← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 128

Sashe 77

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bata damu ba tayi shiru, kanta a kasa har sukazo wurin Event din,Aunty Aynarh ma sun iso, wuri yayi guri, taro yayi taro, kowa ya hallara, chan na聽 hango Alhaji Abba Abu da makaraban shi, Baba Ado ma haka,聽 daga wani bangaren kuma Mairo ce sai fadi takeyi don ta samu yan kwarako su hajia Aliya, chan na hango su Sholingaye da Mrs Splendid suna fadi don sun zo bikin yan gata,聽 hanayen su dankare da zoben zinari wuyansu kuwa Sark'an gwal ne,聽 yan ZBI members ma ba a bar su a baya ba, ga hafseen inda rai da cutielurv sai zara ido suke burinsu a fara chop,聽 wurin dai shak'e makil da duk wasu masoya na ADAY.

MC tagwaye ne MC,聽 bayan ya bada labari aka dan dara ya sanar da kowa a mik'e saboda shigowar Amarya da Ango,聽 duk aka mik'e a na jiran shigowar su,聽 kasancewar聽 baza ayi Bridal Train ba daga Amarya sai Ango zasu shigo.
Daga waje,聽 Armstrong ne yazo daidai saitun kunne Zaid yana mai rada kan "Please dont make any scene here,聽 i beg you" da kyar Zaid ya fito daga Mota, Aunty taatuh ta dan gano "something is not right,聽 sai kace ba auren soyayya ba?聽 Duk tasan shi Zaid din wani irin mutum ne,聽 amma abubuwan聽 da ta lura dashi na nufin wani abu" share wa tayi dai suka fito da Ziyada.

A jere suke tafia,聽 duk聽 da ba su rike hannye ba sunyi kyau sun bada maana matuka, shiga hall din sukayi,聽 sansanyar waka me taushi me ratsa zucian masoya ya karade hall din,聽 tafia suke a kasaitance,聽 shaharrarun masu hotuna kamar AhmedZol da GeorgeOkoro suka fara aikinsu,聽 Amarya da Ango suka cigaba da tafiya har mazauninsu suka zauna, abun yayi ban shaawa,聽 ba wanda ya take musu baya.
Tun shigowarsu Najwa ta kura ma Zaid ido,聽 bata san dalilin faduwar gabanta ba,聽 ta san fuskar nan, tabbas ta san fuskar nan a wani wuri to a ina?.
Daidai llll wani matakalan benen da zai sadasu da kujerun da aka tanada dominsu Ziyada tayi missing step daya,聽 tangartangar tayi zata fadi, be san lokacin da yayi saurin tarban ta ta baya ba tare da fadin "i got you" sai da ta gyara tsayuwarta kafin ya saketa,聽 daga baya kuma ranshi ya baci,聽 duk yaji haushin abun da yayi,聽 don me be barta ta sha kasa ba? Dama ya barta ta fadi" duk ya bi ya tsani聽 kanshi,聽 juyawa kawai zaiyi ya bar gurin nan,聽 ba zai iya ba.

Ji yayi kafanshi ya mai nauyi,kamar an sa magnet an rike mai kafa,聽 sai da Ziyada ta rigashi zama kafin ya karasa ya zauna kan kujerar alfarmar gefenta,聽 nan aka shiga yi musu聽 hotuna,聽 fuskar Zaid a daure, amma da yake shi mai kyau ne,聽 baa gane labarin dake kan fuskarshi.
Nan MC tagwaye ya cigaba da gudanar da program of events, a ka gayyaci Amarya da kawayenta suzo suyi rawa,聽 nan aka dinga yaba kyaun kawayen Amarya da suka fito cikin maxi gowns dinsu,聽 sun bada kala da suka sa Amarya a tsakiya, daga bisani aka kira Mothers din Amarya nan Mairo da kawayenta suka fito suna wani irin rawan bariki,聽 kamar ba uwar Amarya ba,聽 Abdulmajeed聽 ina ma k'asa ta bude聽 ya shiga don kunya,聽 rawan da Mairo keyi ba girma dai,聽 abun kunya,聽 sai da Hajia Aynarh ta rada mata a kunne聽 "kedai ba girma,聽 ji wannan rawan da kike gaban surukai,聽 wannan ba wayewa bace" Mairo kamar ta faska mata mari a ciki,聽 amma ganin zata jawo abun kunya聽 don public suke, kuma press na nan yasata yin Murmushi聽 sai abun yayi kama da suna shiri.

