← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 128

Sashe 117

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tausayi a bashi ya kasa magana, sai gyada kan da yayi, kafin ya ankara har Daddy ya bar parlorn. Mairo ta durkushe tana jin zafin Hajia Aynarh hat ranta, zuciya ya sata shiga dakin Hajia Aynarh, wanda sai da tayi nadamar shiga din kunnenta suka jiye mata shagwabar da Hajia Aynarh ke ta narka ma Daddy, wato ya bata mata rai shine ya kirata don ya lallasheta?.
Ganin Hajia Mairo ya sata daure fuska tare da cewa "Abbana, zan kiraka" Kamar an watsa mata ruwan zafi haka taji da kyar ta samu tace "Hajia Aynarh, kiyi hakuri, ba sai kin Auri Daddy ba, na son yana son aurenki ne don ya huce takaicina, amma wallahi ba sonki yake ba, ni yake so, sannan nasan kema haka, donAllah a bar wani maganar auren, ki taimaka min in koma dakin Mijina". Wani Dariar rainin wayau wanda ya k'ular da Mairo Hajia Aynarh keyi, wanda a da, in ta kuskura ta mata irinshi sai sun kwashi yan kallo, amma da yake yanzu tayi sanyi, kasan cewa komai tayi sai sadda kanta k'asa.
"Hajia Mairo, wa ya ce miki ni da Abba bama son juna? Aiko munfi Indiawa soyayya, in muna tare ji muke kamar mu hade juna, to in ma tunani kike Auren huce haushi zaayi dani, na miki kama da irin matan nan da zaa auresu don guce haushi? Soyayya zai sa mu aure, kuma nima ai zanso ki koma dakinki, don ba zan so duniya tace na firdaki daga dakinki don na auri Mijinki ba, ni zan ma fi so ki dawo dakinki don ki koyi yanda ake zama da miji, jidai abunda kike cemai, wai "Daddy, Babanki ne?" kafadu ta daga alamun ina ma ruwana, ta dora da cewa "Some hausa girls sha, wanda ya biya allonsa ya wanke" ta raba ta gefen Mairo ta bar mata dakin, Anan ji take kamar ta shak'o Hajia Aynarh ta mata dukan tsiya, don wallahi Hajia Aynarh ta mugun rainata, ta ga gadon baccinta, amma ba wani abu, ita tayi abunda ya sa ta rainata•.
**

Shafa kanshi tayi tace "Zaid, tashi na dafa mana Abincin rana, munyi latti, yaushe aka gama har aka kaima Umma" kamar karamin yaro ya mak'e kafada tare da sake gyara kanshi kan cinyarta, ya ciro wayarsa daga Aljihu ya latso Idi, ringing daya ya dauka "Idi, Lunch muke so" daga bangaren Idi yace "me kukeso?" "Random foods dai" yace "To, bari inyi ordering, zaa aiko yanzu" "Ehen, harda tuwo, a tsaya gidan Hajjo a kai mata nata" Idi yace "Angama Oga, sai me kuma?" Yana jin dadin yanda Idi ke mishi abubuwa, bari ya faranta mai rai Zaid yace "Shikenan, Thank You Idi, nikam Idi, ina brother dinka da kace ya gama Secondary School?" Idi yace "Anas, yana nan, be samu Jamb ba" Zaid yace "baka gaya min ba, Oya ka mai processing School a Cuba, naga akwai wani sabon School na manta sunan, kayi searching, ka mai processing ka gaya ma Faisal" Idi ya gane cewa Oganshi na wani yanayi na nishadi, zai fara godia yaji yace "Shuttup Idi get us lunch" sukayi daria tare kafin suka kashe wayar.
Maama ta sake shafa kanshi, tace "ina alfahari da kai, sosai" yace "Haka nake sonji" tace "to still dai ka tashi muje mu hada So6o, Babanka na so" shagwabe fuska yayi yace "cant we just buy?" mikewa tayi wanda tasa dole shima tashi tace "Nope, ni zan mishi" tayi gaba, yana binta a baya yana bubbuga k'afa kamar dan yaro har suka isa kitchen.
Da mik'o kaza, dauko wanchan suka dafa Sobon wanda yaji kayan kanshi su Na'ana, citta da karamfani, tana tacewa a dan Jug, yana bata labarin komai da Allah ya hore mishi, ta san Sada yana da kudi tun tuni, amma bata taba zaton danshi zai samu Arzikin ninkin ba ninkin na babanshi ba, Allah kenan, buwayi gagara Misali.
"Maa,me kike ganin zan ma Danuwana?" Maams tace "Zaid, abunda zakana AbdulMajeed ai ba sai na gaya ma ba" yace "Amma ai shawara da dadi" tace "kayi mishi abunda ya dace, Zaid, Abdulmajeed ne, ka mishi komai" jinjina kai yayi yana amincewa da duk abunda tace, ba wai don ya san abunda zai ma Abdulmajeed ba.

