Sashe 16
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya cigaba da cewa "You are now my Son, this is your House, all i have is yours kaji?" dan gajeren Murmushi Zaid yayi, a kwanakin nan ba kasafai yake magana ba, zai iya irga maganganun da yayi tunda yazo Gidan, Alhaji yace "Zaid, lets plan your future, zaka koma School, ba zaka cigaba da zama ba karatu ba" a dan tsorace Zaid yace "Bana son Makaranta kuma, zata bi ta kasheni" Alhaji Sadam ya murmusa "you are a very smart and wise boy Zaid, theres a great future ahead of you, zan kai ka Makarantan that noone will ever find you, i will take you far far away, and if they somehow find you, they'll have to go through me, saboda kai yanzu nawa ne, and they cant take it away, kagane?" a hankali yace "ni sai na kashesu, sun kashe min Iyayena" Alhaji Sadam ya sauko kasa inda Zaid yake, ya kama hannunshi, cikin dabara yace "kar ka damu, idan ka girma, zamu harbesu" Zaid ya gyada kanshi, wai shi nan Alhaji wayau ya mishi beson yara da rik'o ba.
Haka Alhaji suka tafi Supermarket da Zaid, ya mishi Siyayya, kayan sawa, kayan wasa da sauransu.
B A Y A N W A T A D A Y A
Zaid da Alhaji Sadam sunyi wata irin shak'uwa ta so da k'aunar junansu, wani abu dai da zaka fahimta da Zaid shine mugun shirushirun shi, iyakacinshi da maaikata a ko aa, da Alhaji kadai Zaid ke dan fira, har iyau duk dare Zaid sai yayi Kuka kafin yayi bacci.
*
Zaid ya kan tambayi Baba ina matarshi? Sai yayi daria, yace "shi baya da mata" "yaranka nawa?" sai yace "Zaid ne yarona, sai Yarana kasansu ai (Yaran NGO dinshi, yaran Gidan Marayu)" Zaid sai yace "Ina nufin yaranka da ka haifa" sai Baba yayi murmushi sai yace "Ban tana haihuwa ba" Zaid sai yace "to kayi aure mana" sai yace "Zaid mata ba sa so na" sai Zaid yace "Saboda meyasa basa sonka?" Baba sai yace "ba zaka gane ba Zaid, you are too young, idan ka girma, i promise to explain everything to you" Zaid ya jinjina kai yace "kar ka damu ni ina sonka sosai kaji Baban Zaid, baban Yara" Baba sai yaji dadi sosai, yana ganin duk duniya baida wani arzikin da ya wuve Zaid, yana gode ma Allah da Allah ya hadashi da Zaid, don yana matuk'ar sonshi.
* *
Damuwan Alhajin Daya,inda zai kai Zaid karatu, inda wani wanda ya sanshi ba zai taba zuwa ba, ina zai kai Zaid inda ba zai samu matsi da takurar rayuwa ba? Ina zai kai Zaid inda wani mugun ba zai so shi da mugunta ba? K'asar waje zai kaishi, ko ma ya kaishi India? Ya ji kwanakin nan ana maganar makarantun India masu kyau, ya tare Zaid da maganar, maimakon Zaid yayi murna, sai ya daure fuska yace "shi baya son ya bar kasarnan,anan zaiyi karatun shi" Alhaji Sadam yace "Zaid my Son, bana so su maka wani mugun abun, shiyasa zan nesantaka dasu" Zaid yace "nidai i wont leave Nigeria" ya fada yana finalizing maganarshi tare da murtuke fuska. Sam baya son ganin Zaid ya shiga damuwa da sauri yace "Sorry. Ba zaka bar Nigeria ba amma we wont be staying here again,indai kana Kano,Kaduna,Abuja one way or the other, ko ba dade ko ba jima sai kun hadu, kuma idan wani abu ya sameka, i dont know What i'd do, Zaid you wont understand, but i love you, you are all i have now, i dont want to lose you".
