Sashe 35
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gidansu ya shaida musu gashi nan zuwa, ba sai an aiko daukanshi ba zai hau Taxi. Sallama yayi a gaban Parlorn Gida tare da shigowa, da Sauri yaran suka tashi suka fada mai tare da rungumesu, Matarshi itama tazo tayi hugging dinshi tare da mai peck, kunya ta bashi sosai don a kan gidan kowa hakan ta faru, ya matsa gun Mahaifanshi ya durk'usa ya gaida su, da farinciki suka amsa suna mai ya hanya. Mummy tace " kaje Kayi Wanka, kazo muyi dinner muna ta jiranka" yace "wai yanzu bakuyi dinner ba har 10?" tace "dole muke jiran ka" ya murmusa yace "Well, bani kadai bane, da bak'uwa nake" Mummy tace "bakuwa kuma daga ina?" yace "Tun Dubai muke tare da ita, its a long story, to cut it short bata da inda zata zauna, let her stay here for sometime" Mummy tace "Ayyah, OK tana ina?" yace "just a min nace ta jira daga waje barin mata iso" ya fita su kuma suka tsura wa k'ofan parlon Ido. Shigowa sukayi a tare. Kan Najwa a kasa ta tako, Mutumin yace "Najwa, meet My Daddy, Mummy, Wife sister and my brother" Mummy tace "welcome my daughter" Najwa ta dago da murmushi kan fuskarta ta zubesu fes kan Mummy, Mummy na ganinta ta zabura tare mik'ewa tsaye gabanta na dukan Uku-uku, wasu tunani na dawo mata, tunanin da bata so ta taba tunawa, wannan yarinya na mata kama da wata, tsanar yarinyan lokaci guda ya darsu a ranta ba don komai ba don kama da yanayi da takeyi da Yesmeen. Cikin daga Murya tace "Ke ya sunan Uwarki?" Najwa tayi shiru, Mairo kamar zata kifeya da Mari tace "ko ba kya ji ya sunan Mamanki?" Najwa da sauri ta 6oye bayan Mutumin da tazo dashi, yace "Haba Mummy? Menene? Me ya faru" Mummy cikin hargowa tace "Ta amsa ni" Najwa ta dago da mamaki tana mamakin Sudden change din Matar, don me zata tambayeta Sunan Maama dinta?ko wani mugun abun zaa mata? To ko matar ta san Maama dinta? Baki na rawa Najwa tace "Sunan Mamata Khadija" duk sunji dogon ajiyan zuciyan da Mummy ta sake, tace "Babanki fa?" tace "Erhm sunan shi Muhammad" Mummy ta sake sauke ajiyar zuciya, kawai yarinyan bata mata bane, mtsw ta daure fuska tace "Majeed, yarinya nan ba zata zauna da mu ba, so ka fita da ita" tsulum Zinatu tace "Yes Ya Majeed, i dont like her, tell her to go out". Majeed yace " Mummy why? Kin santa ne?" Mummy tace "Bansan ta bs, amma batayi min ba, irin su ne ke shigowa gidan mutane su rusa gida, bar ganinta karama, you dont know what shes capable of, maybe shes after you or something" nan da nan Nana taji tsanar Najwa, Majeed ya hadiye miyau yace "Mummy ba haka bane, bata san kowa a Nigeria ba, yau ta zo kasar, an sace mata Kaya, komai aka sace mata" Mummy tace lallai Majeed har yanzu yaro ne, baka san kaidin Mace ba? Tace an sace mata komai sai kai kaji tausayinta, kace bari ka kawo ta gidanku? Kila dama abunda take so kenan ka kawo ta gidanku" Majeed ya yarfa hannu kasa yace "Mummy please, wallahi akan idona komai ya faru, please let her stay" Daddy yace "Maryam, ki barta danAllah" Mummy tace "kaima ka yarda ko Daddy, besides muna fama da kanmu ya jajibo mana wata?" Daddy ya mata alama da ido, Mummy