← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 128

Sashe 111

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yadai Najwa?" cewar Maama da ta dago ta kalleta bayan ta sallame Sallahr,  Najwa cike da murna tace "Maama guess what?" tace "Najwa,  gaya min,  menene?" "tashi muje, Bhaiyya na parlo" ta dan zabura "Najwa me kike nufi? Bangane ba" Najwa ta mike tsaye ta kamo Maama ta tadata tsaye tace "Your Son Zaid is not Dead. he's here(Danki Zaid be mutu ba, ya na nan) " yi tayi kamar zata fadi,  Najwa tayi saurin kamota, tace "Maama,  relax,  i promised you i'd find him and i did(Maama,  ki kwantar, alkawari na maki zan nemoshi,  kuma nayi)" dabas ta zauna kan Gado gabanta na dukan uku uku,  tsoro takeji,  bata san dalili ba,  kar hakan na cikin mafarke mafarken da na ta saba na haduwanta da Zaid,  bata son hakan ya kasance ba gaskia ba,  tana so ta ga Danta, tana so ta taba shi,  tana so ta jishi a jikinta, tuni hawaye suka soma sunturi a kan fuskarta.
Najwa tace "Maama tashi muje,  yana parlo" kamar an sa mata battery, ta mike da sauri tana gaba Najwa na binta a baya,  burinta kawai ta ga danta, duk girmanshi sai ta rungumeshi. 
***

Zaid ya dan yi dariar takaici "Ni ko zan gaya maka wacece Hajia Mairo, Matar da bata damu da damuwar kowa ba sai tata,  Matar da 'yayan wasu ba 'yaya bane sai  nata, da kunena naji kawarta na bata shawaran ta kasheni sabida zan girma na  zamar mata threat, saboda kar wata rana nace komai nawa ne,  Wallahi ta yi niyyan kasheni da na tsaya,  ko ba ita ba,  zata sa a kasheni, sabods abun dunia? She made me a monster,  ta saka na aikata Sabo da Zunubai, saboda ita na sha Giya, duk na zabure saboda  son daukan Fansa,  saboda ita nayi hurting dukanku ba tare da saninku ba,  daga kai Baba Abba,  Abdulmajeed, Zaineema,  Ziyada even innocent Zinatu,  ba wanda cikinku be dandani Azabata ba, saboda tsananin Mugunta na,  har a matsayin Kurma na zo musu ina kuntata musu ba tare da saninsu ba" durkushewa yayi yana kuka me ban tausayi yayin da dakin yayi shiru kamar ba kowa cikin Dakin,  kowa da tunanin da yake a ranshi,  barin ma Abdulmajeed da Nura Kurma ya fado mishi.
Gaban Maama ya fadi,  jikin ta yayi sanyi sakamakon jin kalaman da suka gama fitowa daga bakin Zaid,  gabanta ya fadi,  me yaronta ya Zama? Me daukar fansa ya maida mata Yaro? Me ya zama?  Duk yanda take son share ma danta hawaye,  duk yanda take son rungumarshi ta shafa bayanshi ta gaya mishi komai zai wuce yayi kamar ba ayi ba, duk yanda take son tabbatar mishi da she's here, ba zatayi ba,  sai ta tabbatar da ya wanke zunubanshi ta hanyar tuba,  sai ya nemi yafiyan duk wanda ya k'untatawa, sai ya gyara laifikanshi,  in ba haka ba,  shi da Mairo duk daya suke, ta san da wuya ta iya abun da take tunanin yi,  amma Allah zai bata iko, don har ranta bata son Danta ya kasance cikin marasa Rungumar k'addara"

