Sashe 5
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zeenatu ta basu labarin abubuwan da ya faru tun daga ranan da aka dauketa, ba laifi ta danyi ladab ta nutsu ta bar rawan kai duk da ba a mata wani mugun abun ba, Bayan Sallahr Isha AbdulMajid ya sami Daddy a parlo zaune yake tambayanshi ko akwai wanda yake zargi da yake son ganin bayansu, a iya tunanin Daddy, zuciyarshi ba ta hango mai kowa ba, don shi yana da kyakyawan mu'amala da mutane, Mommy tayi charaf tace "Ai Boy in gaya ma, wannan aikin abokan gaba ne, sun ga Allah ya daukaka Mahaifinku, so suna hassadarshi, shi yasa suka bullo ta haka, amma ta Allah ba tasu ba, zamuyi tightening Security kan ku duka, you shall no go out without an escort" dariyan ba zaiyiwu ba AbdulMajid yayi, yace "sai kace wani dan jariri, aa, i dont need anyone to guard me, Allah shi zai kareni" Mommy ta rude tace "Haba Boy, kar kace haka, ka manta abunda aka maka jiya jiyan nan? Ka manta abunda aka ma k'anwarka? Ko bakaji lokacin da yace 'he's coming for us all?' dole sai munyi taka tsantsan" yace "Mommy, don yayi threatening dinmu sai kar mu cigaba da hidindimun mu? Don kar ya sake mana wani mugun abun? Kar ki manta, duk abunda ya samu bawa daga Allah ne" Daddy yace "haka ne Majeed, amma zaman lafiya yafi zama dan sarki".
"Hello, Nana" a yangance Nana tace"yes, who is this" irin muryar da ke rikita yanmata Zaid yace "Erhm, you shouldnt worry about who am i, rather worry about what i have for you" da mamaki tace "tell me" yace "its about AbdulMajid Abba Abu" tana daga kwance ta mike tsaye tace "meya sameshi?" yace "bakomai, nasan baki da wani burin da ya wuce ki aureshi, i can make that happen"nan da nan ta rude tace "gaya min danAllah" yayi murmushi yace "ki sameni a Silverbird, by 9" dif ya latse wayar. Daga kai tayi ta kalli agogo 8:12pm, da sauri ta fada toilet don yin wanka,da yake guntun tunani gareta, bata tsaya tunanin waye wannan ya kirata ba, kuma don me yake son taimaka mata, sam bata wasa da abun da ya danganci Majeed, don Son shi take sosai tana ji zata iya komai donshi, bayan ta fito daga wanka ta chanchara kwalliyarta,ta dauki makullin motar ta ta bar gidan ba tare da ta nemi izinin kowa ba, ba tare da damuwan dare ba.
Nana Asmau Mati Nakowa diyace tilo a gun Senator Mati Nakowa,ita kadai suka haifa,Sen. Mati da matar shi Sayluba sun dorawa Nana soyayyar duniya, suna mata duk wani abun da take so shiyasa take cin karenta ba babbaka, Nana irin Spoilt brat din nan ne wanda bata da me tsawatar mata,ba tajin magana ko kadan,ba abunda ba ta sha na daga kayan maye, ta bi maza ta bi mata,So Daya ne Tak, shi take wa AbdulMajid Abba Abu wanda kwatakwata ba ta gabanshi, sam bata burgeshi banda Mommynsa da take sonta, duk gidan daga Mommy, Zaineema sai Zeenatu ke sonta, ba da wani abu Mommy ke sonta ba sai don ita diyar Mati Nakowa ce, kuma Hajia Sayluba Aminiyarta ce, idan suka hada yaransu aure, zaiyi raising Standards dinsu, Mommy akwai son Abun duniya gashi su ba matsiyata ba, a cewarta da kudi ake neman kudi, bata abu don Allah, sai don neman suna, shiyasa yake abota da matan Senators, Gwamnoni da masu hannu da shuni, garin shishiginta ne ta shige ma Hajia Sayluba, ganin Nana na ma dan Mommy mahaukacin So ne yasa ta neman ma diyarta auren Majeed, Mommy kuwa tace Aure anyi an gama, duk yanda ta bi da Majeed don ya amince da Nana ya k'i, ya bujire mata, tayi tayi amma a banza,Daddy ya sa baki amma Majeed yace "ba kalarshi bace, bata da kamun kai" Shekaru biyu kenan ana bin Majeed ya Yarda yak'i, ita kuma Mommy na da san 'yaya, bata so ta tilasta mai, tace a bari ya sauko har ya amince da kanshi sai ayi. Wannan kenan.
