← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 128

Sashe 81

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya ta sake a guje ta rugo gunshi ta runkukumeshi tare da fashewa da kuka,"My Forever,聽 kar ka sake bari na ni kadai DonAllah" be son kukan nan,聽 aa yana so,聽 ta cigaba,聽 it gives him joy, hannu ya sa ya tureta ya wuce daki,聽 binshi take a baya tana tambayarshi聽 me zata dafa mai,聽 ya shiga daki ya buga mata kofa a fuska.
***
Isowarta ke da wuya,聽 ta ci karo da gidan makil da masu tsaro,聽 tace ma me Napep barin anso maka kudinka, yace "to Hajia kiyi sauri" ta wuce tana sababi,聽 tazo shiga aka dakatar da ita,聽 tace "Kai gafara chan,聽 matsa min in shiga" wani yace "baa shiga Hajia" cike da masifa tace "ban gane baa shiga ba" yace "Umurni ne聽 daga Oga,聽 yace kar a bar ko waye ya shiga" Hajia Mairo聽 ta dara tace "ni ai ba kowa bace,聽 ku bude ni surukar shi,聽 matsayin uwarsa nake" dayan yace "ku bude mata" dayan yace "baka da hankali ne? Bakaji Oga yace kar a bar kowa ya shigo聽 ba,聽 ko yanzu da zai shiga sai da ya kara jadadda mana" sukace hakane,聽 Mairo tace "kai bansan iskancin banza ku bude聽 min na shiga,聽 ko wallahi na sa ya koreku" daya yace "Hajia da kin kirashi kince mai kina kofar gida" nan fa daya,聽 da tana da numbernshi ai da taji dadi,聽 kuma numbern Ziayda be shiga,聽 tace "wayar ba chaji kaidai聽 kaje ka ce mishi ga Mamansu a waje" suka ce to gwara hakan, shiga dayan yayi ya dinga kwankwasa parlo,聽 Zaid da Ziyada聽 a tare suka karasa Parlorn,聽 shi ya na tunanin waye ke kwankwasa mai kofa,聽 ita kuma tana rokon Allah yasa wani dan gidansu ne.
Officer yace "Sorry Oga,聽 Bakuwa kukayi" yace "Uban me nace muku?聽 Nace kar ku bari ko waye ya shigo ko?" yace "bawanda ya shigo,聽 dama tace mamar matarka ce, kuma surikarka,聽 shine nace bari a sanar da kai" ran Zaid bace yace "ba ce muku nayi kowaye ya zo kar ku bari ya shigo ba?" police ya kalli Ziyada sai yaji ta bashi tausayi yace "Oga Mahaifiyar Matarka fa ce" cikin tsawa wanda ya tabbata Mairo taji聽 yace "koma uwar wacece" Jikina rawa ya juya yana cewa "OK Sir".聽 Zaid ya waiga yaga Ziyada na kukan hawaye,聽 ya murmusa聽 a ranshi yace "its time" Zai ci mutuncin Uwa gaban diyarta,聽 ya juya gun mai tsaron yace "Ko kuma Kai,聽 barta ta shigo" Ziyada ta daka tsallen murna,聽 tana farinciki zata ga uwarta" Zaid ko Murmushin gefen kumatu yayi.
****

Ghen Ghen,聽 Zaid and Mairo,聽 Round one Fight.
Me kuke tunanin zai faru?
Me zakuce game da abunda Zaid ke ma Ziyada,聽 nima na sha hawaye na,聽 amma Zaid akwai dan...

Vote and Comment line by line,聽 God Bless you as you do.聽

#1love
#ADAY
#bibiliciousfreakingfans
#anatare
#nagode

馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱

NA

BIEBEE ISA

庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Wattpad:@biebeeisa

Pg3鈨�2鈨�

Hajiya Taatuh na rabuwa da Hajia Aynarh ta kira Alhaji Ado tace mishi "sun kai amarya yanzu za taje Airport ta wuce Abuja, shima ya sanar da ita zai biya Bauchi yau amma InshaAllah gobe zai dawo Abuja suka ma juna fatan Alheri kafin suka katse wayar.

