Sashe 41
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 4 min read
DADE ANA YI....sai gaskia馃挱
NA
BIEBEE ISA
庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Wattpad:@biebeeisa
Pg2鈨�0鈨�
Mummy kwance a k'asa ita ba sume ba,
ita ba a mace ba, idonta k'ek'eshe, kamar
wacce aka tsungula, ta fasa Ihun "Waiyo ni
Mairo na shiga uku, wani dan kutumar Uban
ne ya sa aka rushe mana Kamfani, kuma don
Mugunta ya saida Filin, kai Allah ya isa,
kuma wallahi shari'ah mu dasu har k'iyama,
kotu zamu maka Macutan Maha'inta"
Majeed ya dagota yace "Mummy ki kwantar
da hankalinki, ki daina ihu hakan nan".
Cike da Masifa tace " kai min shiru, dont tell
me to calm down" kamar an tsikareta ta
tashi tsaye kamar ba ita ta zube k'asa ba,
tace "bani key din Motarka" Majeed yace
"Mummy mana" tace "Majeed, ka bani Key
din Motarka" ya ciro ya bata ta karbe ta fita,
ya bita a baya, kafin ya bi bayanta ta shige
motan ta sa lock, horn tayi Maigadi a bude
mata, ta sa kai ta bar Gidan, Majeed sai dai
ya tsaida me Adaidaita ya bi bayanta bayan
yace da su Ziyada kar su fito.
Bata tsaya ko ina ba sai *Abba Abu and
Son's Furnishing Company*, ta hango Daddy
tare da wasu suna maida zance, ba ta su
take ba, wasu k'arafa ta gani na electric wire
an zagaye wurin da su, ansa 'donot touch',
parking tayi ta fito a fusace, cikin daga
murya tace "wani daniskan ne ya msna
rusau?" hankali mutane da 'yan jarida
sukayo kanta, Daddy yayi saurin k'arasowa
gunta yana kiran "Maryam me kikeyi a nan?"
Daddy ka barni da Marasa Mutuncin nan,
watsattsu, ka nuna min uban da ya sa aka
rushe min Kamfani" duk yanda ya so janta
ya turata mota abun yaci tura, k'arshe ma
zuwa tayi wurin electric wires dinnan wai
zata fara cirewa.
Tsautsayi ya sata kama wire din farko, da
shocking ya jata sai da ya kaita bakin Titi,
ihu ta saka kamar sabuwar mahaukaciya, ko
da yake da k'yar ne in Shocking din be ta6a
mata k'wak'walwa ba, dama ko mayafi bata
dauko ba, dankwalin da ke kanta tayi
fancikali da shi, ta kamo wuyan wani
Mutumin da bata san ko waye ba ta dinga
lafta mishi duka ko ta ina, 'yan jaridu suka
samu rahotan dauka.
Majeed kamar ya sa ihu don takaicin
Mummy, isowarsa kenan, da ya bita nan sai
ta arta a guje, sai ya bita chan, abun haushi
ko dankwali babu kanta, da k'yar ya
kamota ya chusata cikin Mota ya ja Motar
ya wuce Gida, shikenan Mutuncin Family
dinsu ya gama zubewa, yana ganin Mummy
na bubbuge bubbugenta yayi banza da ita ya
k'yale..
*
Yau Kasuwa MashaAllah, ciniki
sukeyi sosai, ko mutum beyi niyan siyan
Zogalar Baba Hajjo ba, da ya ga Najwa sai
ya siya, wasu kan ce "Hajjo Mai zogala ina
kika samo Balarabiya?" Sai tayi murmushi
tace "Jikata ce" wasu yan zuk'i tamallen sai
suce ai ko ga kama nan" sai dai tayi daria,
din bata san ta inda suke kama da Najwa ba.
Nan da nan suka saida Zogalar nan tas, har
ana zuwa Cigiya, Hajjo taji dadi, tace to
"Tsohuwa tashi mu tafi Gida, an gama
saidawa" Najwa ta murmusa tace "wai
yanzu abin nan da dadi ne har Mutane ke
siya?" Hajjo tace "ke dai ba kin k'i ci ba,
dadi sosai ma" Najwa tace "ban sanshi bane,
ban taba ci ba" Hajjo tace "tunda yanzu kina
tare dani, zaki fara ci".
Suka mik'e suka fara tafiya, sai da Hajjo ta
siyo k'ulli k'ullin Gobe kafin suka samu
Motan da zai kaisu Gida, Najwa cikinta ya
fara kukan Yunwa, suka zauna zuru Jin
Radio, ba abunyi, Radion ma Batiran sun
mutu, Najwa ta zuba ido taga ko Hajjo zata
mata tayin Abinci amma shiru, kai ga dukkan
alama ba a daura sanwa a gidan ba, don
bata ga alamu ba.
Hajjo ta lura da Najwa, ta rasa yanda zatayi,
batayi tsammanin ba zata iya cin Zogale ba,
habar zaninta ta ciro cinikin dazu, ta irga
Naira 100, tace " ina zuwa" Najwa a wahalce
tace "kije dani" Hajjo ta gyara Zaninta a
kanta tace "yanzun zan dawo" bata jira
cewar Najwa ba tayi gaba, Najwa ta dafe
cikinta tana rok'on Allah ya kawo mata
Majeed, she's very Hungry, kuma baza ta iya
ce mata tana jin Yunwa ba.
Jim Kadan sai ga Hajjo ta dawo da Indomie,
murmushi ya subuce ma Najwa, kamar taga
Annabi don dadi, Hajjo tace "Dama na san
Yunwa kikeji, gashi ya k'i boyuwa a fuskar
ki" Najwa sadda kai k'asa tayi tana
murmushi, Hajjo ta cigaba da zolayarta tana
cewa, matsalar Farar Mace kenan, ana gane
farincikinta ko akasin haka ta fuskarta.