← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 128

Sashe 39

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 6 min read

barsu da Mummy, "Mummy donAllah ki dinga hakuri, yarinyar nan abun tausayi ce, Mom donAllah ki kara hakuri, nan da lokaci kadan zata koma wurin Iyayenta please Mommy" ita bata san meyasa ba ta tsani yarinyar, zuciyarta kanyi zafi duk lokacin da ta hada ido da ita,yanzu ma bata son maganar da sukeyi, tayi saurin chanza maganan ta hanyar cewa "Dan Deputy Governor Amjad yaga Ziyada yana so kuma, zai zo" Majeed yayi shiru chan yace "ina fatan ba tallanta kikayi ba" Mummy tace "aa wallahi ina gida Mom dinshi ta kirani ta ke rokana wai yaronta yaga Ziyada yana so, kuma dama tana son mu karfafa zumuncin mu" ga yanda tayi magana zaka rantse da Allah iyakar gaskiarta kenan, Majeed yace "to duka Ziyadan kwana nawa tayi a Kanon tunda muka dawo garin? Ina ya ganta?" Mairo ta daburce tace "Oho fa, kila ko a makaranta, ai inaga ba damuwa bane ba ko?" Majeed yace "hakane, amma in Ziyada bata so, sai dai yayi hakuri". Mairo tayi yak'e tace " Eh mana" amma a ranta tace "dole ko ta yarda". * "Zaineema kidaina zama cikin daki, ki dinga fitowa cikin 'yanuwanki, kullum ki dinga kulle kanki cikin daki? Sai kin kamu da wani ciwon?" kamar jira takeyi ta fashe da kuka tace "Wallahi Daddy sharrine, sharri aka min, ba ruwana da kowa, ban taba sanin wani da namiji ba in ba Khalid ba, Daddy ya k'i yarda dani, ina son Khalid, ina son komawa dakina, i dont want it here" Daddy ya rungume diyarshi yana shafa bayanta, yana matukar tausayin yaranshi, ba yaran kadaii ba, shima yana tausayin kanshi, akwai abubuwa da dama da be san yanda zai fassarasu ba, akwai abubuwa da yawa da yake sonyi, amma ya kasa, akwai abubuwa da yawa da yake son ya tabuka, akwai abubuwa da yawa da yake son tunawa amma be iyawa. Kwalla a cika mai ido yace "Zainee, hakuri zaki cigaba dayi, ki mika wa Allah Alamuranki, inaji a jikina komai yazo k'arshe, tashi kiyi wanka yaruwarki ta dawo, na san duk hayaniyan da akayi ba ji kikayi ba don hankalinki be gurin" Zainee tace "Ziyada ta iso?" kai Daddy ya gyada mata ta mike tace "barin shiga toilet". Ya murmusa tare da fita daga dakin. * Add Shiga dakinta tayi, idonta ya sauka kan Bakuwar da ke kwance kan Gadonta, jefi jefi take sauke ajiyar zuciya, Ziyada ta kutsa kai sosai cikin dqkin ba tare da tace ma Najwa komai ba ta shige toilet, Najwan ma bata san ta shigo ba, wanka Ziyada tayi ta fito ta shafa mai ta sa kaya. Jin motsinta ya sa Najwa dagowa a hankali, idonta fes kan Ziyada, ta madubi Ziyada ta ga Najwa na kallonta, kamar karta juyo, amma sai ta samu kanta da juyowa sosai suna fuskantan Juna. "Me yasa muke yanayi? aa ba yanayi mukeyi ba kama mukeyi, kama ba na wasa ba" zuciyar Ziyada ta raya mata, tunanin da Najwa keyi kenan itama shi din takeyi, chan sai tayi murmushi har ranta tace "Ziyadatu, welcome home, i'm so sorry nayi using dakin ki, nayi using toilet dinki, nayi using kayanki, nayi using Gadonki, kiyi hakuri, Ya Majeed ya kawoni nan" Ziyada kallonta kawai takeyi sosai kafin chan tace "Dont worry, i dont Mind" ta juya ta cigaba da shafa Mai, tana gamawa ta bude wardrobe dinta ta zaro Doguwar riga ta saka. Zinatu da Muhsin suka shigo dakin da gudu suka rungume Ziyada suna fadin "Oyoyo Ya Ziyada" murmushi tayi tace "Kun kwaso warin rana kuke hugging dina? Ku wuce kuyi wanka ku cire uniform" Zinatu tace "Dhurr, bana warin rana saidai Muhsin" Muhsin yace "liar, Ya Ziyada, ina Chocholates din da kikace zaki kawo min?" ta mik'e ta jawo jakkanta ta ciro ledan Chocholates ta bashi, ya fita da gudu yana murna. Zinatu