← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 128

Sashe 33

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱 NA BIEBEE ISA 庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Wattpad:@biebeeisa Pg1鈨�7鈨� Kyafta idanuwanta tayi sau uku kafin ta sauke su fes kan Mutumin da ke kusa da ita sannan ta saukar da dubanta ga handkerchief din da ke rik'e a hannunshi, mika mata ya sake yi, ta sa hannu ta karba, ta goge hawayenta, ya mata nuni da hancinta inda Majina ke zuba, ta dan ji kunya, haka ta goge kafin ta k'wak'ulo murmushi. Maida dubanshi yayi ga TV din da ke gaban Seat, ya gyara zaman headphones a kunnenshi. hankali a hankali take jan majina, ba ta damu da kallo ba, abunda ke dawainiya da ita ya fi karfin Kallo, tana sheshek'a, hawaye na bin kuncinta har bacci barawo ya saceta. I N D I A 5:45am "Yesmeenah, yau Najwa ko bata Sallah ne? Banga ta zo gaida mu ba" daria Maama tayi tace "Yanzu da gabanta ka fada hakan da taji kunya, wai ko bata Sallah ne, haha, tana yi fa, k'ila ta makara, ko bayan Sallah ta idar bacci ya ci k'arfinta ta koma" ya mik'e tare da cewa barin dubota. Ko da ya bude dakin Najwa be ganta ba, sai Pooh da ke ta bacci kan Gado, ya dawo yace "ta tashi, tana toilet" Maama tace "Oya kazo ka kwanta kafin na tada ka Shirin Office" murmushi yayi ya haye Gado ya kwanta ya bar Maama kan Gado tana Adhkar. Gari ya dan fara wayewa Maama ta shiga Kitchen, ta shiga hada musu breakfast, da sauri ta shiga dakin Najwa, ta ga bata nana, a zaton ta tana Toilet, ta bude baki tace "Najwa, kiyi sauri ki fito ki shirya, School Bus ya kusa zuwa". Ba ta jira komai ba ta dawo dakin baccin su. Ta hau kan Gadon inda Pappa ke zaune, "rise and shine Papi, wake up" da murmushi ya bude ido tace "Good Morning Papi" "Good Morning Yesmeenah" "Oya a shiga toilet ayi wanka" ta samu ta turashi wanka. Ta ja bargon ta ninke ta kakkabe bedsheet zata fara gyara Gadon kenan idonta ya sauka kan wata Farar takkada, tayi dan jim daga nesa kamar tana son gano wani abu game da takardan, a hankali ta taka har zuwa gaban bedside drawer, ta dauki takkadan ta bude. Gabanta ya fadi ganin rubutun Najwa kwance kan takardan, kasa karantawa tayi ta fita da gudu tayi dakin Najwa tana k'wala mata kira. Shiru Najwa bata daki, bata toilet, Maama ta fita parlor tana kiran Najwa, ba Najwa ba alamunta, sai da ta zagaye Gidan tana kiran Najwa amma shiru, Dakin Najwan ta koma hannu na rawa ta ware takarda ta fara karantawa gabanta na duka chalugude. "Good Morning My Beloved Parents, a Lokacin da za ku ga wannan Message din, i'm long Gone. A kullum burina shine ganin Farinciki dauwamammiya ya wanzu a cikin Gidanmu, inda zamu yi rayuwarmu ba tare da ganin hawayen daya daga cikin mu ba, Maa, Hawayenki tamkar saukan garwashi ne haka nake ji a zuciyata, so da yawa nake danne nake shanye bakincikin da zubar hawayenki ke jamin, don kar in k'ara miki wani zafin. Paapa, Maama, Na tafi Nigeria, na tafi neman Yayana, zan ganshi indai yana raye, zan dawo dashi Gida no matter how long it will take, i'll find him and i'll bring him home. Kar ku yanke Adduarku gareni, kar ku damu, i'm 18, i will be just fine. Paapa take care of Maama before i come back. And Maama ki adana hawayenki kuma sai ran da na dawo miki da Zaid Bhaiya, rannan kiyi kukan farincikin ki ba mai hanaki. Maa, Paaa, please be fine, Be happy. I want you to be proud of me, ina so na zama abun Alfahari a gunku. 