← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 128

Sashe 94

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read

A yanda suke ta amince dashi,聽 Zuciya ce qanda bata da k'ashi,聽 Allah ne shaidarta tana son Zaid sosai,聽 ta kalleshi da idonshi ke a lumshe,聽 bata yi kokarin raba jikinsu ba tace "ina so na san dalilin da ya sa ka ma Mummy abunda ka mata,聽 shin ka santa a wani gu ne?聽 Shin ta taba maka wani abunne? Akwai wani unfinshed bussines ne tsakninku?聽 Meyasa ka gaya mana bak'aken Maganganu, meyasa ka Azabtar da zuciyata?" ta lura yanayinshi ya chanza,聽 kanta na k'irjinsa ta rantse ta ji bugun zuciyarsa ya chanza, Yana Son Ziya,聽 a yanzu faranta mata shine Wajibinshi, baya son ranta ya baci,聽 baya son ta shiga damuwa,聽 ba ya so ta tsani kanta saboda kuskuren Mahaifiyarta, sabida Farincikinta da kwanciyar hankalinta ba zai gaya mata Alakarahi da Mahaifiyarta ba,聽 kamar ba zai tanka ta ba yace "Ziyaaa,聽 there are certain things that are better left unsaid (Akwai wasu abubuwa da rashin fadansu shine Alheri) saboda ke zan manta da komai ya faru, ki san na baki matsayi babba,聽 zan sadaukar da kuddirin da na girma dashi tun ina da shekara 11 saboda ke,聽 Son ki ya girmi komai da nake da, so kema ki manta da komai ya faru" taji seriousness a muryanshi,聽 tana tsoron jin wani abun da zai ruguje mata farinciki ko nashi,聽 ta sake gyara kanta a jikinshi cike da shagwaba tace ""Mu koma Gida" a hankali ya bude idanuwanshi,聽 yace "i like it here daga ni sai ke,聽 no body else,聽 just us" gyada kai tayi kafin ta zauna da sauri tana dukkan kirjin irin shima ya tashi zaune,聽 haka ya zauna yana kallonta ta nuna shi da yatsa tace "Kar ka sake karya min zuciya,聽 kar ka yaudareni,聽 na baka daukkan so,聽 na baka dukkan kaunata, daga yau har zuwa ranar da zan ja numfashin karshena" kallonta ya tsaya yi kamar hoto,聽 tana jiran amsa daga bakinshi,聽 be san me zai ce mata ba,聽 dama duk wasu kalaman da yake gaya mata da Armstrong ke rubuta mai ko ya karanto mai,聽 be san ta yanda zai maida mata martanin kalamanta ba,聽 ya kuma san kalamanta na bukatar amsa,聽 ido ta bude tare da dan bugunshi a kirji tace "Ehem Ina jinka" gyada kai ya hau yi kamar k'adangare yace "Nima haka" Dak'una fuska tayi tace "kaima mene?" yace "abunda kika fada" turo baki tayi tace "ni gaskia ban yarda ba" be san me zai ce mata ba,聽 be san ya zaiyi ba,聽 kar ta gano be iya komai ba,聽 kar yayi hurting dinta inta san cewa duk abubuwan da yake gaya mata ba yin kanshi bane,聽 da sauri ya hade bakinshi da nata don kar ta gano gazawarshi, sun dade a wannan yanayin kafin ya saketa dukkansu idanunsu a lumshe,聽 bakon feeling na shigansu,聽 jikinsu dukka na rawa,聽 ba su saba ba,聽 ba su taba ba,聽 this is their first,聽 kalma daya ya san zai iya fada mata kuma yayi meaning dinshi, cikin wata irin murya yace "You are My Always and Forever" cikin sanyin Murya tace聽 "Always and Forever?" ya tallabo fuskarta da hannu bibbiyu yana gyada mata kai kamar lizard yace "Always and Forever,聽 i promise" da sauri ta rungumeshi tace "Allah ya dauwamar damu cikin farinciki da zaman lafiya,聽 Allah ya kwabe fitina tsakaninmu,聽 Allah ya bamu zaman lafiya da zuria dayyiba" shima rungumeta yayi yana dariya yace "Amin My Forever".

Sun dau tsawan lokaci a haka kafin yace "Hello Madam,聽 a dagani ko?" kunya ya lullubeta sosai ina kasa ta shige don kunya,聽 ta boye fuskarta cikin kirjinshi,聽 yayi daria yana kara matseta a jikinshi,聽 Wayarshi yayi k'ara,聽 ko motsawa beyi ba, Ziyada ce ta zame jikinta daga gareshi,聽 ya samu ya dauka wayan "Idi ya? Alright" ya kashe wayan ya sa takalma ya bude kofar dakin,聽 ya amsa sakon sa Idi ya bashi,聽 "Yauwa" kadai Zaid yace ya maida kofa ya rufe, ya dawo kan Gado ya mika mata Wayar yace "Ga Akwalar wayarki" kallon wayar tayi ta sa hannu ta rufe bakinta saboda murna kafin ta rungume shi tace nagode sosai, I love you so muc,聽 ya akayi aka dauko?聽 Naga anyi sauri" a takaice yace "Jirgi ya hau" Awwn,聽 thanks my forever" ya manna mata peck a goshi, ya mike ba zai iya sauraranta tayi waya da yan gidansu ba yace "bari inyi wanka mu fita ganin gari tunda baki fita ba tunda kika zo" ta gyada mai kai ta na kunna wayar,聽 toilet ya shiga don yin wanka,聽 ita聽 kuwa ta latso Mummynta.