Anty Aynarh ta nufa Gidan Alhaji Abba na yanzu don ta sanar dashi an kai Ziyada gidanta, kuma ta dauka motar ta da ta bari a gidan da zasu kai amarya, ko da ta isa bata san hayaniyan Mairo sai ta kirashi a waya tace tana waje, ba a dau lokaci ba sai gashi ya fito da Murmushi, bayan sun gaisa ya tambayeta Ziyada tace "Tana chan lafiya, Gida yayi kyau, kuma abun mamaki Gidan da kuka tashi nan ne gidan" Daddy yayi jim kafin yace "ikon Allah, kila Alhaji Labaran Zaidun ya sayar ma Gidan, don Zaid din be san mu da gidan ba" Anty Aynarh tace "nima dai nayi mamaki" Daddy yace "amma ba wani abu bane, Allah ya basu zaman lafiya duk daya ne, ba zan dai gaya ma wannan mahaukaciyar ba don tana聽 iya zuwa ta rokeshi ya bamu Gidan" Hajia Aynarh tayi daria tace "Lalala, Alhaji Abba ba ruwana wallahi" Daddy ya Murmusa yana jin kansa wasai, tun jiya yake jinshi kamar an zare mai wani haki daga kafa yace "Nagode kwarai Hajia Aynarh, kin tabbata masoyiyata, tunda kin maida yarana kamar naki, banda gida, banda mota, banda kudin aurenki, da ina da ko da biyu daga cikin jerin abubuwan nan ne da na fito cikin sahun Masu neman Aurenki, Hajia Aynar ta runtse ido, wani irin dadi na shiga duk wani sasan jikinta, abunda ta dade ta na tsumaye kusan shekara 20 tana so taji wannan maganar daga bakin Alhaji Abba,ta tabbata ko meye Hajia Mairo ta mishi na mallaka ya fara kuncewa, tayi tsumayen kalaman kauna daga bakin shi, a kanshi ta kasa zaman Gidan Aure saboda sonshi, Aure biyu ta kaso don Alhaji Abba ya aureta, ta sa mayafin gyalenta ta rufe ido, wai ita kunya, yayi dariya yace " Zanyi kokari in ga na mallaki ko da biyu daga cikin abubuwan nan inzo na aureki, ta juya mishi ido, tace "Idan na ara maka kudin Aurena zaka aureni?" yace "Aa, ni da kaina zanyi aikin neman kudin da zan aureki, ke gimbiya ce, ba zaa aureki da kudin bashi ba, tace "ina iya ara maka kudin sadaki, in ka samu ka biyani, Gida kuma da Amincewarka zaka barni a gidana, abu na, naka ne, na sha gaya ma da dadewa" kasa magana yayi ya murmusa, daidai fitowar AbdulMajeed daga Gida, Daddy ya yafito shi yace "Zo ka kai Auntynka Gida, ta gaji" cike da ladabi yace "To Daddy" Aunty Aynarh ta kura ma Daddy ido, shima kallonta yakeyi, har Majeed yaji kunyan kallon da suke wurga ma junansu da angani an san na so ne, a ranshi yace "ai in Mummy ta fito yanzu ai mun bonu duka" don kansu suka bar kallon junansu, ta mika ma AbdulMajeed Key, suka shiga mota suka wuce Daddy be shiga gida ba sai da yaga sun kule, a hanya ne Anty Aynarh ke sanar da AbdulMajeed inda aka kai Ziyada,聽 sosai ya jinjina maganar amma daga karshe ya musu fatan Alheri.聽
鈥⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€�

