Sashe 62
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
da dangana, InshaAllah zan zo Bayan Laasar na dauke su" haka sukayi Sallama. B e san tsawon lokacin da ya dauka a haka ba, yaci kuka har ya gode ma Allah, rashin aikinyi ya fi daga mai hankali, yanzu in suka bar Gidan nan, ya rayuwansu zai kasance? Abinci zai musu wuya? Ya zaiyi ya kula da Mahaifanshi da k'anen shi? Hannu biyu ya daga sama yana rok'on Allah sauki a lamarinsu, kafin ya tashi ya dauro Alwala don zuwa Sallahr laasar. A gajiye ta shigo Gidan, ranta a bace, kafin ta dawo gida sai da ta biya Gidan Hajiya Aliya kawarta, tarban da ta saba mata ba irin shi tayi mata ba, ta gaya mata yanda sukayi da Matar SSG Hajiya Aliya bata yi mamaki ba, Mairo ta bukaci dubu dari biyar gun Hajia Aliya don ta koma gun Bokansu don ya mata maganin damuwarta duka, Hajia Aliya ta juya mata baya, nan suka hau sama sukayi zage zage tare da tona ma junan su Asiri, karshe dai yaran Hajia Aliya suka ma Hajiya Mairo rashin kunya da wulakanci suka wurgota waje, Daki ta wuce straight tana zuwa ta zube kan Gado, komai ya juye mata, bata da kowa, bata da Mafita, bakin cikinta a saida tangamemen Gidan nan, anya ba zata kira Alhaji Nakowa ta nemi sauki gunsa ba? Kar dai ya ga gajiyawarta ya rainata, Tsaki tayi ta fada toilet da tunani dubu dari da chasa'in a kwanyar kanta. Na'eelah ta zagaya baya don kiran Zaid a waya, tun jiya ba su hadu ba, Ringing daya ya dauka, a lokacin ya koma makeup wurin Rita Phillips, kamar bazai dauka ba yayi excusing kanshi ya dauka, cikin yanayinshi yace "Eelah" tace "akwai Matsala, Dad dina ya gano ina Kano, ranshi ya baci, yace in dawo Gida, kar ma in sake inje PH, already ya min Booking ticket,yana expecting dina a Abuja by 8, i'm scared, he sound soo serious, kana ina Z?" cikin rashin damuwa yace "then ki koma, just write them a note, tell them zaki je Kauye dubo Danginki, in kin ganesu, zaki dawo ki tafi da Nura, su taimaka su kular miki dashi kafin lokacin dawowarki" tace "nagane, so yanzu yaushe zaka dawo Gidan, ina ganin Sun rasa case dinsu na Court, Majeed ya dawo hankali a tashe, yanzu ma Mom din ta dawo, daga gani Plans dinka are in place, I want to see you kafin na tafi please" ya danyi guntun tsaki, yace "makeup ake min, kinsan ana daukan atleast 5hours anayi, i'll come see you a Abuja As soon as Possible" cike da kwantar da murya tace "Please, let me see you before i go" dan shiru yayi, ya ga ta taimaka mishi sosai, kuma tana sonshi, bawai don tausayinta ba, sai don ya rama mata halacin da ta mai, don shi beson zama indebted to others, yafi so in ka mishi abi ya rama maka, yace "Ki rubuta wasikar, ki aje inda zasu gani, i will send Arm to pick you up" be jira cewarta ba ya kashe waya. Wayar ta bi da ido, tana ba kanta tausayi, a fili tace "Ina sonka Z, sonla ya makantar dani, ina abubuwa marasa kyau don kai, har cutar da bayin Allahn nan mukayi wanda zuciyoyinsu ba komai sai tausayi, Allah ka yaye min son Z, Allah ka yafe min, da sauri ta chusa wayar tsakanin ta, ta waiga baya taga ba kowa ta wuce ciki don