← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 128

Sashe 86

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tambayoyi zuciyarta ta fara jefo mata"To shi wannan Zaid din wanene? Meye hadinshi da su? Ta ya akayi ya san Tarihinta? Ko dai Coincidence ne?" da sauri ta karkada kanta "Babu yanda zaayi ace wannan shine Zaidun Sada, Guiltiness kadai ke addabar Zuciyarta, ba wani Zaidun Sada, wannan be da wata alaka da Dan K'anin Mijinta, kowa ya san Mahaifinshi Sadam Audu Gatan Marayu, ba shi bane ta fada tana jin hakan na zama a Zuciyarta, Zuciyarta ma bata so ta sa abun a ranta ballantana ta yarda da hasashen da a baiyane yake, Zuciyarta ta karyata mata duk wani tunanin da yake kawo mata, ga zahiri tana gani, amma ta rintse ido tace ba haka ba, Zuciyarta na gaya mata karya, taki yarda ta amince da gaskiar da yake a baiyane, bata so ta yarda da zahirin gaskia, Zuciyarta ta dinga gaya mata abubuwan da take so ta yarda dasu.

To shi wannan Zaid din me yake so? Meyasa ya gaya mata bakaken maganganu? Meyasa ya ke son rabata da Ziyada? Hankalinta ya tashi ainun da ta tuna Ziyada na gurinshi, kuma yana so ya musu farraqu, hankalinta ya tashi da ta tuna Zaid ya fi karfinsu, Zaid fa qya linka Alhaji Nakowa so dubu dari, ta kasa karawa da Alhaji Nakowa ina zata fara da Gatan Marayun da Arzikinshi ya karade Afrika gabaki daya? Tata ta kare,
Nan hankalinta ya sake tashi, ita ba wannan ba, ita dai ta samu Ziyada ta dawo garesu, hankalinta ba zai taba kwanciya ba sanin Ziyada na tare da wannan Mutumin me kyaun dan Maciji, hankali tashe ta nufa Gida don su samo Mafita.
****

"Mummy Don Allah kiyi shiru, ki bar Ihun nan haka"cewar Abdulmajeed cikin damuwa, kamar an kara ingizata ta kara fasa wani ihun, Hajjo tace "Hajia, komai yayi zafi maganinshi ALLAH, ki yi ta sallalami, ko menene zai zo miki da sauki, Daddy ko ya gama kulewa matuka da wannan iface ifacen da mummy keyi ya zata ganin Ziyada a gidansu na da ne ya sata hauka haka, cikin bacin rai yace "Haba Maryam, Haba Maryam, me kikeyi haka? Ke wai yaushe zaki girma ne da in abu ya sameki ki daina Ihu? Kin tasa yara gaba kina Ihu, me kikeso ki yi? ki daga musu hankali? Nima ki daga min?" cikin kuka tace "don ba kaga Halin da Ziyada take ciki bane da baka tsaya nan kana min fada ba" da sauri suka hada bakingun cewa "Me ya samu Ziyada?"duk suka maida hankalinsu gunta ta ja majina tace "Mun aura ma Mugu ita, ya na son raba mu da ita, bayan ya siya Gidanmu dan cin fuska ya kaita Gidan, yanzu kuma ya saka jamian tsaro, wai kar wanda ya zo mishi Gida ita ma ba zata fita ba, kuma ya karbe wayarta"..

Jikin Majeed ya fara rawa, Daddy ya samu bakin cewa "to saboda me?" Mairo ta karbe tace "Ohon ma Shegen, wasu surutai yake tayi marasa kan Gado, ba ku ji bakaken maganganun da yake ta gaya min ba kamar na kashe mai wani, tsanarmu a fuskarshi nake ganinshi, ya yaudare mu da halaiyanshi na gari, ashe kyaun dan maciji ne, gabanshi fari cikinshi bakikirin,da alamu dan shayeshaye ne don sai da yayi tatul ya zo ya tata min rashin mutunci, Ziyada harda Suma".

Abdulmajeed hankali tashe yace "to wai duk saboda me? Me muka mishi Mummy? Ko be yarda damu bane? Ko zaton makwadaita yake mana shiyasa yake son ya rabamu da ita? Wallahi ba ruwanmu da abunda ya tara, in gani yake Auren kudi mukayi mata wallahi yayi kuskure, Mummy ni fa ban ma gane ba" Mairo tace "da ba gabana akayi ba da nace karya ne, ni bansan meyasa yake haka ba, bansan me muka mishi ba, wai randa aka kaita Porthacourt ya tafi, Ziyada kadai ta kwana cikin wanann wakeken Gidan" Daddy ya jinjina kai cikin tausaya ma diyarshi yace "ga Ziyada da tsoro baiwar Allah".
Mummy tace "wai be taba sonta ba, wai be aureta don so ba, ya aureta ne don ya mata wulakanci" Daddy yace "Maganar banza da wofi, in ya san be sonta meyasa ya Azazzala sai ya aureta cikin kwana biyu? Meyasa ya tado manya masu fada a ji a Nigeria suzo neman mishi Aurenta? Kuma na san in ba da dagaske yake ba Alhaji Ado ba zai bata lokacinshi ya dauko Aminanshi suzo neman aurenshi ba, ba kuma za su kashe kudinsu a banza ba, har dai bashi suka biya mana na Miliyan25 muka rabu da Alhaji Nakowa for what? Ba don shi sukayi ba? Nidai banda komai balle ace wani abu suke nema a guna shiyasa suka zo neman Diya wurina, in Kudi ne ai su ne Kudi, to maganar be aureta don So ba be tashi ba, in laifi aka mai ai sai ya fada ayi sulhu, in kuma misunderstanding ne sai a zauna a tattauna har a gano inda matsalar take, amma Koma dai menene harda Yarinta".

