Sashe 112
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read
Daddy kasa magana yayi kafin Zaid ya karasa gun Ziyada, wanda kwatakwata ta kasa nago ido ta kalleshi, ranta tafasa yakeyi, wanda take so kamar ranta ya yi duk wadannan abubuwan laifukan don daukar fansa, sanyin murya yace "Ziyaada, kamar yanda kika sani, da so nayi in chusa miki sona, in wulakantaki in sakeki, ko kuma in sa Yara na su miki fyade, kiyi ciki in koraki Gida, wannan zai sa hawan jini ya kama Mummynku, shine dalilin da Amjad ya fara nemanki da aure na tarwatsa maganar, amma along the way, komai ya chanza, ke kin sani". Kamar yanda be jiran amsar kowa ya taka ya isa gaban Zaineema, sai binshi ake da ido daga gun wannan zuwa gun wannan.
"Zaineema, ke kadai zance nafi jin zafin abunda na miki, na miki sharri mafi muni, wanda zaiyi wahalar kankaruwa"Jikin Zaineema ya fara rawa, kamar ta ma san me ya mata, ta san sharrin me ya mata, kafin yayi magana ta juya ta kalli Mummy da Imani ya gama shiganta tace "Mummy kin gani ko? Kin ga abunda san zuciyanki ya ja ko? Mummy, abunda kikayi ya dawo garemu, mu da bamu san lokacin da kikayi abun ba, Mummy ina zaman lafiya da khalid, kinja Zaid ya rabamu" Kuka sosai ta fashe dashi Zaid ya dora da cewa "Ni na san lokacin da Khalid ya shigo Kaduna, a lokacin na tura Armstrong da yaje ya dasa zargi a cikin Zuciyar Mijinki, Ni--" be karashe maganar da yake shirin yi ba yaji lafiyayyun tagwayen mari a fuskarshi, dagowa yayi ya kalli me marin.
**
Zuciyarta ke barazanar fasa k'irjinta ya fito, labarin da takeji kamar almara, bata taba tunanin duk girman laifukanshi zasu kai ga wannan Girma ba, hankalinta ya fi tashi data ji shine sanadiyar raba auren Zaineema, bata san me kuma yayi bayan wannan ba, ba ta san ko zata iya dauka ba, ba ta san me kunnenta zasu cigaba da jiye mata ba, da sauri ta fada gabanshi, ta katseshi ta hanyar bashi kyawawan Mari a fuska, dagowa yayi ya kalleta, idanunshi sun k'ek'eshe saboda ya gaji da kukan, juyowa yayi ya maida hankalinshi kanta yace "Maa, kiyi hakuri, Kiyi hakuri na ban zama dan da kike burin na zama ba, kiyi hakuri kin haifi Dan da ya saki kuka, ki yi hakuri kin haifi yaron da am you are disappointed in him, ki yi hakuri kan Yaron da shi burinshi ya dau fansar abunda aka Mahaifanshi, Maa, ki yafe min donAllah" da sauri ta gyada kai tace "Yafiya? ha, ai ban tunanin akwai wanda zai iya yafe ma, wani Mutum ne me tsoron Allah zaiyi abunda kayi Zaid? Wani mutum me mai Tauhidi da Ikhlas zai yi abunda kayi? To Meye Bambancinka da Mairon? You are even worse than her, Zaid kana Sallah ma kuwa? Wallahi ka ban kunya, ka bude baki sai fadin maganganu kake kamar wanda yayi abun arziki, mtss am disappointed in you, bansan me dukiya ya maidaka ba, bansan kalar tarbiyan da kasamu bayan rabuwar mu ba, abu daya na sani, i didnt born you to be a Monster, da na san haka zaka girma ka zama, wallahi da na barar da cikinka tun kan ka zama gudan Jini da na-- " cike da tashin hankali yace "Maa" katseshi tayi ta hanyar gwabe mai baki, tace "kar ka kuskura ka kirani da wannan sunan, tun lokacin da ka makance ka fara kauce hanya daga danan na daina zama Maamanka, tun daga lokacin, Zaid anya kuwa zaka samu rahamar Allah" a kausashe Daddy yace "Yesmin ki bari, kiyi shiru, kar ki ki mishi baki DonAllah" tsohuwa Hajjo da karfin hali ta tako don lallashin Yesmin, Paapa ko kasa magana yayi, jikinshi yayi matukar sanyi, Yaronsu yayi laifi babba, dole a hukuntashi, be taba ganin Yesmin dinshi haka ba, shiyasa ba zai shiga tsakanin hukuncin da ta tanadar ma Yaronta ba.
Yesmin ta share hawayenta tace "Yaya ku rabu dashi Mutumin banza ne, meyasa zaiyi hakan? Ku me kuka mishi? Kanshi farau rabu da iyaye? Shi hukuma ne da zai dau hukunci a hannunshi? Meyasa be yi amfani da kudinshi yayi Sharia da Mairo ba? Meyasa ya hada da yaran da basu san komai ba? Meyasa?" kamar an tsunkuleta ta matsa kusa dashi "Anya Da na ne kai kuwa? Anya Zaidu na ne kai? Ta sa hannu ta yaga rigar da ke jikinshi, ya rage mai Ves, habarshi ta rike ta juya yanda zata ga gefen wuyanshi, tambarin da ta mishi na nan, ta sake ta kamo hannunshi ta duba, ta dai tabbatar shine, hankalin ta ya kara tashi ta tureshi, tace "tafi, you must never show yourself to my face again, in ka k'ara, zan Tsine maka, sai ka shiga Garin Porthacourt fa kyau" zubewa kasa yayi ya rik'o kafarta yana rokonta gafara, yana mata magiyan kar ta mishi haka, kafa ta sa ta hankadeshi, har sai da ya k'ume da bango.
