← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 128

Sashe 95

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga Zaid sai Ziyada,聽 Bangaren Dabbobi suka nufa, nan Ziyada ta dinga tsalle taga wild Animals su Lion, Tiger,聽 Chimpanzee da sauransu,聽 abun ya kayatar da ita matuka, waya aka bugo ma Zaid daga Kaduna, dauka yayi yace "Hello Babangida" bayan gaisuwa Zaid ya buga Salati, da sauri yace "ba wanda ya k'one ko? Is everyone safe?,聽 Alhamdulilah i'll make the call" Faisal ya matso kusa dashi yace "Oga,聽 is everything Alright" Zaid cikin wani yanayi yace "Gobara akayi a Gidan Marayu,聽 amma ba wanda ya kone suna lafia" ka kira Julius Berger,聽 suje su chanza Ginin Gidan a rushe inda ya k'one" suna wannan Ziyada na chan bata san me ake ba,聽 hankalina na kan kallon dabbobi,聽 ji tayi an mata sallama,聽 dagowa tayi ta kalleshi.
"laa,聽 Ya Amjad ina wuni" Amjad yace "ashe ke din ne,聽 ya kike ya gida ya su Mummy?" tayi murmushi聽 ta amsa da lafiya lau muke" yace "ke dawa kuka zo?" ta murmusa tace "ni da Mijina"聽 da mamaki ya zaro ido yace "ashe kinyi aure" tace aikuwa,聽 bata ankara ba sai ganin Zaid tayi saman kansu yana haki kamar tsohon zaki,聽 shi be san da wa ma take tsaye ba,聽 yana waya ya hangota聽 tana fara da wani Namiji ba shi ba,聽 ranshi bace,聽 bata lura da yanayin da yake ciki ba tace "Ga Mijina na nan" Amjad ya zaro Ido yace "ZSA" Zaid ya juyo ya kalleshi, ba yabo ba fallasa yace "Amjad" Amjad yace "Dont tell me kaine Mijin Ziyada" Zaid ya tsuke fuska be amsa shi ba,聽 sai Ziyada tace "Eh Shine Mijina" Amjad yayi wani irin dariya yace "Seriously Zaid Sadam Audu? Seriously kai ka auri Ziyada? Ohh now i see why you call me telling me to leave her,聽 ashe so kake kai ka aureta,聽 i was so stupid to believe聽 all you said" Ziyada tace "Whoa!聽 What are you talking about?" Zaid ya riko hannun Ziyada yace "mu tafi" Ziyada ta聽 tirje聽 tace "Me yake cewa My Forever?" Amjad yace "tsaya kiji, kin tuna randa na fara zuwa gidanku,聽 randa na fara ganinki?聽 From my looks kin san ina sonki da duk wani abunda nake dashi,聽 kin san na mutunmiki,聽 ki tambaya Mummynki yanda na fara sonki da ta nuna min pictures dinki,聽 bansan ya akayi ba,聽 ban san ya akayi聽 ZSA ya san cewa ina sonki ba,聽 bansan ya akayi ya san nazo gidanku ba,聽 bansan yana da numberna ba,聽 sai kirana yayi yace min in rabu dake,聽 ke yar iska ce,聽 ciki ki kayi shiyasa aka cireki daga Baze University,聽 and kuma ana tunanin kina da HIV,聽 ganin ki kamila ya sa zuciyana kokonto,聽 but ganin shi he's always a serious man,聽 ban taba zatan zaiyi making dinshi up ba,聽 ban yi zaton yana da wani dalilin da zai min karya ba,聽 shiyasa kika ba tare da na ce miki komai ba na fita a lokacin,聽 but yanzu na gane ya shiga tsakaninmu ne don ya sameki kuma ya ci nasara tunda gashi ya aureki" tuni Hawaye ya soma kwaranyowa daga fuskarta,聽 kirjinta kamar zai fashe saboda bakinciki,聽 tafiya ta farayi bata san ina take jefa kafarta ba,聽 bata damu da sauran mutanen da ke kallon ta ba,聽 buguzum buguzum take tafiya,聽 a guje Zaid ya bita,聽 ya riko hannunta,聽 tana juyowa ta sauke mishi hadadden Mari a a fuskar shi,聽 ta juyata cigaba da tafiyarta,聽 bata da masaniyar inda zata,聽 binta ya cigaba da yi,聽 yana mata magana,聽 da karfi a juyo tace "me zakace min?聽 wani karya zaka min Zaid?聽 Daukar Karuwa ma kake min ashe bansani ba?聽 Dagaske Zaid?聽 Ni Zaid?" zai yi magana tayi saurin dakatar dashi tace聽 "Baka da abinda zakace聽 min,聽 Zaman mu Ya k'are,聽 Zargi a shigo tsakani,聽 dole ka sakeni Zaid,聽 dolenka"...

