Sashe 8
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
聽 聽 聽聽 Kwanci tashi ba wuya gun Allah, yara suna ta zuwa Makaranta har sun kai Primary 5,idan Abdulmajid yazo na daya, Zaid zai zo na biyu, next term Zaid zai zo na daya AbdulMajid yazo an biyu, haka sukeyi.
Hazak'arsu na ba mutane Mamaki,聽akwai wani rana da Zaid na kwance kan cinyar Mamanshi, kamar an tsunguleshi ya mike yace "Maa, wani abu kamar Y din da ke kasan wuyana ciwo ne?" tayi murmushi tace "aa Zaid ba ciwo bane, Y ne ni, na maka shi da razor" ya zaro ido, yace "Maa, kin kusa yankani?" tace "aa Zaiduna, akwai dalilin da ya sa na maka, kuma idan na haifa maka k'anne suma zan musu" da alamun tambaya yace "saboda mene?" tace "saboda duk inda aka ganku an san ku 'yanuwan juna ne" ya dan yi nazari yace "kamar in kanina ya bace,idan mun kai girman Baba da Baba Abba da mun hadu zamu gane juna ko?" mamaki ya bata sosai, kawai tayi murmushi ta gyada kai, yace "to Maa, bazai goge ba?" tace ba zai goge ba har tsufa, baka san ana zane a fuska ba? Ko a ma mutum bille ko a mai fashin goshi, har tsufa ba zai taba gogewa ba, kaima naka kamar haka ne, amma naka a gefen wuya ne na zana maka 'Y' a bayan hannunka kuma na zana ma 'S',da sauri ya juya bayan hannunshi,yace "ina 'S' din?bangani ba" tayi dariya ta cire mai riga ta nuna mai zanen 'S' dinshi a wurin da ake Allurar rigakafi, yace "lahh, ya akayi ban taba gani ba?" tace "ya akayi ka ga na wuyanka?" yace "rannan ina duba mudubi nagani" tace "wannan kuma saboda kana sa riga, kuma hankalinka be kawo akwai wani abu a gun ba shiyasa baka taba gani ba" yace "Eh Mami,idan kin haifa min k'anenna, i will take care of them" tayi daria ta saba jin haka daga bakin Zaid, tace "to Zaid kayi ta Addua, Allah ya kawo masu Albarka" Zaid yace "Ameen, Maa 'Y'&'S'na nufin ke da Baba ko?" tace eh Zaid, kana da kaifin basira, "Allah ya sa har girmanka" yace "Ameen" haka ya cigaba daa mata tambayoyi ita kuma tayi ta bashi amsa.聽聽
*
A kullum burin Zaid be wuce yazo gidan Baba Abba ba,yana son Baba Abba, yana son聽 AbdulMajid,ba don komai yake son zuwa ba sai don k'anwar Abdul Zaineema da ke da shekaru 4, tun tana jaririyarta yake son ta, yana son yara, da yazo yake daukarta, in gaban Hajia Mairo ne sai ta daka mai tsawa, "Donubanka ka ajiyeta, kai yaushe aka gama daukan ka da kai zaka dauki wani? Salan ka kada min ita" dariya kawai zaiyi yace "Mama ai na iya daukanta, zainee bata da nauyi dagaske ba zan kada ta ba" Rankwashi take sake mai a kai, da sauri yake ajiyeta yana yak'e me kama da kuka, gobe hakan bazai hana shi daukan ta ba, baida zuciya ko kadan, so da yawa sai Abdulmajid yace "Zaid, donAllah聽 kar ka k'ara daukan Zaineema, bana so Mama na rankwashin ka akai, ka kyaleta, nima bana daukanta" Kamar Sakarai dariya kawai zaiyi bawai don yaji ba, abubuwan
da Mairo ke mai, in wani ne ba zai sake marmarin zuwa Gidan ba, gabanshi zata kira AbdulMajid ta bashi wani abun marmari, ta hana Zaid, sai dai AbdulMajid ya bashi a bayan idonta, ko kadan abubuwan da take mai bai damun Zaid, ko don yarinta ne be san kanshi bane oho.
