← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 128

Sashe 23

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

聽 聽 Ba su sha wahalan bude k'ofofin Gidan ba, yanmatan nan su biyu tantiran 6arayi ne, ko ya k'ofa take sai sun budeta, daga Warri Amstrong ya musu waya suka taho ta jirgi.
Zaid ya bi Gidan da Ido,wani tangamemen Hoto ya gani na Familyn Abba Abu gabaki daya, ya matsa kusa da hoton ya kura ma hoton ido, idonshi yayi Jazir ganin murmushinsu. Amstrong ya katse mai tunani yace "Oga, we have to hurry" Zaid ya basu Go ahead da su hau Sama, suka hau sama, da dakin Farko suka fara, Office ne, Zaid ya musu nuni da su wuce sauran dakunan, shi kuma ya kustsa kai cikin Office din tare da mace daya. Zaid ya bi Office din da kallo, wani save ya gani, ya ce macen tayi mai unlocking, Makullai da suka fi dari ta ciro daga bujenta, ba daukan lokaci save ya bude, Zaid ya karasa ya dinga ciro files files yana budewa, murmushin gefen fuska yayi ya tattara duka a hannunshi, aka rufe Safe din suka rufe Office.
Amstrong kuwa yayi Babban Gamo, don Ghana MustGo din kudin da Baban Nana ya basu ba su kaishi ko ina ba sai dakin Mairo, Amstrong ji yake kamar yayi ihu don Murna, ga wasu Sark'a daham da Yankunne da suka samu a wurare dabandaban, har dakin Abba da AbdulMajid sai da suka shiga, suka samo abun amfani.
Zaid da murmushi a fuskarshi yace "lets get going guys, i'm done here". Amstrong yaja ghana matan suka tattara jewelries din, bayan dayan ta sauka ta dauke ma mai Gadi hankali suka sa komai a booth suka bar Gidan,bayan ya ba Maigadi kudin da be san yawansu ba, Maigadi ya kwashi godia.
**
聽 Bayan sunje masauki amstrong yace "Oga ya zaayi da kayan nan?" Zaid ya murmusa yace "Its all yours, share among yourselves".suka hau shewa "Osheyyy, sai Oga"..
Su sun san Oga yafi karfin komai, su gaba ta kaisu.
*
Manage this please, i'm preety occupied these days bear with me.

Vote and Comment please.

#1love
#ADAY
#bibilicioufreakingfans
#anatare
#nagode

Biebee Isa
[12:06, 25/09/2017] 鈥�+234 803 414 9368鈥�: 锟斤拷A DADE ANA YI....sai gaskia锟斤拷

NA

BIEBEE ISA

庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Wattpad: @biebeeisa

Pg1鈨�4鈨�

A hankali a gabatar da Dinner party cikin yanayi na Girma, kowa sai san barka, haka taro ya tashi lafiya, da k'yar Nana ta tafi gidansu, don a cewarta a yau din zata bi Majeed. Mummy ta lallabata, kan cewar gobe da Safe zaa kaita gidansu Mijinta kafin a samo musu wurin Zama.

A gajiya a ka koma Mansion din Abba Abu, Zaineema da Ziyada suka shiga dakin AbdulMajid Zaineema ta kalli Yayanta don yau ya gama kasheta tace "Haba Ya Majeed, kunya ka so bamu ne dazun? Naga kana ta shan kamshi kana bata rai, haba Ya Majeed, zakayi ma Azziki k'ulli, ba kowa ake ba irin damarka ba" galala ya kalli K'anwarshi yace "kasan dai duk da aurenki ina iya miki dukkan tsiya ko? Ni ba tsaranki bane Zaineema,ki fita idona" Zaineema ta ta6e baki, tasan la shakka zai iya mata duka, ta wuce fuu ta bar dakin.
Ziyada ta bi bayanta da murmushi.

