Sashe 49
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
hakura" ta kalli gaban Mota inda taga Dattijuwa, ta dan rusuna tace "ina wuni? hajjo ta amsa da faraarta, sai da Daddy ya kalli su Zaineema kafin suka gaidata, dama duk gidan daga Zaineema sai Zinatu ne ba sa yi da Hajia Ainau, Daddy ya mata alama da ido yace " thats My Mom" ta bude ido tace "are you serious?" Ya daga mata kai, ai da sauri ta zagaya gaban motan ta rungume Hajjo kamar ta santa, ta zube k'asa a guiwowinta, tana kwasar Gaisuwa, Mama Ina wuni? Ya gida ya Jiki? Mama ya kike? Ya kowa da kowa" Hajjo ta amsa baki har kunne tana jin dadin yanda Hajiyar ke gaidata, kunsan Yarbawa da Biyayya, da kissa nan da nan Hajiya Ainau ta shiga Zuciyar Hajjo. Daddy yace "To Fallalu ku tafi ko?" Hajiya Aynarh ta dinga daga ma Hajjo hannu har suka bar Asibitin, hakan ya ma Daddy dadi. Idonshi ya sauka kanta, Ko ba a fadi ba ya san tana cikin damuwa, tunda suka gaisa dazun da safe da suka shigo ta mai ya jiki, be k'ara jin Muryarta ba, tana da damuwa, ina ma zai iya jin damuwarta, da ya yaye mata shi da iyawarshi, ya lura da yanda take tirjewa na bata son tafiya, har yanzu din ma tirje ma Hannun Ziyada takeyi "lets wait a little longer" yaji ta fada a hankali, Ziyada ta mata Ido da Mummy, Najwa ta marairaice tace "Please" Ziyada tace "OK". Mummy ta lura da su basu tafi ba tace "Ehen?" Ziyada tace "Erhm zan tsaya sai anjima ina zaki tafi" Mummy ta galla ma Najwa harara tace "kefa? Come on wuce" kafin Ziyada ta kare Najwa, Majeed yayi Charaf yace "Mummy, let her be if bata son tafiya,Najwa zaki bi su Hajjo?" Da sauri ta Girgiza kai Alamun Aa, yace "Oya zauna abunki" da sauri ta zauna, Mummy ta buga tsaki ta shige toilet, Majeed ya maida dubanshi ga Ziyada yace "Zuzu, Monday zaki fara Zuwa Northwest University, i'm sure zakiga a lot of changes, na san baki saba Schooling a irin Makarantun ba, not like your Base University" Murmushi tayi tace "I dont Mind at all YaMaji, Allah ya saka da Alheri Amin". Sosai yaji daidi yace "i'm proud of you". Ya maida dubanshi ga Najwa dake wasa da yatsun hanayentayace "Ina wayanki?" tace "Uhmm?" Yace "Uhm"tace "yana Gida" "ba ki mayi amfani dashi ba ko?" "Eh nasa Charge" Ziyada tace "ina zata iya amfani dashi bayan she spent the Whole day Crying, in ka ganta jiyan nan sai ka tausaya mata, ta shiva damuwa sosai, ta k'i barin k'ifar dakin nan, binibini sai ta lek'a ta Window taga ko ka farfado, da akace ka farfado kuwa murna kamar tayi mene, da Mummy ta koramu Gida tayi kuka taso ta kwana fa, tsakar dare ina ganinta tana Sallah tana cewa Allah ya sa karka mutu, hahaha Adduar da ta yi tayi kenan a baiyane, Allah ka sa Ya Majeed kar ya mutu" kunya ya lullube Najwa, ashe kowa ya san kalar damuwan da ta shiga? Nana sai binta take tayi da kallon tsana, Majeed ya dinga jin wani irin abu na ratsar shi, ya tsura mata ido, ganin bece komai ba ya sa Najwa dagowa ta kalleshi, karaf suka hada idanu, ta so dauke kai sabida wani kwarjinin da ya mata, amma ya datsen kallon yanda ba zata iya dauke ido daga