← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 128

Sashe 123

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hajia Mairo ta ware a Gidan Maama ana ta fira da ita, nan tace ma Aunty Karima in an gama ma yara gyaran jiki itama sai an mata, don itama amaryarce, shewa ake tayi.
Su Zaid da Abdulmajeed sukayi Sallama a Parlorn, amsawa akayi, suka sake gaisawa, Zaid ya dan kalli Hajia Mairo yace "Mummy ina wuni" da fararta dukda ta na kunyanshi tace "lafiya lau Zaid, ya akaji da hidima?" dan dariya yayi ya danyi gaba yace "Aunty Karima. Ina Baby wannan yace sai yaga matarshi zai bar gidan nan yau" Abdulmajeed yace "lahh, karya yake, wallahi cewa yayi na rakoshi wurin Zuzu, wai yana missing dinta" Mummy ta watsa mai hannu alamun dak'uwa tace "baka da kunya ko? Oya zo ka fice, kar ka sake ka shiga dakin yanmatan nan, ba su kadai bane" Zaid yayi kamar be jita ba, yayi gaba, burinshi yaga matarshi, yaji muryan Mummy na cewa "harda kai Zaid, zo ka wuce, oya out both of you" Zaid ya turo baki ya fasa shuga dakinsu Najwan ya zo ya dungure Majeed ya tusa k'eyarshi suka fita suna mitan an hanasu ganin matayensu".
Maama ta sa daria tace da Mummy "ai kece daidai su, dazun wai ina dakin Paapansu Zaid yake ta wani fi'ili wai matarshi na dauke da juna biyu, kamar kanshi farau" nan fa Mata suka fara tofa alabarkacin bakinsu "Ahh MashaAllah, su Ziyadatu har an harbu? Allah ya inganta" Mummy dai tayi ta murmushi.

Idi yayi Sallama a bakin kofar Parlorn, wata diyar Baba hussaini da ake ce ma Cutielurv ta lek'a, suka gaisa yace "kice ma Maman gatan marayu ga sak'o nan" Cutielurv ta koma ta sanar da Maama, tashi tayi ta nufa waje, har kasa ya durkusa ya gaidata kafin yace "ga Sak'o nan, inji Gatan Marayu" a ranta tace "Allah ya kara budi na Alheri Gatan Marayu, tace ku shigo dashi, Yaran Idi suka dinga shigowa da Akwatun nan, yan parlo sai kallo suke dai.
Maama tace ga Lefe nan "Yara sunyi wa Iyayensu" ko bata fada ba, sun san Zaid take nufi, "Hajia Mairo saiti guda, Amaryarta saiti guda" Guda aka sa, Mairo tace "MashaAllah, Allah ya biyashi da Gidan Aljanna" suka amsa da Ameen, nan suka kwantar da Akwatunan suka shiga budewa dayan bayan daya, sutura guda hamsin Harda dinkakku ready made, da kayan shafa, da mayafai, da yankune da sarka Zinari. Maama tace "Hajia, ki dau wanda kikeso sai akai ma Amarya nata ko?" Hajia Mairo tace "na dau wannan" na farkon kenan, na aka hau guda.
Tace "Toh, ku tashi mu dinguma muje Mukai ma Amarya lefen nata".
Haka ko akayi, Mata su ka cika motocin da aka tanada dominsu gaban Gida, aka loda akwatunnan Aunty Aynarh aka nufi Gidan Amarya, Yanmatan aka bari a gida.

Hajia Aunty Aynarh zaune cikin Kawayenta, yanuwa da abokan arziki, wanda kallo daya zaka musu kasan cewa wayyayu ne, hutu da kudi sun zauna musu, fira suke na yarda gobe zata kasance, su ma sunji sanarwar Hajia Mairo a radio, wata tace "Ahh, Uwargidanki ta burgeni Aynarh, ba ruwanta har gayya take" wata tace "ke ba duk bariki bace, mun san komai ruwan kissa ce dai kawai" dayar tace "ke ai hakan yafi, indai akan burge Miji ne, kowa ya biya allonshi ya wanke, ba boka ba mallam, nidai Aynarh ina rokonki kar kiyi kishin jahilan matan nan" Hajia Aynarh ta dara tace "kawayen Arziki, kunsan banda damuwa, ba ruwana da ita, zamuyi zaman lafiya, don mu ba yara bane, amma ina anzo kan Miji, kowa yayi ta kansa" shewa suka sa suna Jinjina ma Aynarh, nan suka fara zancen Manya, kafin sukaji Sallamar Mata da dan hayaniya daga waje.

Maama ce ta rafka sallama kafin sauran suka rufa mata baya, wanda harda Mairo, da yake abun na Mata ne masu kissa suka tarbesu hannu bibbiyu ganin Mairo, Mairo na ganin haka itama ta kwasa a guje ta rungumo Hajia Aynarh, Hajia Rufaida babbar Aminiyar Aunty Aynarh ta rangada guda, Mummy tace "Kanwata, na k'agara kizo Gida mu hadu mu kwantar da hankalin Mijinmu" itama da yake ta iya tace "wallahi Yayata nima ji nake kamar na jawo gobe, na kagara na kasance tare da ku" nan Manyan mata a ka sa shewa, Mummy tace "Lefenki ne muka kawo miki inji Mijinmu" Aunty Aynarh tace "Ahh, Allah sarki Abbana, har da dawainiya?" Mummy tace "wallahi dawainiya kam, saiti biyu daya na Uwargidarshi sarautar Mata, da kuma ta amaryarshi wacce bata laifi" kamar wasu kawaye suka kashe ta hanyar tafawa, Maama da marakabanta saidai su bi Mummy da kallo, su bi Aunty Aynarh da kallo, sun san dukkansu Kissa da Kissisina ne, wanda yafi shi ya iya" nan aka jawo Akwatuna aka bubbude suna kallo suna yaba kayan.