Hayaniya suka danji daga Parlo, alamun sun dawo, yaran suka shigo suna rungume Maama, tace "Zeenah, Muhsin ya School? Suka amsa tace "Najwa, kuje ku musu wanka, kafin a kawo lunch" Muhsin ya fita gun Najwa a guje, don yana sonta, Zaid ya dauka Zinatu a kafadarsa ya fito daga kitchen din, inda yaga Najwa na kiciniyar cirema Muhsin kaya, yace "Baby a parlo a ke cire kaya?" tace "No Bhaiyy" ba tare da ya amsata ba ya kashe ma Ziyadan da ke zaune ido, tare da wurga mata kiss ta iska, a kan Idon Abdulmajeed, ya wurga musu harara duka, suak tuntsire da daria, Zaid yace "Ha'an, mutum ba zai iya kallon matarshi ba?" Abdulmajeed yace "kaidai ka sani" daria Zaid yayi ya maida hankalinshi kan Zeenatu, yace "Baby Zeenah, kin yafe min abubuwan da na miki?" duk hankulansu ya dawo kansu, tace "ai ba ka min komai ba" yace "aa na miki, nidai ki yafe min" ta zaro ido tace "me ka min, ka gaya min?" Abdulmajeed yace "Zinatu, Wala tajassasu" ta kalleshi tace "banda tsananta bincike" ta maida kallonta gun Zaid taxe "Na Yafe maka har duniya ta nade" Murmushin jin dadi yayi yace "nagode, Ziya, kuje a musu wanka, suna warin rana" Najwa ta daga Muhsin, ita kuma zinatu ta bude baki ta na cewa "Ina warin a nan? Ya Majeed wai ina warin rana? Nifa ban ma shiga ranan ba" Ziyada tace "Mu shiga nikam na miki wanka" Zinatu ta dan bata fuska tace "nifa na iya, da kaina zanyi" Ziyada ta kalli Zaid, Zaid yace "No, kije a chudaki sai a barki ki k'arasa ko?" ba musu ta shige dakin Najwa a guje. Ziyada ta bi bayanta. Zaid kuma ya koma kusa da AbdulMajeed yana mai chakulkuli. Abdulmajeed na tureshi yana "kai wai ba zaka girma ba? Goaway" Zaid kam Dariya yake tayi.
**
2PM

