← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 128

Sashe 96

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar me tsoron wani abu ya bude k'ofar dakin a hankali yana lekenta, jingine ya ganta da Gado, kar dai fevern tane ya dawo, fitarshi yanzu maganin da suka bari a bauchi yaje ya siyo. Hannunshi dauke ne da Ledan Magani, da Basket bag me dauke da Abinci wanda bansan daga inda Zaid ya samoshi ba, zuciyarsa ya kai nesa ya karasa gareta, murya cikiciki yace "kici Abinci, in kin gama ki sha magani, be jira cewarta ba ya juya da sauri don kar ta mishi maganar da baya so, cikin zafin nama ta mike ta is gareshi ta rungumoshi ta baya kafin ta kwantar da kanta kan bayanshi, runtse idanunshi yayi yana jin hannunta rungume ta kirjinshi, sun dade a tsaye, jin hawayenta a kan bayanshi ya juyota a hankali yana kallon cikin idanunta yana me tsoron abunda zai fito daga bakinta.

"Kayi hakuri" ta fada a hankali, sadda kanta kasa tayi yasa yatsun shi biyu ya dago fuskarta, suna masu kallon juna, a hankali ya girgiza kansa yace "I hate fighting you, bana so har raina" da baki ta sake ce mai "i'm Sorry" Murmushi ya sakar mata yace "Na gaya miki abubuwa da yawa sun faru ai? Na gaya miki nayi abubuwa da yawa da ba zan iya gyarawa ba sai dai ba zan sake maimaita su ba, abunda Amjad ya fada gaskia ne, ni na ce mishi haka saboda kar ya aureki, saboda ni nake son Aurenki, amma na rantse miki shine karamin abu daga cikin ayyukana, i was a monster, i did inhuman things, Na gaya miki somethings are better left unsaid saboda kwanciyar hankalinmu duka, rashin fadan shine Alheri, ban san me zai faru ba saboda fadar abubuwan nan, and To God, i'm scared to lose you, i know the curiousity would be there, but for me can you let it go? For me can you forget about everything? For me can you ignore things that are yet to come? Can you forget the past and focus about the future? (Kuma tsakani da Allah ina tsoron na rasakai, na san zaki so kiji menene, amma zaki iya sharewa don ni? Zaki iya share komai, zaki iya dode kunnuwanki ta wasu da zasu baiyana nan gaba? Zaki iya share baya mu maida hankalinmu kan gaba?)".

Be jira ansarta ba ya tallabo duka fuskarta da hanayenshi biyu yace "Wallahi Tallahi na chanza saboda ke, Wallahi na ajiye abubuwa da yawa saboda ke, i want you to trust me, ina so muyi putting komai a gefe, mu biyu kadai ne na junanmu, kin manta me nace miki dazun a bauchi before all that happened? You are my Always and Forever, baki yarda bane? Please believe me, I want you to trust me, ki yarda dani Ziyaa, i'm a changed person".
Juya kalamanshi takeyi, har ranta ta gasgata kalamanshi, In kafiri ya karbi Musulunci sai a cigaba da kiranshi Arne? In Mazinaci ya tuba ga Allah tsakaninshi da Ubangjinshi ne, wannan kuma tsakaninta da mijinta ne, ba zatayi judging dinshi a laifin da ta kamashi a baya ba, zata dauki hukuncin da zata kamashi a gaba, a hankali ta dauki hannunta ta kai daidai kumatunsa da ta mara, ta shafa a hankali ta hada idanuwansu, tace "I trust you, I trust you with my Life" bude hannayenshi yayi mata tayi sauri ta shige cikin jikinshi kyakyawan runguma ya musu.

