← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 128

Sashe 104

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana cikin tashin hankali amma Kukan da Yaranta keyi ya na kara tada mata hankali, bata so ta bude ido taga ba mafarki takeyi ba,聽 bata so ta tashi daga mafarkin da take,聽 ta zata ta yarda kwallon Mangoro ta huta da k'uda,聽 in dawowan zasuyi Meyasa ba su dawo tuntuni ba sai yanzu da ta manta da shafinsu,聽 meke faruwane? Kukan da su Zaineema da Zinatu keyi na kara sata cikin damuwa,聽 so take ta bude ido ta lallashesu,聽 amma in ta bude ido hakan na nufin ta farka daga baccin da take.聽 Ruwa Ziyada ta yayyafa mata,聽 amma ko motsi batayi ba,聽 kukansu ya tsananta "Mummy please ki tashi" Daddy "please kace mata ta tashi" Daddy ya fincike hannunshi daga gun Ziyada,聽 nan hankalin yan India yayi kansu, Murmushi yayi ya matsa daf da ita,聽 don yaga idonta na motsi,聽 tsugunna wa yayi yace "Maman Yarona(kamar yanda ya kan ce mata a da=Abdulmajeed聽 yake nufi ) , na san kina jina,聽 ki tashi, kin tada hankalin yaranki" ba kunya ba tsoron Allah ta bude ido a hankali ta saukesu fes kan Sada.

Bakin Miyau ta hadiya,聽 idonta ya ciko,聽 cikinta ya duri ruwa kamar zata fara gudawa,聽 a haka ta tashi tsaye tana raba ido,聽 Mijinta take kallo, Daddy ko kallon gefenta beyi ba, ta kasa kai dubanta gurin Yesmeen,聽 ta san ta cuci Bayin Allahn nan,聽 ta san ta ha'incesu,聽 ta san ta shiga tsakaninsu, Maama daga baya tana kallon Mummy cikin ido,聽 duk wasu abubuwan da suka faru suka soma kwaranyo mata,聽 kuka take sosai, da sauri Mummy ta sadda kanta kasa,聽 itama hawaye take,聽聽 tana me kunya hada idanuwa dasu, bata taba jin Nadama ya shigo mata lokaci guda聽 ba irin na yau,聽 da na sani k'eya ce,聽 amma tayi dana sanin duk wasu abubuwa da tayi,聽 kar su rabata da 'yayanta,聽 a hankali ta kai dubansu gunsu,聽 da gan kan Majeed... Zaineema.. Ziyada.. Zinatu da autanta Muhsin,聽 cirko cirko sukayi suna son jin bayanin Meke Faruwa, Hannu ta sa a fuska ta fashe da wani irin kukan Nadama, duk wani numfashi da take ja,聽 da da nasani take janshi,聽聽 a hankali suka yo kanta su duka a tare,聽 da baya da baya take ja,聽 suna binta,聽 tana baya,聽 suna binta har saida ta ci karo da bangon Kitchen, Abdulmajeed ya karasa gunta zai rungumeta, ya bata comfort,聽 ya gwada mata "koma me tayi,聽 suna tare da ita, dakatar dashi tayi da hannunta, girgiza mai kai tayi tare da zubewa a k'asa, kukan da yake ta kokarin boyewa ya fashe da, baki na rawa yace "Mummy.." sauran Yaran suka taya shi suna nufar inda Uwar take.

A kan guiwowinta ta sauka,聽 duk yanda taso magana ta kasa,聽 sai taji harshenta ya mata nauyi, ba abinda take iya yi sai kuka,聽 nadama fal ranta,聽 Abdulmajeed ya firgita da yanayin da ya ganta,聽 takowa yayi kusa da ita ya sauka kan guiwowinshi,聽 bakinta yayi nauyi bata iya komai sai kuka da girgiza kai, ganin abunda ke faruwa yasa聽 Zaineema matsowa kusa dashi itama ta kai guiwowinta kasa,聽 Ziyada ma hakan tayi,聽 Zinatu da Muhsin ma sukayi hakan, duk abunda sukeyi kan idon Paapa da Maama, Abdulmajeed ya fara magana聽 yace "Mummynmu akwai taurin rai,聽 ba abu kadan ke daga mata聽 hankali ba, ba komai ke sata kuka ba, ba komai ke sata shiga yanayi ba,聽聽 bansan me ta muku ba,聽 bansan meke tsakaninku ba,聽 amma ina so ku sani,聽 tun da nake da ita, i've never seen her like this,聽 ban taba ganinta haka ba,聽 ban taba ganin regrets kwance a kan fuskarta ba, bansan me ta muku ba,聽 amma ina da tabbacin cewa聽 tayi nadama,聽 a kan fuskarta na karanta da tana da yanda zatayi,聽 da ta koma lokacin baya ta gyara kuskurenta,聽 donAllah, don Girmansa, kuyi hakuri,聽 ku yafe mata".

