Sashe 63
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
but InshaAllah when everything is settled Ya AbdulMajeed zai kawo ni" bata san uzurinta ba amma tace "OK Baby, hada min Kayan Mama, Ki kawo mana Parlor, ta waiga ta ga Hijab din Hajjo, ta dauka ta saka mata, ta tayar da ita, rike da hannuwanta suka isa Parlo, Bakinciki uwa ya kashe Mairo, Daddy ko Dadi kamar ya shideshi, har na dan lokaci kadan ya manta da damuwar da suke ciki, ya ji dadin yanda Aynarh kema Mamarshi. Ziyada ta fito hannunta dauke da dan karamin trolly a kunne Majeed tace " Ya Maji i want us to talk" Majeed yace "now?" ta girgiza kai tace "lokacin da kake da lokaci" ya ja hancinta "Zuzu ina da Lokacinki Always, gaya min damuwarki" baki na dan rawa tace "dama wannan ne yace yana so yazo Gida" Majeed ya ja numfashi, suna da babbar matsala yace "Zuzu, akwai abunda ya faru, ki bari in komai ya zama settled sai yazo ko? Daga fuskarta ya karanci ranta ba haka yaso ba, ta kirkiro murmushin da ko labban bakinta be kai ba tace "OK" ajiyar zuciya yayi yace "Fine, bayan kin dawo School gobe, zanzo Gidan Aunty Aynarh, then we talk OK?" kai ta daga mai tare da Murmushi. "Anya Hajia Aynarh ba mu daura miki nauyi ba? Hardasu Mama?" cewar Daddy, Murmushi tayi tace "Meye daurin nauyi? Ka manta duk Girman Gidan nan nikadai ke ciki sai masu Aiki, ai ni bazan damu ba in ku duka zaku koma Gidana" Mairo ta wurga mata harara ita ko ta kashe mata idanu, Majeed yace "Zuzu ina Zaineema?" Ziyada tace "Uhm tace ita zata zauna nan, ba zata ba" Majeed yace "Barinje in ganta" Dakim ya nufa, da k'yar ya shawo kanta ta samu ta hada kayanta, a tare suka fito, Majeed yace "to Pure Heart kefa?" duk suka waiga gun da Majeed ke kallo, duk ta daburce dauke da kayan Hajjo, tace "Erhm, umm ni ina nan, zan taya Mummy da aiki" Mairo ta galla mata harara, Majeed ko yaji dadi, yana son ya dinga ganinta ko hankalinshi zai kwanta. Daddy yace kuzo kuyi ta tafiya kar Magariba ya muku a hanya, Majeed ya ja Akwatin duk suka fita Waje banda Mairo da ta koma daki don kanta da ke barazanar fashewa, aka sanya kaya a booth, suka shiga Mota, Hajia Aynarh harda makala ma Hajjo seatbelt kamar zasu bar garin, Daddy dadi dai, suka daga musu hannu byebye suka tafi. Wayarta yayi k'ara, tafi so in sun kirata taje chan Bq suyi wayarsu, don nan zata sake tayi magana, da sauri tayi baya don amsawa, kamar yanda take hoping su Maama ne, sun dade suna waya kafin ta yo hanyar cikin Gida, lokacin Gidan ya fara duhu, alamun Sanda taji, tana waigawa taga Nura ya shigo ta gate yana magana da Maigadi, nan Maigadi ya karantar dashi komai, na ganin da yayi an fita da Yaran Gidan da Hajjo, Zaid ya jinjina kai ya ciro abu ya mika ma mai gadi, kafin ya sake sanda yana takawa cikin Gidan, Shikenan, ta kama Nura na magana da Maigadi, wato Maigadin ma minahiki ne, yaci saa ba wanda ya ganshi, yana shiga Daki AbdulMajeed ya fito daga toilet Majeed yace "Allah Sarki Bawan Allah, shaf na manta daku, abubuwan sunyi yawa kuyi hakuri kaji?" Nura dai kafeshi da ido yayi, ciro wata