← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 128

Sashe 115

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dariya sukayi duka sukace "Daddy Aure kuma?" Murtukr fuska yayi yace "Eh din Aure,  ko na wuce ne?" Daria sukayi duka,  Paapa ya daura da cewa, "da kuma auren Dana Abdulmajeed da ya ma sunanta Yaya??" Daddy yace "PureHeart"
Ta tashi da gudu ta fada daki tana cewa "Kai Daddy kai Daddy" Paapa ya kalli Zaid yace "Gatan Marayu,  na bar komai a hannunka" Zaid yace "I got this Pop" Paapa ya kalleshi yace "Pop?" su Ziyada suka fashe da daria,  Zaid yace "Ina Nufin Baba" Daddy yace "Allah ya shiryaka,  Sada muje ka rakani Zance ko?" Zaineema tace "don dai Aunty Aynarh ce Daddy wallahi da ba mu yarda ka auro wata ba" Daddy yayi daria yace "Kunsan dai da tsohuwan Zuma ake magani ba? Maryama ta Abba" aka hau shewa,  Hajjo tace "yi maza ka saki layi gaban suruki" Daddy yayi daria yace "Ai Khalid Dana ne ba suriki ba" Khalid ya mik'e yace "bari na shiha cikin Gari,  zan dawo Anjima" to sai ka dawo inji su, Hajjo tace "Ja'ira dauko gyalen ki raka shi" ta mak'e kafada,  Daddy ya ja hannun Paapa suka fita,  Hajjo tace ni ku jirani ku kaini Gida, ta bi bayansu bayan ta ma Maama Sallama,  Zaineema ta kalli Maama,  ta mata alama da ta bishi,  ta mike ta gyara zaman gyalen da ke jikinta ta fita ba tare da ta ce ma khalid komai ba,  Khalid ya bi bayanta bayan ya ma Maama da Zaid da AbdulMajeed sallama, Zaid ya ciro waya ya latsa yace "Ga khalid nan fitowa, ku kaishi inda yake so .

Maama na kallon Zaid ta gefen ido, yanda yake waya ya matukar burgeta, wani sonshi takeji, tashi tayi ta shiga daki,  Abdulmajeed na son ganin Najwa yace "Uhm,  bari na ehm shiga ciki" Zaid yayi Daria, Abdulmajeed ya shige dakin Najwa ya rage  daga Zaid sai Ziyada a Parlorn, ya k'araso gunta ya zauna kusa da ita ya riko hannunta ya kai saitin zuciyarshi yace "na wahala Babe,  kinji yanda sonki ke neman fasa min zuciya?" kanta a k'asa tace "a randa ka gane Najwa, na ga ka mjn wani kallo,  gabana ya fadi,  na zata zaka tsaneni,  na zata zaka sakeni,  na zata zaka rabu dani" yace "Tab,  kinsan Auren Zobe? To shi mukayi, kinsan me zai faru dani in na rabu dake kuwa?" ta dan dago tace "aa bansani ba,  gaya min".

"Erhm, kinsan me zai faru dani in na rabu dake?
First, I will have a Headache, Heartache, Malaria then Typhoid and Kidneys stones, HIV and AIDS, Fcq, Tsd, Uccd, Rfs, Rabies and Ebola and I will die" wani irin dariya Ziyada ta fashe dashi harda kwallah, cikinta kamar ya fashe don daria, shima darian yakeyi, sai da tayi dariarta ma ishi kafin ta rungumeshi tace "Allah ya tsareka My Forever, hakan ma ba zai faru ba InshaAllah, amma meye Fcq? Tsd? uccd, rfs? Meye su?" daria yayi yace "yo wa ma ya sani?nadai san zan kasance tare da ke har abada da yardan Allah" kafin ya hade bakinsu cike da kauna.

Murmushi suke ma juna kafin ya dora kanshi kan kafadarta, yana kallon Dakin Maama, fuskarshi ta dan sauya, ta lura dashi tace "Ka shiga, tana ciki" girgiza kai yayi yace "bata son ganina" girgiza kai tayi tace "ka shiga My Forever, nasan shes waiting for you, komai ya wuce, ka shiga ka ganta, kuyi magana" wani tunani yayi kafin ya dago ya bata peck kan goshi yace "nagode" tare da mik'ewa ya nufa "Dakin Mamaa da Sallama".

Tana tsaye tana kallon Madubin jikin wardrobe dinta, ko da ya shigo ta hangoshi jikin madubinta, kamar jiranshi take ta sauke naunauyar ajiyar zuciya, baki ya cire yace "Maa" bata amsa ba illa runse idanuwanta da tayi daidai da saukowan hawayenta, a nutse ya taka ya rungumeta sosai yana hawaye, ba ta hanashi ba, hawayensa ke zuba a kan kafadunta, bakinshi na rawa yace "Maa" hannunta na rawa ta kai kan sajensa tace "Zaid, Zaid My Son".
****
Hello Lovers! Ya kuke? Sorry sorry na makamakale kwana biyu.

So how's this page ? Kowa ya yafe ma kowa? Ina fata yan ™Zaid kun yafe ma Mairo, da kuma yan ™Majeed sun yafe ma Zaid? Nima dai na yafe musu lol.

Ehen kunji Zaid zai kamu da cututtuka for Ziyada? Hmm. Intresting.

NajwanMajeed?
AbbanAynarh?

