← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 128

Sashe 55

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

a k'asa, wata bak'ar Mota k'irar 508 ta tsaya daidai gabanta, haka kurum taji gabanta ya fadi, shiyasa take son Ya Maji ya dinga zuwa daukota, ita bata son Samarin nan marasa kunya, masu tare yanmata a waje, tsaki kawai ta ja, ta gilashin Motan ta hango Drivern na waya, suna hada ido ya sakar mata da wani irin murmushin da ya sa jikinta rawa, da sauri ta dauke idanunta daga gareshi, amma ta kasa gaba ta kasa baya, ka kwarjini ya mata, har yanzu bai bar murmushin nan ba, ya bude k'ofa, tuni ta fara jin k'amshin shi, sanye yake da 'yar black top, idonshi da glass amma k'ilan bana gayu bane don farine it might be medicated, ba dai ta sani ba ya fito ya fara taku zuwa gabanta, tuni jikin Ziyada ya fara rawa, tasan Yayanta Majeed me kyau ne, amma meyasa tafi ganin kyan wannan halittar? Ko dai Aljani ne? Tambayar da take ta ma kanta kenan, har sai da ya bude baki yace "Hello My Happiness, its nice to finally/physically meet you" ya fada yana kara mata wannan murmushin. Wani Yanayin da zata rantse bata taba shiga irinshi ba ta shiga lokaci daya, kamar robot ta tsaya kallonshi, ya gama kasheta, ya santa ne da yake dangantashi da Farincikinshi?" kasa motsa baki tayi, ya dan daga hannunshi yayi waving daidai fuskarta yace "Hello? Yadai?" firgigit kamar wacce aka tada daga bacci, yace "Okay, lets get you home" sai da k'wakwalwar kanta yayi mata nazarin abunda ya fada don ita kwatakwata turancin ya dauke mata "ya kaini gida yake nufi?" da sauri ta girgiza kai alamun aa, kar suje Gida Ya Majeed ya ganta, ba zai ji dadi ba. Ya dan marairaice fuska yace "Ok, mu bar School premises first" bata samu chance din bashi amsa ba sai ji sukayi ance "Bahbah, ba wannan bane Zaid Sadam Abdu, the youngest Multibillionaire?" abokai biyu ne ke maganan kuma zasu girme ma shi Wannan din, sai taji dayan yace "Kai Muje mu tambayeshi, Allah ya sa shine, ai mu mun warke" bata ankara ba sai ji tayi ya finciko hannunta ya jata da gudu, ya bude murfin k'ofan gaba, ya tura ta ciki, shima ya zagaya da gudu ya tada Motar, suna jinsu sukace "Wallahi shine mu bishi" suma suka koma suka tada Motarsu, da gudu ya Ja Motarshi yayi Gaba, su ka bishi a baya, gudu yake sosai, ganin jikin Ziyada na rawa ya dan kallota yace "Calm down, i'm not gonna kidnap My Happiness, I got you, trust me" ta dago kai ta kalleshi, ya kashe mata ido daya, ko me wannan bawan Allahn keyi, to ya na tasiri a kanta, duk abunda yayi kashe mata jiki yakeyi, k'asan Gada yayi parking, ya kallota yace "I want you to be my Forever" bakinta yayi nauyi, yace "Ok, Sunana *ZAID SADAM ABDU* hotonki nagani a Wayar Friend dina, he's your friend in some Social network cant remember which actually, Mss_Ziyada isit?yeah i think, tunda naga pic dinki naji ina sonki, na sa a nemo min ke, shine aka ce min kina Kano a NWU, ina da numbernki, amma ban kiraki ba, nafison mu hadu one on one, kawai naji ina son haduwa dake, you know daga wani Gari na taso nazo Garin Kano saboda ke? Tun