← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 128

Sashe 40

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wayarta ta dauko ta latso Majeed, ringing
daya yayi ya dauka "Hello zuzu missing
me?" cikin murya "Yamaji ka dawo Gida, in
ba so kake su kasheta ba, ka rabata da
gidan nan" da sauri yace "Najwa? Me suka
mata? Mummy ce ko?" yanda taji shi a rude
ya sa ta cewa "kawai kazo Gida".
Cikin Mintunan da basu wuce 15 ba sai ga
shi ya dawo, a kidime, yana tambayar Ziyada
meyafaru? Ziyada ta warware mai abubuwan
da suka faru tun bayan fitarshi, Sosai ya
tausaya ma Najwa, Ziyada tace " YaMaji,
kai da ka kawo ta Gidan nan don ka kareta
daa sharrin Mutane, an gudu ba a tsira ba,
YaMaji tana da hakuri, kar ka tauye mata
hakki, ka rabata da gidan nan, don zaifi a ce
tana wani wuri da gidan, coz Mummy da
Nana are not going to stop matukar suna
ganinta a gidan nan".
Tabbas ya san maganar Ziyada hakane, dole
ya rabata da gidan nan, yar gata ce, ba
baiwa ba, ya sake kallonta, har yanzu idonta
a lumshe suke, ya kalli Ziyada yace "Ki dan
zaban mata kaya, ki sa mata a jakka, shes
leaving this house" Ziyada ta mike ba tare
da tace komai ba ta shiga zaban mata kaya,
kala 5 ta bata, ta taimaka mai ta kaita
Motaa, duk a idonsu Mummy, be bi takansu
ba. Suka fita daga Gidan.
Tuk'i yakeyi a hankali, be da inda zai kaita
da ya wuce chan, anfi shekara 5 rabon da
yaje Gidan, duk da yana son zuwa amma
zuciyarshi na nuna mai ba kowa a gurin,
inda yake son zuwa is just an empty place,
duk da ya san akwai mutum a ciki, amma sai
yaji baya son zuwa, ba shi kadai ba, harta
Daddynshi ya kance mai yana jin wannan
yanayin, so da yawa sun sha kamo hanya su
zo gurin amma sai tsautsayi ya samesu, ko
taya ta fashe, ko wani abu ya faru a gida
wanda zai so dole su juya. A ranshi yayi
Addua, Allah ya bashi ikon zuwa yau. Binibini
yake kallon Najwa ta mudubi, chan kawai zai
kaita ta samu sukuni. Be ankara ba sai
ganinshi yayi a k'ofar Gidan, Hamdala yayi.
Ya kalli Najwa da har yanzu idanunta a
lumshe suke yace "Ina zuwa, barin shiga ciki
in ga tana nan" kai kawai ta gyada mai. Ya
bude ya shiga gidan da Sallama, Ba abunda
ya chanza na daga gidan sai dai tsufa da
gidan ya karayi saboda rashin kula, Majeed
duk sai yaji ba dadi yanda sukayi forsaking
dinta, Sallama ya k'arayi, da mamaki wata
tsohuwa ta fito daga baya tana amsa
Sallama baki na rawa tace "Abdallah" kai a
k'asa saboda Kunya yace "Naam Hajjo" tace
"yau kaine a gidan nan?" Girgiza kai yayi
yace "Hajjo ki yafe mana, donAllah"
murmushi tayi tace "Abdallah ina Abba?
Yana lafiya? Ya yanuwanka? Ina auta zinatu
nasan tayi wayau yanzu ko?" kwallah ya
cika mai ido, yanzu Hajjo bata san an haifi
Muhsin ba? Muhsin na da shekara 5, anya
Allah zai bar Daddynsu kuwa? Ya san a
yanzu suna fama da kansu ne, amma Ji
Mahaifiyar Daddynsu kamar Almajira, duk ta
tsomare ta rame tayi duhu, Me ya faru da
sauran shekarun da suka gujeta? Inallilahi
wa ina ilaihir rajiun, Allah ka yafe mana,
Allah kasa mu zama masu jin k'ai
Mahaifanmu, a karon farkon da ya tsani
Halaiyar Mummynshi, ya san duk laifinta
ne,da wayanshi so da yawa Hajjo zata zo
Gidansu Mummy ta mata Wulakanci akan
idon Daddy amma be da ikon magana. Duk
kunya ta rufeshi wa zai yarda wannan ce
Mahaifiyar Abba Abu? Su da basu san cinta
ba su san lafiyarta ba, ta ya zai kara mata
nauyi? Dole yayi setting komai daidai, dole
ya gyara kuskurensu na baya, duk da suna
fama da kansu ba zasu kara banzatar da
rayuwanta ba.
