Sashe 38
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba, so karki damu everything will be fine". Bakinta na rawa tace "Mummy fa?" yace "tace zaa kula da ke har in dawo" jim tayi ba wai don ta yarda dashi ba, ko safiyar nan sai da ta zabga mata harara, ta san fa Mummy bata santa, amma don me zata cemai zasu kula da ita? Isit a trap?" lura yayi da ita yace "karki damu Najwa Mummy will take care of you for me, ita tace haka, kuma i trust my Mom more than anything, in zatayi zatayi, in ba zatayi ba ba me sata yi, so since she said it, to zatayi, kedai kawai ki dinga shafa maganin nan akan lokaci" Yak'e kawai Najwa tayi ta gyada kai. PORTHACOURT Ng Ya san Hardwork din Mahaifinshi ne, ba zai manta ba, lokacin K'asar Italy Babanshi da Mamanshi sukaje don ganin Haduwar Company din nan, tuna Mahaifanshi ya k'ara tada mai hankali, sun rabashi da nashi Mahaifan, amma suna zaune da nasu Yaran, ba zaiyiwu ba,a hankali zai watsa su duka. Wayarsa ya dauko yayi dialing number ya kara a kunne yayi magana umurni ya bada da a rushe ABBA ABU AND SON'S FURNISHING COMPANY, ba don komai ba sai don idan sun shiga matsi suna iya saida Companyn su samu kudi, to kuma zasuji dadi, shi kuma zai shiga k'uncin, don Bak'incikinsa shine Farincikin Iyala Abba Abu, amma inyayi haka, tunda yana da possesion of Takardun Mallakan Gurin so komai zaizo a sauk'ake. ** Bayan wasu 'yan kwanaki K A N O Gidan wata tsohuwar k'awarsu Hajiya Balaraba Matar Depyty Givernor din Garin suka nufa, bayan long process aka ma su Hajia Mairo da Aliya wurin her Excellency. Suna haduwa suka hau shewa, chan cikin dakin suka k'ulle suna firan yaushe gamo, fira tayi dadi aka sako mulki, suna fira ne dan Hajiyar ya shigo, zaiyi tsaran Majeed, amma tafiya yake kamar dan shekara 15, Abun mamaki yaron nan be zame ko ina ba sai kan cinyan Mamarshi, ya daura kanshi a kan cinyarta ya fara zuba shagwaba. Wow Mairo ta shagala da kallonsu, duniya bata ga abun da ya burgeta ba kamar Hajia da danta, shagwaba yake ta zuba mata dai biye mishi take tayi, tace "Amjad ga wasu Mummies dinka nan, ka gaida su" sai a lokacin ya kallesu, da murmushi lan fuskarshi yace "My Mummies, ina Kwananku" Mairo baki har kunne ta amsa. Hajiya Balaraba tace "kun ganshi nan, shekararsa 29, amma ko budurwa be da ita" ya wani buga kafa kamar dan yaye yace "Mom nace miki ba zan yi aure ba, bana so inyi nesa dake, so na hakura da Auren" Hajia Balaraba tayi daria sosai, tace "kunji ko? Maganar kenan, bayan na gaya mishi in yayi aure a nan zai zauna yanda zau dinga ganinja kullum" ya wani mak'e kafada wai "uhm uhm". Haushi ya cika Hajiya Aliya, irin ya ma zaayi k'aton Gardi kamar wannan yayi ta sakata gaban su haka kamar me shan Nono, ita ko Mommy Mairo burgeta sukayi, ina ma Majeed zai dinga mata haka?. "Amjad" Mairo ta cire baki ta kirashi, ya kalleta, ta danyi jim kafin tace "ba zaka zauna haka ba aure ba, shekara 29 fa? Yaro na he's 28 amma har yayi aure, meyasa ba zakayi auren ba a kawo matar nan? Yanda ga Mom dinka ga