So the Million Dollar Question.
*ARE YOU READY FOR THE FINAL AND LAST PAGE?*

#1love
#ADAY
#bibiliciousfreakingfans
#anatare
#nagode.

Biebee Isa.

💭A DADE ANA YI....sai gaskkall

Wattpad:@biebeeisa

Pg4⃣0⃣

Hannunta biyu ya kamo, haka kamar dan shekara 11 yake ta tsala kuka mara sauti amma me ciwo "Maaa, kice baki tsaneni ba donAllah, kice kin yafe min, donAllah kice Allah ya min Albarka, Mami ki samin Albarka, na tuba, ba zan k'ara ba, ba zan sake ba, kiyi hakuri kinji Maa".
Kamo fuskarshi tayi da hannu biyu tana shafashi kamar tana son gano wani abu daga gareshi cikin sanyi tace "kayi hakuri D'ana, na bamu wahala, na wahalar da zukkatanmu duka, nifa na haifeka, ta ya zan tsaneka? Kuskure kayi kuma ka gyara, kuma a lokacin da akwai wata hanyar gyaran da zakayi ba tare da da na nuna maka jan ido ba, da nayi, hakan da nayi ne daidai, ka yafe min Yarona" dan yatsar shi ya sa mata a baki tare da fadin "Shhhh Ma, kar kice komai, gaki a nan, hakan ya wanke min komai, balle kuma meye laifi in Uwa ta hukunta Danta? Shh, kukan ya isa" ya sa hannu ya dinga share mata hawayen da ke zuba a fuskarta ba tare da damuwan goge nashi da ke zuba a nasa fuskar ba.

Cigaba da shafa fuskarshi tayi, hawayen ba su bar zuba ba, amma fuskarta cike da annuri, ta so tayi hakan tun ranarda ga fara ganinshi, dama be bata ba, "Haka ka koma? Haka ka zama? Wannan yarona ne? Haka ka Girma? Ina Alfahari da kai Zaid, wallahi ina alfahari da kai" rungumeta yayi yace "Naji dadi, Naji Dadin da kike Alfahari dani, Naji dadi Mami, ina sonki fiye da rayuwa da kanta, kece komai na Mami, naji dadi da ba ki tsaneni ba, naji dadi wallahi" dariya tayi sosai tace "nima naji dadi, ba zaka gane kalar farincikin da nike ciki ba, nima ina sonka Yarona, Allah ya Albarkaci Rayuwarka, Allah ya Albarkaci Rayuwarku kai da k'anwarka Najwa, ya Albarkaci Rayuwarku tare da Yanuwa da yaran Musulmai duka".
"Ameen" ya amsa, yana jin kanshi a cike da murna, yana jin dadin yanayin da ke shiganshi, Allah ka sa karshen bakincikin mu kenan, Allah ka sa mu samu dauwamamiyar farinciki, Allah nagode maka, Alhamdulilah Ala kuli hal".

Ba ta damu da Girman da yayi ba, bata damu da saura k'iris ya shiga shekara 30 ba, rungume dan yaronta takeyi tana shafa kanshi kamar dan shekara 11 da ta bari a Hassan Ibrahim Gwarzo, ta yi kewanshi sosai, kalamai ba zasu baiyana farincikin da suke ciki ba, ba ta so ta daina jin dadin nan, Godia take ta ma Ubangiji Azzawajala da ni'ima da baiwar da ya ba Danta, zaune tayi kan Gado, shima ya zube kan guiwowinsa tare da daura kanshi akan cinyoyinta, tana shafa mai laulausan gashinshi, suna fira irinta Da da Mahaifi.
(Ubangiji ka bar mu da Mahaifanmu, ka kara mana So da k'aunarsu, kasa suyi Alfahari damu, kasa duk wata kalma da zai fito daga bakinsu ya kasance Albarka suke sama na, Cikin Mahaifan da suka rasu Ubangiji Allah ka yafe musu, ka sa sun huta, ka haskaka k'abarinsu, domin Albarkar Fiyayyen Halitta. Wanda suke da rai kuma Allah ya kara musu nisan kwana Ameen).
****

Zaune take kan stool din Madubin dakinta, ta ji shigowarshi, kamshin turarenshi ya fara sanar da ita da Jaan dinta ne. Kin dagowa tayi har sai da ya shigo dakin gabaki daya, wani abu take ji game dashi wanda ba zata iya bayaninshi ba. Ba kullum suke haduwa su ke6e don yin soyayya ba, ba kullum suke waya ba, amma Soyayyar gaskiar na dashe a cikin rayukansu, daidai Gadon da ke kallon Madubin ya zauna, ya kasance tana kallon madubi amma shi take kallo, shima Madubin yake kallo amma ita yake kallo. Murmushin k'auna suke aikawa ma junansu, kafin Abdulmajeed ya fara magana "PureHeart, bansan ta inda zan fara magana ba, randa na fara ganinki, tun a jirgi, domin Allah naji wani abu game dake, bansan ko meye ba, amma duk kukan da kike yi a Cikin Jirgi haka kurum na tsinci kaina da shiga damuwa, bansan dalilin da ya sa na kasa hakura ba har sai da na tanka miki, bayan nan, zan iya cewa wannan k'auna ce ta jini da bata yankewa, girman yanuwantaka na da girman gaske, saidai rashin sani ya sa a k'i fuskantarsa.
Chapter 115 · 0% Book details