"Abdallah yadai me ya sa ka kuka?" "Hajjo ki
yafe mana, donAllah" Murmushi tayi tace "ba
kuyi man komai ba" kuka yakeyi, karar
Wayarshi ne ya katseshi, Hajjo tace ana
maka waya, matsawa cahn gefe yayi ya
dauka Daddy ne, ya dauka da Sallama jin
muryan daddy yayi cike da tashin hankali
yace "Daddy lafiya?" Abdulmajeed, Yan rusau
sun rushe mana Company, yanzu wurin fili
ne, kuma wani yazo da takardun filin wai
filinshi ne" Inalillahi wa ina ilaihir rajiun
Majeed yake furtawa, hankalinshi a tashe
yace "Daddy gani nan zuwa, calm down, ka
gaya ma Mummy? Daddy yace "Aa na kasa"
"to gani nan zuwa, Calm Down Daddy".
Hajjo tace lafiya Abdallah? Murnushi ya
kwakulo yace " lafiya Hajjo, Bakuwa na kawo
miki ta tayaki zama, zan dawo InshaAllah,
wani abu ya taso yanzu" Hajjo tace
"Matarka ka kawo min? Tana ina?" yayi
murmushi yace ba matata bace, kawar zama
na kawo miki, tana mota, barin shigo miki
da ita, fita yayi sai chan ya dawo da Najwa,
Najwa kamar me koyan tafiya, daga Nesa
Hajjo ta kura mata ido, da murmushi tace
"Ziyadatu haka kika girma ko? MashaAllah"
Majeed yace "ba Ziyada bace, ashe ba ni
kadai nake ganin kamarsu ba" "to wacece?"
Majeed yace "sai na dawo Hajjo, zan miki
bayani, Najwa you are staying here for
sometime, shes my Grandmother, help her
with the housechores take care sai na dawo"
sauri sauri Majeed ya fita daga gidan.
Najwa ta bude ido a hankali ta zubesu kan
Hajjo, yanzu bata jin yajin a ido suka kura
ma juna ido, a tare suka sakar ma juna
murmushi, Hajjo ta miko mata Hannu, Najwa
ta amsa tana jin matar har ranta, tace "ki
zauna a nan kinji Jikata, zan fita sanaa in
dawo, ince bakya tsoron zama ke kadai"
Najwa tace "ina tsoro, kije dani" Hajjo tayi
murmushi tace "da kin zauna, rana zaki
kwaso kawai gashi a gajiye kike kuma da
alamu idonki ba lafiya?" Najwa tace "ina
zakije?" "talla zani" Najwa tace "Meye
Talla?" Hajjo ta murmusa tace "wurin saide
saide" Najwa tace "me kike saidawa?" Hajjo
tace "Zogale" "meyene Zogale?" Hajjo tayo
dariya tace "naga alama wannan matar so
kike ki sani latti" ta kwaso robobin sannarta
ta harhada komai duk a idon Najwa, wani
abu tagani kamar leave, bata san meye ba
dai, a ranta tace "shi zata sayar?" Hajjo tace
"to na tafi, sai wurin laasar zan dawo" Najwa
tace "da ni fa zaki" Hajjo tace "da dai kin
zauna" Najwa ta karba Roban Hannun Hajjo
tayi gaba tace "ko ki zo mu tafi ko na tafi ni
kadai na bace" Hajjo tayi daria tabi bayan
Najwa, tana jin Son Najwa har ranta, ji tayi
kamar sun shekara tare.
Wani Ihun da Mummy ta sake ya sa duk
suka taru Parlor, zaune tayi dirshan a kasa
kamar yar bori, kowa na tambayan Mummy
me ya faru? Ba ta amsa su ba sai sambatun
da take tayi.
"Shikenan tawa ta sameni, ta kare mana,
bamu da sauran abun tunkaho, shikenan
waiyo Rayuwarmu, mun bonu mun lallace".
Ziyada tace "Mummy me ya faru? Kiyi
magana mana" su Zinatu already kuka
sukeyi, Zaineema na tamabayan Mummy,
Nana ta ciro waya ta kira Majeed, sai jin
ringing din wayar tayi a Parlorn ta dago ta
kalleshi, ya karaso da sauri, Mummy na
ganinshi tace "dagaske ne Yaro?/)dagaske
sun rushe mu? Sunyi hijacking filin mu?"
Mummy Calm down" cikin tsawa tace "Dont
tell me to Calm down, ka amsa ni" a hankali
yace "Eh Mummy dagaske ne" luuu Mairo ta
yanke jiki ta fadi.
******
Bibilicious freaking fans, thanks for all your
support, Waya ta gyaru, Nagode muku da
masu kirana da message, Ga Barka da Sallah
na baku. Dont forget to Vote and Comment
line by line please.
Sai mun hadu bayan Sallah.
Ku ajiye min Naman Sallahna, sai nazo muku
yawan Sallah.
#1love
#ADAY
#anatare
#bibiliciousfreakingfans
#muyibikinsallah lafiya
#nagode
Biebee Isa.
Add Vo
Chapter 40 · 0% Book details