A hankali ta taka gunshi ta sha mur wanda har ranta zuciyarta karyewa take,  a kausashe tace "Zaid" da sauri ya dago daga durkuson da yayi, nan da nan bakincikin fuskarshi ta sauya zuwa farinciki,  Murmushi ya darsu a fuskarshi da sauri ya mik'e yana kokarin rungumarta tare da fadin "Maaa" ja baya tayi kamar wanda dodo ya tunkaro,  da mamaki suka bita da ido,  banda shi da be damu ba k'ara nufarta yake, ita ko sai baya take kamar wanda abun tsoro ke bin ta daga k'arshe ta daga mai hannu tare da  fadin "dakata Zaid,  kar ka tabani" gabanshi kamar zai fadi k'asa,  tsoro ya cika kirjinshi,  hawaye dama ba su tsaya ba,  baki na rawa yace "Maaa" duk binsu ake da kallo,  Najwa ta karasa gun Maama,  ta riko hannunta tace "Maama,  me kikeyi haka? Baki ganeshi bane? Your Zaid? Wanda kike kuka kullum saboda rashinshi a India,  Maama meyasa kike mishi haka, donAllah ki bari" kamar ta fashe da kuka haka takeji amma sai tace "Haka ne Najwa,  amma nayi asarar hawayen da na zubda sabo dashi,  bansan yana nan Nigeria yana zubda tarbiyan da na mai,  bansan yana nan yana cutar 'Yanuwanshi na jini ba"
Zaid ya zube k'asa kan guiwowinshi yana  kuka kamar ba namiji ba yace "Kiyi Hakuri,  Maaa, banda wani Zabi da ya wuce aikata hakan,  tun ina karami na k'uddurta Niyyan tarwatsa Gidan Baba Abba don a ganina da saninshi aka kasheku,   na san nayi laifi, amma wallahi dana san kuna da rai,  da banyi abubuwan da nayi ba,  da na bi ku India munyi zaman mu, Maa, kar kiyi fushi Dani" be tsaya jin wank magana ba,  kamar me tabin kwakwalwa ya bude hanayenshi biyu yace *Wani Dan Halak zai ki yin komai in ya ji an kashe mai Mahaifa,  an hau kan dukiarshi kuma shima ana neman hanyan kasheshi? Wani dan halak zai folding hanayenshi ya zuba ma Matar da tayi sanadiyar hakan idanuwa? Balle kuma Danhalak din na da Wadatan maida zaune tsaye a duk lokacin da ya so,  wallahi ko da talaka ne ni sai na bi duk hanyar da zanbi na dau fansa,  balle da kudina*. Da alama kwakwalwar Zaid ya tabu,  tunda ga Mahaifanshi ga kuma kanwarshi ba ya bukatar kowa da komai,  he's got Nothing to lose,  indai zai kasance tare dasu,  be damu ya  rasa kowa da komai ba, su kadai ne Farincikinshi, zai gaya musu komai, be damu da abunda abun zai haifar ba, shi dai yana so a gama komai a gurin nan once and for all.

Kujera ya samu ya zauna don basu labarinshi, farawa yayi daga randa ya gudu daga Gida,  da haduwanshi da Alhaji Sadam Audu, da gajeren Tarihin Gatan marayu,  da yanda ya  nuna mai so kamar dan Cikinshi, da yanda ya ke kaunarshi,  da yanda ya maida komai kan sunanshi, da yanda yake mai nasiha kan shan giya da daukar fansa da yake cewa zaiyi, da yanda yake shiga damuwa  in yaga ranshi ya baci, komai ya gaya musu har bayan rasuwan shi.  Kuka kowa keyi,  sun tausaya ma Zaid matuka,  Maama kuwa ji take kamar taje ta lallashe shi,  ta bashi hakuri kan komai da ya faru,  amma ta kasa, sai ta gama jin komai, Mairo kuwa,  kunyar abubuwan da tayi takeyi,  tayi nadama matuka,  ina ma zata iya dawowa da lokaci baya ta gyara kurenta,  amma kash,  Bakin Alkalami ya bushe,  Ya Cigaba da cewa;