Najwa da take cikin tashin hankali ta rugo da gudu ta rungume yayanta da yakr durkushe k'asa, tace "Maama, dont do this, donAllah kar ki koreshi, Maama ki tausaya mana duka, muyi rayuwarmu mu kadai for once" Maama cikin bacin rai tace "Najwa, ki tashi ki shige ciki kafin ranki ya baci" taurin kai tayi, ganin Maama na shirin dukan Najwa ya sa Abdulmajeed yazo ya durkusa kusa da Zaid yace "DonAllah Maama ki yafe mai, kiyi hakuri, wallahi i reason with him, amma ta kan abunda Mummynmu ta muku duka, be kamata ace kina mishi mugun alkaba'i, kinsan bakin uwa, Maama shi me laifi ne, amma cikin rashin sani ne, nidai wallahi na yafe mishi, donAllah kiyi hakuri" Jikin Maama yayi sanyi tace "AbdulMajeed kar ya baka tausayi, tuban muzuru yayi, kuma ai ba kai kadai ya ma laifi ba" da sauri Ziyada ta durkusa tace "Maama wallahi nima na yafe mishi, kar ki manta duk abubuwan da Mummynmu ta muku kun yafe mata, mu su waye da ba zamu yafe mishi ba" Maama tace "Saboda kina son shi ko? Bayan wahalarshi da kika ci" kasa magana tayi sai girgiza kai da ta hau yi, Zaineema kam kasa motsi tayi, an fama mata mikin dake zuciyarta, Daddy yace "Duk abunda ya faru ba laifin Zaid bane, laifin wanchan Anamimiyar--" Paapa ya rufe mai baki da hannunshi, ba dadi zagin Uwa gaban Yayanta, duk da laifinta ne, amma uwa uwace, zasuji ba dadi, kuma abun zai tsaya musu, Daddy yayi shiru, Paapa ya matsa kusa da danshi ya dagoshi yace "Yesmeenah, ki yi hakuri, ki bashi chance".
Kusan cikin yanayin ihu tace "Dama daya kachal zan iya bashi" Zaid kamar jira yake yace "Anything Maa, wallah zanyi duk abunda kikace don ki yafe min, i'll do anything, dont leave me" kamar ba zata yi magana ba tace "Zaid, na baka kwana Biyar, kwana Biyar Kachal ka gyara laifukan da kayi, ina so cikin Kwana Biyar, komai ya daidaita, i want you to Fix Everything" da sauri yace "InshaAllah, zanyi gyara komai, Maa, nidai ki yafe min kar ki tsinemin, ina sonki Maa sosai, Wallahi ina sonki fiye da rayuwa da kanta. " Sosai Uwar taji tausayin Danta, amma ya zatayi? A fannin gyara suke.
Fuska ta hade tace "Good! Kaje ka fara gyara kafin kwana Uku, sai komai ya daidaita zan san abunyi, kaje yanzu" mikewa yayi ya karaso gunta, hawayenshi ba su daina zuba ba, yace "Please Maa, Can I Hug you Now? (DonAllah Ina iya rungumarki?).
Wani abu taji ya choketa, abunda take so tayi kenan itama, ta rungumeshi, amma sai ta juya ba tare da tace mai komai ba ta fara tafia kafin hawayen da ta dade tana boye suka soma wanke mata Fuska, Najwa ta bi bayan Maamnta, shima cikin kunan rai ya juya da sauri zai bar gurin, Paapa ya rik'o hannunshi, ya kalli Abdulmajeed yace "ka shiga dasu ciki" Abdulmajeed ya share hawayenshi ya daga Ziyada kafin ya ja hannun Zaineema tare da ca Hajjo "muje Hajjo" suka shige chan cikin dakin Najwa.
Mairo da take ta wurga idanuwa tace "Daddyy donAl--" bata karasa ba Daddy ya buga tsaki ya fita daga Parlorn, zata bi bayanshi Pappa ya katseta ta hanyar cewa "Aa Hajia Mairo, ki barshi, ba yau ba" chak ta tsaya kafin ta sake marairaicewa ta kalli Zaid da har yanzu hannunshi na rike da a babanshi, zatayi magana Papa yayi saurin cewa "Aa Hajiya Mairo, wannan ma ba yau ba, ki tafi kawai, zan nemeki" ba gardama ta kama hanyar fita taji muryar Zaid bayan ya karasa gunta yace "Me kike so? Kudi kike so? Dukiya? Zanbaki ko me kike so, amma DonAllah kar ki rabani dasu kuma, duk Afrika, ba matashin da ya kaini kudi, ki dauka duka, ki dauki komai, amma kar ki sake raba ni dasu, zan kwashesu mu bar k'asan, wallahi ba zamu sake dawowa ba, kar ki dai rabamu donAllah". Paapa ya sake karasowa gun shi ya riko kafadunshi, Mairo kuwa a guje ta bar Parlo.