A Tsakiyar Parlorn a ka sauke duka kayyan da Idi ya kawo, Coolers 6 ne, Tuwon Semovita da Miyan agushi, sai Fried rice, sai fried spaghetto da taji kanyan lambu, sai couscous da Miyan kayan lambu, sai Salad da Coslow, sai Pepper Meat na chicken da beef, sai kuma So6on da su Zaid sukayi yayi sanyi sosai. Zaineema sun dawo daga yawon ganin garin da sukaje, duk ta gaji.
A lokacin su Daddy suka shigo, duk yaran suka musu sannu da zuwa, Daddy yace "Shagali zaayi banda mu?" Najwa tace "wa ya isa yaci Iyaye na ba sa nan?" Zaid yace "ganta fa, ci fa za tayi kafin shigowanku" 6oye kanta tayi a cikin hannuwanta, Papaa yace "Yesmeenah ina muka samo coolers? da baki ta nuna Zaid Paapa yace "Au, ashe daga wurin His Grace Gatan Marayu ne" Zaid ya turo baki yace "Nifa kuna addresing dina formaly, nifa a cikin Gida Zaid nake, Da, K'ani, Yaya a wurinku, Daddy ka gaya musu" Daddy yace "wai baka san halin babanka ba? Aifa ba zai bar tsokananka ba, tsokana kamar dan shekara 6" duk akayi daria.
Maama tace "Oya azo a ci Abinci duk kowa ya tankwashe k'afarshi, Yaya kai kuje Kan Table, a kawo muku naku chan" Daddy ya zauna a k'asa wurin Muhsin yace "saboda mu bare ne ko bak'i, to nima anan zanci, baki san cin Abinci a tare na k'ara donk'on Soyayyah da zumunci ba".
Paapa ya dawo kusa da Maama shima ya zauna, yace ina na "Umma?" Zaid yace "Idi ya aika mata da nata" Daddy yace "Yauwa, nidai a zubo min Tuwo" Najwa ce ta bude coolern tuwon ta ciro mulmula biyu ta zuba mai, yace "aa daya ya isa". Maama tace "Zaineema ki zuba khaleed abunda yake so" ta dan gefen ido ta kalleshi, ta mike ta ciro plate ta zuba mai Couscous, Abdulmajeed yace "haan, ba zaki tambayeshi me zai ci ba?" Khaleed yace "Kai ina ruwanka? Mutum da mijinta? Ita tasan cimar shi?" Daria sukayi Abdulmajeed yace "Ahh, Allah ya baka hakuri" da kanshi ya zaro plate ya zuba ma kanshi Fried Rice, Mama ta zuba ma kanta da Paapa tuwo a plate daya, Zaineema ta zuba fried rice, Ziyada ta sa ma Muhsin da Zinatu Taliya, kafin ta zuba ma kanta Friedrice da coslow, Najwa kam Salad din kawai ta zuba a plate, Ziyada ta dan kallo Zaid kowa shagalinshi yake banda shi, "Oga ba zaici abinci bane?" turo baki yayi yace "an damu inci ne? Maama ta sa ma Mijinta, matata kuma kanta kadai ta sani, kanwata ma Mijinta ta serving, shi kuma danuwana da kanshi ya zuba, ita kuma wannan babanta ta sama mawa, ni da baa sona ba, wanda ya sa min, abincin ma ba zanci ba" Daria sukayi, Najwa tace "Laah, Bhaiy, sorry me zakaci?" Turo baki yayi yace "baa ci" tace "Haba mana Bhaiy, kayi hakuri, in zuba ma tiwo?" yace "ni ban cin tuwo" Abdulmajeed yace "sai rice" Zaid yace "eh din, amma yanzu kizo muci Salad din" karo musu salad din tayi, da plate din pepper meat, tazo ta dire gabanshi, suna ci tare a kwano daya, daga inda yake yana wurga ma Ziyada kallon soyyaya, ita kuwa duk nauyinsu Maama take, ta kawar da kanta tana cin fried rice dinta, Ziyada ta tsiyaya Sobo ta dan kurba, Zaid yace "Ziyaaa, Sobon yayi dadi? Ni na yi fa" tace "kaii, amma yayi dadi, ban taba shan Sobo me dadinshi ba, saboda maama na tayi" Zaid ya marairaice yace "Nifa nayi, ku tambayi Maama kuji" Abdulmajeed yace "You Spoilt Brat, bana tunanin ko ruwan zafi ka iya dafawa" Zaineema da Khaleed suka sa daria, Najwa ma darian take, turo baki yayi yace"Maama kice musu ni nayi" Maama bata tanka ba ta cigaba da cin tuwonta, Zaid kamar yaro sce "Maama kice musu ni nayi donAllah" ganin gardaman ba k'arewa zai ba Daddy yace "Mallamai ku mana shiru, in ana cin abinci ba a magana".
Nan suka natsu, Abdulmajeed ya faki idon Daddy ya ma Zaid Gwalo, Zaid ya balla mai harara.
Chapter 117 · 0% Book details