Sashe 12
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
Pg8鈨�
聽 聽聽
聽 聽聽 Wani Mutumi yace "yanzu kina nufin Alhaji Sada Abu da matarshi ne wadannan?" da sauri ta gyada kai,nan da nan Mutumin ya daura hannu a kai yace "shikenan munyi rashin mutum mai kirki da sanin darajan dan Adam" wani yace "yanzu dai ko a k'arasa da si kano, ko a kira Police, su dauki report a damk'asu ga danginsu a Sallahce su". Wani ne yace da Mairo ta shigo ya kai ga gida don fada ma 'yanuwanta, ba musu ta shiga motar suka kama hanyar Kano, Gidan Hajjo suka fara yi inda tana shiga ciki ta sake fashe wa da sabon Kuka, Hajjo ta taso da sauri dama tun jiya take jin wani abu zai sameta ko nata,cikin sanyin jiki take cewa" Mairo, lafiya? Meya samu Abba?" Mairo ta fashe da wani kukan tace "Sada, Allah yayi ma Sada da Yesmin rasuwa, sakamakon hadarin da sukayi, Motarsu ta ci wuta, suka da k'yar aka shaida su ne" kan Hajjo ya shiga juyawa "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun" take maimaitawa, "Sada? Yesmin? Sada mai jin kanta?" wasu zafafan hawaye suka soma kwaranyowa daga idaniyarta, Mairo na tayata. Hajjo ta daure tace "Ina Abba?" "yana gida, be sani ba dai" Hajjo tace "Ina tausayin Abba, ina tausayin halin da zai shiha in yaji mutuwar danuwanshi, ku kaini gun Abba, in gaya mishi Sada ya rasu, ku kaini in lallashi Abba, ku kaini in kasance da Abba a yayin da zaiji mutuwar danuwanshi". Kuka sosai Hajjo keyi, Mairo ta kamo hannunta suka fita daga gidan.
*
聽 聽聽 Jinyake kanshi ya mai nauyi, he cant remember a thing, tun bayan Waliman da aka gudanar a Abba furnitures, yana ta son tunano wani abu amma ya kasa, to me zai tuna? Me yakeyi a Gidan Sada? Shifa ya kasa tuna komai, kururuwan Mairo da yaji a tsakar gida ya sashi fita a guje, ganin ba Mairo kadai bace harda Hajjo da wasu mata biyu ya sashi karasawa garesu. Gabanshi na dukan uku-uku, da k'yar bakinshi ya lalubo "mai ya faru? Umma meyasa kuke kuka?" Hajjo tayi shahada tace "Abba sai dai muyi hakuri, Allah ya ma Sada da Matarsa rasuwa sakamakon hadarin Mota da ta riskesu a hanyar dawowa daga Kano" "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun" ya dinga maimaitawa a ranshi, sai wanda ya ta6a rashin danuwa zai fuskanci halin da Abba ya shiga, dama Sada yayi tafiya ne? Tambayar da yake tama kanshi kenan, harda Yesmin? Allah sarki Zaid, sai da ya tsagaita kukan yace "Ina gawar? "Mairo na kukan munahinci tace " an tafi a dauko su" Mik'ewa Abba kawai yayi ya shiga toilet.
**
聽 聽聽 Bayan an kawo Gawarwakin, Abba ya tsura ma Gawar Ido yana kuka, ya kasa shaida danuwanshi ko matarshi, Hajjo Bayan Hajjo ta gama musu Addua,tace "Abba, mutane suna jira ya kamata akai su gidansu na gaskia, in yaso in ka dawo sai ka kira Mahaifan Yesmin ka shaida musu Rasuwar". Hawayensa ya share ya mik'e zumbur.