聽 聽聽 Watarana sun dawo Makaranta, Zaineema na tashi daga bacci ta gansu suna wasa, da gudu ta dauko Zani ta nufo Zaid dashi, da yake itama sosai take son Zaid, cikin gwarancinta take cewa "Zaid, Zaid ka min babu" tashi yayi daga wasan da sukeyi da AbdulMajid, yace "Zo in goyaki" AbdulMajid yace "danAllah kazo mu cigaba da wasan mu, Zaineema kai ma Mama zanin ta goyaki" Ina Zaid beji ba, ya durk'usa ta hau ya zo daura zani kenan Zaineema ta subuce mishi ta fadi gwaram a k'asa, wani irin Ihu tayi wanda da ta ja ihun, sai da tayi seconds kafin ta sake shi, Zaid tuni ya kidime, nan da nan ya fara kuka, AbdulMajid yayi saurin zuwa ya dagota, yana cewa "sai da nace miki kije Mama ta goyaki,yi shiru" ina sam Yarinya ba tayi shiru ba, ihu takeyi sosai. Zaid ya kasa motsi, kuka yakeyi yana bin AbdulMajid a baya suka yi cikin Gida, daga ciki Mairo taji kukan Zaineema, da gudu ta fito, mai ya faru? AbdulMajid yace "Faduwa sukayi da Zaid" ba ta tsaya jin meye ba'asin ba ta hau Xaid da duka, duka bana wasa ba, dukan da ko kai babba akayi ma irinshi sai kaji jiki, balle yaro dan shekara 9, AbdulMajid ya dire Zaineema k'asa yaje yana kama hannun Mamanshi, saidai ta hankade shi, kuka sosai sukeyi duka su ukun, Zaid yana ta kuka har muryanshi ya dishe, kiyi hakuri "Mama, ba zan sake daukanta ba" ina Mairo bata bar dukanshi ba, duk fushi,kishi, jin zafi, hassada, da bak'incikin Yesmin da Sada da ta ke ta fa dashi fiye da shekaru goma, Mairo ta fanshe shi a jikin Zaid yau. "Kashe min ita zakayi? Eyi?in ta mutu ya zakayi? Zaka iya biyana? Ko an gaya maka juyar uwarka zata iya haifa man wata?(Tun bayan Zaid, Yesmeen ko 6atan wata bata sakeyi ba, Mairo ko kafin Zaineema, 6arinta 3, sa ma kanta damuwa da hassadar Yesmin ke barar da cikin).
Kamar daga Sama, Allah ya jefo Alhaji Abba, da alamu duk maganganunta a kunenshi, da gudu yaje don ceton Zaid, harda Mari lafiyayye ya ba Mairo, a razane ta kalleshi, yace "ba tun yau ba na san kin tsana Zaid, ko me ya miki wannan dukan yafi k'arfin shi, Allah zai saka mai" ya dauki Zaid ya sa6eshi a kafada, yayi lamo jikin Baba Abba, yana kuka a hankali, AbdulMajid na kuka ya bi Babanshi a baya. Bakinciki ya turnik'e Mairo, itama daukar Zaineema tayi tana mulmula mata goshinta da ya dan kumbura, amma har yanzu bata daina kiran "Zaid ba".
Gidan Hajjo Baba Abba ya wuce dasu don chan ya baro Yesmin, a Mota AbdulMajid ya gaya mai abunda ya faru, girgiza kai yayi yace "Mairo akwai Azzaluma, kayi hakuri Zaid Allah zai saka maka" yanda ya shiga da Zaid a hannu ne ya sa Yesmin faduwar Gaba, Alhaji Sada na nan shima zuwanshi kenan daukan Yesmin.