Wife dinka? Uhm?" shiru yayi kafin yace "to, Mummy ki zaba min matar da kike so ta zama daughter inlaw dinki" Hajia Balaraba tace "really? Kai amma naji dadi, Hajia Mairo nagode da kika sa hankali a kanshi" . Mairo tace "haba Hajiya Balaraba, ai duk yi wa kaine, in ba damuwa ai ga 'yar wajena nan, Ziyada, na san zai sota" Mairo ta lalubo wayarta cikin jakka ta nemo hoton Ziyada ta mika ma Her Excellency" "MashaAllah, Amjad ka gani?" ta mika mai "Woww, ta yi Mom, ina so Wallahi" Hajia Mairo da takama tace "ai na san zata maka, saboda ta hadun ne" sukayi daria, yace "Mother Inlaw ina Matata? " dadi kamar ya shide Mairo tace "kar ka damu, Yayanta yaje daukota a Baze University, har nan zan kawo maka ita" Amjad ya girgixa kai yace "like every other princess, the prince go to her, itama ni zan zo gunta" . ya mike yace zamuyi magana da Mom, ku gaida gida, ya duka yayi pecking Mom dinshi ya fita daga dakin Mairo taji dadi har ranta. Hassadar Hajiya Aliya ya ki boyuwa a fuskarta, tafi shiri fa da Hajia Balaraba, amma Hajiya Mairo ta mata shigoshigo ba zurfi yanzu ya zatayi da diyarta da ta mata alkawarin auren Amjad? Mtsw, cewa tayi "Mairo tashi mu tafi Gida, lokacin dawowan yara yayi" Mairo tace "hakane, nasan su Zinatu ana hanya" Hajia Balaraba ta mike a dauko rafar dubu daya guda biyar ta basu, Mairo irin abunnan wai ki bari, ba zamu karban nan ba, tace donAllah ku karba, Mairo tace "Allah ya sauwake" ba tun yau ba Hajia Balaraba ta san Mairo da girman kan tsiya, Murmushi kawai tayi taba Hajia Aliya, Hajiya Aliya ta amsa tayi Godia, Hajia Balaraba tace "toh Hajia Mairo, sai munyi waya, Amjad zaizo" Mairo tayi Godia suka tafi. * Sai da Hajiya Aliya ta kawo Hajia Mairo har Gida, Hajia Mairo tana ta jiran Hajiya Aliya ta fiddo kasonta ta bata amma shiru, Mairo tace a ranta *kina karyan tsiya ne" hannu ta sa ta dauko Jakkar Hajia Aliya ta bude jakkarar, Hajia Aliya tayi saurin riko Jakkar tace "Yadai Hajia Mairo?" tace "kaso ma zan dauka" hajia Aliya da mamaki tace "kasonki kuma? Ba bakya bukata ba, ta baki kin ki karba" Hajia Mairo tayi tsaki tace "zancen kike so" ta dauka rafa uku, na ukun ta irga dubu hamsi ta hade da sauran ta maida mata sauran, ta rufe ta ajiye, ta kalli kawarta tace "kawas, mu yini lafiya ta bude murfin motar ta fita, hajia Aliya tace " Mairos, ba girman ki bane ba fa, kin fi karfin dubu dari biyu da hamsin" Mairo ba ta waigo ba balle ta amsata a ranta tace "ko dubu 10 aka bani yanzu hannu zan sa in karba". * Cikinta yayi kuka a karo na ba adadi, rabonta da abinci tun shekaran jiya da daddare, ruwa ma sai na toilet take sha, da ta fita sun dinga kyararta suna tsangwamanta, har rankwashinta Mummy tayi Jiya. Tana cikin yanayin nan sai ji tayi an banko k'ofar dakin da k'arfi, sosai ta firgita. Mummy ce da Nana ne shigowa sukayi, Mummy tace " Danubanki in ba dakin Uwarki bane fita, yau me daki zata dawo, ba zan yarda ku kwana runfa daya ba, bansan mugun abun da zaki mata ba" Najwa ta dago idanuwanta da suka soye saboda kuka