Abdulmajeed yace "nidai bari inje Gidan inga halin da Ziyada take ciki" Mairo tace "wallahi wahalar banza zaka sha, tunda kaga na dawo ba tare da Ziyada ba kasan cewa abun yafi karfina, Ihun nan da kuka ga ina yi, na takaici ne, na takaicin diyar mu na cikin wani hali bamu da yanda zamu fito da ita, bamu da abun da zamu iya yi, sai dai mu nemi sauki daga gareshi". Nan sukayi jugunjugum, har dai Abdulmajeed ya mike yace "hankali na ba zai kwanta ba har sai na san halin da take ciki" Daddy yace "Muje mu ga" Mairo tace "sai kun dawo" tana rungume zinatu da duk suke ta hawaye ita da Zaineema da Hajjo.

Tausayin Ziyada ya kama Najwa da ke rungume da Muhsin tunda Mummy ta shigo tana ihu shima ya fara kuka, itama Najwar kwalla take, Muhsin ya tashi yaje gun Mummynsa ita kuma Najwa ta shige daki don ta basu gu don jajanta ma juna, Daki ta koma tana tausaya ma Ziyada, mamakin Mijin Ziyada take, wai dama shi ya siya Gidan, don rashin kirki ya kai diyar chan? Kuma yana son rabata da danginta, kuma ya wulakanta Mummy? Ziyada harda Suma kuma har yace be taba sonta ba yanda Ziyada take mutuwar sonshi? "How can someone be So Heartless?" ina ma zata iya fitar da ita daga kangin da take ciki, saboda Ziyada ta taimaka mata a wurare da dama, ita haka take bata son taga wanda take tare dashi ya shiga damuwa, haka kurum ta fashe da kuka sanin yarinyar da take sonta kuma kanwa ga Jaan dinta na cikin wani hali kuma ba abunda zata iya yi game da hakan, sosai take kuka kamar laifinta ne, a wannan hali Maaman ta ta kirata.

I N D I A

Maama ta bude murya tace "Papi, kayi sauri ka fito, lokacin waya da Najwa yayi" jim kadan sai ga Paapa ya fito tare da shagwabe fuska yace "haka jiya kika kirata bana nan, sai dai daga baya na kirata kuma har ta fara bacci" tayi daria tace "sorry Papi, gani nayi ba zan iya jiranka ka dawo daga Aiki ba, amma daga yau ba zamuyi waya baka nan ba" yace "yauwa Yesmeenah, oya kirata" ta danna kiran wayan Najwa gami da sa handsfree.
Haka suke a daidai wannan lokacin suke kiranta su ji ya take, in tana da bukatar wani abu, sun fi so su kirata don ita ba zata juri kiran India ba don charges din akwai yawa, ringing biyu ta dauka da Sallama,
Jin muryarta a disashe yasa Maama tambayarta meke samunta? Ko bata lafiya ne? A takaice ta ba Maama labarin halin da Ziyada da Family dinta ke ciki, sosai Maama ta jinjina labarin, tana me tausayawa ma Ziyada kuma tana me kyamatar Mijin Ziyadar ta kuma lallashi Najwa tace ta bar damuwa, ta tayata da addua shi ta fi bukata.

Najwa ta gyada kai kamar Maaman na gabanta ta share hawayenta tace "Maama kiyi Hakuri, kuyi hakuri Please, i am so sorry, i'm useless wallahi, its like kamar nazo hutu ne Nigeria, har yau na kasa cika promise din da na miki, bansan ta inda zan fara ba, abubuwa da yawa sun faru, i'm lost, duk sanda nayi niyyan fita fara neman Bhaiyya na, sai wani abu ya faru da su Abdulmajeed, shine dama zai taimaka min, and its not right suna cikin wani hali kuma in fito mai da bukatana, ina so komai yayi settling ne, ku kars hakuri".
Maama tace "Najwa Diyata, Allah ya miki Albarka, Allah ya saka miki da Aljanna Firdausi, amma ina so ki dawo Gida, na hakura, hawayena kike so su tsaya? To wallahi sun tsaya, in ba so kike hawaye na ya cigaba da flowing ba to ki dawo Gida, hankalina zai kwanta in kina tare dani, hankalina be taba kwanciya ba tunda na san cewa kina Nigeria cikin mutane irin su Mijin Ziyada, na yafe please, come back home" ta karashe tana shesheka, itama Najwan Kuka takeyi tace "Maama, Please hang on a little longer, zan dawo Gida Safe InshaAllah, i'm in safe hands, zuwa Karshen Month dinnan in ban ganshi ba zan Dawo Gida, I promise".
Paapa yace "Najwa, Nigeria na da 36states, and atleast 774 localgovernment area, ta ina kike son fara neman shi? Da me zaki fara nemanshi? Hoto? Wannan hoton fa Zane ne, wa zai ganeshi? Ki ji Maamanki Najwa ki dawo Gida, ana ta wuceki a School, ki dawo Please" Najwa cike da tausayi da son Mahaifanta tace "Paapa, support dinka nakeso, ka kwantar ma Maama hankali, i know he is still out there lonely and alone, ku dan karamin time din da nace, karshen Month din nan, in ban ganshi ba, i am coming home, i promise, Kaji Paapa na? " Paapa ya suake Ajiyar zuciya tare da kallon matarshi ta gyada mai kai alamun ta amince, yace "You have till end of this Month" da dan dariyarta tace "Thank You Paapa, I love you Both".
*
N I G E R I A
Chapter 86 · 0% Book details