Whatsup Lovers? Late night post huh?聽 Bear with me gab muke da landing,聽 I heart Y'lls to pieces.
Vote and Comment

#1love
#ADAY
#bibiliciousfreakingfans
#anatare
#nagode.

Biebee Isa.
馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱

NA

Wattpad:@biebeeisa

Pg3鈨�7鈨�

Zaid ya kai hannunshi kan fuskarshi ya shafa sajensa kamar yana goge zufa a jiki, ranshi ya 6aci, ya k'ara isa gurinta yace "Ziyaada, listen" ta waigo ta kalleshi rai a 6ace tace "Me zaka ce min? Kalaman Yaudara zaka sake watso min?" ranshi ya 6aci, inda ta san girman Laifin da tayi, inda ta san girman laifin daukar hannu ta mareshi cikin baiyanar Jamaa, da bata fara ba, ya rantse inda Armstrong na nan, ya ga Marin nan, ba zai damu in Ziyada matarshi bace zai mata ligiligi runtse ido yayi ya bude a hankali, murya cike da Umurni yace "Shiga Mota ki jirani" be bata damar gardama ba ya juya inda Amjad ke tsaye ya k'arasa yana kaiwa kusa dashi ya dunk'ule hannu ya kai fuskar Amjad wanda ke tsaye yana murmushi, beyi zaton hannun Zaid a fuskarshi ba, taba gefen bakinshi yayi cikin jin zafin, har ya fitar mai da Jini, ya yunk'uro don ramawa, yaji an rik'eshi ta baya, Odilen Zaid ne, Zaid ya kalleshi yace "Ziyada Mayata ce, kar ka sake ganinta a ko ina ka mata magana, ba ruwanka da ita, kasan meyasa baka aureta ba? Saboda kai banza ne me gajeren tunani, kuma Ziyaa,, ta fi karfin Banza mai gajeren tunani" har ya juya zai tafi ya kuma sake juyowa yace "Ehen hak'ar dama don kar ka aureta ne, kuma ba ka aureta ba, so kaga hakana ta cimma ruwa, what i'm saying is, inka sake mata kallon Yariska ko wani abu, zan sani kuma zan nemeka, kuma kasan abunda zan iyayi, so ka kula"
"Oga What do i do with him?" cewaar Odilen da me rike da Amjad, Zaid ya juya, ba tare da ya sake kallonsu ba yace "let him go, he is Stupid" ya wuce inda sukayi parking Motoci Faisal na take mishi baya, nan aka zubar da Amjad a k'asa kamar wani kayan wanki yana nadaman tsautsayin da ya kawo shi Bauchi.