Da k'arfi ta sake kwala mai kira "Zaid" nan ma shiru ba amsa,聽 da baya da baya take tafia har ta ci karo da Dakinsu na da,聽 ta bude da karfi,聽 wayam baya nan,聽 kamar zararra ta nufi dakin AbdulMajeed ta wangale nan ma baya nan,聽 da gudu ta nufi dakin Daddynsu ta banka da k'arfi,聽 nan ta sauke naunauyar ajiyar zucia ganin聽 Zaid sanye cikin wasu Farar riga da Wando fari 3quater, yana zaune kan Kingsized bed yana latsa laptop dinsa,聽 ganinshi ya sa ta jin sanyi,聽 wani sabon so da kaunarshi na shiga duk wani lungu da聽 sakon jikinta, a daddafe ta karasa聽 ta hau kan Gadon,聽 ko kallo daya bata samu ya mata ba,聽 cigabawa yayi da harkar gabanshi.

Ta kasa karantar yanayin da yake ciki,聽 meyasa yake yin haka?聽 Ko gajiar bikin ce be sakeshi ba?聽 Yanda yake wayoyinsa cikin kwanciyar hankali ba tare da ya dago ido ya kalleta bane ya sata mamaki ainun,聽 kamar ba shi ba,聽 kamar ba Zaid dinta ba, bakinta na mata nauyi,聽 da kyar ta samu ta juya harshenta "My Forever" yanda kasan ba da shi takeyi ba,聽 yayi banza da ita,聽 a ranta tace "ko dai be ji ba?" ta sake kiranshi da "Zaid" nan ma shiru yayi mata, wannan shine "hakuri" da Daddynta yake ce mata ta yi? Wannan shine kawar da kai din da ake ta mata magana a kai? Tun baaje ko ina ba? Dama haka maza suke da sunyi aure? Ba haka yake ba da, kamar ba loving and caring Zaid dinta ba,聽 wanda bata taba so ba sai a kanshi,聽 wanda shine ya koya mata yanda zata soshi?聽 Duk ya rikide ya chanza,聽 bata so tayi imagining wani abu is about to go wrong,聽 bata so tayi tunanin chanjin nan da wani manufa,聽 bata so tayi tunanin komai,聽 gwara tayi ta mai uzuri, da sauri zuciyarta tace "ko dai yana da aljanu? Don sharetan da yakeyi ta tabbata ba yin kansa bane,聽聽 Ko moodswing ne? Ai ana haka,聽 wani lokacin kaji baka son yi ma kowa magana,聽 to kila hakan ne,聽 bari ta bashi space,聽 ko anjima zai dawo daidai.

Mikewa tayi zata bar dakin ta tsinkayi muryansa a sama "Ina Wayarki?" da sauri tace "Yana daki" muryarsa cike da umurni yace "dauko" da sauri ta fita Daki ta shiga dakinta ta bude jakkarta ta dauko wayar, komawa tayi dakin da ta bar Zaid ta mika mishi wayan, amsa yayi da karfi kamar fizge, ta kalloshi da sauri, a gaban idonta ya kashe wayar ya jefa cikin aljihunsa ya cigaba da latsar wayarsa da laptop, gabanta ya fadi, me hakan ke nufi? Me Zaid ke nufi? Me yakeyi haka? For how long zata cigaba da mishi uzuri? Bakinta na rawa tace "Meyasa ka kashe min waya? Meyasa ka kawoni Gidan nan? Shin baka san Gidanmu bane nan?" Zaid ya fashe da wani irin dariyan da daga ji kasan cewa bana lafiya bane,聽 kafin yace "thats what you dont know,聽 This is my house,聽 it has always been My house(shine abinda baki sani ba,聽 wannan Gida聽 na ne,聽 dama chan Gida na ne" ta ja baya tana kallonshi, a iya sanninta,聽 ta san wannan gidansu ne,聽 shiyasa suka saida gidansu na Abuja suka dawo Kano,聽 yana nufin da ya siya gidan ne ya zama nashi.
Chapter 81 · 0% Book details