聽 聽 聽聽 KADUNA
聽 聽
Gida ne Unguwa guda a Mando Kaduna hanyar Airport, da wuya kaga Wakeken Gida mai Girman Gidan, Zaid be tashi cikin talauci ba, amma bai taba ganin Babban Gida kamar wannan ba, gabanshi ya fadi, ya fara nadamar biyo mutumin, kar dai ace dan yankar kai ne, Mutumin ya lura dashi, murmushi yayi yace "Gida na ne, kuma nikadai ke zaune a ciki sai masu aikina" Zaid dai kasa magana yayi.
Horn yayi da gudu maigadi yazo ya bude gate "Sannu da zuwa Oga" cewar Maigadi, Mutumin ya daga hannu Sama ya murmusa yace "Thank you Samuel". Ya kalli Zaid da yake a tsorace yace " Mu shiga ciki ko?" Zaid ya bi bayanshi, sai da suka yi dan tafiya kafin suka shigo main gidan, sannu da zuwa ake ta shigowa ana mishi,duk uniform ke sanye jikinsu, kuma abun mamaki duk Maza ne. Mutumin yace "Zaid, muje in nuna maka dakinka" ba tare da yace komai ba ya bi bayanshi, hawa sama sukayi kafin suka zo gaban wani daki,Alhajin ya sa hannu ya bude dakin, bakin Zaid ya fadi k'asa, ido kuri ya ke kallon dakin da akace nashi ne,ko Girman dakin zai kai girman dakin Mamanshi a kano, dakine wanda akayi adon kwalliyan da blue color a hankali ya shiga yana bin dakin da kallo.
Chapter 14 · 0% Book details