takkada yayi a cikin dukunnanen Aljihunshi ya mika ma Majeed, Majeed ya Murmusa ya karba ya fara karantawa; _ Assalam Alaikum, ina me baku hakuri ga Dawainiyar da kuke da mu, nasan kuma kuna fama da kanku, hakan yasa ni tafia neman danginmu a k'auyen Bichi, InshaAllah zan dawo nan ba da dadewa ba don tafiya da Yaya Nura, ku cigaba da kula min dashi, Ubangiji Allah ya saka muku da Alheri. Nagode nice Naeelah_. Allah Sarki cewar Majeed, Ya kamo hannun Nura kamar ya san me yake cewa yace "Kayu hakuri, zaka daina ganin k'anwarka na dan lokaci, zata je ta dawo kaji" ya shafa kanshi kamar dan yaro, yace bari naje Masallaci nayi Sallah, Majeed ya fita daga Dakin, a Parlo suka hadu da Daddy shima Masallaci zaije, Zaid na kallonsu ta hannun kofa, ya ciro waya ya kira Ziyada, nan take shaida mai sunzo Gidan Wata Auntynsu, chan zasu kwana, a hankali yayi ta bugun cikinta har sai da ta gaya mai abunda yake son sani, ya mata Sallama yace "zaije Masallaci" A fili yace "so ba kowa a Gidan yanzu? Daga ni sai Mairo, sai Zaineema? Perfect, ya fito daga Parlo ya nufa gun Maigadi, yace " bani abun nan da Arm ta kawo jiya" jiki na rawa Maigadi ya dauko ya bashi, Zaid yace "yaushe zasu dawo?" Maigadi yace "Chan suke Maghrib da Ishai, so sai bayan Ishai, sai ma sun gama karatun Masallaci da sukeyi bayan Ishai, so zasu kai 8;30" Zaid ya Murmusa yace "yanzu 6;22, ina da lokaci, Maigadi ya Murmusa Zaid ya shige ciki, daidai k'ofar Dakin Mairo ya zubar da wani abu, kamar ruwa, in ba ka kalli wurin ba, ba zaka san akwai abu a zube ba, Murmushi yayi na mugunta, da tafito ta taka zata sul6e ta fadi, k'ila ta samu karaya, ko tsagewar kafa, ko gocewar k'ashi, Allah ya sa duk abubuwa Ukun su sameta" A ranshi yace "da kin fito Hajia Mairo, zakiyi muguwar faduwa, wani mummunan abu zai samu k'ashin jikinki, ko na hannunki, ko na bayanki, ko na kafafunki ko kuma duka, Allah sa haka" ya wuce dakin Majeed cike da Annushuwa. Add Duk abubuwan da yake kan Idon Najwa, tunda taji an bude kofan dakin Majeed ta leko, tasan ba lafiya ba, ganin Nura ya shigo da wani abu yayi hanyar dakin Mummy, ta san cewa he's upto Something, Sai da tayi kusan Minti 11 tana neman abunyi, kafin ta yanke hukuncin dauko Mopper, a hankali ta bude kofan, ta karasa gaban Dakin, tsugunnawa tayi ta lakuto abun kasan, kamar mai, kamar sabulun ruwa, yauki da santsi gareshi, mopper ta sa ta goge, ta shiga toilet ta wanke Mopper din, ta dawo da ruwa ta zuba ruwa a kasa ta sake gogewa, santsin da yawa, sai da ta dau tsawon lokaci tana gogewa kafin ya gogu, har ta taka taga lafiya lau, ko Mummy ta taka ba abunda zai sameta. Da sauri ta koma ciki. Kasa kunne yayi don jin Ihun Hajia Mairo, shiru ba wani labari, har kusan awa daya ya shude, ya na jin karad bude k'ofa ya mike da sauri yana lekenta, dadi ya ziyarceshi, tana fitowa ta wuce kitchen, baki bude Zaid ya bi inda ta bi da ido, ya akayi haka? Ta wurin tabi ya sani, ranshi a bace ya latso wayar Armstrong, yana mai fada, abunda ya bashi beyi ba, ko tangarda batayi ba balle ta fadi, Arm da