AbdulMajid ya kalli Ziyada yace "Yayanki ta k'i hankali har yau" murmushi Ziyada tayi tace "I miss your dramas" da kalamanta ta tausasahi, kan cewa ya saki jikinshi ya cigaba da alamarinsa, K'addararsa ce haka, Sosai yake son Ziyada,Jininshi ya ma fi haduwa da ita, inda ta bambanta da Zaineema kenan, tafita kaifin tunani da basira, idan zatayi magana tana amfani uwauba hak'uri, in kaga Ziyada na daga murya to ka kaita bango ne, ko Zinatu ta mata rashin kunya, ba kasafai take kulata ba, ba dan komai ba sai kawai bata da son hayaniya.
Gyada mata kai yayi alamun yaji duk abunda tace kuma InshaAllah Zaiyi yanda tace, murmushi ta mai ta tashi ta fita tare da kullo mai k'ofa. Sai da yayi Nafila kafin ya kwanta bacci.

Walima Akayi a Abba Abu's Mansion, da daddare Amarya ta tare a dakin AbdulMajid. Anan zata fara zama kafin su tafi Kano inda AbdulMajid ke aiki.
A daren rannan burin Nana ya cika, kusan fyade ta mai, a ran Majeed mamakin Nana yake tayi, sam ba ta da kunya, ta ya zaa samu mace haka? Allah kayi mana da kyau.
Daga daren Jiya, wani irin zafaffen So ya sake rufe Nana, AbdulMajid ya kai Mijin da zaa buga gaba a nuna shi, duk da be biye mata ba, amma hakan ya wadatas.

I N D I A

Alhaji Sada ya kalli Matarshi cike da So da k'auna yace "Yesmeenah, ku shirya gobe zamu Taj Mahal" murmushi Yesmeen tayi, ta san don ta saki ranta Mijinta ya tsiro da wani tafiya, zatayi k'okari ta saki ranta, ko don kwanciyar hankalin Mijinta da tillon diyarta, tace "Allah shi kaimu Gobe Papi, zan gaya ma Najwa ta shirya".
Da Najwa taji maganar tafian taji dadi sosai, lokaci ne da zata k'ara kusanci da Mahaifanta, in ba rabon su sake haduwa, to ba zata mance moments din da zasu samu gobe ba.
*

锟�

Washegari suka dafa abinci kalakal ita da Maama, suka shirya wurin k'arfe 9 Vijhay yazo daukarsu, Najwa ta dauko Pooh (Mage) ta sata a Mota, duk yanda Maama tayi kar aje da Magen nan Najwa ta sa Shagwaba har sai da Paapa yace abarta ta tafi da Magenta, Najwa a gaba, Maama da Paapa a baya suka dau hanya.

锟�

Tafiyar Awa Hudu sukayi suka iso TajMahal(7th wonder of the World), ba zuwan su na farko kenan ba, bayan sun zagaya ne suka samu wuri daga chan Garden suka shimfida Carpet, suka yi lunch.
Najwa ta kafe Iyayenta da ido, gani takeyi kamar ganin k'arshe take musu.
Idonta ya ciko da hawaye, Alhaji Sada ya lura da ita yace "yadai Najwa? Are you OK?" Maama ta juyo kallonta ga Najwa tace "Kya huwa beti? (Meya faru diyata?)" Najwa ta murmusa tace "Maama, Paapa, i was just thinking,Ina Ya Zaid yake? Is he alright? I just want to meet my Brother" Maama ta fashe da kuka, Najwa ta taya ta, sai da sukayi me isar su kafin Maama tace "Najwa, bansan ya Zaid yake ba, bansan ya yanayinshi yake ba, bansan da wa yake kama ba, Yana kama dani? Ko da k'anwarshi, ko da Papanshi? But I'm sure ko a Ina yake, he's grown into a Prince Charming" ta k'arashe magana hawaye masu zafi na bin kuncinta ta cigaba "If only he's here with us, we'd be a loving and a whole Family".