Inda ya mata kwatance a Silverbird din ta nufa, sai dai ta duba bata ganshi ba, ta latso last call dinta, tace "Hello banganka ba, kana ina?" cikin yanayinshi yace "turn around" tana juyowa ko taga mutum a bayanta har tana niyyar bigeshi, ta dan ja baya,kallo ta bishi da shi sama da k'asa,"Wow, guy dinnan ya hadu sosai,na k'wadaitu dashi, don dai Son gaskia nake ma AbdulMajid da shi na aura, amma shi wannan din sai na huta dashi ko so daya ne" cikin sakwan da be wuce goma ba tayi tunanin nan, a zahiri kuma tayi wani shuumin murmushi tace "Ouch, ka ban tsoro" a dakile yace "lets talk shall we?" be jira amsarta ba ya wuce kan kujerun da suke jere a gun ya zauna, ta ta6e baki tace "shi kuma wannan wani iri ne" ta bi bayanshi ta zauna. Ya fara magana ba bata lokaci, "idan kin koma gida, kice da Babanki, da ya ba AbdulMajid gudummuwan 20million,idan ya tambaya na meye sai yace saboda 6arayi sun tare shi suyi robbing dinshi ne, shiyasa ya bashi gudummuwa ya maida abubuwan da ya rasa bayan nan, sai ki ritse AbdulMajid ofcourse bayan kinsha 'yan abubuwanki in otherwords 'drugs' yanda zakiji dadin aikinki, ki danyi making Scene na idan be aureki ba zaki kashe kanki,and kawo kunnenki" ya rada mata wani abu a kunne, shewan murna tayi, wow, meyasa bata taba tunanin hakan ba, lallai this guy gt the brains,har ta fara murnan ta auri Abdulmajid,chan kuma sai ta kalli Zaid tace "Ya Sunanka? And why do you want to help me?" murmushin da ke sa 'yanmata raina kansu ya mata, yace "i love helping people" tace "dagaske? Maybe zaka iya taimaka na" ya mik'e kai tsaye yace "kiyi abunda nace kiyi, zaki ban labari".
Ya wuce ya barta Zaune, bata wani damu ba, babban burinta ta mallaki AbdulMajid Abba Abu.
Grand towers Hotels
Idonshi lumshe cikin kwamin wanka, da alamun yana jin dadin ruwan nan, ya gama da Abuja kuma, be yi zaton abu zai zo mai da sauk'i har haka ba, amma bayan tataunawar shi da Nana ya ga Alamun cin nasara, kara shiga cikin ruwan yakeyi, Jijiyar gefen kanshi tayi tsaye yayin da abubuwan da suka faru a baya suka shiga dawo mai kamar a lokacin suke faruwa.
聽 TUNA BAYA
Mallam Abubakar Dikko asalin mutumin K'asar Sudan ne, Hijira yayi ya dawo Nigeria don k'uncin rayuww, Mutum ne mai wadatan zuci, yana da hangen nesa, yana da kuma da kirki sosai, 'Yar fillo Hajjo da ke kawo mai fura yana siya a kasuwa inda yake sai da Azurfa da Zinari ya Aura, Hajjo mace ce mai tsananin Kyan gaske irinsu ne a ke kira da sadaka yalla, a nan cikin Unguwar Rigiyar Zaki ya kama musu gida, Bayan Aurensu Mallam abu ya bude makarantar Allo a k'ofar gidansa yana koyar da Almajiran da basu wuce 10 ba.
Bayan Shekara daya, Allah ya azurta Hajjo da Juna biyu, dadi kamar ya kashe Mallam Abu ji yake kamar ya hadiyeta don dadi, kula ta musamman yake bata, da wuri ma yake tasowa daga kasuwa, bayan Allah ya sauketa lafiya ta sa mu Danta namiji lafiyyaye, ran suna yaro yaci sunan Mallam Abu inda aka mai inkiya da ABBA聽 haka suka cigaba da rainon Abba har Allah ya k'ara ba Hajjo juna biyu bayan Haihuwar Abba da wata 1, ji take kamar tayi kuka amma da lallashi da bin baki ta hakura, Mallam Abu ya samo mata wata tsohuwa mai kula da ita, bayan wata 9 ta sake haihuwan Namiji, ran Suna yaro yaci sunan Baban Hajjo wato SADA.
聽 聽 聽 聽 聽聽 Wata Goma tsakanin Abba da Sada amma sai kayi zaton shekarunsu daya, don girmansu daya wayon su daya, haka suka dinga Kula da yaransu har suka kai munzalin shiga makarantar boko, wani Firamare na cikin unguwa Mallam Abu ya kaisu, dama tun suna shekaru 3 yake fita da su gaban gidanshi ya hadesu da Almajiran da yanzu sun fi 30 ya koya musu.
A halin yanzu zaka gane banbancin Abba da Sada, Abba yaro ne da ka ganshi kasan dan fari ne, gele ne sakarai, baya maida hankali a karatun shi, Mallam Abu kuwa na hukunta shi tare da wanda ba sa maida himma, haka zaije gida yayi ta ma Hajjo kuka, wai Mallam baya sonshi,yafi son Sada, hankalinta na tashi idan yace hakan, haka zata dinga janshi a jiki tana lallashi don dai ya bar jin wani iri, Abba na da tsokanan fada kuma idan ya jawo fada Sada ke shigan mai, baida wani wayau sai yanda abokan su sukayi dashi. Sada ko yaro ne mai wayau mai himma, ga tattali, duk k'ank'anta kudi sai ya tara su, Abba ko da ya cinye kudinshi zai bi na Sada ya dauke, Sada be magana. Mallam yafi Jan Sada a jiki saboda yafi himma kuma yana son yaron saboda ya san ya kamata. Hajjo kuwa a baiyane take nuna tafi son Abba, don a ganinta Mallam na nuna dayan biyu, shiyasa take jan Abba jiki,ta goya mai baya kan komai, zai lallata abunsa yace na Sada yake so, Sada sarkin hakuri yana gani zata kwace nashi ta ba Abba kamar bashi bane Yaya. Wannan kenan