Sosai Zaid ke tausayin Babanshi Alhaji Sadam, he loves him equally amma akwai boyyayen fushin da ke dank'are a zuciyarshi, yana so ko ba komai ya dinga faranta mai rai, amma in ya tuna ya rasa uwa da uba hankalinshi na tashi, in ya tuna babu yanda zaayi ya samu k'anne zuciyar shi na baci,shifa sai ya kashe Maman Abdulmajid itace silar rabuwarshi da Iyayenshi, sai ya kashe Baban Abdulmajid, kai harta Abdulmajid din da Zaineema sai ya kashesu,but Babanshi yace sai ya Girma zasu bindigesu, to yanzu dole ya koma Makaranta, tunda Baba na son yayi karatu he'll do it for him, a hankali yace "Rivers-Porthacourt,a current afairs shows that, its the largest, Biggest and Widest State in Nigeria" Baba ya danyi guntun tunani yace"a Porthacourt kake son yin karatun?" kai kawai Zaid ya daga, Baba yayi murmushi yace "Porthacourt it is".
*
A kwana a tashi
K A N O NIGERIA
Zaune take gaban Dr, Doctor ya shaida mata cewa tana dauke da Juna biyu wata 1, sosai tayi murna, ta sanar da Alhaji Abba, murna dauke kan fuskarshi yace "Allah ya inganta" yace "barinje in sanar da Hajjo" fuska ta daure, in akwai abunda ta tsana be wuce yanda Abba ke rawan jiki kan Hajjo ba, yanzu Hajjo na ci mata tuwo a kwarya, kwanaki cewa yayi "zai dawo da Hajjo nan gidan, sai da Mairo tayi shige da ficenta kafin ya bar maganar dawowa da Hajjo Gidansu, tace"riga Mallam massalaci, meye abun gaya ma Hajjo? Ai ka bari cikin ya fito ko?" dariya kawai yayi yace "ai don tayi addua, ta sa mana Albarka" baki kawai Mairo ta ta6e.
NewDelhi
Tun shekaran jiya take jinta wani iri, tana jinta ba daidai ba, tashin zuciya na daga cikin abunda take fuskanta, abokiyar aikinta Simi ta lura da ita tace "Mrs Sada, are you Okay?" Yesmeen ta cije le6e tace "i think i'm sick" Miss Simi tace "you should see a Doc, there's a Doctor for the Staffs, i will take you there". Miss simi ta bude murya tace da abokin aikinsu " Bhaiya ham vaapis aaenge(we'll be back soon)" daga bangarenshi ya amsa.
Ta kamata suka k'arasa dan clinic din staffs a cikin asibitin, bayan 'yan gwaje gwaje, Likita ya shaida mata tana dauke da juna biyu wata daya, Allahu Akbar, hawaye Yesmin ta fara na farinciki, for the first time in a very long time, shekaru 11 rabonta da haihuwa,nan tayi excusing kanta ta hau keke napep ta tafi gida, kasa hakuri tayi Sada ya dawo daga aiki, ta kirashi a waya ta shaida mai tana dauke da cikin wata 1,Shima dai sai da yayi hawaye, don da ya tsammaci haihuwar sai yanzu Allah yayi, ya godewa Allah yace "gashin nana dawowa" bayan shudewan lokutta sai gashi ya dawo, nan ya tarar da ita tana kuka, da sauri ya k'arasa gunta, "Yesmeenah, Me ya sa kike kuka? Wannan ya wuce kukan farinciki don i can see sadness in your eyes" tsagaita kukan tayi tace "Papi,na tuna Zaid,na damu naga Zaid" yace "Yesmeenah, kiyi hakuri,zamu koma ga Zaid, i promise you, for now lets take care of Zaid's sibling" rungumeta yayi yana shafa cikin Jikinta wani dadi na sake ratsar shi.
