← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 128

Sashe 91

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yatsina fuska yayi yana ajiye cokalin shi cikin abincin da yake ci hadi da dafe kanshi dake wani irin sarawa kaman zai bude gida biyu yana kiran Allah. Hakan ya dawo da hankalin Maama dake danna wayarta tana kokarin kiran Najwa kanshi. Da sauri ta mike tana kama hannunshi da fadin "Subhanallah, lafiya?"
Hannunta Paapa ya rike dam yana jin bazai iya bude bakinshi ya fada mata abinda yake ji ba, bama zai iya magana ba a yanayin da yake jin kanshi. Gabaki daya yanda yake riko Maama yana dafe kanshi da dayan hannunshi ya rikita mata lissafi.
Bude bakinta tayi da nufin tai mishi magana taji kanta yai wata irin dokawa kaman an kwada mata karfe, ba shiri ta sake dumtse hannun mijinta dake cikin nata tana durkushewa kasa hadi da fadin "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un" wani duhu-duhu take ganin yana lullube mata idanuwanta data runtse gam tana salati da neman taimakon Allah jin yanda kanta ke sarawa.
A hankali duhun dake cikin idanuwanta da kanta take jin yana budewa da duk numfashin da take shak'a. Kamun wasu images da bata fahimta su fara mata yawo cikin kanta. Daki ne take gani da kujeru a cikin shi da labulaye ruwan kasa masu haske.

Kamun ta ga mutane guda biyu a tsaye suna hira, tana jin sautin maganarsu da dariyar da suke sai dai fuskokin su take son gani da dukkan zuciyarta, kaman sun san me take so suka juyo. Wata irin dokawa zuciyar ta tayi har cikin kunnenta. "Ammi..." Maama ta fada tana kara dumtse hannun Paapa cikin nata.
Saboda yanda kanta yake ci gaba da bugawa. A mafarki, a ido biyu, a cikin maye, zata gane dakin da tai kuruciya a cikin shi. Yola ne, asalinta, tushenta, garin iyayenta da kakaninta. Yar Yola ce ita, bude idanuwanta tayi tana jan wani irin numfashi kaman wadda tasha gudu, kamun a hankali komai ya soma dawo mata.
Da duk wani abu da zata tuna, da yanda ciwon da kanta yake yi yake sauka, har lokacin hannunta na cikin na Paapa da babu abinda yake gani sai Zaid da AbdulMajeed dan gun Yayanshi lokacin yarintar su. Sai dan uwanshi, dan uwanshi da yake kauna da dukkan zuciyar shi.
Kano yake gani da yanayin komai na rayuwar su na dawo mishi kaman film aka kunna. Kamun yaga fuskar Mairo, yaga fuskar da a yanzun yake da yakinin har mutuwarshi ta riske shi bazai taba mantawa da ita ba.

Musamman kalamanta da suka zauna a kirjinshi da zafi kaman garwashi, kanshi ya saki da dayan hannunshi yana dafe kirjin shi dake kuna.
*"Ina so ka dauki matarka, da wasu 'yan kudi, ku bar k'asarnan, kuyi nesa da k'asar nan, kar ku sake waiwayen Nigeria, duk inda ka san muna iya haduwa ko ba dade ko ba jima kar kaje gun, wurare kamar Makka da Madina, Ina so ku manta da Mahaifarka, ku tashi ku tafi yanzu"* Kalamun Mairo ke dawo mishi kamar a lokacin take mishi,
Ware idanuwanshi yayi akan Maama, da ta sauke nata idanuwan cikin nashi cike taf da hawayen da suke gab da zubowa, na Paapa cike suke da yanayin da bazai misaltu ba, kamun ya mike tsaye daga kan kujerar da yake yana dago da Maama. Goshin shi ya hada da nata "Na tuna...na tuna komai..." yake fadi mata muryarshi na rawa.

Kai Maama take daga mishi hawayenta na zuba. "Me mukai mata? Me yasa zatai mana haka?" Saida Paapa ya hadiye wani abu daya tsaya mishi a wuya kamun yaja numfashi da fadin "Bansan dalilinta ba. Bansan me yasa ba, in akwai abinda nasani shine kowacce kaddara na faruwa da dalili..."
Hannuwa tasa ta tallabi fuskarshi cikin tata, babu abinda take so, babu abinda take muradi da duk wani abu da ta mallaka daya wuce taji kafafuwanta kan kasarta, ta sauke idanuwanta kan yan uwanta, kan yayanta, ta shaki iskar data banbanta da duniyar nan da Mairo tai musu sanadin shiga.
"Let's go home" ta ce wasu sabbin hawayen masu dumi na zubo mata. Sumbatar goshinta Paapa yayi yana jin yanayin da bazai misaltu ba. "We are going Home. Komai yazo karshe Yesmeenah " In hankali da nutsuwar shi sunyi dubu gida suke kira mishi.a
Kama hannunta yayi suka shiga ciki dan su fara shirye-shiryen daya kamata, kamun ai musu visa ne aiki, sun san zai dauki lokaci amma abu daya suka sani, Zasu Gida.
Tana shiga daki ta zaro wayarta Paapa yace"Wa zaki kira?" "Najwa.." ta amsa shi tana dialing number din Najwa hadi da kara wayar a Kunne.