rubuta wasikar. Najwa ta fito daga maboyanta, tunda taga Naeela ta zo baya ta biyota, zarginta ya tabbata gaskia, Naeela da Nura ba abunda sukace sune ba, Iphone 6 ke hannun Naeela, aiko ba karamar mutum bace, kalamanta na waya tayi amanna da Nura take, saboda tayi amanna be gidan, kuma ta dan fahimci wani abu, Nura shine ke son wani abu da Familyn su Majeed, ita Naeelah kawai tana taimaka mai ne saboda tana sonshi, ta jinjina kai, InshaAllah ba zasu ci nasara kan Majeed dinta ba, zatayi protecting dinsu InshaAllah, da taimakon Allah zatayi exposing Nura Kirikiri, a fili tace "Allah ka taimakeni". I N D I A Tunda ya dawo aiki, kanshi ke sarawa, zama yayi kan sofa ya dafe kanshi da duka hanayenshi, yana so tunano wani abu,tunanika kala kala suka shiga dawo mai a hankali, amma ba zaice ga abu daya k'wak'wara ba, ya dan gano wani abu, shi dai ya san yana da Danuwa daya da kuma Mahaifiya amma sam kamaninsu sun bace mai, haka kurum yaji yana son zuwa Nigeria gun Matarshi da Yayanshi, bayan nan ba zai iya baiyana me yake ji ba, haka Maama ta iske shi, itama duk wani sukuku take, "Sannu da Zuwa Papi" cikin yanayi yace "Yesmeenah, ina so naje Nigeria" ta numfasa tace "wallahi ,tun da na tashi nake jina wani iri, sai tunanin Gida nake, Ko Umma na da Abbana suna da rai? Ko sun bar Adamawa?" ita atleast ta tuno nata Mahaifan, ta kuma gano inda suke, bayan nan ba abunda zasu iya tunawa game da Dangin Sada ko Garin da Sada ya fito, kwantar mai da hankali ta hau yo tace "Papi, mu cigaba da Addua, yanda muke iya tunasu, a hankali komai zai dawo mana, InshaAllah, mu k'ara hakuri, Muje kayi wanka na kira maka Diyarka ku gaisa ko?" kamar dan yaro ya gyada kai, ta kamo hannunshi suka shige daki. tart from the beginning K A N O Kan Idanunta Naeela ta shiga wata Mota bak'a, nan zarginta ya tabbata, they are not what they say they are, sunada wani mummunan k'udiri, to wa zata fara sanar mawa? Majeed? Ko ta gayama Hajjo? Amma ai bata da wani Hujja, jiki sa6ule ta shiga cikin Gidan, akwai Mutane amma kamar ba kowa, chan dakinsu ta shige. ** Hajiya Aynarh tayi Sallama a k'ofar Parlor, kowa duk na dakinshi, ganin sunyi nisan kiwo ne yasa ta daukar Waya ta kira Alhaji Abba, a lokacin yana toilet, Mairo jiki ba kwari ta dau wayan, ganin Hajia Aynarh ne ya sata dauka rai a 6ace "Hello Alhajina" Mairo ta fusata tace "Alhajin Ubanki, munafuka tsohuwar kilaki, zaki kira min Miji kice mishi wani Alhajinki?" Hajiya Aynar ta murmusa tace "Fito Parlor ki gaya mun duk abunda kike son fada min a fuska na, amma ki kula, kwanan nan, saurin hannu ne dani, abu kadan sai in mari Mutum" dip ta datse Wayan, ta bar Mummy da takaici, oh tana ma Gidanta? A Parlornta? Aiko yau za ta sauke ma Hajiya Aina duk wani abu da ke kanta, yau sai taci Ubanta, da sauri ta dira kan Gado ta fita Parlo a fusace. Daidai da fitowar Majeed, kallo daya Zaka gane yana cikin damuwa, ganin Hajia Aynar sai ya fadada murmushinsa, ya k'araso, daidai da isowan Mairo, ta ja ta tsaya, bata son abunda zai k'ara ta6a Majeed, Yaron ya ga rayuwa, abunda tayi niyyan