Paapa da zuciyarshi ta gama karaya ya juya ya kalli Yesmin da kukan ta ya tsananta,聽 ta san bond din da ke tsakani Da da Uwa, ta san cewa聽 Mairo ce聽 sanadiar duk wani bakincikinta,聽 ta san cewa Mairo ta mata farraku da danta, bata tunanin zata iya mance abunda Mairo ta mata, a zatonta zata ji tsanar Mairo da duk wani abunda ya danganceta, a zatonta zata cuzguna ma Mairo da mafiyin abin da ta musu,聽 amma ga mamakinta,聽 sai taji sosai聽 zuciyarta ta karye, sosai taji tausayin Mairo da Yayanta.
A hankali ta gyada ma Paapa kai,聽 a hankali ya matso kusa dasu, ya na kallonta ya maida dubansu ga Yaran,聽 Murmushi ya sakar masu wanda ko ba a ce ba ma sun gane danuwan Daddy ne wanda sukayi tsananin kama, Abdulmajeed聽 ya kala yace "Ku shiga Ciki" kallonshi cikin Ido Abdul keyi yana tuna inda ya sanshi,聽 Murmushi Papa ya sake,聽 yace "trust me,聽 everything is going to be fine" da sauri Majeed ya tashi ya mikar dasu duka, ya hada su gabaki daya ya turasu cikin Daki, Papa ya kalli Najwa,聽 kallonta kawai yayi tasan abunda yake nufi,聽 takowa tayi ta shiga Dakin itama,聽 ko baa gaya mata ba,聽 tasan cewa "Mummy ce sanadiyar komai" hankalin su duk tashe,聽 a yanda suke jugumjugum,聽 irin suna zaman jiran likita yazo ya sanar musu da cewa anyi Tiyata lafia patient bata mutu ba,聽 ba me cema kowa kala,聽 kowa da sakesaken da yake a zuciyarshi.聽

Tausayinsu Majeed yaji shiyasa Papa ya tura su daki,聽 ba zai so Yara suji laifukan Mahaifiyarsu ba, ko wace uwa ana So Yaranta suyi Alfahari da ita a duk inda suke,聽 suyi koyi da ita , duk da dai uwa uwace ko da uwar banza ce,聽 wani irin Alfahari zasuyi da ita? Baya so su samu聽 confusion din Uwa da Yaranta, duk da suna da dalilan musu ramuwar gayya, amma these are his nieces and nephews, suna da Jinin Yayanshi a jikinshi, yana sonsu fiye da zato,聽 so don su ba zai bari Mahaifiyarsu ta聽 wulakantu a kam idonsu ba.
Maida idonshi yayi kan Hajia Mairo,聽a takaice yace "Kinsan kin Cuce mu?" ba bata lokaci ta daga kai da sauri alamun eh, "kin san kin Zalunce mu? Ni,聽 Yaya,聽 Umma,聽 Yesmeen?" sabon kuka ta saka ta na daga kai tace "na sani,聽 na sani wallahi,聽zai zama Rainin Wayau in nace ku yafe min, dukkan ku nan na Zalunceku,聽 na Hainceku,聽 na cutar da ku,聽 gabaki dayanku nan, na chancanci duk wani hukuncin da zakuyi min,聽 amma duk da banda idon kallonku,聽 banda bakin da zan muku magana nace DonAllah ku yafe min, bansan ta yanda zan gyara laifina amma wallahi na bari,聽 dama chan hassada ne da bakinciki,聽 amma ku yafe min".

