← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 128

Sashe 21

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar ba zaiyi magana ba yace "Uncle,first of all ba Companyn Sadam Audu da zaa Saida, Joint Companies dinshi kuma a raba, theres no close down of the Orphanage house,idan an kulle ina zasuje? Idan an kulle ribar me akaci? Ba zai bari handwork din Baba ya tafi a banzaba, yayi imani Baba ba zai ji dadi ba idan aka kulle gidan Marayun nan, Baba ya sha gaya mai cewa yana son Marayun nan,ko da zai tashi baida ko sisi ba zai wofintar da su ba, to shi don me zai sa ya watsar da lamarin su? Shima ai marayan ne, in ya koresu ina zasu?.
"I will continue where Babana stopped, zamu cigaba daga inda ya tsaya, GM's da Maaikatan ko wani Company su cigaba daga inda suka tsaya, zaa cigana da Gina Masallatai, zaa inganta Mak'abartu, zaa cigaba da aurar da Marayu, zaa cigaba da kula dasu, ba abunda zai tsaya, zaa dasa daga inda ya tsaya,nothing is going to change, komai na Alheri ya isa gareshi, duk ayyukan Alherin da zaayi akan abunda ya fara, Allah ya kaimai ladar ya sa silar shiganshi Aljanna kenan, hanyar da zan nuna mishi nawa kaunar kenan.

Hawaye ya gangaro fuskar Alhaji Dauda, Zaid yayi tunani, Zaid yayi wayau, nan ya sa mai Albarka, suka rok'a ma Baban Zaid gafarar Allah. Zaid yace da Alhaji Dauda zai danyi tafiya ya dan huta, Alhaji Dauda yace "Bakomai, amma ya bar tafian sai bayan anyi General Meeting da ko wani Member of Sadam Audu's Worker.

聽 聽 聽 聽 3 M O N T H S L A T E R

聽聽 Gidajen talabijin, Gidajen Radio, Social networks, Magazines, Jaridu, ko ina Maganan Young Billionaire akeyi wato Z Sadam Audu,sunanshi ya zagaye Globe, Girma ya kamashi, yana aikin shi ba tare da wata damuwa ba physically but mentally, Rasuwar Baba tayi breaking dinshi, ba Faraa ko kadan.
Har gida katsina Zaid ya kai Iyah gun yaranta da jikoki,a cewarahi ta tsufa, gwara tayi retire hakan nan, ya shaida mata zai dinga zuwa gaidata don yana sonta sosai yayi Sallama da katsina bayan ya mata wani kyauta ta ban mamaki har da biya mata Makka,kafin duk ya dauke yaranta da jikokinta Aiki a Companies dinshi dabandaban, dama da yawa cikinsu sun kammala degree dinsu, aikin ne dai babu. Maakaitan Gidanshi na Kaduna, kuma ya maidasu Company maigadi kadai ya bari da mai shara.