nashi ba, da ido ya mata alamun ta zo wurinshi, a hankali ta tashi, taji kafarta ya mata nauyi, da kyar ta k'arasa har gabanshi, kanta a k'asa, Murmushi yayi mata, cikin k'asan mak'ogaro yace "have you been Eating?" da sauri ta daga kai ta kalleshi yace "kin rame, ki dinga cin Abinci, ina so idan na maida ma Maama ke tace kinyi k'iba" bata san lokacin da ta fashe da dariya ba, Ziyada ta kallesu tayi Murmushi tana raya wani abu a ranta, Nana ta buga tsaki tace "sai ki samu wuri ki zauna kin ma mutane tsaye a ka" da sauri Najwa ta koma wurin zamanta ta zauna, Majeed bece da Nana komai ba, ya dai so ta kalleshi ya tabattar mata "da cewa komai zai zama daidai" amma ta k'i dagowa balle ta kalleshi. Mummy ta fito daga toilet, tace "Yaro kaci Abinci mana, da kaina na dafa maka, Taliya kake so ko Shinkafa?" kai ya girgiza alamun "aa" yace "bana jin cin komai Mummy" tace "OK, ka gaya min in kaji Yunwa kaji?" kai ya gyada mata" ya maida kai ya kwanta, kusa da Ziyada Mummy ta zauna, ta na jan diyarta da firan Amjad, don daga Nanan har Najwan haushi suke bata. Sallamar Daddy da Hajia Ainau ya ratso kunuwansu, duk suka zuba ma k'ofar shigowa Ido, Daddy ke gaba, sai Hajia Ainau, sai wata yarinya rik'e da kwandon basket, Gaban Mummy ya yanke ya fadi kamar taga fatalwa, yanayin da ta gansu sun shigo suna fara'a kamar wasu maaurata, Najwa da Ziyada suka amsa sallamar, Mummy ta fara huci kamar Jirgin da zai tashi sama, Aunty Aynarh ina wuni? Cewar Ziyada da Murmushi, duk miskilancinta bata ma Hajia Aynarh, Matar da ke zuwa Abuja don kawai taga 'yayan Daddy? Hajiya Aynarh tace "dont stand there, come and give me a big hug" da sauri Ziyada ta k'arasa gun Hajia Aynarh ta rungume, Daddy sai faraa baki kamar gonan Auduga, duk da bata san Najwa ba amma taga tana kama da Alhaji Sada, itama bude mata hannu tayi alamun itama tazo, tasowa tayi cike da kunya ta rungume Aunty Ainau, tace "wacece Wannan?" Daddy yace "Najwa kenan, Bak'uwad Majeed ce" Hajiya Ainau tace "Allah Sarki, kamar Jinin Marigayi" be gane Marigayin da take nufi ba sai kawai yace "Eh haka fa" cike da Kissa tace "Hajia Mairo ashe Yarona beji dadi ba?" Mairo ta fara kumfan baki, Hajia Aynarh ta murmusa a hankali daidai yanda Mairon kadai za tajita tace " sai haushi kikeyi kamar karya" a fili tace "Haba, ba kya ganin Yarona na bacci, be fa da lafiya, ke kullum muka hadu sai kinyi ihu, to Allah ya baki hakuri". Hajiya Aynarh ta k'arasa inda Majeed ke kwance, Nana ta kalleta tace "Sannu" bakin harara Hajiya Aynarh ta wulla mata, bata amsa ba ta kai hannu goshin Majeed, a hankali Majeed ya bude Ido ya zubeshi kan Aunty Aynarh, Murmushi yayi yace "Aunty" tace "yarona ya jikin?" cike da shagwaba yace "naji sauki Aunty kice su Sallameni" Nooo boy, ka kara hutawa, har sai BP dinka ya gama sauka ko?, hakuri zakayi, kaci Abinci?" a hankali ya gyada kai alamun "aa" tace "har past to1? Aa ba zan yarda ka zauna da yunwa ba" ta juya da sauri, ganin Najwa ta fi kusa da Basket din da Gloria ta ajiye ya sa ta cewa "Baby na, dauko min Basket din nan, kizo