daga garin Porthacourt, yanzun nace barin zo in nemeki a NWU, ina zuwa kuma bansha wahala ba, da ke na fara cin karo, ina ganinki i recalled your face so well, nayi taking risk din zuwa gareki, ko zaki min wulakanci i wont mind, Saboda i love you so much". "My Forever, ki Amince dani, Aurenki nake son yi, ki gabatar dani wurin Mahaifanki, if you need me to give you time, you have Forever to think about it, i have Forever to wait for you, coz you are my Forever". Zuciyar Mace Rauni gareta, balle a ka samu wanda ya kallamlamceta, nan da nan Ziyada ta fada ma wannan Guy din, Zuciyarta ta Aminta dashi, Zuciyarta tayi naam dashi, a yau ta fara ganinshi, amma sai ji tayi kamar don shi akayi ta, in bashi ba sai rijiya. Da ya lura maganganunshi sunyi tasiri a Zuciyarta, sai ya bude Mota ya fita, ta bishi da Ido, Keke Napep ya tsaida yayi magana, ya ciro 1k ya bada akan idonta, ya dawo wurin Motar ya bude mata ta fito, jiki ba kwari, ya rakata har gaban Mai Napep yace "Ka tuk'ata a hankali, kar ka dauki kowa" Mai Keke Napep yace "Angama Oga" ya juya gareta, ya sakar mata murmushin da ya san yana tasiri a Zuciyar 'yanmata yace "Stay Safe My Forever, sai na kiraki, I love you so much". Tunani dubu dari a Zuciyar Ziyada ta rasa tunanin me zatayi, ita dai kawai ta san tana son ZSA, haka har suka iso har kofan Gida, tayi mamakin yanda mai Napep din ya kawota har Gida, sai kuma batayi mamaki ba, don Zaid din ya mai bayani, shi da ya bar PH yazo dominta, dadi kamar ya kasheta, ta shiga gida baki kamar gonan Auduga. Da daddare ya kirata, chan daki ta kulle Kanta, suka sha Soyayya, tana mamakin kanta, tana da wuyan sabo, bata san mutane, amma itace nan ta zage take waya da wani wai Saurayi, ashe haka abun yake? Cikin Wayan Awa Biyun da sukayi, Ziyada taji a ranta cewa bata da Miji sai Zaid, tana jin shi cikin Jinin Jikinta, cikin Bargo da duk wani tsoka na jikinta. Washegari da Majeed ya sauketa a School, har ya juya zai tafi ta tsaidashi, tace mishi " YaMaji, kar ka damu, yau ma zan hau Keke Napep, i know you are committed, tend to other things" Majeed ya dan nazareta, ya lura tun jiya take ta walwala, yace "Zuzu, is there anything you are not telling me?" da sauri tace "No, ofcourse not YaMaji" yanda tayi magana ya san cewa k'arya take mai, ya gyara zama jikin Mota yace "tun yaushe kika fara min k'arya? Zuzu are you inlove?" Fuskarta ta bashi amsa, saboda nan da nan yayi ja, da sauri tace "Bye YaMaji, kar nayi lattin lectures" ta juya ya dakatar da ita ta hanyar cewa "Zuzu" ta juyo yace "I'd like to see him" kasa boye murmushinta tayi, tace "Bye Ya Maji" da sauri ta wuce yayi Murmushi yace "Yara Sun Girma". K O T U A tunaninta k'aramin case ne tunda sunada all evidences, za kawai a ba Nakowa Rashin gaskia, a hukuntasu, Nana ta mayar musu da Credentials din Majeed a wuce wurin, shiyasa taga gwara taje tayi representing Family dinta, taje Kotun ba tare da ta sanar da kowa ba a gida. Kotu ta cika Mak'il, Nakowa da Iyalanshi sun hallarta, a ka karanto Sunan Shari'ar, Alk'ali ya buk'aci da a kira Mijin Nana ya fito gaban Kotu, Lawyern