Daga bisani ya rada mata a kunne cewa "I'm hungry" a hankali ta janye jikinta daga nashi ta tafi kitchen, plates da serving spoon ta dauko musu, lekawa tayi daki yana tsaye inda ta barshi "Oya dauko Lunch Bag din" dauka yayi suka fito daga parlorn suka isa dining area, ta zage zip din ta fiddo da warmers din, ta bude coolern farko Peppersoup din jan nama ne, dayan kuma hadadden Couscous ne wanda ya ji kanya lambu da hanta, ki samun Peppersoup din da yawa, sai abincin kadan, a plate daban daban tayi yanda yace ta tura mishi gabanshi, ita kuma ta zuba Couscous din da dan yawa, ta sa naman a ciki, harta zauna tayi saurin tashi don dauko ruwa a fridge, tana budewa taga Fruits da drinks kala kala, bata ganin sanda ake kawo duk wani abun amfaninsu, babban roban ruwa ta dauko da wasu Orange drinks din daga kallo kasan foreign ne, ta kai kan table, lokacin Zaid cin Couscous dinshi yake cikin kwanciyar hankali, itama ta fara cin nata, kura mai ido tayi yanda yake cin abincinshi ya burgeta, tana kallon ya ture ya janyo plate din peppersoup din, har zai fara ci ya fasa tare da k'ura ma plate din ido, kamar naman zai yi magana, ta lura da yanayin chanjin fuskar shi, ta dan taboshi tace "Yadai? Lafia? " Murmushi yayi tare da girgiza kai yace "Duk sanda zanci Peppersoup din jan Nama, na kan tuna Babana, yanason Jan Nama, ya san fa yana da Gout amma be fasa ci ba, Doctor ya kirashi ya hanashi, sai yace ya bari ashe in ya dawo Gida yana sa a masu aiki su dafa mishi, da Dr ya gane be daina cin naman ba, sai ya kirani yace in kula da abincin da yake ci, Baba be ji dadi ba da na sani, ina zuwa duk RedMeat din da ke fridge sai da na sa aka fitar dashi a gidan, sai Kaza saboda ban san Kifi shima ya bar ci, wai kinsan me Mutumin nan keyi?" ya tambayeta yana daria, ta girgiza kai itama tana dariar ba wai don tason dariyar me yakeyi ba, ya cigaba yana cewa "Wai sai mutumin nan ya siyo Naman shi ko ya sa Masu aiki su dafa mai amma kar a gaya min, sai yaje bayan k'ofa ya ci abunshi, kullum fa haka yakeyi, har sai da na kamashi redhanded yana ci a bayan kofa, could you imagine, the Whole Alhaji Sadam Audu Gatan Marayu boye bayan kofa yana cin nama a boye?" daria suke gaba daya, bata taba ganin faraarshi ba kamar yau, yanda yake bata labari yana daria tsakaninshi da Allah ita ba wai labarin ya bata daria sosai bane, amma ganinshi cikin annashuwa yasata biye mai tana daria, tace "to ya akayi ya rabu da cin Nama? " Zaid ya tsagaita darianshi yace "Wa? That stubborn Old Man, ai ba zai bari ba, sai da ya kasance indai ya sa a dafa mai sai dai ni na kwace na ci, kullum haka muke, a dafa mai in cinye sai in sa mishi Kaza, wai sai yace be son Kaza, ji yake kamar Dusa, ke har ranar da zai mutu sai da yaci Parpesun kan rago".

Ziyada tace "Allah Sarki, Allah ya gafarta mai ya sa ya huta" Murmushi Zaid yayi ya cigaba da cin Naman, "Matarshi fa? I mean Mamanka" jimm yayi tare da tsagaita taunar naman da yakeyi kafin daga bisani yace "ban taba ganin Matarshi ba" Ziyada da mamaki tace "Bangane ba" a takaice yace "Matanshi ba donAllah suke son shi ba, yana da wani laluri da Mace ba zata iya zama dashi ba, su kance baya iya haihuwa, to duk wanda kika ga ta aureshi, to ba dan Allah bane sai dai don dukiyarshi da abun da ya tara, to tunda muka hadu be sake wani auren ba" kai ta jinjina bakinta na nauyi zatayi magana yayi saurin katseta don ya san me take son cewa, a takaice yace "i'm only his adopted Son, the son he never had, the son he always wished for(Ni Yaron da ya rika ne, nine yaron da be taba samu ba, Nine yaron da ya dade yana son samu) ".. Ya danyi jim kafin yace "My Parents are Dead". Allah sarki, sosai ta tausaya mishi, akwai tambayoyin da take so ta mishi, amma zata share, tace "Ubangiji Allah ya gafarta musu duka, ya sa sun huta, ya sa Aljanna ce makomarsu" ya ansa da Amin, ta chigaba da cewa "akwai hikima babba a taimakon maraya, balle shi wannan Marayu sama da dubu ya inganta rayuwarsu, ya dauke su kamar nashi, ai tashi tayi kyau InshaAllah,sai dai mu roki Allah ya inganta k'abarinshi" Sosai aji dadi da adduointa, yace "Ameen, i'm sure da ya ganki da ya soki, sabida yana son duk wani abun da nake So" blushing ta fara yi a hankali tace "Kana sona?" bata san yaji ba yace "Fiye da tunaninki" kallonta ya cigaba dayi kasa kasa, da sauri ta maida kanta kan plate tana cin Abinci, har suka gama ya tashi ya koma daki ita kuma tayi clearing gun da suka ci Abinci ta danyi kallo a ZeeWorld har wurin to 11 kafin ta kashe ta koma Daki don bacci.

Har ta hau Gado taji shigowarshi, juyawa tayi da sauri kasancewar duhu ne ta kashe Wuta bata ganshi ba, da fitilar wayara ta haka shi, tsaye ta ganshi cikin fararen shorts da top karama, ta dan muskuta tace "Bakayi bacci ba" cikin mintunan da sukayi kama da har abada yace "Erhm Eh banyi ba" ya karaso kan Gadon ya zauna, ta tashi zaune duk da cikin duhu ne amma tana hangenshi, tace "Lafiya? Kaje daki zan kwanta" da sauri yace mata "ina jin tsoro ne" ido a ware tace "Wani irin tsoro kuma?" yace "ba zan iya kwana ni kadai ba, ina tsoron dodo ne ko me ake cewa?" Ziyada ta fahimci ya ma raina mata wayau, ta juya mai baya tayi kwanciyarta tare da jan bargo.
Chapter 96 · 0% Book details