掳Main aapako bahut pyaar karata hoon(i love you so very much)掳" Najwa. Maama ta dafe kai hawaye na zuba daga idaniyarta, Najwa ta tafi Nigeria neman Zaid? Me Najwa ke tunani? Nigeria Sarita Vihar ne? Shikenan ta rasa Najwa itama, Shikenan ta rasa yaranta duka, Paapa ya shigo dakin yace "Yesmeenah ina Najwa? Na ji kina ta kwala mata kira" Takardan hannunta ta mik'a mai, ya karba ya karanta. "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun"cewad Paapa, ya sake karantawa, jiki na rawa ya rungume Maama da take jin duniyarta na barazanan Tarwatsewa, tun yaushe take shirye shiryen? No wonder ta cika fita kwanakin nan" ita dai Maama ba tace komai ba, sai chan tace "Vijhay yabsan wani abu, tare suke k'ulle kullensu" da sauri ta tashi ta ja mayafin da Najwa tayi sallah ta sa, Alhaji Sada ya bi bayanta, ba su tsaya ko ina ba sai gaban shagon Vijhay. Kwankwasawa sukayi yana budewa ganinsu ya sa shi sadda kai irin na marasa gaskia. Murmushin takaici Maama tayi tace "Vijhay aap isake baare mein pata tha? (Vijhay dama ka sani?) kai ya gyada mata, tace "hamen sab kuchh bata(ka gaya mana komai)" nan Vijhay ya gaya musu duk abunda ya sani game da tafiar Najwa har zuwa jiya da ya kaita Airport ya dora da fadin "main bahut maaphee chaahata hoon aapako bata nahin karane ke lie, mujhe maaph kar do (I'm very sorry for not telling you, please forgive me)". Kuka yaci k'arfin Maama da sauri ta shige cikin Gida, tana tausayin Najwa, da ta san Nigeria da ba tayi marmarin zuwa ba, Nigeria ba wani abu sai tarin Maha'inta, duk da ba a taru aka zama daya ba. Hannu ta daga sama tana rok'on Allah ya Tsare ya kare mata diyarta a duk inda take. 8:35am Tagumi sukayi duka, sunyi jugum, Paapa beje aiki ba, Maama ko rike da letter din Najwa wanda ta karanta yafi a k'irga, kirrrr Wayar Maama yayi k'ara, bata waya take ba, amma Pappa ya mik'e ya dauki wayar ya duba, international number ce, hannu na rawa ya dauka tare da sa Speaker "Maama..." wani tsalle da Maama tayi ta amsa wayar hannu Pappa murya na rawa tace "Najwa beta, are you OK?" Najwa ta murmusa kamar suna gabanta tace "Maama i did well didnt i?" Maama kuka yaci karfinta tace "Najwa diyata, ki dawo Gida, duk yanda nake son kasancewa tare da Yayanki, ba zanyi risking life dinki ba" Najwa tace "Mamma neman Yayana gudan jini na ne risking life? Maama, nayi nisan da ba na jin kira Already ina Dubai, lokaci kawai nake jira na hau Jirgin Nigeria, Just Pray for me". Maama tace " Najwa Wahala kawai zakiyi, ki dawo gida, bansan me zanyi ba idan kema na rasaki, bansan ya zanyi ba, Najwa please" Najwa tace "Maama, i want you to be my strength please, let me do this, donAllah Maama, ki bari na dawo miki da cikon farincikin ki, i can please Maama" Duk inda Maama ta bullo ma Najwa sai Najwa ta bulle, ba yanda ta iya, kuka kawai takeyi, Paapa ya jinjina