Rivers PH
Gida ya siyan musu madaidaici 3bedroom a G.R.A Phase 3 Porthacourt, nan k'asan Unguwan akwai wata Private School
Norwegian International School, nan yayi enrolling Zaid duk a suna 2nd term, haka suka dauka Zaid JS2 don ya ci interview din da suka mishi, ba nisa daga Gidansu zuwa School din, tsaf za a tafi a k'afa amma Baba sai da ya samo ma Zaid Drivern da zai dinga kaishi Makaranta yana dauko shi, akwai mai kula da komai na Zaid, ana ce mata Iya, tun daga Kaduna Baba ya taho da ita,sun dade suna aiki tare da Baba, a gidan Marayu take itace kamar matron din Marayun,ganin Zaid ya saba da ita ne kuma tana da kyaun halaye shiyasa ya dauko ta ya kawota nan PH don ta kula mishi da tillon danshi, chan kuma wata tsohuwa tayi replacing dinta.
Duk da dakinshi na nan be kai dakinshi na Kaduna hadewa ba, Zaid be nema wani abu ya rasa ba, kome yake so ana mishi, Iya zata zauna ta ta mishi hira amma ba ya kulata, ya daura ma ranshi wani abu da shi kadai ya san ko meye.
Saboda so da kaunar da Baba ke mishi, haka ya dawo PH da zama, ya kanje Abuja ko Kaduna Aiki amma be wuce kwana 7 yake dawowa PH, yafi zaman PH yanzu, da yake babban mutum ne, haka ya fara bugabuganshi a nan garin PH duk don ya kasance tare da Zaid.
Bayan Wasu Watanni
Wani Ikon Allah a rana daya Allah ya sauke Yesmeen da Mairo lafiya, Dukkansu Mata suka Haifa, murna gun Mahaifansu ba magana.
A bangaren Mutan India, shagali Sosai mak'ota suka musu don suna shiri sosai, duk wata bidi'ar sai da sukayi duk da Yesmeen da Sada na dojewa,ba wanda ya kai Vijhay murna, don yana san Sada da Matarshi, tunda suka zo Kasar, kullum yana da abinci a gidan, shiyasa son ya shafi Babyn su, Maman wata Kaveri 'yar wata 8 tafi kowa zak'ewa, haka sukayi Shagali suka tambayi Sada ya sunan baby, yace "su bari sai bayan kwana 7 zai sanar dasu". Ranar Suna Sada ya yanka k'aramin dabanshi, ya rada ma diyyarshi Suna Najwanatu, NAJWA SADA ABU, anan ne sukayi wani Shagalin, abokan Aikin Yesmin da Sada sunzo da iyalansu,Yesmeen ta samu Gifts me tarin yawa, ta kuma ga mutane, ko a Nigeria ta haihu iyakan mutanen da zata gani kenan, hakan ya faru ne sabida zaman lafiyan da sukeyi da kowa,sun iya zama da mutane, shisa indiawan ke sonsu.
A Kano kuwa, banda goggagun mata Yan bariki, ba macen arzikkin da tazo Suna, Suna akayi na yan k'arya, don yanzu burin mairo ya cika, wanda a da be wuce ta zama a bar nuni ba, inda duniya zata san da zamanta, aiko gashi ta zama Matar Baban Mutum, matar Abba Abu guda, Suna akayi sosai kamar Biki, inda Yarinya taci suna ZIYADATU, Ziyadatu Abba Abu.
*
A halin yanzu, Hajjo ta zama abar tausayi, ba dama taje Gidan Abba, sai Mairo ta ci mata mutunci kamar ba Uwar Mijinta ba, Abba kam ba yanda zaiyi, ya kan ba Hajjo hakuri kan cewa ta hakura da zuwa gidanshi shi zai dinga zuwa,tun yana zuwa har ya daina zuwa, ya rasa gane me ke controlling dinshi.
Daga k'arshe dai Mairo ta sa suka koma Abuja da zama kwatakwata.
6years later