Sashe 87
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda ta shiga daki take ta cizgar kuka kamar zata fitar da idanunta saboda Kuka, wannan wani irin Rayuwa ce? Wannan wani irin abu ne? Bata taba zaton akwai Mutane Irin Zaid ba, tana jinshi ya shigo, tayi banza dashi, duk da Zuciyarta na mata kuna, bata so tana shareshi, da tana da yanda zatayi ta cizge son shi daga ranta da tayi hakan, "tashi ki zauna" ta ju muryarshi cike da umurni, burus tayi dashi, "in baki tashi zaune kin bar Kukan nan ba, zan ma Ya Gidanku abunda ya fi na yau" da sauri ta tashi zaune tana sharar hawaye tana girgiza kanta "DonAllah kar ka musu Komai, na tashi" a wulakance ya kalleta ya watsar, ya fita daga dakin.
Komawa nashi dakin yayi ya zauna, ba wai kukan ne ke damunshi ba fa, kawai ta cika mai kunni da ihu ne, be son damuwa, wayarshi ya dauka yana Waya.
Tunda suka iso Unguwar suka hango Motan Jamian tsaro a gaban Gidan, Daddy ya kalli AbdulMajeed, suka karasa garesu da Sallama, musulmin cikin ne ya amsa, Daddy yace "munzo ganin MaiGidan ne" yace "to ku kirashi a waya" AbdulMajeed yace "kuce mai Mahaifi da Wan Matarshi ne" yace "Aa ai ku zaku kirashi kuce mai kuna Kofar Gida, mu ba ruwanmu, Aikinmu shine hana fita da fice a gidan nan, ko waye yazo, dazun ma dan shi yace a bar Mamarta ta shiga shiyasa aka barta, amma da ba haka ba" Daddy yace "ku taimaka ku sanar dashi zuwanmu" nan sukayi biris da lamarin, Wayarshi Daddy ya ciro don kiran Alhaji Ado ya sanar da shi halin da ake ciki, amma wayarsa Kashe(kasancewar ya bar kasar). Sun kusa Awa Biyu a kofar Gidan, ganin mutanen nan ba wani tausayi ko imani tattare da su yasa Daddy Lallaba AbdulMajeed kan su tafi, ba don ya so ba su ka tsaida Adaidaita suka bar Unguwar.
Bayan Maghrib
Ganin kuka ba zai fissheta ba ya sa ta tashi ta fada wanka, tayi alwalan maghrib kafin ta fito ta shafa mayyukan da ke gaban dressing mirror dinta, bude daya daga cikin Akwatinan da Anty Taatuh ta shigo dasu a ranar da aka kawota tayi, bata taba budewa ba sai yau, dama ina kwanciyan hankalin dubawa, Akwatin cike yake da dogayen riguna, da kananun kaya irin na matan turawan nan, ta bi wata riga聽 navy blue color me torches din re da kallo, ta dauka ta daga ta na duba tsawon jikin Madubin Wardrobe dinta, iyakar rigar guiwarta, hannun dan guntu ne, ta ina zata fara sa rigar nan? Ai da kunya, ta ma saka taje wurinshi ya wulakanta ta? Amma fa na zaiyiwu su cigaba da zama haka ba har karshen rayuwarsu, dole ita zata kokarta wurin karkato hankalin Mijinta gareta duk da ba abu bane me sauki, ta kan gani a littafan hausa Mazaje masu tsaurin raayi, ta hakan ake shawo kan wasu, tasan this is reality, amma zata gwada ko Allah ya sa ta dace, tana son Mijinta, kuma zata iya hakuri dashi in dai har zasu zauna lafiya.
Saka rigar tayi ta daura zani a kai tayi sallahr Maghriba, tana kan dardumarta taji kiran Sallahn Isha'i, ta tashi tayi Sallahr ishai, ta hada da shafa'i da wutir, ta zauna tana jera ma Allah Kirari, tana adduar Allah ya kawo karshen komi ya basu zaman lafiya da Mijinta, Allah kuma ya kwabe Fitina tsakaninsu, a karshe kuma ta kara da Allah ya daidaita tsakanin su" ta shafa. Ta mike ta linke hijab da zanin da tayi sallah. Ta sake shafe jikinta da turarruka masu k'amshi ta gyara fuskarta, dan jambaki ta zizara a baki, ta sake kallon kanta a mirror, sosai rigar yabi jikinta, ita ta san tana da kyau, ko da bata shafa jambaki ba, ina ga ta shafa.
Sai da ta shiga Kitchen ta dafo ruwan zafi聽 da kayan shayin da ta gani a wajen, bayan ya tafasa ta sa a wani Jug me kyau, ta dauko saucer kalan jug din ta hada mai, ta dauko tayi dankin Oga.
Nan gabanta ya fadi da ta tuno wurin wanda zata je, jiki na rawa ta fita daga dakinta, tana karanto adduar shiga gida bismillahi walajna.. Bata san ko ya dace ta karanta shi ba ita dai ta karanta, ta murda k'ofan da Sallama.