聽 聽 Kamar yadda akeyi, nannade su kawai akayi a likkafani ba tare da wanka ba(Saboda k'onewa sukayi, anfiso a rufe su hakan ba tare da wankan gawa ba) aka dauki Gawarwakin nan, aka tafi dasu Mak'abartan k'asan layinsu a k'afa, Mutane ko sunzo da yawa, Manyan Mutane, yan Kasuwa da dai sauran su,haka aka rufe su kamar yadda Addini ya tanada, sannan suka dawo Gida a ka cigaba da zaman karban gaisuwa.
聽 Kafin kwana Biyu Mutuwar Alhaji Sada Abu da Matarshi Yesmin ya zagaya k'asa baki daya, don Babban mutum ne, wanda ake damawa dashi a k'asarmu Nigeria,dai cinciridon zuwa gaisuwa akeyi, Manyan Mutane suna ta zuwa ma Iyalan Sada Abu gaisuwa. Kowa yazo sai ya tausaya ma Abba, don cikin yini daya ya zabge ya jeme, su Mairo kamar dagaske, ana ta karban gaisuwa. Tun ranar rasuwar Abba ya kira chan gidansu Yesmin ta Landline ya sanar dasu Rasuwar, Washegari sukazo aka yi ma juna gaisuwa yau kuma suka juya Yola don karban gaisuwa, suma suna zaman Makoki. Wannan kenan.
聽 聽 聽 聽 聽聽 LAGOS Nigeria.
Bayan barinsu Gida, ticket din Jirgi suka siya na Lagos,ko da suka iso, wani katafaren Hotel suka je, kwanan su daya, a halin yanzu duk wata damuwar su ta yaye,kamar an dage su daga K'aya, ba sa jin komai, ba sa tuna gida, sunji kawai sun gaji da Gida be shiyasa sukace zasu chanza Environment, to ina suka dosa? Tambayar da Sada keyi a zuciyarsa kenan, don shi ya k'agara ya bar k'asar nan,fuk wani numfashin da yake daukar wa a Nigeria ji yake kamar ana sassake shi.
聽聽 Yesmeen na kwance kan Gadon Hotel din, tana Kallon TV tashar B4U kamar bata da wani matsala, Sada ya fito daga toilet ya kwanta kusa da ita "Yesmeenah, kina son India, kina ta kallonki" Murmushi tayi tace "Ina son Indian film, ban gajiya da Kallonsu" wani dan guntu tunani Sada yayi,yanda bai san zama a Nigeria, gwara suyi chan da Nesa, irin Asia dinnan, bari dai ya shawarci Yesmin yace "Will you like it if we move to India?" cikin doki tace "Like? I'll love" sukayi daria, yace "then lets make it Happen" ta tashi da doki suka fita don fara processing tafia India.
Ba kamar yanzu bane da ake shan wahalan Visa and all, nan da nan suka samu ticket din EGYPT AIR, wanda zai sa dasu da k'asar Egypt kafin sun wuce India.
Tafiar ta kasance gobe, kawai Sai Yesmin ta kasa bacci da daddare, zuciyarta ya mata nauyi, tada Sada tayi, ya tashi yace "Yesmeenah lafiya?" ta dan matse k'walla tace "Papi, Zaid fa? Ya zamu tafi mu barshi? I hate thid place, muje Kano mu dauko shi mana" Sada ya tashi zaune, yace "Yesmeenah ba mun gama maganar Zaid ba,ba yana Makaranta ba? So kike mu datse mishi karatu? Zamu dawo mu tafi dashi idan sunyi hutu,Abba da Mairo zasu kula dashi, zai ma fi jin dadin zama dasu ga Zaineema ga AbdulMajid, kar ki damu, zamu dawo mu daukeshi kinji?" shiru tayi don ta kasa gardama mai, ta koma ta kwanta.
Washegari suka bar kasar, suna barinta zuciyarsu tayi musu nauyi, ji sukayi kamar an kawo Boader an saka tsakaninsu da Nigeria.