Paapa ya hadesu duka ya rungume yana lallashi " Yesmeenah, i'm a bad Husband, and a bad Father, na kasa hada Da da mahaifiyarshi, na kasa ba Matata farinciki, na kasa hada kanwa da yayanta, ku yafe min, bansan ya zanyi ba" Maama ta dago tace "haba Papi, don me zaka ce haka, why are you blaming yourself like its your fault? Kar ka manta we are in this together, kaine k'arfinmu, in ka karaya ya zamuyi?" kukan da yazo ma Najwa mai k'arfi, da sauri ta tashi ta la6e bayan Bishiya tana kallon Iyayenta na lallasan Junansu. Yaushe zata tsayar da hawayen nan? Ji take Ina ma ta matso da sati biyun da ya rage taje Nigeria kusa, ina ma zata iya ganin Yayanta, sai da ta ga sun natsu kafin ta koma gunsu tare da sake musu murmushi tace "Oya muci abinci kafin yayi sanyi".
**
Maama ta dinga ba Najwa labarin Zaid, "Zaid baya son Kifi, ko k'arnin kifi yaji zai kama amai, Zaid na son abu mai sanyi" tayi daria tace "Zaid na son wasan banza, yana son tsalle-tsalle sosai, to yanzu da girma yazo mai, shekara 28 ko yana yin abunda yakeyi a yarintan shi?" Paapa yayi daria yace "Haba Yesmeenah, i'm sure ya bar dukka abubuwan da kika ambata" Najwa na daria ta kalli Iyayenta sa suke faraa suna maganar Zaid, tace "Paapa, a Nigeria, wani state kuke?" dogon tunani Paapa yayi yace "To God i dont remember" mamaki ya kama Najwa tace "Maama fa?" Maaman ma tunani tayi tace "ikon Allah, i cant remember, all these years ban taba tunanin sunan gari ba" abun kuma sai ya zama kamar Almara Najwa tace "Ya akayi haka? Ya ba zaku tuna ba?" "Wallahi ban tuna ba" Maama ma tace "nima Wallahi ban tuna ba" "to ya baku manta Sunan k'asar da ku kazo ba?" Shiru sukayi duka, basu san dalilin ba, Najwa da abun ya gama daure mata kai tace "Okay, 'yanuwanku fa? Your parents" Paapa yace "Najwa nidai i cant remember, wlh i dont remember anything concerning Nigeria" yanzu kuma abun tsoro ya fara ba Najwa tace "Ina kukayi aiki? Bakuda Contacts din coworkers din ku? Ko Schools din da Yaya Zaid yayi? Anything you cant just forget Everything, think harder, Maama, Paapa" Cikin daga Murya Maama tace"Najwa, dont you get it? We cant remember a thing, Najwa,ban san me ya faru dani ba, bansan ya abu ya kasance ba, nasan abun zaiyi kama da tatsuniya, amma its real, mun munce komai, amma abunda ni ko Paapanki muka kasa mancewa shine Yayanki Zaid, mun kasa, mance shi muna da tabbacin yana Nigeria, but ba musan inda yake ba, above all ba zamu iya zuwa gunshi ba".

Najwa tayi jigum tana tunani, amma takasa gane komai, yanzu ba wani hanyar da zai sadata da Yayanta kenan? Kawai shiga Nigeria zatayi, to ina ta dosa? Ita da ko hoton Yayanta bata dashi, ta ya zata fara nemanshi, anya zuwa Nigeria ba bad idea bane? Amma Hawayen Mahaifanta fa?, no she wont give up, not now da saura 'yan kwanaki ta tafi Nigeria, Allah zai hadata da danuwanta da yardan Ubangiji, kuma zata shaidashi ta hanya mai sauk'i don Maama ta gaya mata cewa Yayanta na da irin mark dinta a hannu da wuya, so InshaAllah everything will be fine. Da haka ta ja su da wasa har suka warware suna Family Play.

A B U J A NG
Chapter 23 · 0% Book details