Sashe 103
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rigima Ziyada ke ta ma Zaid tun tashin su yau da safe don ya sanar da ita Tafiar gaggawa ta kamashi zuwa Taraba, zai biya Kaduna ya ga Gidan Marayu kafin Jirginsu ya tashi zuwa Taraba's state. Ziyada tace ya tafi da ita, hakuri ya bata cewar tayi hakuri, ya dawo, da ya dawo zai musu processing Visa suje any country of her choice, sannan in sun dawo Gida zasu yi Parking su koma Gidan Babanshi na Asali a Kaduna, dolenta ta hakura amma taso ta bishi don bata son yayi nisa da ita. Alfarma ta rokeshi da ya barta a koma Gida har sai ya dawo, da farko k'i yayi, yace tayi hakuri ta zauna har randa zai dawo, tace "itadai aa, ba zata iya kwana ita kadai ba " ba yanda ya iya ya amince mata da taje Gidan, a daren da zai tafi, makale suke da juna kamar cingam, baya so ta bishi sabida bussiness zaije yi, da wuya ya samu time dinta. Washegari da kanshi ya rakata har Gida bayan an musu siyayya a Shoprite, sunfi Minti 20 a gaban Gidan cikin Mota suna manne da junansu kamar kar su rabu, shagwaba take ta zuba mai, shi ko yayi ta biye mata, "i'll miss you i'm My Forever" rungumeta yayi yace "i'll miss you more" sun dade a haka kafin daga baya ya rakata har Cikin Gidan, suka gaisa da yan Gidan banda Mairo da ba wanda ya lura be gaisheta ba. Daddy ya masa godian Hidiman da yakeyi dasu. Ziyada a boye ta share hawayenta da zai tafi, shima duk yaji ba dadi, ta zama wani bangare na jikinshi.
****
Najwa sunyi waya da Su Maama sun gaya mata Jirginsu zai tashi a ranar da daddare, but zasuyi transit a Dubai washegari su iso lagos, dadi ya ziyarci Najwa, ta musu fatan a iso a lafia.
B A Y A N K W A N A B I Y U
Tun daga garin Allah ya waye yake jin nauyin jikinsa, ya kanji kunnenshi yayi wani irin Yammm, hannunshi kan mai nauyi wurin dagawa, Da k'yar yaje Sallahr Asuba da taimakon AbdulMajeed ya dawo Gida, duk da shima yace be jin dadin jikin nashi, Hankalin Yaran Gidan ya tashi, Daddy da Ya Maji basu lafia, duk da ya Majin ba kwance yake ba, duk suka zauna suka rafka tagumi suna kallon Daddy. Mummy ta lallabasu suka koma dayan dakin tace "a bar Daddy ya samu bacci" da kyar suka fita suka barshi shi kadai.
kishingida yayi kan Katifarsa yana tunano abubuwa da suka shude shekaru sama da 20, ya tuna Mutuwar kaninshi da Matarshi, gawarsu da ya kasa shaidawa Saboda k'una, ya rufe kaninshi da Matarshi da hannunshi, wani side na kanshi ya buga kamar an kwala mai darma, da sauri ya girgiza kansa, runtse idanunshi yayi ya na son tunano exact abinda ya faru, sai ya gano Me ya faru da Sada da Yesmin in ba mutuwa sukayi ba? A hankali komai ya soma kwaranyo mai,
Kalamanta da abubuwan da suka faru suka so mai sintiri a kwalawa kamar a lokacin ake yinsu
"ina so ka maida sunan duk Takaddun nan daga Sunanka zuwa sunan Abba" ya tuna Sada be mata gardama ba yayi yanda tace yace "nagama" shi karan kanshi yaji mamaki, ya tuna da tsoro ya tambayeta "Meyasa? Don me zaiyi haka?" ya tuna tsawar da ta mishi tace "shuttup, baka son ka mallaka Dukiyoyin Sada?" yace "ai yana bani dukkan abun da na buk'k'ata, hakan yayi" ya tuna yanda ta girgiza kai tace "aa, beyi ba, kana son dukiyan Sada" ya tuna yanda ya maimaita abunda tace kamar karatu" beyi ba, ina son dukiyan Sada" murmushi tayi ta kallo Abba tace "good".