ta tabe baki tana ma Ziyada nuni da Najwq tace "kingan Karuwan nan? Ya Majeed yazo da ita" Ziyada ta dago cike da tashin hankali idonta bude tace "Zinatu, ina kikaji wannan word din?" Ko a jikin Zinatu tace "Aunty Nana tace Karuwa ce" Ziyada tace "Get out" Zinatu tace "What?" cikin daga murya tace "nace "ki fita" Zinatu ta buga tsaki tace "mtsw dama baki dawo ba" kafin ta fita. Ta gefen ido take kallon Najwa, da alamun taji abinda Zinatu ta fada, haka kurum Ziyada taji ba dadi, sharewa dai tayi ta ciro Chocholate DiaryMilk ta ba Najwa, Najwa ta girgiza kai Alamun Aa, Ziyada ta ajiye mata kan cinyarta, ta juya ta bar dakin, Najwa ta bita da ido, kafin ta dauki Chocholate din tana sha, tayi missing chocholates sosai, Ziyada taji tausayinta, Majeed ya bata labarin haduwansu, ita bata da matsalan zama tare da ita. *WASHEGARI Kamar yanda aka fi cewa, Ziyada tafi kowa Miskilanci duk cikin yaran Hajia Mairo, ba ruwanta da kowa, magana be dame ta ba, Miskila ce, ba ta shiga harkan kannenta balle raini ya shiga tsakani, tana jan Girmanta, bata shiga harkan da ba nata ba, shiyasa ma yanzu ta cigaba da cin Abincin da ke gabanta, ba tare da ta tanka Mummy ko Nanan dake ta muzgunawa Najwa ta hanyan sata aiki mara amfani, tana sane dasu amma sai tayi kamar bata san sunayi ba, har lokacin da Nana ta daga hannu ta kamtse Najwa da Mari wai don ta kawo mata Plate, plate din ya fadi kasa by mistake, sai kawai ta mareta, Najwa taji marin nan sosai, Ziyada kamar zatayi magana amma ta fasa don a ganinta ba ruwanta, kuma ai Najwan na iya ramawa, sai kuma Mummy da ta rankwasheta wanda ta ga hawaye a idon Najwa. Rigimar Nana yasa ta cewa Najwa ta tashi ta mata Ginger Juice, akwai Ginger a fridge, tayi grating tayi sieving, Najwa ta shiga kitchen din don cika umurnin Nanan, Mairo tace "Maiya ai naso ta kawo gardama yanzu in nakasa shegia, wallahi s tsaneta kamar mutuwana" Nana tace "Wallahi Mommy na fiki tsanarta, sai kinga yanda My Majeed ke damuwa da ita" Mummy tace "Ziyada kinyi kokari da kika kwana da ita, Yayanki be jin magana wallahi" ko tak Ziyada bata ce ba. Najwa ta fito kanta a k'asa, ta kawo musu Ginger juice din, ta ajiye, Nana tace "danuwarki zo nan, ni zan zuba?" Najwa ta a matso sumsum ta zuba mata a cup ta bata, Nana ta kai baki, taji wani gartsi garsti ta zubar, tare da mik'ewa tace "donubanki kasheni kike sonyi? Tarugu kika saka?" Najwa ta fara zare ido, tana girgiza kai tace "Nahii" "Mummy sha kiji" inji Nana "Mummy ta kai baki ta furzar da sauri, ta dauki Jug din ta watsar ma Najwa Ginger a fuska, sai idon Najwa, Dif Najwa tayi na tsawon seconds kafin ta sa ihun " YA ILLAHI, IDONA". Ko a jikin Mairo illa dukkan da ta hau Najwa dashi Nana na tayata"Kafin ki kashenu da yaji gwara na nakasa ki, don ance kiyi mana Ginger Juice zakije ki sa mana tarugu?" Ziyada cikin zafin rai ta finciko Najwa daga hannun Mummy, ta jata sukayi daki, Mummy na kiran Ziyada, Ziyada tayi burus da ita, Najwa kuka takeyi don wani irin radadi da zafi takeji a idonta, kila shes going blind, makanta ya sameta, ji tayi ana wanke mata ido da ruwa, muryan Ziyada taji tana cewa "ki bude idonki" girgiza kai Najwa ta hau yi irin ba zata iya ba, Ziyada tace "ki bude, in ba haka ba, zaki makance, gwara a wanke, yunkurin budewa tayi amma radadin ya sa ta runtse ido tana kuka sosai, Ziyada a tausaya mata, da kyar ta wanke mata idon tasa kafin fa hure ba idon ba harta fuskarta yayi Ja, Ziyada ta jawo hannunta ta fito da ita daki, kwantar da ita tayi kan Gado tana mata sannu, ta fita chan sai ta dawo da Gishiri ta sa mata a baki tace ta lasa. STORY CO
Chapter 39 · 0% Book details