K A N O

Zaune聽 suke a Parlo gabaki dayansu suna shan Tea and Bread da kwai, Wayar Mummy tayi k'ara,聽 ganin Ziyada ta sa ta saurin ce musu Ziyada ce,聽 duk suka tsaida kalacin gabansu na dukkan ukuuku suna rokon Allah ya sa lafia,聽聽 dauka tayi tare da sa Handsfree,聽 muryan Ziyada ya karade Parlorn "Hello Mummy ina kwana" bakin Mairo har rawa yake,聽 tace "Ziyada,聽 ya kike?聽 Kina lafiya?聽 Ince mijinki be miki wani abu ba?聽 Yana muzguna miki?" Majeed聽 a chafe da "Zuzu kina jina?聽 Are you Alright?" Zaineema ma tace "Sis kiyi magana, kina lafiya?" Zinatu ma tace "Ya Ziyada" dariya sosai Ziyada keyi tace "Relax Guys,聽 i'm fine, who is missing me?聽 me ya faru ne,聽 naga you sound worried kamar an ce muku ban lafia"Mummy tace "yo ba dole ba,聽 sanin wnada na barki dashi ai hankalin mu dole ya tashi,聽 ki gaya min if hes hurting you,聽 Daddynki da Yamajinki sunzo gidanki an hana su shiga" Ziyada tace "ku saurareni,聽 Mummy,聽 abunda ya faru聽 rannan was a complete misunderstanding,聽 amma komai yazo karshe yanzu, yanzu munyi tafiya munzo bauchi,聽 yazo wani aiki ne,聽 amma zamu dawo nan ba da dadewa ba,聽 ku kwantar da hankalinku,聽 everything is alright kunji?" Ajiyar zuciya suka sake a tare,聽 Mummy ta kara da cewa "haba nidai ince,聽 na san Alhaji Zaid ba haka yake ba,聽 akasi aka samu,聽 kice mai ba wani abu,聽 komai ya wuce,聽 ki tabbata kin samo ma Gatan Marayu takwara kafin ki dawo Kano" kai Ziyada ta dafe saboda kunya duk sunji kunya,聽 Ziyada ta shaew maganan ta hanyar cewa "YaMaji ina Daddy?" Daddy yace"Ina jinki yar gidan Ya Maji" tayi daria bayan sun gaisa tace "Daddy kuyi hakuri kunzo an hanaku shiga" Daddy yace "bakomai Allah ya muku Albarka" sai da Ziyada ta gaisa da Hajjo kafin tace ina Najwa,聽 tace kinsanta da kadaicwa tana daki" Ziyada tayi daria tace zan kirata,聽 sun dade suna waya kafin sukayi sallama.

B A U C H I

Sai da ya tabbatar ta gama waya kafin ya fito daga shi sai towel,聽 rintse ido tayi gam,聽 shi ko ya mata daria ya bude jakkarshi ya shirya hankali kwance jikin nan sai kamshi yake,聽 yace "Oya Muje ko?" tace "wai ina?" ya kashe mata ido yace "sightseeing" ta turo baki tace "bayan baka dauko mun kaya masu kyau ba" yace "to wa ya ja?聽 Ba sai da nace miki ki shirya kayanki聽 ba?" ta murguda mai baki,聽 yace " bari a kawo miki kaya,聽 wasu iri kike so?" tace "Doguwar riga Jallabiya" waya ya dauko ya latsa yayi waya,聽 ta bishi da kallo tace "wai kai komai sai dai kayi waya?" be tanka ta ba ya sakar mata murmushin gefen fuska.
Ba a dau lokaci ba aka kawo dogayen riguna a paper bag kala kala,聽 designs designs, sai jakka da takalmi, duk sun mata kyau,聽 wata Ja da ta dauke mata ido ta dauka ta shiga toilet tasa, chan sai ga ta tafito,聽 yatsunshi na karshe guda uku ya daga mata alamun tayi kyau tayi murmushi, suka fito daga hotel room din suka shiga lift suka sauka k'asa.
Convoy dinsu har sun taru suna jiran sakowanshi,聽 Faisal na daga gefe,聽 ya kalleshi yace "Yanzu duk motocin nan ni suke jira, DonAllah ba sai kun bimu ba,聽 Yankari Game reserve kadai zamu" Faisal yace "Okay Mota Uku kawai za su bi" Zaid ya marairaice yace "Daya donAllah" Faisal ya karasa gun Motar tsakiya ya bude baya ya na me kallon Ziyada yace "Biyu,聽 Madam Bismillah" Ziyada ta shiga tana Daria,聽 Zaid ya buga mai harara,聽 aka bude聽 mai shima ya shiga baya wurin Ziyada,聽 Faisal聽 ya kalli sauran drivers din ya sallamesu,聽 yace motar Steve kadai zata biyosu,聽 shima ya buda gaba ya zauna ya kalli Driver yace "YGR zamu" Driver ya ja motar聽 sai Yankari Game Reserve.
Chapter 94 · 0% Book details