"Tun da na mallaki hankali na,  na ke da labarin Gidan Baba Abba a tafin hannuna,  na san shige da ficen kowannensu,  na sa da suwa sukeyin Bussiness,  nasan Alakar su da mutane,  sannan abunda na sani shine,  Matar Baba Abba bata hada Yayanta da kowa ba, daga son Yaya, sai son Kudi, a Porthacourt na girma,  na son lungu da sakon bullo ma lamura, a nan na gane cewa,  in kana so ka ga tashin hankalin Hajia Mairo to ka taba mata abubuwa biyu da suka fi komai mahimmanci a rayuwarta 'YA'YA,  da KUDI,  a hankali na fara taba Dukiyarta wanda ba nata ba da kuma Yaranta a lokaci guda,  da Babban na fara".

Karasawa inda Abdulmajeed  ke tsaye yayi, Kuka Abdulmajeed yakeyi sosai yace "Ka tuna Yarintar mu?bana tunanin zaka tuna, ina dai so ka sani, Na tsani kaina da na sa k'afa na  shure abubuwan yawa dake tsakanin mu a da,  na tsani kaina da na cutar da kai don son ganin Mummynku cikin bakinciki, kana tunanin ta ina na cuceka? Bari in gaya ma, A hanyarka ta zuwa Abuja daga Kano a motarka Mercedez Benz akwai Ownership Documents na Abba Abu&Sons Furnishing Company, da wasu signed contracts na other shareholders,  daidai Zuba akwai Yarana da suka tareka,  suka kwace maka Mota wanda duk wani abu me amfani na cikin Motar wanda yayi causing dinku asarar almost 20%, in har zan tuna da kyau,  harta kayan  da ke jikinka sai da ka tube musu".  Da mamaki suke kallonshi, AbdulMajeed ya bude baki, Daddy ko jinjina kanshi yayi, Mummy ta tuna bakincikin da ta shiga a lokacin ashe Zaid ne. Zaid ya dan  dafa Abdulmajeed yace "dont be shocked bro, wannan ba komai bane.
A hanyar dawowan Zinatu da Muhsin daga Makaranta,  na sa an dauke min Zinatu, wanda akayi requesting 10mil,  har mukayi waya" ya juya ya kallesu yace "kun tuna? Ya kalli Ziyada yace, "Har nace miki Ziyaa i'm coming for you?" Well lokacin ne dai,  sannan kun tuna Nana Nakowa ai?" be jira amsa ba ya cigaba "Ni na azalzala mata ta hura wuta akayi aurenku,  ranar auren Yarana suka je Gidanku,  duk wani abu masu amfani suka kwashe, wannan shine Karayar Arzikin ku na farko,  wanda sai da kuka saida Gidanku na Abuja wanda ni na siya ba tare da saninku ba don a ganina Gidan Baba na ne,  kawai na karbi abu na ne,  so da kuka dawo Kano,  well wannan ma Gida na ne, da kaje Dubai neman aiki A Hilal Construction Company,  ni na hana a daukeka aiki,  da na ga ka dukufa wurin neman aiki sai na sa Nana  ta dauko min Credentials dinka duka" AbdulMajeed ya dauko rinannun idanuwanshi ya kalli Zaid,  yanzu abunshi ya bar bashi mamaki,  tsoro ya fara bashi.

Zaid ya taka har gaban Daddy yace "Baba Abba,  kar kaga laifina,  makancewa nayi da son daukan fansa,  Furnishing Company dinka,  ni na sa aka rushe,  aka saida filin,  wanda nine na siya, Bayan kun sayar da Gidan da muke zaune a ciki, wanda shima nine na siya ga hanyar turo muku Alhaji Labaran, kuma na sa aka tare ku a hanya da kuka karbo kudi a banki kai da AbdulMajeed  a ka karben kudin, kumaburina na mallaki Gidan da na yi yarintana a ciki,  kuma don na tada hankalin Hajia Mairo na kawo diyarta cikin Gidan da take ikirarin nata ne".
Chapter 111 · 0% Book details