← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 128

Sashe 26

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

聽聽 Amsa sallamar da akayi sukayi, hankalinsu gabaki daya kan k'ofar, MD Fannaz Ventures ne da wasu mutane biyu,Daddy ya k'arasa gunsu yana musu sannu da zuwa, aka gaisa a mutunce, MD yace da Mairo "Madam ya jiki?" Mairo ta kwakulo murmushi tace "da sauk'i Alhamdulilah" "Allah ya k'ara sauk'i" suka amsa musu. MD yace "Alhaji Abba, maganan Shares dinnan ne, kace zaka ban kudin,in kudin be samu ba, kabani shares din ga masu siya nan" Zufa ya keto ma Daddy, zaiyi magana Mairo tace "MD, donAllah ka bamu lokaci, wani ifti'la'i ya afko mana, amma InshaAllah zamu biyaka" MD yace "Hajia Mairo kenan, nima iftila'i ya auko min na karayar Azziki, a halin yanzu, Mahaifiyata na fama da Cancer za mu fiddata Egypt, ko da suka mana budgeting kudin, ana bukatan Miliyan 20, saboda Cancer din ya kai Stage 8, Chemoteraphy din na tsada, tsakani ga Allah banda isassun kudin da zaayi hidiman nan, shisa na yanke hukunci saida shares din a gaugauce" Dakin yayi shiru sai k'aran Ac din da sheshek'an masu Kuka. Daddy zufa ke keto mai, Mairo kanta yayi zafi, ganin ba me niyyan Magana Md ya sake cewa "DonAllah ku san yanda za kuyi dani, Mahaifiyata na cikin hali" shiru sukayi suna tunanin yanda zasu Samo Miliyan Ashirin, ba sa tunanin ko hade kudaden account dinsu duka zaa yi ba zai rufe miliyan biyar, Majeed ya ja iska ya fesar yace "Alhaji, zan kawo maka kudinka Gobe InshaAllah".
聽 Suka bi Majeed da Ido, MD yace "toh Allah ya yarda, Madam Allah ya k'ara sauk'i" ba ta amsa ba, sai bin shi da ido da sukayi, yana fita duk suka maido dubansu ga Majeed. Ya san bayani suke nema ya samu wuri ya zauna kana yace "Mummy, Daddy kunsan dai wannan Jarabawa ce daga Ubangijin mu,Karayar Azziki ne, so sai mun rungumeshi ko mun k'i ko mun so,MD na bukkatar kudinshi,Mummy kin ci bashi banki har miliyan 15,Mummy ta ya zamu biyasu duka?" ya kafa mata idanuwa yana son ta bashi amsa ido jawur tace "Boy, wallahi ban sani ba,ban san ya zaayi ba"a zuciyar ta kuma tana tunanin zuwa gun Bokanta don a rufe musu baki kar wanda ya sake musu maganan kudin da ake binsu bashi, zuciyarta kuma tace "tusa fa bata hura wuta". Majeed yace "Mummy, Daddy, Muna da Azzikin da za mu biya bashi" suka ce ta ina! Yace "a sa Gidanmu a Kasuwa, a saida shi ayi settling masu bin mu bashi" Mairo ta zaburo da ga kan Gadon Asibiti, Jiri ya dibeta ya maidata kan Gado, tace "AbdulMajid, a saida Mansion? Tabb so kake asirinmu ya tonu?" Majeed cikin dacin rai yace "Asirin ki zaifi tonuwa if you go bankrupt, don terere zaayi dake, gwara bakinki聽 alekum a saida a biya mu koma Gida Kano, Daddy ka fada mata" Alhaji Abba, ya hadiye Miyau yace "Maryam, hakan ne mafita,hakuri kawai zamuyi, kinga MD a gaugauce yake son kudin nan, idan baa samu ba ba mu san abun da zai iya yi ba" kan Mairo ya shiga sarawa tasan basu da wani mafita da ya wuce wannan, ba abun da tafi ji kamar zama abun kwatance wurin kawayenta, ba yadda zatayi illa ta amince a saida Gidan.