Ba a kwana ba ya tuna lokacin da ya ganta tayi nisa da tunani, ya tuna tambayarta
"Maryam tunanin me kikeyi haka?"
a takaice ta bashi ansan "tunanin Kashe Sada da Yesmin nikeyi" ya tuna yanda hankalinshi ya tashi cikin rudu yace
"Saboda mene Maryam? Sun ba mu duk abunda muke da burin samu a rayuwa"
"hakane, amma zamansu a doron k'asa barazana ce a rayuwata, shiyasa na yanke hukuncin kashe su"
Ya tuna yanda ya durkusa kan guiwowinshi ya na kuka yana rokonta gafara"Kiyi Hakuri Maryam, ba sai kin kashe su ba DonAllah, Sada danuwa na ne, kuma ina sonshi sosai"
Ya tuna yanda ranta ya baci tace "sai ka za6a ko ni ko shi"
Ya tuna yanda beyi dogon tunani ba yace "ke na za6a uwar 'yayana, ina sonki, kece farincikina, zan iya rabuwa da kowa don in zauna dake, amma Sada danuwana ne, akwai Babba Alaqa tsakaninmu, ina neman Alfarma da ki barshi raye,in bakya bukatar ganinsu zan sa shi su bar garin,amma kar a kashe su donAllah Maryam"
A kausashe tace? "in kuma hakan zai bani farinciki fa?"
Ya tuna muryarshi me cike da tsoro da rashin jarumta yace "da hannuna zan kasheshi don baki farinciki, amma ina rok'onki da kiyi hakuri" shiru tayi kafin tace "Zasu bar k'asan, zasuyi nisa da mu, ba zasu taba dawowa ba har duniya ta nade"
Ya tuna tashin hankalin da ya shiga da tace haka, ya tuna yanda ta daka mai tsawa tace
"Ko ka fi son a kashesu?"
Ya tuna yanda ya girgiza kai da sauri yace
"a saka su suyi nisa damu"
Ya tuna yanda ya durkusa har k'asa yana mata Godia kan amincewarta na ba zata kashe su ba. Ya tuna Komai, Ya tuna Wallahi, Maryam ta dadw tana zaluntarshi, Maryam ta shiga tsakaninshi da k'aninshi, wai kuma sai gashi bayan kwana biyu a ka kawo Gawarwaki guda biyu wai Yesmeen da Sada, Anya sun mutu? a baiyane yace "aa ba su mutu ba".
Maryam ta ha'ince ni, maryam ta zalunce ni, Kuka yakeyi sosai, be sama ma Yaranshi Uwa ta gari ba, k'arshen zamanshi da Maryam yazo, ba zai iya ba, a hankali ya tashi ya na dafe da bango ya fita waje, besan yanda zaiyi ba, amma yasan ba zai iya cigaba da zama dashi ba, don albarkacin yaransu, da ya maka ta Kotu.