*BAYAN DAURIN AURE*

Daga inda aka daura auren aka dunguma zuwa _ Abba Abu & Sons Furninshing Company_ don yin Reception na daurin auren da kuma Walimar Bude _ Abba Abu & Sons Furninshing Company_ cikin Haraban Company aka saka canopies da kujeru, akayi decorating wurin.

Sanye yake da Milk Shadda da ta sha Aikin sky blue, annurin fuskarshi baya daukewa, hakan ne ya fito mai da cikar zati da kamalarsa, ya hadu iya haduwa, ga Kyaun Fuska ga na Hali, Namiji daya tamkar dubu, burin ko wacce diya mace, Abdulmajeed Abba Abu kenan Angon Najwa Sada Abu, an daura aure burinshi ya cika.
A nan wurin taron bude sabon Kamfanin Babanshi yake gaisawa da abokansa da suka zo taya shi murna, sai hotuna suke tayi, ya dan samu ya kebe da Zaid yace "Kai, nidai na tafi Gida, zanje ganin Matata" Zaid yayi daria yace "kai dai ba an daura ba shikenan, ka tsaya mana ana ta zuwa maka murna, kuma kasan yanzu zaa bude Company dinnan, your presence is needed" Abdulmajeed yace "Kai, wallahi Gida zani, company zaa budeshi with or without me, and Abokaina su samu Aliyu gashi chan sai na dawo" be jira cewar Zaid ba ya faki idonsu Daddy ya sabe, Zaid ko sai daria yake.

Taron ya samu hallartan Manyan mutane zagaye da duniya, Shugaban Kasa be samu suwa ba sai ya turo wakilinshi, nan aka ci aka sha, Baba Abba yayi godia ga mutanen da sukazo tayashi murna, nan aka zo bude Company, Baba Abba na gama mutanen na baya, Scissors aka bashi don ya yanka abunda akayi ado wanda zai sadaka da cikin Company din, Alhaji Abba rike da Scissors din, gefenshi Danuwanshi ne rabinjikinshi Alhaji Sada, dayan gefen kuma Zaid gatan Marayu ne, sai autanshi Muhsin, akace ya yanka bayan an irga ukku, k'asa k'asa Daddy yace "Zaid, ina danuwanka?" Zaid ya dan sosa k'eya yace "Erhm Daddy, yaje ya dawo" tsaki Daddy yayi ya yanka dan igiyar ledan aka hau tafi raf raf raf, yayi gaba aka biyoshi a baya, shiga sukayi da jamaa duk wani lungu da sak'on Company, nan aka yi addua a masu bada gudunmuwa na badawa..

Zaid na waya ya hango Baba Ado sun shigo Kamfanin da mutanenshi, da sauri ya katse wayan beyi zaton zai samu daman hallartar taron ba, yana zuwa ya rungume Baba Ado, "Barka da Zuwa Baba" Baba Ado yace "Allah ya ji k'an Gatan Marayu, muna lafia?" yace "Alhamdulilah, barka da zuwa, Bismillah" alamu ya ma Idi, tuni aka ma Baba Ado wurin zama kan wata kujera ta Alfarma, Zaid ya shiga cikin Kamfanin ya ma Daddy da Paapa magana cewan ga Abokin Babanshi yazo, da sauri suka k'araso inda yake, yana ganinsu shima ya mik'e ya mik'a ma Daddy hannu don suyi musabaha, dan rankwafawa Daddy yayi alamun Girmamawa, don Baba Ado zai girmeshi nesa ma ba kusa ba, yanda Daddy yayi haka Paapa yayi, suka gaisa cike da Girmamawa, Baba Ado yace "Alhaji Abba na tayaka murna, ga Amarya ga kuma sabon Kamfani, Allah ya sa Alheri, ya kwabe tsautsayi da fitina" Ameen suka amsa gabaki daya, Zaid yace "Baba, wannan shine Babana Mahaifi, ashe basu mutu ba, suna k'asar India" maida hankalinshi yayi gurin Paapa, Paapa ya dan sadda kai, Baba Ado ya dafo shi yace "Allahu Akbar, ashe da rabon ku gana" Paapa yace "Munji labarin komai daga wurin Zaid, munji kalar guddumuwar da kuka ba Zaid, ba abunda zamuce sai Allah ya saka da Alheri ya biyaku da gidan Aljanna, Allah ya kareku daga sharrin mutane da Aljannu, Allah kuma yaji k'an Baban Zaid ya gafarta mai, Allah ya biyashi da Gidan Aljanna" Baba Ado ya murmusa yace "Ameen Ameen" Zaid yace "Ina Aunty Taatuh?" yace "tana Gidan Hajia Aynarh, ka san tun bikinka suka zama kawaye, ina Matarka?" Zaid ya dan sausauta murya yace "ka kuma zama Kaka" Daddy yayi alamun zai bugi Zaid, yayi daria ya doje, Baba Ado yace "kunsan, ban taba ganin farincikin Zaid haka ba? Ban taba ganinshi ya sake da walwala haka ba, Allah yaji k'an gatab marayu, burinshi ya sama mishi farinciki" Zaid ya murmusa yace "Allah ya ji kan Babana" suka amsa da "Ameen".
******

GIDAN AMARE.
Chapter 123 · 0% Book details