tace "Alright, just one Night" tana fadan hakan tace "Zinatu, Muhsin ku wuce muje" tayi ciki yaran suka bita a baya, Daddy ya dafa kafadun Majeed ya mai alaman 'Sorry' kafin ya rufawa Mairo baya, Nana sai da ta matso kusa da Najwa ta wurga mata harara kafin ta wuce dakinta itama, Majeed ya kalki Zaineema yace "Zee please, ki tafi da ita dakinki ku kwana tare" Zaineema batace komai ba tayi ciki, ya san hakan na nufin bata amince ba. Ya kalli Najwa da ke ta hawaye yace "I'm sorry you had to witness this, Mummy na da trust issue, bata yarda da kowa" Najwa ta murmusa tace "dagaskianta ai, banji haushi ba, kaine dai zan ba hakuri, ka samu matsala da Family dinka saboda ni" yace "Noo its nothing, yanzu dai zo kici abinci, i'll talk to Mum zata barki ki zauna for as long as you want" Murmushi tayi, ya karasa kan dining table, Rice and stew ne da plantain, yace "zo ki zauna kici" tana zuwa wurin table din kamshin ya cika mata ciki ta matsa baya tace "I cant eat this" yace Oh sorry, baki saba da spices din Naija ba, zakici Indomie Noodles?" tace "yeah, ina cin Indomie ko a India" yace "Alright, biyoni" ba musu ta bishi baya, wani daki ya bude mata yace ta shiga tayi wanka ta bude drawer ta zabi kayan da zai mata, a tsorace tace "dakin waye? Kar suji haushi fa" yace "dont worry, dakin Ziyada ne, my FAV Sis, ba ta da matsala she wont mind, besides tana Makaranta". Najwa tayi murmushi har ranta, har taji tana son Ziyada din, yace "Oya, jekiyi wanka, kafin ki fito nagama dafa miki indomie din". Ya juya ta bi bayanshi da ido a ranta tace "Can i trust this one?". Bibilicious freaking fans, ga Najwa a Naija, gata a Gidan Wan Babanta, gata a gaban Dragon Mairo lol. Rayuwan Najwa ya chanza daga lokacin da ta shigo Nigeria. Komai ya fara faruwa a gurinta daga lokacin da ta shigo garin Kano, ya rayuwan Najwa zai kasance gaban Hajia Mairo? Ku biyoni don jin ya zaa kaya. **** Nuseryber , miemiewaziri0 taatuh meeteelabo a appreciate you for commenting line by line #1love Thanks all, you've been supportive, like always Dont forget to Vote and comment please. #1love #ADAY #bibiliciousfreakingfans #anatare #nagode Ad skia馃挱 NA BIEBEE ISA 庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Wattpad:@biebeeisa Pg1鈨�8鈨� Sai da ta gama k'are ma dakin Kallo kafin ta fada toilet tayi wanshi,a toilet din ma Kuka tayi tayi, fitowa tayi tare da tsane jikinta, sai da ta shafa mai din da ta gani kan Madubi kafin ta nufi Sif din Ziyada, a sama taga wat 'yar doguwar riga mara nauyi, Najwa ta dauka ta sa, tana mamakin yanda rigar ta mata daidai kamar nata. Majeed ya k'wank'wasa dakin,ta mai izinin shigowa, da ya shigo daga nesa sai ya ga ta na mai yanayi da Ziyada, har kasa daurewa yayi "daga nesa kamar Ziyada wallahi" murmushi tayi kawai, yace "food is ready" ta daga hannu sama tace "Allah ka sa in iya ci" daria ta bashi Sosai. Kan dining suka nufa, daga jin k'amshin ta san cewa zata iya ci, haka ta zauna taci Indomie dinnan, Majeed ya dinga bin duk wani motsinta da kallo. "Oya tashi ki koma daki" ba bata lokaci ta tashi, suka nufa daki,ya mata umarnin dauko Hijab