mamaki yace "Ka tabbata ta wurin ta bi?" a fusace Zaid yace "what nonesense? Ba ni na saka da kaina ba? Ta wurin ta bi" Amstrong yace "it cant be, abun nan yana da karfi, ko lightly ta taka sai tayi mummunan faduwa balle tiles ne santsin yayi yawa, its impossible ace ya bushe, maybe wani ya gani ya goge" Zaid yace "kar ka gaya min maganan banza, wa zai goge, ba kowa a gidan fa" haushi ya sa Zaid kashe waya, ba haka yaso ba, yaso Hajia Mairo ta nakashe, wuri ya k'ure amma zai san abunyi kafin gobe. Haka ya dauro Alwala yayi Maghrib. WasheGari Da sassafe Aunty Ainah ta tashi ta hada masu breakfast da taimakon masu Aiki, ta shiga dakin Yara, ta tashesu, ta umurce su da suyi Sallah, ta ja su kan dining, ta zuba musu breakfast, Dankali da liver sauce, sai Tea a gefe kuma farfesun kayan ciki, sosai sukaci, kafin ta ja Muhsin ta fara mai Wanka, sannan ta chuda Zinatu, ta shirya su cikin Uniform dinsu, kafin ta kaisu Makaranta da kansu bayan tace lokacin break zaa kawo musu Abinci, su fada me suke so, Muhsin yace Indomie and Boiled Egg, Zinatu tace Friedrice da coslow, tace "Alright zata kawo musu lokacin break " da ta dawo Gida tayi nata wanka, ta lek'a dakin da aka sauke Hajjo, har k'asa ta durkusa ta gaidata tace "Mama Ina kwana, ya kwanan bakunta?" Hajjo ta amsa da faraarta tace "Mama ki fito muyi Kalaci" tare suka fita, Ziyada ta sauko shirye cikin wasu riga da skirt na Material, ta gaidasu duka, ta tambayi su Zeenah, Aynarh tace "haba ai sun dade makaranta". Sukayi breakfast tare tace ma Ziyada ita zata sauketa Makaranta, sannan ta wuce Aiki, ta ba yan aiki umurnin karfe 9;30 a gama Abincin Zeena da Muhsin zata zo ta dauka, bayan tace da Hajjo ta saki jikinta sai ta dawo ba dadewa zatayi ba, Sukayi ma juna Sallama ta musu fatan a dawi Lafiya, Hajjo ta kwadaitu da halin Aynarh, har tana cewa InshaAllah in komai ya lafa zata sa Abba ya aureta, don ta lura yana sonta itama. Yau ma kamar kullum dukkan su Uku suka fita, ko wanne da abunda yaje nema, Daddy yan bugabuganshi yaje, Mummy neman mafita take, Majeed kuwa yaje bada ciguyar me sayen Gida ne, Zaid najin kanshi a sama, shi kadai a Gida, wani tunani yazo mai, zai samu dama cin uban Mairo hankali kwance, waya ya dauko ya latso Armstrong. Ringing daya ya dauka, be tsaya amsa gaisuwan Amstrong ba yace "Bring me Cocaine" Amstrong ya san iyakacin Zaid Giya, ko sigari be sha, yau shine da cewa a kawo mai Cocaine? Me zaiyi dashi? Amstrong yace "what for if i may ask?"a fusace yace "stop asking questions and do as i say, Now" ya kashe wayan, ya kalli Tea da Bread din da Majeed ya kawo mai kafin ya fita yayi tsaki, ta ya zai fara shan wannan abun? Sake latso Armstrong yayi yace "ya taho mai da breakfast". 2pm Lecture daya tayi ta dawo Gidan Anty Ainarh, Waya suke tayi tun bayan Sallahr Azahar, fake feelings dinshi yake ta karanto mata, ta yarda da duk wani kalamanshi, duk maganar da yayi ya samu zama a zuciyarta, har ta sanar dashi cewa yau zatayi maganar shi da Yayanta, ita tana so a musu aure as soon as possible" Zaid ya yi shiru