A ka kira Zaid da Ziyada Zsquare kamar yanda MC tagwaye聽 ya laka musu, ganin yanda yake shan kamshi ya sa batayi yunkurin tashi ba,聽 sai da ya tashi don karan kanshi, kafin itama ta tashi,聽 suka je sukayi tsaye a dancing floor, wak'an *Rihanna work* aka samu su, ba wanda ke rawa cikinsu, tsaye dai sukayi, wakan taushi sai tashi yakeyi, kamar an bashi umurni ya sa hannu cikin aljihu ya ciro bandir din naira dubu, kamar yanda yaga akayi dazun ya shiga zuba mata a jiki, ya karar ya sake ciro wani ya lika mata.聽 Wannan abun da yayi ya burge Mairo,聽 nan ta shiga hura hanci burinta ya gama cika,聽 ko ba komai Zaid ya siya mata mutunci gun聽 kawayenta. MC tagwaye yace "Mr Zaid,聽 lead your wife here,聽 its time to cut your Wedding cake" ya nuna musu Cake dake daga gefe, Zaid yaji takaici, amma聽 ji yake kamar ana ingizashi,聽 baya kasa yin gardama ga duk abunda akace yayi a hall dinnan,聽 anya mutanen nan sun barshi haka, duk yanda yakeso ya bar gurin ya kasa,聽 besan ya akayi ba amma ya tsinci kanshi da kamo hannunta ya ja su聽 suka nufa inda 3steppedcake dinsu yake,聽 da taimakon聽 mutane suka聽 yanka cake din,聽 aka ce su ciyar da juna,聽 nan fa daya,聽 babu yanda zaayi yaci abunda be san wa yayi shi ba,聽 ya yanka ya matsa kusa da ita daidai kunenta yace "i'm sorry i cant eat this,聽 bansan wa ya yi ba" ya sa mata cake din a baki,聽 a kunyace ta karba ta sa a baki, akace "Ziyada,聽 feed your husband" gabanta ya fadi,聽 kar fa ya bata kunya,聽 idonta ya kai kan wani Bottle water da cup, tunda baya cin abunda be san waya yishinba,聽 shes sure zai sha ruwan da ya saba sha,聽 a yangace ta karasa gun ta dauko Robar ruwan da Kofi,聽 a ranta tana adduar kar Zaid ya bouncer ta,聽 ta bude ta tsiyaya a cup,聽 a yangance ta kai cup din bakin shi, kamar bazai karba ba ya karba, ji kake raf raf tafin mutane,聽 sosai hakan ya bada maana, MC yace "Zaid yaje ya bar matarshi,聽 don zaa gayyata Family dinta dancing floor" kamar jira yake ya wuce yaje ya zauna,聽 kamar MC ya sani be ce abokan Ango suzo suyi rawa ba,聽 don be da Abokai,聽 kila sai dai su Baba Ado聽 su fito a madadin abokan lol.

Aliyu Abokin Abdulmajeed聽 ya ja AbdulMajeed聽 har inda su Zaineema suke da Najwa don da cewa yayi ba zaije ba, Abdulmajeed ya riko hannun Hajjo, Zaineema聽 ta rike hannun Zinatu da tun dazun ake rawa,聽 Zinatu ta kamo hannun Muhsin suka nufa Dancing floor inda Ziyada ke jiran zuwansu,聽 har sun kusa聽 isa gun Muhsin ya kwace hannunshi daga hannun Zinatu ya聽 ruga a guje inda Najwa ke zaune ya ja hannun Najwa,聽 Najwa na girgiza mai kai tana "please Muhsin let me go" yace "No,聽 you are family" bata da wani zabi da ya wuce ta bi bayanshi,聽 nan suka聽 rike hanaye suna zagaye Ziyada Aunty Aynarh ta zo ta musu liki,聽 Mairo ma haka, da kyar Daddy yayi joining dinsu, ganin Family dinta wuri daya cikin farinciki ya sata fashewa da kuka ta rungumo YaMajinta,聽 rungumeta yayi yana lallashi,聽 shhh kar ki bata kwalliyanki mana" Zinatu ma ta fashe da kuka,聽 duk tauri rai na Mairo sai da tayi hawaye,聽 da kyar aka lallashesu suka koma mazauninsu.
Sai next agenda wato REFRESHMENTS.
Ehen,聽 lokaci yayi na chop, babban makasudin zuwan yan ZBI da bibiliciouswattpadiansfans kenan,聽 sai da aka fara da Appetizer

锟�

Kafin aka gabatar daAbinci kala kusan 4, da chapman,聽 abundai sai wanda ya gani.

锟�

Walima dai yayi walima Zaid ya mike shi ya gaji,聽 ya ma yi kokari cewar Baba Ado,聽 ban yi zaton zai tsaya haka ba, tana ganin ya mike itama ta mike,聽 to ina zai tafi ya barta,聽 kafarshi kafarta, suka bar hall din,聽 Yan ZBI suka bukaci a sa musi wakar Ado Gwanja, nan suka shiga kwaso Shoki.

Yana tafia ya zaro wayarshi,聽 "Come get me home Arm?" Ziyada ta yi turus,聽 to ai ba zata bishi ba, murya a disashe tace "MyForever" chak ya tsaya,聽 tace "ina zaka?" be amsata ba yayi gaba abunshi turus ta tsaya "me聽 hakan ke nufi?聽 "Ya gaji ne,聽 kila kanshi ke ciwo" cewar wani sassan zuciyarta,聽 da sauri ta mai uzurin gajia ne,聽 zuciarta na gaya mata Zaid ya chanza,聽 amma bata so ta yarda,聽 tafi so ta mai uzuri,聽 Armstrong聽 yaji tausayinta ya karaso gunta,聽 yace da su Idi ya shiga ya gaya ma Aunty Taatuh Amarya na waje.聽 Hakan ko akayi,聽 Aunty Taatuh najin takaicin聽 yanda Zaid ya bar Amarya Waje,聽 Thank God聽 ma ba wanda ya lura da ita,聽 ta ma Aunty Aynarh Magana kan cewa tazo su maida Amarya Gida.聽 Haka dai aka watse aka bar Dj da yan ZBI members (lols).

WasheGari Asabar.
Chapter 77 · 0% Book details