Mummy ya sanar dashi cewa Hajiya Mairo kadai ta Hallara a Kotun, Alk'ali ya tambayi ina Mijin Nanan? Mairo tayi karya tace baya k'asar, nan da nan Alk'ali yayi watsi da lamarin yace, an daga Sauraron Kotun har sai Mijin Nana ya dawo, tace Sati me zuwa zai dawo, Kotu ta daga Sauraron case din sai bayan Sati Biyu, aka Sallamesu, Hajiya Mairo ta gama wurgansu Hajia Sayluba da Nana da bak'aken maganganu kan Nana, wai Karuwar Babanta, ta ja Motarta ta wuce, Alhaji Nakowa ya Murmusa yace " kina da sauran baki har na sati biyu, Bayan Sati Biyu bakinki zai mutu Murus". * * * * Yau Laraba yayi dropping Ziyada a Makaranta, ya bi ta Rijiyar Zaki gun Mallam Sanda, Mallam Sanda ya nuna mai ba wata Matsala, ana ta Addua da saukar Kurani, InshaAllah akwai Nasara, Iyayen zasu dawo Hayyacinsu, Yayan kuma zai bayyana gaban k'anwarshi in dai yana da rai, Godia Sosai Majeed ya sakeyi, ya ja Motarshi ya tafi, be san ya akayi ba be ankara ba sai gani yayi wata ta zube a gaban shi, k'ii ya ci burki don kar ya takata, da saurinshi ya fito waje, titin Rijiyar Zakin be da kyau, ya tsugunna gabanta yace "Baiwar Allah? Tashi a hanya? Baki da lafiya ne?" dago Fuskarta tayi, budurwa ce da ba za ta wuce du Ziyada ba, yana hango boyyayen kyaunta da wahalar rayuwa ya boye a fuskarta, kayan jikinta kwandala biyar ba zaka siyesu ba, bakinta ma rawa tace "Kayi wa Darajan Manzon Allah tsira da Amincin Allah ka taimakeni" Majeed Sarkin tausayi ya sa hannu cikin Aljihu, dubun biyun da ya rage mishi ya ciro ya bata" yarinyan tayi murmushi me ciwo tace "ina ma kudi zasu magance min damuwata?" ya tsura mata ido, yana tausayinta har ranshi, yace "taso mu shiga mota" ba gardama ta bi bayanshi suka shiga Mota. "Baiwar Allah Meye damuwanki?" Sunana Na'ila Shehu, ni Marainiya ce, Ina da Yaya daya Nura, Kurma ne, be jin magana be iya maidawa, sai dai ya mayar da nuni da hannu, Rayuwanmu ya chanza tun randa Mahaifanmu suka rasu, Yayana be da wani mamora, gidan da muke haya yau da Asuba aka mana koran karnunka, bamu san inda zamu dosa ba, ka taimakeni, kamar yanda Allah ke taimakonka, ka rufa min Asiri, yanda Allah ke rufa ma Asiri, na san baka sanni ba, ka bami masauki, zan nemi Aikatau, InshaAllah ko zuwa nan da Sati daya zuwa Biyu, zan samu yanda zanyi don Girman Allah". Jikin Majeed ya gama sanyi, shi yasan shima yana da bukatan Taimakon, Babban Gida da Motan da aka ga ya na hawa, ana mishi zaton Shi wani Hamshakin maikudi ne, to hamshakin ne, amma a da ko? Tausayi Na'ila ta bashi, duk da shima yana da bukatan taimakon, zai taimaka mata ita da Yayanta, ko a boysquaters su zauna, kafin su samu yanda zasuyi, Allah ya bashi ladan, ya kalleta da tausayi yace "Ina Yayanki?" M ajina ta ja, tace " yana Ja'en" Majeed yace "ki nuna min hanya" tace "toh". Ya ja Mota, sun danyi tafiya me nisa kafin suka iso Ja'en, da kwatance suka iso wani Unguwa, Unguwan dai sai a hankali, da hannu ta nuna wani wuri tace "ga Yayana chan". Majeed ya kai dubanshi ga inda take nune, wani ya gani a tsugunne, yara sun zagayeshi suna waka, "Kurma ne, Bebe ne,
Chapter 55 · 0% Book details