Mota ya shiga ya ganta zaune ta hade kai da bango, ba zai mata magana ba yanzu ransu bace yake, in ta sake mishi wani abu, ba zai iya dauka ba, shi yana ma iya bugeta in ta tunzurashi, dukkansu sai huci suke kamar Zaki, ganin yayi sun dau hanyar Hotel din, ba zai iya sake kwana a hotel din ba.. A Bauchin ma gabaki daya, ji yayi garin ya fitar mai akai, ya kalli Faisal yace "Kano" Faisal ya kalli driver yace "to the Airport" Driver ya cika umurni ya dauke hanya, Ziyada sai sheshekan Kuka take, shi ko yayi banza da ita..
Suna isa Airport Faisal ya siyan musu Ticket, suka tashi Faisal ya musu fatan a sauka lafiya kafin ya kira Idi yace "su shirya, Oga na nan zuwa Kano cikin 45mins".
A cikin Jirgin ba me kula wani, har suka iso Kano ta bar kukan amma ta cigaba da kumburi, be mata magana ba ya fita tana binshi a baya, har inda ya ke ganin Motocinshi, na tsakiyar ya shiga, bata da wani zabin da ya wuce ta shiga wannan, be damu da masu musu sannu da zuwa ba, yayi banza dasu, itace ma ke amsa su, yanda taga yayi mugun dauke kai ya sa ta shan jinin jikinta, tunaninka kala kala har suka iso Gida, be bari anyi Parking ba ya fito ya mata slamming door a fuska, binshi tayi da kallo, "wai ai maka laifi a fika zucia" ta fada fili, ta dauki jakkarta ta shiga gida.

Yana shiga daki ya buga kanshi da bango don ya san ba zai iya shan Giya ba, so yake yayi ihu, takaici goma da ashirin, ga Rigimar Ziyada, ga Gidan Marayunshi anyi gobara, dafe kanshi yayi a baiyane yace"Ya Illahi, have mercy" shi din me Laifi ne, shi din me zunubai ne, shi yasan ba zai iya gyara abunda yayi ba, abu daya ya sani, bazai sake maimaita mistakes dinshi ba, abu daya ya sani ba zai kara yin abunda zaiyi hurting Ziyarshi ba, zuciyarshi ta dinga mai sake sake "Least abunda yayi musu kenan, to ina ga taji manyan laifukanshi? me zai faru in taji shine sanadiyar duk wani bakincinsu?" tsoro ya kamashi sosai, be son fita balle su hadu ta tambayeshi takkadar saki, be san ya rayuwa zata kasance mai ba tare da Ziya a ciki ba, be san me zaiyi da kanshi ba in ta rabu dashi, ba zai kara hurting dinta ba, meyasa ba zata yarda da hakan ba? A shirye yake ya zama abunda take so ya zama, sosai yayi nadama, toilet ya fada don watsa ruwa, ko da ya fito kin zuwa gunta yayi don karta tada mai hankali da maganar Saki, sai ya kwanta lamo yana waya kamar munafuki duk dai don kar taji muryarshi ta san cewa yana ciki.

"Tun tana sa rai zai biyota daki, har dai tagaji ta fito ta shiga Kitchen don daura abincin dare, tazo fita daga kitchen shi kuna ya fito daga daki, wuceta yayi ya bar parlo da alamu fita zaiyi, kar fa ya tafi wani gari ya barta ita kadai fa kamar randa aka kawota, nadama abunda tayi ya fara shigarta, ko zatayi fushi dashi, be kamata ta daga hannu ta Mareshi a gaban yaranshi ba, be kamata ta tsinkashi haka ba, ko bakomai Mijinta ne fa, tsoro ya kamata, kar ta kasance cikin Matayen da wutansu ke daban saboda rashin kyautata ma Miji, kitchen ta shiga ta kashe gas din, jikinta yayi sanyi, yunwa takeji amma bata da karfin dafa wani abu, daki ta koma ta rafka uban tagumi, tana ji aka kira Sallahr Maghrib, ta tashi ta dauro Alwala tayi Sallah. Tana idar wa ta daura kanta kan Gado ta shiga tunani, they were happy, yau ne karon farkon da taga Soyayya ingantacciya a idon Zaid, na Awannin da sukayi suna nuna ma juna So, taji wani irin dadi mara Misaltuwa, ko ba shi bane ya roketa da ta manta da komai shima ya manta kuma don ita? Meyasa taki mai uzuri? Meyasa ta watsa shi gaban mutane? Hawaye suka fara gangarowa daga idanunta, haka har aka kira Ishai tana zaune kan dardumarta, tana isha'i tayi shafa'i da wutir.
Chapter 95 · 0% Book details