A waje AbdulMajeed ya ga Daddy, yayi saurin karasawa gunshi yace "Daddy, ka bar jin jirin ne? Ka koma ka kwanta"
Mommy ta fito da sauri jin muryarsu, Duk yaran suka biyo bayanta har Hajjo, Mummy tace "Ah Daddy, har kaji sauki ne? Ta karaso gunshi zata taba shi yayi saurin janyewa, yace "kar ki sake ki tabani, muguwa Azzaluma" yaran suka kalleshi da mamaki, Abdulmajeed ya shiga rudu a hankali yace "Daddy..." Mairo bakinta a bude ta kasa magana, be taba mata haka gaban yara ba, ga mamakinsu sai ganin Daddy ya fashe da kuka ya zube kasa "Kuyi hakuri ku yafe min Yarana, ban zaba muku uwa ta gari ba, ku yi hakuri, na zaba muku jahila cikin jahilai a matsayin Mahaifiyarku" Ziyada ta fashe da Kuka, Zaineema da sauran Yaran ma suka fashe da kuka, AbdulMajeed ya rik'e Daddy yace "Daddy donAllah in Laifi ta maka ku shirya kanku, ku mahaifanmu ne, muna son ku duka, kuyi hakuri ku shirya kanku" Daddy cikin dan tsawa yace "In shirya da wannan hatsabibiyar? Tsakanina da Maryama Allah ya isa, ta shiga da tsakanina da
danuwana Sada, ta salwantar mun dasu" cikin Zafin Nama ya makuro Wuyanta "Ina kika kaimin Sada da Yesmin? Ina kika kai min su? Ina kikace su tafi? Ina Maryam?" a duk zatonta Zuciyarta ya fito daga Kirjinta, kasa motsi tayi, ganin komai take kamar a film, ta gama tsorata iyakan tsorata, karyarta ya kare, Asirinta ya tonu, Ajalinta yazo" Hajjo ta matso kusa dashi ta dafa tace "Haba Abba, me ya sameka haka? ina zata kai Sada? Ka manta Sada da Matarshi sun Mutu? Ka manta da hannunka ka rufesu? " da sauri yace "Wallahi basu mutu ba, basu bane, cikin makircinta ne tace sune, Wallahi ita ta salwantar dasu, Umurnin ta suka bi suka shiga dunia" Hajjo ta durkushe a gun tana kuka me tsuma rai, su Ziyada da Zaineema Kukan suke, Najwa da ta gama fahimtar komai ta fashe da wani irin dariyan da ya juyo hankalinsu, a baiyane tace "Alhamdulilah", duk da suna cikin tashin hankali kacokam suka bi ta da ido, da sauri ta isa gun Baba Abba ta rungumeshi tare da kwantawa kan kafadunshi, Baba Abba be da wani kuzari a kunne tace "Babana, kace Alhamdulilah" be san dalilin da ya sa ya biye mata yace "Alhamdulilah" daidai Sallaman Mutanen da ba zai taba Mance Mury
馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱
NA
Wattpad:@biebeeisa
Pg3鈨�8鈨�
Yaran Mairo gabaki daya sukayi kanta, Najwa tayi gun Maamanta a guje, Abba ya matso daf da danuwanshi ya ci burki a gabanshi, kallon kallo suka tsaya yi ma junansu, hawaye tuni ya wanke musu fuskoki, da sauri Sada ya karasa ya rungume Yayanshi, kuka suke a jikin junansu, Abba kamar zai shideta saboda kuka, Sadan ke bubbuga mai baya alamun rarrashi, har sai da ya tsagaita kukan, sake shi yayi ya karasa inda Hajjo ke tsaye tana ganin duk abunda ke faruwa kamar Mafarki, Sada ya tsaya a gabanta, yana hawayen farinciki, a tsorace ya sa hannunshi ya rik'o nata, lumshe idanuwa tayi hawaye na gangarowa kan kumatunta, shine, Sada ne, Autan ta ne, kafadunta ya rik'e, ya sa hannu ya share mata hawaye,聽 hannunta na rawa ta daga ta kai kan fuskarsa,聽 baki na rawa tace "Sada kai ne?" rike hannunta yayi da ke kan fuskanshi yana gyada mata kai,聽 "nine Umma,聽 nine Sadanki" "Allahu Akbar"cewar Hajjo, Maama ta matso kusa da ita ta rungumeta,聽 "Yesmeen,聽 ashe kuna raye?" wani kukan suka fashe dashi, sai lallashinsu Abba keyi.