*
Ko Darduman da ya idar da Sallah be ninke ba ya hau kan Gado yana Waya, inda aka kirashi daga Maaikatarsa ta Bauchi, wai ana bukatar shi a Maaikatar saboda wasu clients da suka samu daga London, karamin tsaki yayi yace "kuma dole sai ni? Ba gaka ba? Or Zan turo Faisal" Cike da ladabi mutumin yace "Oga sai dai kayi hakuri, sunyi insisting sai sunga CEO din company din ne" Zaid ya buga tsaki yace "matsalarsu, in representative dina ba zaiyi tending dinsu ba, they should forget it" yace "Oga, zaiyi causing dinmu Millions of Pounds" Zaid cikin daga Murya yace "I dont care" Manager ya kwantar da kai yace "this is the Company your Dad spent his time and energy Building, ba zaka sa muyi asarar nan ba" Zaid ya rintse Ido ya bude ya sauke su kan Ziyada da ta shigo yanzun da Sallama hannunta rike da tray, kallonta yakeyi kallon kurilla, be san me yakr tunani ba, ji yayi Manager na cewa "Oga, are you there?" cikin sanyin murya Zaid yace "Yes i'll see you Tomorrow" ya kashe waya ya mik'e tsaye ya na kallon Ziyada, kallo yake binta da shi, kallon da be san na menene ba, takawa yakeyi a hankali har yazo gabanta, sansanyar murmushi take binshi dashi, tana murnan Zaid ya fara dawowa kan hanya.
Ba ta ankara ba sai jin wani irin Zafin da bata taba sanin akwai irinshi ba akan kafarta, wani tsalle tayi ta ja baya, sai a sannan take jin muryan Zaid na cewa "kar ki sake shigo min daki, dan gulma harda hado min Tea, waya san irin Asirin da ke ciki? Da da ki ka kawo ni kike son na sha? Ki kara gobe a jiki zan watsa miki, sai sannan ta lura da ba sakin Jug din tayi ya fadi a kasa ba, shi Zaid din ne ya dauka ya kwarara mata a k'afa, murmushin takaici tayi ta share hawayen da ke fuskarta ta kalleshi da jajjayen idanunta tace "Ba a horo da Wuta Zaid" ta ajiye tray din kan wani drawer da ke gun, ta fita daga dakin da gudu, binta yayi da wani irin kallon da be san na meye ba.
Toilet ta nufa ta sake ma kafarta ruwan sanyi, tun daga guiwanta har kasan kafafunta, kuka take me taba zuciya ganin yanda kafar tayi Ja, tasan in ta shafa ko ta sosa kafar zai tashi ya ja ruwa, kuka take tayi, bata da abunyi da ya wuce ta zuba ma wurin ruwa, akwai radadi, ta dau lokaci me yawa a toilet kafin ta fito ta cire rigar jikinta ta saka Nightgown, ta kuddura a ranta, in Allah yayi duniya don Manzo ta fita harkan Zaid kenan, Allahn da ya jarrabeta da sonshi shi zai yaye mata" tana jin zafi ta hau Gado ta kwanciyarta tare da jan bargo a jikinta, tun tana kuka har bata san Lokacin da bacci barawo ya saceta ba.
***
2:35am
*"ZAID" yaji wata kakausar murya na kiranshi, ya dago ya kalli fuskar a razane, fuskar da ba zai taba mantawa bane, fuskar Babanshi , Gatanshi, baki na rawa yace "Baba" cikin tsawa yace "kar ka sake ka kirani da wannan sunan, ni ba Babanka bane, ban taba haihuwa ba, banda da, dana sani na barka a inda na tsinceka, da na sani, da ban baka duk wani jin dadi na rayuwa ba, na baka gata, na baka suna na, na baka duk abunda kake bukata don ka zama good example gurin mutane na kasa da kai,聽 ban raineka ba, ban baka duk abubuwan nan ba don ka zama Jahili ba, ban bar maka tarin dukiyata ba don kayi amfani dashi wurin hanyar banza ba, nuna karfi da isa a kan na k'asa da kai ba, kana amfani da dukiyar dana bar maka ta hanyar banza, Zaid i'm so disappointed in you" Kuka Zaid keyi kamar ranshi zai fita, "Babana, ka min afuwa, ka yafe min, na tuba wallahi" Kuka sosai Zaid keyi, daga bisani yace "zan yafe ma da sharadi daya" da sauri Zaid yace "ko ma menene zanyi wallahi" Baba yace "ka chanza halinka for good, ka rungumi kaddararka, ka nemo yafiyan wanda ka sa6ama wa, matarka, she's innocent" kafin yace wani abu bat Baba ya 6ace mai*.
Daidai nan Zaid ya farka daga baccin da yakeyi, duk da AC da ya karade dakin Zaid be fasa zufa ba, zufa yakeyi sosai, kunna hasken wayanshi yayi ya duba lokaci, Yasan Mafarki ba gaskia bane, amma meyasa zaiyi mafarki da Baba? Hankalinshi ya tashi, da ya tuna yanda sukayi da Baba, a hankali ya sauko daga kan Gado ya zura takalmanshi ya fita daga dakin, dakin Ziyada ya nufa, yaci saa a bude yake, ya kunna hasken dakin ya karade ko ina, chan karshen gado ya ga ta rakube tana bacci, jefi jefi tana sauke ajiyar zuciya me nauyi, wani abu da be san meye ba ya dirsa a Zuciyarshi, a hankali ya hau kan Gadon ya yaye bargon da ke rufe a jikinta, ya kai dubanshi kan kafarta, nan yaga kafar ta fara jan ruwa, da sauri ya sauka ya je dakinshi ya bude firstaid box ya dauko wani ointment, ya dawo da dan sauri ya hau kan gadon, k'afarta ya daura kan cinyarshi ya shiga shafa mata Man a kafa, ya dau lokaci yana yin haka, kafin wani abu ya cizgeshi yayi saurin jayen kafan ya aje kan gado, ya gyara mata kwanciya ya rufeya da bargo ya kashe wuta ya fita.