聽 聽 聽 聽 PH Nigeria

聽 Zaune kan Parlor ya daura k'afa daya kan daya yana karkadawa, hannunsa rik'e da gwangwanin lemu yana kurba, kallo daya zaka mai ka san jin dadi ya mai yawa,balle yanayin da yake ciki yanzu, farinciki da annashuwa kadai ke fuskar,yana da Labarin wainar da ake toyawa a Abuja, Musamman labarin doguwar Suman da Mairo tayi har an zata ta mutu, labarin ya sa shi farinciki matuk'a, jefijefi ya kanyi daria a ranshi yace "ai dama an rufeta tayi mutuwan da ba shiri" chan kuma yace "ai gwara ma da Allah ya sa ba lokacinta bane yayi, don Mutuwa hutu ne gareta, bata gama girbe abunda ta shuka ba" wayarshi tayi k'ara, ya sa hannu ya dauka "Idi" daga bangaren akace "Hello Oga, sun sa Gidan a Haya, shareholder dinnan Fannaz ya bukaci Share dinshi" Zaid ya murmusa sosai yace "A siya Gidan, suna buk'atta sosai, so nothing higher than 50million". Idi yace " Okay Sir" Zaid ya latse wayar yana jin kanshi cikin wani irin Jin dadi, a hankali a hankali komai na tafiya mai yanda yake So.
Dayan wayanshi ya ciro ya kira Managern Sadam Audu Orphanage house, Cikin muryan Nine Oganka Zaid yace "Ana Bukkatar wani abu a Gida?" Manager yace "Aa 'yallabai komai akwai" Zaid yace "zan turo kudi ayi Ordering Swings(Liluna) da kayan wasan Yara, sannan a kwashe yaran Weekends akai su wurin shak'atawa,ayi treating dinsu sosai, a siya musu Popcorns da icecream, su ci pizza sannan ka biya da su boutique a siya musu kaya,idan na samu lokaci zan zo" a ladabce Manager yace "Zaayi yanda kace, Allah ya kara budi, ya daka da Alheri, Allah ya ji kan Gatan Marayu" Zaid yace "Ameen Nagode, yauwa, munyi magana da Goggo, tace nan sashen Manya akwai Mata 3 da suka daidaita kansu da wasu a nan cikin Gida,sai daya kuma mallamin Islamiyansu ya ke sonta, ni bansan Gori, amma goggo tace anyi bincike sosai kan Malamin, ba zai bada matsala ba tunda ya san Asilinta yace yana sonta, ina so kaje ka shaida ma Malamin cewa 'amincewa da Aurenta yana nufin bashi ba mata kallon kaskanci don ta fito daga gidan Marayu,kar danginshi su wulakanta ta ko su yada maganar da zai bata mata rai, yin hakan barazana ce ga shi da danginshi gaba daya, zan sa a daure su, in ya amince sai a bashi ita" Manager yace "Allah Sarki Gatan Marayu, da kana da rai da ka ga Yaronka ya zama abun Alfahari, be bari marayunka sun tagaraya ba, be watsar da alamuransu ba, ya tsaya musu, ya nuna musu Suma 'ya'yane,sun ma fi wasu da ke gaban Iyayensu Jin dadi, Allah ya saka da Alheri ya k'ara girma" a tak'aice yace "tura ma Yakubu Matan nan da zaa aurar, suje Company su zabi irin Gadaje da kujerun da suke so, a musu duk abunda suke so, su kuma mazan a hada musu lefe, sannan a basu gidaje a Compound inda zasu zauna" Manager yace "InshaAllah 'yallabai, zaayi duk yanda kace". Zaid ya latse wayan, ya dauko wata 'yar waya ya kira Company dinsu na Bauchi.
*
聽 聽 聽 聽
聽 聽 聽聽 I N D I A