A tsorace suke su duka 3, Hajjo tace "lafiya? Me ya samu Zaid din?" karaf AbdulMajid yace "Mamanmu ce ta dukeshi don sun fadi da Zaineema" Yesmin ta kawar da kai don jin ba'asin dukan, ba tun yau ba ta ke lallashin shi kan hakuri da daukan Zaineema sai ya girma, amma bayaji, rai a bace Hajjo tace "sai ta bugeshi? Da gangan zai kadata ne? Meyasa Mairo bata da tausayine? Anya kuwa Abba, anya nan gaba zaa je gidanka?". Zuciyar Sada duk ba dadi yace " Aa Umma, ai laifi yayi, don ta hukuntashi ba wani abu bane, shima ina shi ina daukan Zaineema" Alhaji Abba yace "Sada Maryam bata da kirki, hakuri na ya k'are, wallahi nagaji da ita, ta maidani sakaran Namiji, don taga ina mata shiru-shiru, zan sauwak'e mata gaskia". Hajjo tace " ka sawwak'e mata, tayi hankali" da Sauri Sada yace " Aa danAllah, hakurin zaka cigaba da yi, da Nasiha da lallami zata daina InshaAllah " Hajjo ta kumbura tayi fam ba tace komai ba. Sada ya da cigaba da bashi baki har ya hak'ura,聽 kafin yace da Yesmin "Ki shafe shi da Robb, ai sai ku tashi ku tafi kafin Maghrib yayi, AbdulMajid mu tafi gida" Abdul ya mak'e kafada Alhaji Abba ya gane nufinshi, cikin bacin rai yace"zaka zo mu wuce ko sai na sa6a ma" Alhaji Sada yace "kasan dai ba zai yarda ba ko, kai dai kawai ka tafi".
Bayan komawarsu Gida, Yesmin ta dafa ruwan zafi, ta ma Zaid wanka dashi, lokaci zuwa lokaci yake sakin Ajiyar Zuciya, duk shattin hannuwan Mairo a jar fatarshi, muryarsa a dishe yace "Maama, ki haifa min jaririya kinji? Ba zan kada miki ita k'asa ba" wani kuka ya kubce mata, ta rungume danta, tana tausaya mai, tana tausaya ma kanta, ta son Mairo bata sonta bata son danta, Mairo na kishi da ita, Kishin Sauri wanda hausawa kece ma yafi Kishin kishoyoyi masu auren Miji daya Zafi (Kishin sauri:Kishin da Matan 'yanuwa{Matan Ya da Matan K'ani} ke yi da junansu).
聽 聽 聽 聽 聽 聽聽 BAYAN聽 SHEKARA DAYA
Alhaji Sada Abu mutum ne mai Amana da Gaskia,ga aiki da kwazo ba Ha'inci, Alheririkan Allah sai samunshi suke tayi ta k'ofofi da dama,baya ganin k'yashi yake taimaka ma gajiyayyu, duk mai ya ta6a Allah na dafa mishi. Alhaji Abba na aiki a wani board na Trust fund wanda samun aiki a gurin sai kana da mai maka Alfarma, Alhaji Sada ya sama mishi aiki gun, don yana da connections da yawa.
聽Bayan聽 gama Primary dinsu Abdulmajid, Alhaji Sada ya saka su a secondary boarding, makaranta ce mai ji da kanshi kuma sai dan wane da wane ke ciki wato HASSAN IBRAHIM GWARZO, yanzu haka suna chan JSS1 komai dinsu daya. Cikin Abubuwan Alherin da Alhaji Sada ya samu a shekarar nan sun k'unsa da Tamfatsetsen gidanshi da ya gama ginawa a hotoro, Gida ne Wakeke, wanda zaa iya ginin gida uku ciki,randa ya gama Ginin, rannan Ya Mallaka ma Alhaji Abu gidan ya tashi daga ciki, bayan ya mai gyaregyare duk da ba wani abun da ya samu gidan don du du gidan be wuce shekara 6 ba.
Sannan ya siya Shaguna 5 a bakin Titi ya rushe su ya Gina k'aton Shago inda zai zuba kayan Kafintoci, Shawara yayi da Abba na yana son Fita k'asar waje inda zai Siyo kayan aikin Kafinta, da kattakon su, ya zuba a shagon" nan da nan Abba ya bashi goyon baya na cewa ya tafi Italy su ke da irin kayyayakin nan, kuma ya bashi shawara ya tafi da Yesmin suna dawowa kawai sai su wuce sabon Gida, Sada ya Amince da batun Abba ko da ya gaya ma Hajjo ta sa ma abun Albarka, Yesmin ta ji dadi sosai, zata fita kasar waje, duk da tana zuwa Makka.