tace "kiyi hakuri, ku bari Abdulmajeed ya dawo" Nana ta galla mata mari tana huci tace "Abdulmajeed din tsaranki ne da ubanki? Uban me kika ma Mijina da yake kwakwarki? Anki a barki din" Mummy tace ai darajarshi taci shiyasa ta kwana har 8 a gidan nan, kuma dai don kar in fuskanci fushinshi wallahi da na koreki daga gidan nan, amma dole ki koma boysquaters, shima yazo ayita ta k'are". "Zaki tashi ko ba zaki tashi ba?" shiru ta musu Ta riga ta galabaita, ta mika wuya suyi yanda zasuyi da ita, da sun san yanayin da take ciki da ko magana ba su sata ba, bata ankara ba sai ji tayi Mairo ta ja ta a kasa kamar wasu kayan wanki suka fita, ba ta bar janta ba, Azaba ma ya hanata kuka, sai dai ta lumshe idanuwanta. A ranta take cewa "Allah gani gareka, kila ma mutuwa zanyi, Allah ka sa Maama da Paapa su yafeni". Cikin hargowa taji ance "Mummy---" duk suka kalli Kofa, Majeed ne da Ziyada ne tsaye, da sauri Mummy ta saketa, Nana ta fara sosa k'eya, ba su taba zatan zasu iso da wuri haka ba, Majeed ya tako wurinsu yace "Mummy amanar da kika daukar mun kenan? Mummy ji yanda kike janta kamar wani abun da baaso? Haba Mummy, ina zaki kaita?" Mummy ko a jikinta tace "BQ zan kaita, Majeed saboda kai na barta ta yi tsawon kwanakin nan a gidan nan despite the fact that i dont like her, but na hakura saboda farincikinka, dont use your happiness to take me for granted, i wont take it anymore, Ziyada ta dawo dole ta bar mata dakinta". Daddy ya shigo gidan yace " Yadai meke faruwa? Ziyada sannunku da zuwa" Mummy tayi karaf tace "wanchan bakuwar nakeso ta koma BQ tunda yaro ya nace sai ta cigaba da zama a Gidan nan, ina laifi tunda nace ta koma BQ?" Daddy ya danyi Jim yace "Maryam Hakuri zakiyi, ba yanda zaayi ta koma chan ita kadai, mace ce fa? Yanzu zaki iya barin Ziyada ta koma BQ? Iyi Maryam?" Mairo bata amsa shi ba, ya cigaba da cewa "Kuma na tabbatar Ziyada bazata damu sharing daki da Bakuwa ba do you Mind Ziyada?" Girgiza kai tayi , Daddy yace "kingani Maryam?" Mummy tace "to wallahi dole yarinya ta fito ta dinga aiki don ba za mu dinga ci da katuwar banza ba". Ta kalli Ziyada tace " come with me my daughter" fuu ta wuce Ziyada ta bi bayanta. Daddy ya sauke numfashi yace "kuyi hakuri Majeed, ku kara hakuri" ya wuce daki, Nana ta wurge su da harara tayi daki. Majeed ya kalli Najwa da ke yashe a k'asa, gashin kanta ya rufe fuskarta, ya taka har gabanta ya tsugunna, kamar zaiyi kuka yace "Najwa i'm so sorry, ki yafe min, ban san haka zai faru ba". Da kyar ta dago kanta tace " Ya Majeed, ba laifinka bane, its nothing, kar ka damu" yace "me ke miki ciwo? Me kikeso?" a hankali tace "i am hungry" da sauri ya tashi ya nufa kitchen, flask ya dauko ya hada mata tea, anci saa akwai bread ya dauko mata ya kawo yace "gashi ki fara da wannan, kafin na dafa miki indomie, tashi kije daki " kai ta gyada, ta mike a wahalce ta tafi daki, ta fara cin bread din tana hadawa da tea din. ** Majeed wurin Mummy ya nufa, Ziyada ta mai nuni da yayi hakuri, ta tashi ta fita ta