Shopping suka je ita da Vijhay yi ma Maama siyayyan Groceries, kamar daga sama taji wata na Hausa a gefenta, da sauri ta kalli gefenta, Budurwa ce da ba zata wuce tsararta ba,Wankan tarwada ce, sanye take da Jallabiya Milk color,l, da sauri Najwa ta k'arasa gunta.
"Wallahi Mama India ba dadi, ji nakeyi kamar nayi shekara a ciki, abincin nasu ba dadi, spices dinsu na sani amai, banda indomie, da biscuit ba abunda nake iya ci, yanzu ma nazo Kasuwa, bari dai Mama in koma gida mayi waya, a gaida kowa" ta latse wayar, ganin wata ba indiya tayi a gabanta tana kallonta kamar zata hadiyeta, ba tayi mamaki ba, don a kwanakin da tayi a India ta lura da su Mutane ne masu gulman tsiya, da sunga fatar da ba tasu ba, sun dinga kallonsu kenan, ta sakar mata da Murmushi tare da rabata don wucewa, a fili tace "Shegu Magulmata" Najwa ta murmusa tace "Waiyo Allahnmu, me mukayi ake zagin mu?". Chak ta tsaya don mamaki ta maido dubanta ga Yarinyar da tayi magana tace "Hausa naji kinyi?" Najwa ta murmusa tace "Hausan da kikayi ya jawo ni gareki" da mamaki tace "Naga kamar ba indiyace" Najwa tace "itace" "to ta ya ki ka iya Hausa?" Najwa ta mik'a mata hannu tace "Sunana Najwa Sada" yarinyar tace sunana "Aisha Danlami" Najwa tace "me 'yar wace k'asa ce?" Aisha tace "Nigeria" dadi kamar ya kashe Najwa, ta rungumeta kamar ance mata ga Zaid gabanta, Aisha dai ta bita da kallo.
Muryan Vijhay Bhai taji inda yake cewa "Najwa chalo chalate hain(ki taho mu tafi)" dafe kai tayi tace "main aa raha hoon(gani nan zuwa)" Aisha ta kalleta da mamaki tace "kin fara ban tsoro, ga hausa ga India?" "I speak 4 languages" Aisha tace "Wow,ga turanci" Najwa tayi daria tace "Aisha, ina so mu zauna dake, ina da tambayoyin da nake son miki game da k'asarki, i know we just met, you dont know me, i mean no harm, ina so ki taimakeni, ki bani lokaci mu hadu please, yanzu sauri nakeyi Maama na gida tana jiran dawowa na, da munyi magana yanzu" Aisha tace "laah bakomai,sai ki zo SUNY Delhi ina Hostel, we can talk.ki ban numbernki sai in kiraki ban rik'e numbern ba" Najwa tayi dialling Numbernta a wayan Aisha, ta mata godia sukayi Sallama.

聽 聽 聽聽 A B U J A

"50million? Majeed kana hauka ne? Ta ya zaka saida gidan nan Miliyan 50? Ko Million dari ne ai yayi kadan" Hajia Mairo ta fada rai a 6ace kamar ta bigi Majeed. AbdulMajid ya furzar da iska yace "Mummy, its urgent, i had to sell it, kinga nayi settling bank, na kuma kai ma MD kudin Shares dinshi 30million, yanzu saura 5mil" Mairo ta daka tsawa tace "Uban me miliyan 5 zai mana" Daddy yace "Zaayi settling maaikata fa, kar ku manta" Kan Mairo yayi zafi, tace "a zo a Sallameni, naji sauki" Majeed zaiyi magana tace"a sallameni ko na Sallami kaina".
*
聽聽 Nana ba zaiyiwu in dinga hidima da gidana ba inyi da Gidan Sirrikanki, kince na basu Miliyan 20 na basu, ba laifi na bane da aka sace, ba zaiyuw in kara musu ko dubu dari bane, yanda karayar Azzikin nan ya samesu, anya ba zaa raba aurenki da Majeed ba" Nana ta daka tsalle tace "Wallahi baka isa ba, to dama Kudinsu na aura? Kaine fa babana, na san da mun fi su kudi nesa ba kusa ba amma na amince na aureshi,Son shi nakeyi kamar raina, so ko da k'asa suke ci zan zauna dashi, kuma zan bishi Kano, in kaga daman taimaka musu to, nidai ba zan rabu da Mijina ba" ta tashi fuu ta fice daga gidan.
聽 聽 聽 *
Chapter 26 · 0% Book details