ki zuba mishi Amala" ta kalleshi tace "da kaina na Tuk'a maka, na san kanaso, zakaci ai?". Kai ya daga alamun "eh". Start from the beginning Shikenan, abun ya gama kashe Mairo, tun zuwan Hajia Aynau ta tsaya sandare kamar an dasata, anya matar nan ba da Jinin Oduduwa take tsafi ba? Ji yanda kowa ke sonta, ji bakin Daddy, ji Ziyada, ji Majeed din da yanzu yace mata ba ya jin Yunwa, amma daga zuwanta ace zaici Abincin Yarbawa, wai Amala, muryan Hajia Aliya ta tuna inda take mata gargadi *"Wallahi Mairo kashinki ya bushe in Ainau ta shigo Gidan nan, Yarbawa? Ki raba kanki da kishi da Bayarabiya, Wallahi sai kin raina kanki, don su wuce tunaninki, Mugun yaniska ne, matsafa, kaf zata siye Mijinki da Yaranki kaf, duk su dawo karkashin ikonta"* da k'arfi Mairo tace " Inaaaa Sam, ba zan yarda ba, na fi k'arfinki Ainau, nafi karfin ki bakar Matsafiya, kurwa na da na Iyali na kur, ba ki isa ba wallahi, kinje kinyi barbade zaki kawo ma Yarona Abinci ki shanyeshi ko? Wallahi karyanki ya sha karya" Hajiya Ainau ta san ta gama kashe Mairo da kissanta, ta kara mariaraicewa tace "Abba, lafiya? Me take cewa is she Alright? Mairo abun ya fara tsumata, da sauri ta yo kan Hajia Ainau, Daddy yayi saurin shan gabanta, ya jata suka bar dakin, daidai yanda Mairo kadai zata ganta, Hajia Ainau ta ciro halshe tana mata gwalo, Mairo ta k'ara tsurewa, Daddy ya ci nasaran fiddata waje, Ziyada ta bi bayanta. Da k'yar Daddy da Ziyada suka sa Mummy a Mota, ita sai dai a barta ta je ta ma Hajia Aynau dukan tsiya, wai ta shigo rayuwarsu ne don ta hallaka su, ta ma Daddy Asiri yana binta kamar rakumi da akala, ita ba zata yarda ba, Hauka Mummy tuburan keyi wanda Daddy ya lakanci hakan da Kishi, da abun yayi yawa sai da Ziyada ta fashe da kuka kafin Mummy tayo shiru, a haka suka isa Gida. Majeed ya girgiza kai yace " Ki Kara hakuri Aunty kinsan halin Mummy" tace "kar ka damu, abunda takeyi be taba damuna ba, Baby dauko abincin, mana, kin tsaya kina kallo like a cartoon" ta karasa maganan tana zolayan Najwa, Najwa ta murmusa ta dauko basket din tana tafiya sumi sumi, "Oya zuba mishi, serve him" Najwa ta bude coolers din, taga abu bak'i" yanayinta ya sa Hajia Ainau gane bata san meye wannan ba, tace "baby, baki san meye wannan ba ko?" tace "Nasani, bak'in tuwo ne" hahah suka fashe da daria, Amala sunan shi,Majeed ina ka samo 'yar kauyen nan?" yayi Murmushi yace "chan kauyen Dubai" sukayi daria, Hajiya Aina, tace "ahh yar gayu ne, noway zata san Amala, Oya zuba mishi Miya din, Iwedu ne, kisa mai Gbomo din da yawa" kamshin ya bugi hancin Najwa, sai taji tana son ci, mik'a mishi plate din tayi" Hajia Ayna tace "Aa, dont be a lazy girl na, feed him joor" Najwa ta daburce, wani irin shauk'i ya shigeta, da sauri Nana ta yi yunkurin karbe Plate din, Hajia Aynarh ta galla mata harara da baki tace "Dont touch my plate" Nana tace "haba meye haka? Nice fa matar shi? Ya zakice ma wannan karamar yar iskar tayi feeding dinshi bayan his wife is here, this is not right" Kallon Zakici Ubanki Hajia Aynau ta ma Nana, nan da nan Nana