kai yace "Najwa, I'm proud of you, ina alfahari dake, bring your brother home, your Maama and i will be waiting, Allah ya miki Albarka diyata". Najwa ta murmusa tace "Amin Paapa na, take care of Maama and my Pooh, kuma donAllah kar kuyi fushi da Vijhay bhaiya ni na saka ya min Alkawari ba zai fada muku ba" Pappa yace "Najwa donAllah ki kula da kanki, nasan you're 18, idan kika ga theres no progress, come straight home kinji?" tace "Naji Paapa, Maama na fushi dani ko?" yace "Ya zatayi fushi da abun alfaharinta? She's just scared" Maama kar ki ji tsoro, Allah zai kareni, zan dawo gareki and ofcourse with My brother, now bless me please" Maama ta shara hawayenta, tana murmushi tace "Allah ya Albarkaci rayuwarki Najwa, Allah ya kareki daga sharrin mutum, karfe da Aljjan, Allah ya dawo dake lafiya". "Ameen, naji ana kiranmu zaa fara boarding, i will call you dana isa Nigeria" haka sukayi sallama, zuciyoyinsu na Alhinin rabuwa da junansu. * * Tana farkawa taji cikinta na kukan Yunwa, sai a lokacin ta tuna, rabonta da abinci tun abinci Maama da ta ci daren jiya, dazun a Jirgin India-Dubai bata ci komai ba. Kamar Mallaman Jirgin sun san zuciyarta, don kuwa abinci aka fara rabawa seat by seat. Ta bude abincin ta ga Taliya da miya, warin Miyan ya bugi hancinta, haka kurum taji amai yazo mata, amma da yake yunwan take ji bil hakki, ya sa ta dauke numfashinta tana tura ma cikinta taliyar. Da tayi yunkuri sai da ta fara amayo abincin da ke cikinta gabaki daya. Mutumin da ke kusa da ita ya kalleta cike da tausayi, yanda ya ga ta galabaiita ya sa shi tausayinta, "sannu kinji, sannu" bata iya amsa mishi ba, danna alert din seat dinsu yayi alamun suna neman attention. Jim kadan sai ga attendant din jirgin ta iso, Mutumin yace "She threw up, help her please" Mallamar Jirgin ta taimaka ma Najwa suka shiga toilet, wata kuma ta gyara inda Najwa tayi Aman. Kafin aka dawo da ita, yace "miss, get her fruits and vegies with Orange Juice please" da murmushi Mallamar Jirgin tace "Right away sir" ya juyo ga Najwa da murmushi yace "Sannu, it happens haka, maybe baki san warin spices dinne shiyasa kikayi amai, but ga Fruits zaa kawo miki ki daure ki sha zai zauna InshaAllah" kai kawai ta gyada mai ta na mamakin shi, be ji kyamarta ba, ya cigaba da cin abincinshi, Jim kadan aka kawo mata Fruits, yauwa gwara hakan kan Abincin nan mai wari a cewarta , ta ci banana, apple, grapes da Lemu, ba laifi cikinta ya dauka. Mutumin ya gyara mata zaman Kujeranta, ya kunna mata Tv, haan, mamaki take, to ko shi wannan ba Dan Nigeria bane? Ta ganshi da kirki, muryan Aisha ta tuna inda take mata warning kan Yarda da mutane, har tana cewa; Add Vote "Wasu zaki gansu da kirki, but they are only trying to get advantage of you, wasu chance kalilan suke nema, kar ki bari Kirkin da wasun su zasu nuna miki ya sa kiyi sake ki yarda dasu, they are very manipulative, so Najwa, dont trust anyone". Kai ta gyada a ranta tace ba zata bari kirkinshi yaci galaba a kanta ba. Da Yamma suka Iso Lagos Nigeria, bayan sun fito daga jirgin, kowa kama gabanshi yayi,Najwa ta dauka akwatinta da
Chapter 33 · 0% Book details