#1love
#ADAY
#bibiliciousfreakingfans
#anatare
#nagode

Biebee Isa
馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱

NA

Wattpad:@biebeeisa

Pg3鈨�6鈨�

Pappa yace "Aa Yesmeenah,聽 duba kiga lokaci,聽 yanzu 10pm daidai da kusan karfe 3am dinsu,聽 duk inda Najwa take tayi bacci, kuma聽 gaggawa na me? Mun warke daga duk abinda aka mana,聽 kuma zamu Gida, ki bari da safe sai ayi Waya ko?" Maama tace "Wallahi Papi baka ji dadin da nakeji bane,聽 kawai doki ne ya sa ni mantawa" Paapa ta murmusa yace "muje mu kwanta,聽 abincin ma na san ba iya ci zanyi ba" tayi dariya tace "baccin ma ba iyawa zakayi ba,聽 kawai mu zauna mu jira garin Allah a waye" dariya yayi,聽 yace "gobe InshaAllah za mu fara processing Visa" tace "Allah shi kaimu" ya dan kalleta kafin ya mik'e yace "Zama be ganmu ba, muje mu nuna ma Allah jin dadinmu ta hanyar gode mai,聽 muje muyi nafila" tashi tayi ta bi bayanshi suka shiga daki don nuna Godiar su ga baiwa da jin k'ai din da ya musu.

Suna yin Sallahr Asuba ta zaro wayarta zata kira聽 Najwa,聽 Paapa yace "Yesmeeenah.. Wai saurin me kikeyi?" ta cigaba da latsa waya tace "gwara ta san mun tuna komai,聽 kuma tana da uncle a Kano,聽 ta nemeshi" Pappa ya karbi wayan yace "Kul, kar ki sake, me kike so tayi?聽 Taje ta nemo Abba,聽 ta koma gunshi da zama Mairo ta san cewa diyar mu ce ta salwantar da ita?聽 Kinsan me tama Zaid?聽 Kinsan ko ta Salwantar da Zaid kamar yanda ta mana?聽 Kinsan ko yana raye ko yana mace? Ba mu san me ta mishi ba,聽 ba musan me zata mata ba in ta ganota, tunda dama ba kaunar mu take ba" Maama tayi shiru kafin ta jinjina kai,聽 tabbas hakane,聽 yanzu in Mairo ta gano Najwa,聽 Allah kadai ya san abunda zatayi聽 mata tunda ba imani ne da ita ba, Pappa yace "Zamu gaya ma Najwa, mun tuna komai,聽 zamu gaya mata zamu zo Gida, thats all,聽 koma meke nan,聽 in mun isa sai mugani".

K A N O
NIGERIA 8am

Tun lokacin da ta tashi ko breakfast ba tayi ba ta dauki kudi ta fita,聽 yau ta sha alwashin zata fare neman Yayanta,聽 Cyber Cafe ta shiga,聽 inda tace musu zatayi amfani da system,聽 ta siya Time ta zauna ta fara searching Zaid Sada Abu,聽 clicking taga sunaye da yawa sukayi appearing,聽 mafi yawanci sunayen Larabawa ne, daga k'asa ta ga ansa Search for Zaid Sadam Audu The Youngest Multi Billionaire in Africa(bincika Zaid Sadam Audu, Matashin maltibilonaire na Afrika) ta shiga nan din duk da tasan ba shi din bane. Tamfatsesen hoton Zaid ya kusa mamaye screen din computer
A ranta tace "Mijin Ziyada ne, ta ji labarin Yana da kudi sosai,聽 amma bata san shine multi bilionaire a Africa ba,聽 no wonder yake musu Mugunta ba tare da an dauka Mataki ba,聽 kallon hoton takeyi,聽 ta shagala da kallon idanuwanshi da yanayin聽 hancinshi da yanayin bakinshi, tabbas ta san fuskar nan,聽 akwai inda ta san fuskar nan,聽 a ina? Zuciyarta ta tambayeta,聽 wata sassan Zuciyarta tace "NURA KURMA" zumbur ta gyara zama ta shiga dunian tunani, nan take ta dinga hasasso dalilanta na tunanin Nura Kurma ne, amma anya kuwa? Nura Baki ne,聽 wannan kuma fari ne, ganin hujjojinta na amincewa da shine sun fi karfi,聽 da sauri tace "Yes,聽Shine,聽 ai ko shi Nura Kurman is fake,聽 karya yakeyi,聽 shi ba abunda yace shine ba,聽 ba kurma bane,聽 wani abu yake so tare da su Mummy,聽 kila ya ga bayyamsu don ta tuna mugayen Ayukkan da yake ta aikata tuna karawansu,聽 sanda take wargaza mai duk wani shirin da yayi,聽 tun daga cocaine,聽 da wannan聽 abunda zai yi sanadiyar karewan Mairo,聽 da maganunshi na cewa ta fira daga harkarshi,聽 dalilinta ya bar gidan,聽 saboda ta gane cewa ba kurma bane, shiyasa ya bullo ta Auren聽 Ziyada聽 don ya k'untata musu, ina ga shine dalilin da ya sa ya yi musu basaja,聽 don ya matso kusa da su,聽 don ya samu wasu informations kansu, akwai wani babban abu tsakaninshi da su Mummy, kila akwai wani abu da suka taba mishi ko family dinshi,聽 in ba haka ba,聽 don me zai bata lokacinshi da matsayinshi kan su da ko kafar Azzikinshi ba suyi ba?聽 Akwai boyayyen Alamarin da ke tsakaninsu wanda ya sa yake daukan Fansa ta hanyoyinshi,聽 to ya akayi ba wanda ya ganeshi?" da sauri ta ba kanta amsa,聽 Multi Bilionaire聽 ne,聽 zai iya yin komai, komai zai iya yiwuwa a gunsa,聽 yanzu haka makeup ne.聽 Duk da zarginsa takeyi bata tabbatar ba,聽 amma Zuciyarta da duk wasu sassa na jikinta sun amince da hakan ne.聽
Chapter 91 · 0% Book details