Sosai ya tausaya mata don shi dama zuciyarshi kamar ta mata yake,聽 abu kadan yake karya聽 mai zuciya, jiki ba kwari, yace"Hakkin kowa ne ya yafe miki ko kar ya yafe miki, Ni dai na yafe miki,聽 sai kije ki rokesu gafara, Ubangiji Allah ya gafarta mana,聽 kije kiyi ta Istighfari" kamar ta yi me don murna,聽 ta rarrafa a kasa ta riko kafaffun Yesmin,聽da sauri ta janye kafarta, ba ta tunanin zata iya jure聽 maganganun da Mairo zata mata, tasan rokonta yafiya Mairo zatayi,聽 kuma har ga Allah har yanzu tana jin haushinta, Zata yafe mata,聽 zata barta taji da nadamanta,聽 zata barta da kunyar da zai cigaba da addabarta har karshen rayuwarsu,聽 kuma tasan abunda tayi zai cigaba da damunta in har dai tana da Conscience (hankali ko tunani) "Yesmin,聽 nasan na miki laifuka,聽 na san kin san ban taba sonki ba,聽 nasan kin san abubuwan da nake miki,聽 ba don ni ba Yesmin, ki yafe min,聽 don martaban Manzon Allah SAW" Maama ta runtse ido tace "Na yafe miki Mairo" Godia ta shiga yi mata, kamar dazun da rarrafe ta koma gun Hajjo tace "Umma donAllah ki yafe min,聽 na rabaki da Yayanki,聽 na zalunceki,聽 Wallahi duk abunda Abba ya miki na halin ko in kula duk nice,聽na chanchanci duk wani hukunci,聽 amma na zabi na roke affuwarku,聽 na chanchanci komai amma na zabi na tona ma kaina asiri,聽 ki yafe min donAllah" Hajjo ta share hawayenta,聽 ta durkusa ta dago Mairo tace "Ya wuce,聽 na yafe miki, Allah ya yafe mana" godia ta shiga zuba mata tana mata adduoin karin kwana.

A hankali ta juya ta kallo Mijinta, a sannu take takawa tana isa gareshi, hannu ya daga mata yace "Maryam,聽 kar ki sake ki matso kusa dani,聽 kar ki sake,聽 wallahi zan 6alla ki" chak ta tsaya ta na cizgar kuka,聽 Sada ya matso kusa da Yayanshi yace "Yaya..." "dakata Sada,聽 kar ku yarda da kalaman Yaudaran Matarnan,聽 kar ku yarda da hawayen munafurcinta,聽 ta amsa laifinta ne kawai don taga karyarta ta kare,聽 bata da wani mafita,聽 shiyasa ta saduda,聽 bakusan Maryam ba,聽 bata da mu da komai ba sai kanta,聽 shes too selfish, wallahi ko ganinta bansan yi "Maryam kije na sakeki" da sauri ta zube k'asa,聽 a sannu takejin komai na wargaje mata,聽 duniyarta na rugujewa,聽 Sada ya dafe Yayanshi,聽 yace "Yaja hannun yayanshi yayi parlo dashi,聽 ya zaunar,聽 ruwa ya gani kan carpet ya dauka ya bashi,聽 ba musu Abba ya karba yasha,聽 "Yaya Inallilahi wa ina ilaihir rajiun" a hankali Abba ya fara maimaitawa, ya fita ya basshi zaune, Mairo na nan inda ya barta,聽 ya matsa daf da ita,聽 yace "Ki tashi kije,聽 zan lallashe shi,聽 yanzu yayi fushi sosai, bayan kwana biyu nasan zai sauko,聽 ki shiga ki kwantar ma Yaranki da hankali,聽 ba sai kin sanar da su komai ba,聽 kinsan yara da rik'o" tashi tayi ta share hawayenta,聽 ta nufa inda Yaran suke, tana shiga duk suka yi kanta,聽 k'okarin Murmushi take musu,聽 ta kalli Najwa,聽 tace "Ke Diyar Sada ce da Yesmin?" Kuka takeyi tana gyada kai,聽 Allahu Akbar cewar Mummy,聽 ta kalli Abdulmajeed tace "Kaga yanda Allah ke abunshi ko?聽 Ba tare da saninka ba,聽 ka kawo 'yaruwarka Gida, Shes your cousin" ba wannan yake son ji ba,聽 murya a taushashe yace "Mummy.." Mummy ta murmusa cike da karfin hali ta kalli Najwa tace "Zan iya magana dasu?" da sauri Najwa ta gyada kai ta mike ta fita tare da kullo musu dakin.
Chapter 104 · 0% Book details