Allah yayi ma Zaid kwarjini, Mata sun mai Chaaa, ba sa gabanshi ko kadan,kudi Zaid ya sake Sosai akayi Masallatai da Islamiyu da Asibitoci da Rijiyoyi a kauyuka daban daban da sunan Sadam Audu, duk inda ake neman taimako a Asibiti na tallafi, da yawa cikin mates dinshi ya sama musu Aiki based on their fields, matasan da yayi employing a Maaikatanshi da yawa suke, da magana tazo gun Zaid zaa magance ma ita,har aka ma Zaid lak'abi da 'Dan Baba mai raba Alheri'. Bayan komai yayi daidai ne ya bar k'asar ya tafi France.
*
*
聽聽 For Good 7 Months Zaid na France, in ka ganshi bazakace Yaron nan wani billionaire ne, just like his Baba, he's living a simple life ba wata k'arya ba wani showoff, to yaron da ya gaji azziki ba wanda yayi ma Azziki haye ba.
聽聽 Yayi shirin komawa Naija, yayi shirin kula da Companies dinshi, yayi shirin komawa daukar fansa, yayi shirin cimma burinshi no matter what, wadannan abubuwa biyu su kadai ne burinshi, baida wani buri da ya wuce ganin tabewar Abba Abu, da kuma Cigaba a Companies dinshi.
*
Ko kadan besan Zaman Kaduna, a inda yafi wayau yake son cigabawa da rayuwanshi a Nigeria, PH, Idi ya dauko shi a Airport, Gidanshi ya saukeshi, rayuwa da Baba ya dinga mai yawo a kai, baya bukkatan masu Aiki, rayuwanshi yake sonyi shi kadai a cikin Gidannan da ke da tarin tarihi, dominshi Baba ya siya gidan nan,dominshi Baba ya dawo PH da zama duk irin yanda Musulmai ke gudun zama a garin,dominshi Baba ya jure komai, me zaiyi ma ya saka ma Baba? Tsakanin shi da Baba sai Addua. Mata kuma na ta kawo mai hari, akwai wacce alamuranta suka fi dore mai Kai, Nadiya,a France suka hadu, Nadiya yar Abuja ce, Babanta dan kwangila ne, yarinya ce 'yar shekara 20, amma son da take mai yasa ta dawo PH da zama don sabida shi, don ta dinga ganinshi kullum, duk da bata gabanshi amma bata zuciya ba, sai ta mallakeshi duk daren dadewa.

聽 聽 Karfinshi da hanyoyinshi ya sa yake da full Information din gidan Abba Abu, komai a tafin hannunshi yake na wanda suke hulda dasu, maaikata gareshi a ko ina wanda suke kawo mai wani moves din kowa,it appears Mutumin da Zaineema ke Aure a Kaduna shine GM din wani Company a Zaria, Babanshi kuwa Abokin Baba ne, yana sane da Kwangilar da Gwamnati ke ba AbdulMajid na Tituna da Ginene, kasacewar shi yana da degree Architecture da Msc a Quantity Survey,yana sane da Nana Nakowa na mutuwar sanshi har ana so a hadasu Aure,聽 yana sane da Ziyada ta gama Secondary School ta fara karatu a Baze University inda take karantar International Relation,yana sane da dan Gidan Senator Ali Aminu na Sonta, yana sane da Irin Manyan Matan da Mairo take hulda dasu, itama bata yarda ba itama matar wani ne a Nigeria, yana sane da kowanne Moves din da suke, ko ina bin diddiginsu yake, hankali kwance ya fara gudanar da daukar Fansarshi ta hanyoyinshi. Wannan Kenan..

聽 聽聽 C I G A B A N聽聽 L A B A R I N

锟�

锟�

锟�

锟�

Hello lovers, finally zamu dawo main labari, it wasnt easy to crack my brain for the tuna baya, how was the tuna baya? Sha, this is is the begining of an end.
Vote, Comment, Recommend.

#1love
#ADAY
#bibiliciousfreakingfans
#anatare
#nagode聽

Biebee Isa
[12:04, 25/09/2017] 鈥�+234 803 414 9368鈥�: 锟斤拷A DADE ANA YI....sai gaskia锟斤拷

NA

BIEBEE ISA

庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Bibilicious freaking Fans? How you doing? kwanakin baya, a wani page nace Abdulmajeed na karantar Medicine a Oxford University, sai kuma na dawo nace yana da degree a Architecture and Msc a Quantity Survey, so Afwan, mu dauki Architecture din, zaifi hawa da labarin. Nagode.

