← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 128

Sashe 20

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read

鈥⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€�

Hello Lovers, how are we all doing? Yeah, yeah i know i was mute for days, was busy with Biki, m so sorry, but its all over now, lets keep rocking it.

Please do Vote and Comment.

#1love
#ADAY
#anatare
#bibiliciousfreakingfans
#nagode

Biebee Isa
[12:03, 25/09/2017] 鈥�+234 803 414 9368鈥�: 锟斤拷A DADE ANA YI....sai gaskia锟斤拷

NA

BIEBEE ISA

庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg1鈨�2鈨�

Kuka yakeyi kamar ranshi zai fita, ya rasa Mutumin da yafi kowa mahimmanci a gunshi, mik'ewa yayi daga jikin Baba ya share hawayenshi, ya nemi Dr, don a kai Baba Mortuary, don be so a rufe Baba a Garin PH Kaduna yake so a rufeshi, a mak'abartan da yake daukar dawainiyansu. Hakan kuwa akayi, a聽 Asibiti Zaid ya kwana. Washegari da Sassafe aka wanke Baba aka suturceshi, kafin su ka kama Hanayar Kaduna, da laasar suka isa.

Tun daren Jiya Rasuwar ta zagaye k'asar gabaki daya, daga wurare da dama Mutane suka zo Kaduna, suna jiran gawa har su ka iso. Gidan Baba cike mak'il da mutane, yaran gidan marayu sai kuka suke tayi, su aka ma rashi, basu san ya rayuwarsu zai kasance ba tunda Gatansu ya rasu, ko ina jimami ake tayi.
Kallo daya zaka ma Zaid zakaji tausayinshi matuk'a, ya zama wani abun tausayi, tun yana Kuka har Kukan ya k'i fitowa. A haraban Gidan Baba aka sallaceshi, aka dunguma aka tafi kaishi Gidanshi na gaskiya, Kuka Sosai Zaid keyi, tun balle da aka zo sa Baba a k'abarinshi, sai da Aminin Baba ya rike shi, haka har aka rufe Baba, Adduoi suka biyo baya, sai da kowa ya watse ya bar Zaid tsugunne gaban kabarin Baba.
*
聽 聽 Marigayi Alhaji Sadam Audu Babban mutum ne, a dole gwamnan garin Kaduna ya bada umurnin hutun kwana daya public holiday saboda Shugaban k'asa da zaizo gaisuwa garin kaduna, Tururuwa akeyi gurin yi ma Zaid gaisuwa, Manyan Mutane ne, shuwagabbani da sauransu, Zaid ji yake kamar ya sa hannu a ka ya tsandara Ihu baya son jin kalman 'ashe Alhaji lokaci yayi' ya gaji da magana, tun yana iya amsawa da ka, har ya koma kurman dole, haka zaai ta magana sai dai na kusa dashi su amsa gaisuwan.

聽 聽 Bayan Sati Daya

Har yau Zaid be bar amsan gaisuwan Mutane ba, jefi jefi wasu ke shigowa, Aminin Baba ya shigo Parlor inda Zaid ke zaune da wasu Abokan Baba, ya dan karkato daidai kunnen Zaid, yace "dan Baba, ga CEO Abba Abu's Enterprises da Iyalanshi sun biyo su ma Gaisuwa.
Kirrr kamar k'arar k'ararrawa, CEO Abba Abu's Enterprise? No it cant be, ba zai iya ganin su ba, he cannot face them now, atleast he's not ready, not just now, muryan Abokin Baba yaji inda yake cewa, Zaid ku fito ku gaisa, gaisuwa kawai zasu maka, murya chan k'asa Zaid yace "Nagode" Abokin Baba yace "Aa fa Zaid ba a haka, abunda ma yan gaisuwan sun bar zuwa, kwana bakwai kana karban gaisuwa, don dai wadannan sai kace ka gode kawai? Hmm, don kana Aminin Baba zan daga ma, da ba don haka ba da sai ya mishi rashin kunya. Mik'ewa Zaid yayi ya fita daga Parlorn zai bar musu Gidan, da sauri dan dattijon ya kamashi daga kafada yace "Zaid, dont be like this, nace musu bari a kira danAlhaji su mai gaisuwa, nasan suna ta tsumayin ka, please kaje, it wont take long,atleast Babanka ba zai ji dadi ba idan kana regarding guests dinka" jin an kira Baba ne ya sa Zaid juyawa, be san me zai iske ba, amma zuciyar ba ta fasa dukan chalugude ba, tsoro da firgici ya mamayeshi, har ya isa dakin be san ya shiga ba, tafi kawai yakeyi, zaune suke su Uku, one by one ya bisu da kallo, a zuciyarshi ya dinga ambatan sunayensu a lokacin da ya dora idonsa kansu, Abba,Muhsin, kafin dubanshi ya sauka kan Hamshakiya Mandiya Mairo, miyau ya hadiye mai zafi.