yi ta fasa, juyawa tayi, yana Hangota ya kirata "Mummy" cikin sanyin Jiki ta k'araso, ta zauna, duk aka gaisa da Hajia Aynarh har Daddy ya fito, Hajiya Aynarh tace "Ina Yaran nawa? Suzo mu tafi ko?" Hajia Mairo ta wurga mata wani kallon ina zaki dasu? Cike da Kissa Hajia Aynarh tace "Hajia Mairo, dama gani nayi tunda yaran nan basu san meke faruwa ba, why not in dauke su mu tafi Gidana, yanda Tashin ku ba zaiyi affecting dinsu sosai ba?" Mairo ta galla mata harara tace "Sai kuma nace miki ina bukatan taimakonki, yarana yarana ne ni kadai, ni zan kula dasu, ni zan san yanda zan kwantar musu da hankali, kuma zanyi kai dominsu, ba zamu ta6a loosing Gidan nan ba" Majeed ya daure fuska yace "Mummy, Please Not now" Daddy yace "jeka hado musu kaya, har Uniform, tace daga Gidanta zasu dinga Zuwa Makaranta" ba gaddama Majeed ya tashi ya shige dakin Yara. Ya gansu zaune suna kallon Cartoon, yace musu "Kallo akeyi? Wa zaijr Gidan Aunty Aynarh? Muhsin yace "Niiii" Zinatu tace "bani ba" Majeed ya samu wuri ya zauna kusa da Zinatu yace "Tab yarinya zakiyi Missing, kinga Gidan Aunty Aynarh kuwa? Babba, harda Swimming Pool, kuma ana cin Dadi, gashi kullum sai taje Shoprite, zata siya muku teddies da sauran kayan wasa Woww, nima da zata je dani da naje, amma tace da ku zata tafi" wani sashe na Zinatu na son zuwa ko don abubuwan da Mom dinta ta saba musu dasu lokacin suna Abuja, tum bayan dawowan su Kano komai ya chanza musu, tana son sake experiencing irin wannan jin dadin, a hankali tace "Ok, zanje" Majeed ya sa tafi kamar dan k'aramin yaro yace "Ok lets get your things ready, kowa ya fito da kayan dayake son tafiya dasu" duk suka tashi suka harhada, a wani katon akwati suka fita. Har Zinatu suka fada kan Hajia Aynarh suna rungumarta, daria take tana musu magana, Sai da Gaban Mairo ya fadi ganin wannan katon Akwatin, gani takeyi kamar Hajia Aynarh rabata zatayi da 'Ya'yanta, kafin tayi Magana karaf Hajiya Aynarh tace "Ina Mama(Hajjo)?" Majeed yace "bata dan kinzo ba, barin sanar mata" da sauri ta sauke Muhsin daga Jikinta tace "Nooo, barin shiga na gaisheta" hakan ya ma Daddy dadi, yana son yanda take girmama Uwarshi, Jagora Majeed ya mata har Dakinsu, ya tsaya daga waje. Ziyada na ganinta ta mik'e ta rungumeta, bude ma Najwa hannu tayi itama, ta rungumeta, kafin ta durkusa har k'asa ta gaida Hajjo, Hajjo baki har kunne, ta kalli Ziyada tace "Oya taso ki shirya, nazo tafiya da ku ne" Ziyada ta murmusa tace "Ok" ta fita don zuwa dakin da Zaineema take, Aynarh tace "Mama kema ki shirya mu tafi" Hajjo tace "ayi haka, ni ki barni nan" Aynar harda bubbuga kafa kamar karamar yarinya tace "nidai gaskia Mama ki taho mu tafi, kinsan yaran nan basu san me ya faru ba, damuwa zai damesu, shisa zan tafi da su duka don su rage wasu damuwan" ta kalli Najwa tace "Baby ina kayanku? Duk mu tafi" Najwa ta murmusa, duk runtsi ba zata bar Gidan nan ba, har sai ta tona ma Nura Asiri, tafiyarta na nufin Nura zaici galaba akan duk wani abu da yayi niyar musu, tace "Aunty ga kayan Hajjo nan, ni i cant leave due to some reasons,