cikin wardrobe, ta dauko ta shimfida, ya ja su Sallar Ishai, dama ita kadai ce basuyi ba, ashe Nana na la6e tana kallonsu, yanda suke sallahn nan kamar wasu Maaurata, bakinciki tamfar ya kasheta ta koma daki da gudu. Bayan sunyi adduoi ne yace da ita "Tafiya mukayi mai nisa, ki kwanta kiyi bacci kinji? sai da safe" Murmushi takeyi har zuci, yanayinshi na burgeta, musamman in yace mata 'kinji?' dinnan, samun kanta tayi da bin umarnin shi. Majeed ya shiga Dakinsu, ya iske Nana zaune kan Gado, ta cika tayi Fam, Murmushi ya mata yace "kizo mu fita mu ci Abinci" harara ta jefeshi da shi, tace "kagama da wanchan karuwar?" dimmm yaji wani k'ara a kanshi, kalmar nan batayi ba kwatakwata, Kalmar bata dace da Najwa ba, inda san Wahalhalun da Najwa ta sha, da bata jefeta da mugun alkaba'i ba kamar haka, daurewa yayi ya kai zuciyan shi nesa yace "Nana nah, tashi muje muyi dinner, i'm hungry" ya fada cikin sigar shagwaba. Waiyo Dadi gun Nana, ce mata yayi 'Nanar shi?' ya yarda ita din tashi ce, wani dadi ya lullubeta, gashi har shagwaba yake mata, waiyo ita, wani sabon sonshi ya sake rufeta, Majeed ya fara sonta, Cike da salo da yanga tace "ba baka da time dina ba, sai na wanchan yarinyar?" dunguren kanshi yayi yace "wane ni? Haba Nana nah, i'm hungry please" cike da kissa tace "Oya tashi muje, kasan ban san Zamanka da Yunwa" ta ja hannunshi. Je ki tada Zaineema,Barin je gun su Muhsin, tura k'ofan dakinsu yayi,kwance suke suna kallon Cartoon, Ya k'arasa gunsu, Zinatu ta dauke kai, Majeed ya fara fuskantan Muhsin, yace "Superman bakayi bacci ba?" gyada kai yayi, yace"Uhm uhmm" "Oya fita dining, yanzu zamuyi dinner ko" yaron ba gardama ya fita, daman yunwa yakeji. Majeed ya juya gun Zinatu, kai ta girgiza mai "Ya Majeed if that girl is out there, i'm not hungry" Majeed ya furzar da iska, da wani me saurin hannun ne da ya kai ma Zinatu Duka, amma ba haka yake ba, responsibility dinshi ne faranta ma Family dinshi, ya daure dai yace "Bata nan, ta na daki, lets go" ba musu Zinatu ta tashi. Dakinsu Mummy ya fada, iske su yayi suna gardama da Daddy, zuwa yayi ya shiga tsakaninsu, tare da murmushi mai sanyi yace "Daddy, yaranka na jin yunwa, kaima kana jin yunwa, Suna kan table suna jiran fitowarka, Daddy ya bubbuga kafadun Majeed ya fita parlor, Mumny ta wani dauke kai, kamar bata san da Majeed a gun ba, tsugunnawa yayi gabanta, ya kamo hanayenta guda biyu ya kama ya rik'e, yana so su hada ido amma ta k'i yarda, yasan weekpoint din Mummy. Cike da sanyi yace "Mummy please" tasgi tayi ta janye hannunta tare da cewa "Majeed, bana son yarinya, from first impression, na gaya ma, bata yi mun ba" "Mum Najwa is clean, i trust her" "then you are a fool, nayi zaton kana da wayau, ashe ba haka bane, meye mutanen yanzu ba sayi? Don kawai su cimma burinsu, Boy, gobe ka fitar da ita, ba zata sake kwana ba daga gobe". Ya shashantar da maganan ta hanyar cewa "Mummyn Boy yunwa nakeji, lets have dinner please" tasan bribing dinta yakeyi, don yasan tana son shi sosai, dukan wasa ta kaimai a hannu tace "lets Eat" "Ohh Mumny na you are the best" ya ja hannunta suka fita