Tsura mai ido suma sukayi, Zaid tsaye gabansu yana bunsu da ido suma suna kallonshi, jin muryan Abokin Baba sukayi inda yake cewa "DanBaba ka zauna mana" ba tare da ya jira cewar Zaid ba yace "Alhaji Abba, wannan shine da tillo gun Marigayi Gatan Marayu".
Abba yace "Allahu Akbar, Sannu yaro, Babanka mutumin kirki ne, ban sanshi ba, amma na shaida halayenshi na kirki, kowa a k'asar nan ya san Gatan Marayu mutum ne mai taimako,muma daga Abuja muke zamuje Kano, shine nace tunda hanya ne mu biyo muku gaisuwa,Legacy din Babanka will forever live in Nigerians Mind, don he's a Legend and a Hero.sai dai mu rok'i Allah ya ji kanshi, ya sa taimakon Marayu da gajiyayyun da yayi tayi har karshen rayuwanshi shine hanyar Jihadinshi, halayanshi nagari ya bishi" Kafe Baba Abba Zaid yayi da ido, Abokin Baba ne ya samu ya amsa Adduoin, Mairo ta murmusa tace "Allah ya ji kanshi ya kyautata namu mutuwan" a lokacin Zaid ya gaji da jin muryoyinsu, idan yayi gigin bude baki, to k'ila kasheta zaiyi da kalamai masu zafi, cikin Zafin Nama ya mik'e tsaye ya bar dakin, duk suka bishi da ido, mamaki ya kama Abokin Baba, yana tunanin me ya samu Zaid? Tuni ake zuwa musu gaisuwa amma be taba acting haka ba, meyasa sai yau? Wayancewa yayi "yace kuyi hakuri, kunsan Mutuwa, har yanzu jimami yakeyi, kumai uzuri" Abba yace "haba ai bakomai, radadin Mutuwa zafi gareshi, balle ga wannan ya tashi baida kowa sai babanshi, rana daya ya nemeshi ya rasa,dole ya shiga cikin wannan yanayin" "haka ne" Mairo tace "Daddy sai mu tafi ko?" Abba yace "to Alhaji bari mu tafi kano muka nufa Allah ya k'ara hak'uri" Abokin Baba yace "Ameen Allah ya bada lada angode" Mairo ta sa6i Muhsin dan shekara 3 a kafada, Abba ya amsheshi yana mata murmushi, murmushin k'auna sukayi wa juna,duk kan idon Zaid da yake daga waje, haka suka fita daga Parlorn, a idon Zaid, wanda komai ya gama sukurkurce mai, Wannan Murmushin da ya gani kwance kan fuskokinsu shi ya jagula mai lissafi, like wake murmushi a gidan Rasuwa in ba su ba? Basu da damuwa, basu da wata matsala, ganin da ya musu yanzu ya dasa wani tsantsan tsanarsu a Zuciya.
Its about time, lokaci yayi da zai cizge wannan farincikin a fuskokinsu.

B A Y A N聽聽 K W A N A聽聽 G O M A

聽 聽 Alhaji Dauda Aminin Baba ne na k'ud k'ud, shi kadai ya san Sirrikan Baba, a Parlorn Baba Zaid zaune gaban Alhaji dauda, ba kasafai yake son magana ba, shi so yake yayi nesa da kowa da komai, so yake ya lula chan uwa duniy yayi shirinsa na daukar fansa,a sama ya ji muryan Alhaji Dauda inda yake cewa "Dan Baba, yau kwanan Gatan Marayu 17 da rasuwa, a yau ne nake son sauke nauyin da ya bar mun tun shekaru da suka wuce,kasancewar kai kadai ne d'a a gun Marigayi,聽 bai da dangi bai da kowa, ina mai farincikin sanar da kai cewa "Duk dukiyarshi da abun da ya bari sun zama mallakinka, fadar shi Marigayin ne,sai da na daukar mai Alkawarin Mallaka maka komai, naka ne, komai naka ne".

Shiru Zaid yayi,a iya girmanshi ya san cewa Babanshi Mai kudin gaske ne,ina zai iya da wannan tarin dukiya? Shi da yakeso ya yi nesa da kowa ew komai? Mallaka mai Dukiyoyin nan na nufin am daura mai Girma, Girman da beyi shirin dauka ba, wata farar takadda Alhaji dauda ya mik'o ma Zaid, hannu na rawa Zaid ya kar6a, idonshi ya ciko da hawaye da ya ci karo da rubutun Baba, a hankali ya fara karantawa;

聽 聽 "Zaid my Child, from the day i die, you became a Man, i know you are so weak,but please be Strong, be strong for me, na san kana da hidimar gabanka,komai naka ne, na dade da maida komai under your name,i was just managing everything for you, whatever you decide to do with your inheritance,i'll be proud of you, but banda shayeshaye, take care of yourself for me. Har cikin raina nake k'aunarka, Allah ya raya min kai.
聽 聽 聽 聽 聽 聽 聽 聽 聽 Baban Zaid

Zaid na kawowa daidai ga6arnam ya fashe da kuka,shi yasan Son da Baba ke mai daga Allah ne, mutuwar Baba ta dawo mai sabo fil, sai da yayi mai isarshi kafin ya tsagaita, Alhaji yace "Akwai abokan Aikin Babanka da suke so a saida musu wasu companies na garuruwa daban daban, in kana da raayin saidawa,a na kuma iya tsaida production na companyn textile and feed industry a tsaida shi, Gidan Marayu kuma ana iya sallaman kowa, komai naka ne, you can do as you wish" Zaid ya furzar da iska, ya saida Companies din Baba? Ya saida hardwork dinshi? To akan me? Kudi? Tabdi, ai kudi ba matsalarshi bane, yayi imani kudi da dukiyoyin da Baba ya bar mishi zai isa ta kula da 10 next generations to come ba tare da wani abu ya ragu ba, sannan kuma a tsaida Production din textile da feed Industry? Akan me? Meyasa zai tsaida production din da idan anyi producing Gidan marayu ake kaiwa? Son abun dunianshi be kai nan ba.
Chapter 20 · 0% Book details