聽
NewDelhi India
K'asar ta burgesu sosai, Tun a cikin Jirgi suka hadu da wani Indian Family, suna fira jefi jefi da turanci, inda Sada ke shaida musu "they are new, suna son Gida haka dan Self-contained, Mutum ya shaida masu Shi Landlord ne, yana bada haya, yana kuma saida Gida, Sada yace "yana so ya siya Gida, mutumin yace "bari su isa, sai ya kaisu suyi magana sosai".
Suna isa suka tsaya restaurant suka ci Abinci kafin landlord Vikash Joshi da Matarshi suka shiga nuna musu Gidaje da kudaden gidan a Laptop, nan dai Sada da Yesmin suka ga wani Gida a Sarita Vihar wanda yafi sauran saukin kudi, "We can live here, we can start a new life here" Yesmin ta jinjina kai, sukayi ciniki, inda Vikash ya sanar da su cewa suna iya biyan Kudin rabi da rabi har tsawon Shekara 3, nan da nan Sada ya bada kadan daga cikin kudin in dollars, kafin Suka kaishi wurin chanza Kudi from Dollars to Rupees.
Suka shiga Taxi suka nufi Saritar Vihar, chan tsakiyar Gari Unguwan yake, sun dade suna tafiya kafin suka iso Gidan, Unguwa ce shirushiru,聽 ba za dai a ce ma Unguwan na masukudi ba, dan lowcost ne.
锟�
Komai yaji a gidan, sai dai yayi k'ura, Vikash ya shaida mai, akwai Yaran unguwa da ya fita zai gansu ya sasu tayashi ya basu 50 rupees, yace "to shikenan" zasu tafi Sada yake cema Vikash yana so ya fara aiki, nan ya buk'aci ganin takardun shi, don ya yaba da Sada, da sauri ya dauko mai, Ya dudduba yace "Gobe zaizo ya daukeshi suje gun Aikin, zai taimaka mai" Sosai sukayi ta ma Vikash da Matarshi Godia har suka rabu, Yesmeen聽 tace "Suna da kirki, na zata zasuyi mana k'abilanci, don naji ana cewa ba sa son bak'ar fata" Sada yayi daria yace "to ke bak'ar fata ce? Kina ganin ki Ja, duk kin saje da Indiyawan" Daria tayi sosai, tace "Allah dai ya taimake mu ka samu aikin nan, nima da zaka barni da na nema aikin" kallonta yayi sosai sonta na shigar shi, yace "Anything for you, in har zaa dace, zan amince ki fara aiki" da sauri ta rungume shi tana murna".
Fita Sada yayi yace bari ya nemo wanda zasu tayashi gyaran Gida, Yana fita ya ga wasu yara na wasan k'wallo, da hannu ya ya fitosu, su biyu ne maza matasa ba zasu wuce shekaru 18 ba, dama sunga wucewarsu a Motan Vikash sir, sun san sabbin shiga ne, Sada yace "I want you to help me clean my house?" duk sukayi daria, dayan yace "No English, Hindi , Hindi" Sada ya dafe kai ya ja hannunsu suka shiga Gidan, ya musu nuni da su gyara gidan, Wanda ya fi dan wayewan yace "Sweeping?" da sauri Sada ya daga kai yace "Yes sweeping" dayan da ya lura ba indiyawa bane, ya girgiza kai yace ma dayan "su tafi kawai yan pakistani ne, musulmai ne, su tafi kar su taya su komai" dayan ya girgiza kai yace "ba wani abu su tayasu kawai" dayan ya girgiza kai ya wuce ya bar dayan a ciki, dayan ya kalli su Yesmin yace聽 "Ek Minute" ya fita, Sada ya kalli Yesmin yace "toufa, me hakan ke nufi?" Yesmin tace na daiji wannan yace "(1 minute)". Kafin suce wani abu sai gashi ya shigo, da tsintsiya da Bokiti da liquid soap, ya kusta kai cikin Gidan, su kuka suka zauna a kasan Bishiya, Yesmin tace " Ina ganin kamar dayan yace ba zaiyi bane, don naga wani kallon da yake mana" Sada yace "aiko zan ma wannan Alheri Sosai".