Pg1鈨�3鈨�

I N D I A

Najwa taje Nigerian Embassy, inda aka mata interview, Wani k'arfin guiwa takeji yana zuwa mata, ba ta damu da zuwa k'asar da bata ta6a zuwa ba, bata damu da karatun ta da zata datse ba, ba ta damu da komai ba, burinta kawai taje Nigeria, burinta ta tsaida hawayen Mahaifiyarta, bayan sun dau lokaci suna tattaunawa da Vijhay bhaiya, ta tashi ta wuce gidansu Kaveri don yau yawo takeji, Kaveri na kwance ta shiga, bayan ta gaida Maa din Kaveri ta shige cikin dakinta, duka ta dada mata a baya, da sauri kaveri ta tashi ta daure fuska, "Najwa Sada Abu whats this for?" Najwa ta juya idanuwanta tace "Get up, we are going out" "jahaan ham karane ja rahe hain(Ina zamuje ne)?" Najwa ta murmusa tace "agar yah pichhalee baar jab main ek yaatra par jaana hai main ise aap ke saath rahana chaahata hoon (If this the last time i hang out in India, i want it to be with you) Kaveri da damuwa tace "is tarah baat karana band karo, tum vaapas ho jaega, mujhe pata hai (Ki daina magana haka, zaki dawo, na sani)" ta karashe hawaye na fita idanunta, itama Najwa na hawayen ta rungume Kawarta tace "tumhaaree yaad aaegee Kaveri (I'll miss you Kaveri) Kaveri tace "mujhe bhee tumhaaree bahut yaad aaegee (Nima zanyi kewarki Sosai)".
Kaveri ta mik'e ta taje kanta, ta dan sa lipgloss, sai da sukayi hotuna kafin suka bar gidan.

锟�

A B U J A聽 N I G E R I A

"Dad, inaso ka bashi 20 million saboda robbing dinshi da akayi, they lost alot, ina so ka tallafa musu" Dad din Nana ya murmusa yace "is that all?" Nana ta turo baki kamar yar shekara 8 tace "sai kayi maganan Aurenmu" Dad yace "Shikenan, Gobe sai ayi Processing Kudin sai a kai musu Gidan ko Baby? Da murna tace "Thanks Dad" da gudu ta fada dakinta tana tsalle tsalle.

Tunawa tayi da abunda wannan ya gaya mata tayi, shiru tayi tana tunanin meyasa zai tamaketa? Meyasa zai bata shawara? Kafa kafada tayi a ranta tace "indai hakan zai sani auren AbdulMajid to banda matsala, ba Syrup ba ko Giyace sai na sha" daidai tafiansu Mansion din Abba Abu, ta kur6e kwalba biyu ta syrup, ta fito tana layi, Bayan Mota ta shiga inda Mamarta take zaune da Baban, Driver ya ja su sai Maitama District.
*
Jiki na rawa Hajia Mairo ta tarbesu, ba kasafai Hajia Sayluba Nakowa ke zuwa gidansu ba, yau gashi kuwa harda Nakowan da kanshi ga kuma Nana, ina zaa saka dasu take tayi, ta zauna suka kwashi gaisuwa, ta mike tace "bari ta sanar da Alhaji Abba zuwansu" chan sai gashi sun dawo tare da shi da Yaran Gidan Baki daya, aka gaigaisa, tuni Nana ta matso kusa da Majeed kamar ta shige jikinsa, yana jin tana warin Maganin tari, Dad da Mom din Nana su ka musu Jajen abunda ya faru na Kidnapping Zeenatu, da kuma Robbing din Majeed. Sannan Dad yace da Alhaji Abba ga gudummuwarshi na Naira Miliyan 20 duk da abun da suka rasa ya wuce Miliyan 20, Daddy yace "Haba Alhaji Nakowa, wannan kudi sunyi yawa" Alhaji Nakowa yace "Haba Alhaji Abba, ka bar fadin haka, kaine fa? Zan iya maka fiye da hakan" karaf Hajia Mairo tace "mungode Allah saka da Alheri Allah ya bar zumucni" Hajia Sayluba ta amsa da "Amin". AbdulMajid ma yayi Godia, duk sukayi Godia.
Chapter 21 · 0% Book details