← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 128

Sashe 10

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana isa gida ya fara tatare tattare, Yesmin ta farka tace "Papi me kake tattarawa?" da sauri yace "ina zuwa, sauri nake" haka ya kwashe takardun Mallakar supermarkets 3, da Makullansu,har mukullin Motoci 3 duk da na Yesmin, ya wuce Kasuwa,daga nan ya wuce Office kafin ya je Company.
Kafin Azahar tas ya kwashe komai, ji yake ba zai iya jira ba har bayan Azahar, ji yake umurnin da Mairo ta bashi idan ya wuce minti daya ba zai iya rayuwa ba, so sai ya wuce gidan Abba kawai.
Zaineema na ganinshi ta rugo da gudu ta rungume shi, "Baba Sada ka kaini Zaid" dariya yayi yace "karki damu kinji yarinyata, Zaid ya kusa dawowa" Mairo ta murmusa tace "Zainee, je ki kira Baban ku a daki, kice mai Baba Sada yazo" da gudu yarinyar ta shige daki, ta kalli Sada, tace "har ka dawo da wuri haka?" yace "ai ba wuya na gama kwaso su duka" tace yauwa, ta mik'a mai Biro, yace gashi, ina so ka maida sunan duk Takaddun nan daga Sunanka zuwa sunan Abba, a hankali ya amsa biron, ya dinga chanza Sunanshi zuwa sunan Yayanshi jiki a sanyaye,yace "nagama" Abba da sai yanzu ya samu bakin magana yace "Meyasa? Don me zaiyi haka?" ta kalleshi tace shuttup, baka son ka mallaka Dukiyoyin Sada?" yace "ai yana bani dukkan abun da na buk'k'ata, hakan yayi" ta girgiza kai tace "aa, beyi ba, kana son dukiyan Sada" a hankali Abba ya furta " beyi ba, ina son dukiyan Sada" murmushi tayi ta kallo Sada tace "good, yanzu ka bar komai nan zuwa gobe ka dawo da Yesmin, da kuma Aminnan ka wanda ka yarda dasu su 10, zaka gaya musu ka mallaka ma Abba, dukiyoyinka, zaka gaya musu cewa Abba shi ya gajeka, zaka gaya musu baku san mai zai faru gobe ba, amma kasan ko bayan ranka Abba mai kula da duk wani abun da ka tara ne, yafi ka adani, ya fika kula, ya fika bukkata shiyasa ka mallaka mai komai, Abba zai kula da ku da Al'umma, kana so duk su ba Abba irin goyon bayan da suka baka, and duk wanda ya maka tambaya game da hakan, zakace its your decision,and its final do you understand Sada." a hankali ya gyada kai yace "na fahinta Maman Zaineema" tace "and kar ka ce ma kowa komai" yace "ba wanda zaiji" ya juya ya tafi tsalle ta daka da ta ga komai ya dawo karkashin Mijinta bari dai gobe tayi ayita ta k'are, har Party zata hada na Celebration, ta kashe ma Abba Ido tace "kayi Celebrating mana" Murmushi kawai yayi.

Zaune gabaki daya a parlorn Alhaji Abba, Aminnan Alhaji Sada suna Zaune suna mamakin dalilin tarasu da yayi, don kiransu yayi yace "su hadu gidan Alhaji Abba akwai muhimiyyar maganan da yake son sanar da su". Bayan sun nitsa duka Alhaji Sada ya fara da Bismillah, yace "nasan kuna Mamakin taraku da nayi anan, ba wani abu bane, na tara ku ne don na gaya muku cewa, Duk Dukiyar da Allah ya Mallaka min, komai da na tara, kasancewar Abba ne 'Next of Kin' dina, na mallaka mai komai, na maida komai k'ark'ashinsa"nan ya fara lissafo musu abubuwan da ya Mallaka wanda ya chanza izuwa Sunan Abba, da mamaki suke dubanshi, har Yesmin da ta gama rudewa, bawai don ya mallaka mai take jin Zafi ba, amma ta yanda yace "komai da komai, to saboda me?" ji tayi Alhaji Ashiru yace "Alhaji Sada, komai fa kace, to saboda me?" Murmushi yayi yace "ko bayan ba raina Abba shine Magaji na, shi zai Gaje ni a komai,Wa ya san Gobe? Wa ya san mai zai faru gobe? Nasan ko bayan raina Abba mai kula da duk wani abun da na tara,zai kula da komai, yafi ni adani, ya fini kula, ya fini bukkata, ya kuma fini chanchanta, shiyasa na mallaka mai komai, Abba zai kula da ni da Al'umma gabaki daya, sabida haka ina so duk ku ba Abba irin goyon bayan da kuka bani" Alhaji Sani yace "Amma Alhaji Sada" ds sauri ya dakatar da shi, yace "its my descision, and its Final" duk sukayi gum da bakinsu suna juya maganan a ransu, Yesmin da bata san hawaye na zuba daga idaniyarta ba, ta san this isnt right, something is wrong somewhere, tana kallo Alhaji Sada ya dauki kwallin da ke dauke da da komai nashi ya Mik'a ma Abba, Mairo ta hau tafi raf raf tana cewa "Allah ya tayaka rik'o" Abba yace "Sada, ba zan baka kunya ba, yanda ka yarda dani ka mallaka min komai, inshaAllah zan baka Mamaki, i wont let you down,Allah ya saka da Alheri ya bar zumunci" Sada yayi murmushi yace "bakomai Sada, abu na naka ne, komai yanzu kuma naka ne" suka rungume juna. Ya kalli jama'an dake gurin yace "InshaAllah ran Jummaa zaayi 'yar gutun walima don taya Abba Murna". Da haka aka watse

聽聽 Ranar juma'ah aka sha Walima a Company da yanzu Ya koma ABBA ABU & SON's FURNITURES,inda Alhaji Sada ya k'addamar da taron ya shaida ma Mutane cewa komai yanzu na Alhaji Abba ne. Mairo na jin mutane da yawa suna tsegumin abun, har wata na cewa "ina aka ta6a irin haka? Komai fa ya mallaka mai, anya an bar Alhaji Sada haka kuwa?" dayar tace "me kike nufi?" tace "gaskia wannan aikin asiri ne, ba cikin hayyacinshi yake ba, waye don zumunci zai yi kyuata da hardwork dinshi gaba daya, kuma da ranshi da lafiyar shi, bawai ya ba shi manager ba, gabaki daya fa ya mallaka mai?" dayar tace "gaskia da alamar tambaya,Aikin Asiri ne" hankalin Mairo ya tashi, nan tazo ta musu tatas, ta kore su daga wurin waliman, ba a gama Waliman ba ta wuce Dorayi gun k'awarta Aliya Bashir.
*
聽 聽 "Ina zaton nagama mai wuyan, ashe da yawa mutane sun dago ni". Aliya tace "Ai muddin Mutane na ganinsu, to tunanin da zasuyi tayi kenan" Mairo tace "anyi baayi ba kenan" Aliya tace "kawai a kiyi mai gaba dayan" Mairo ta kalleta da alamun tambaya tace "Mai kike nufi?" a takaice tace "ki shek'e su duka" Mairo ta gwalo idanuwa tace "kai, aa, ba zan iya ba, rashin imani na be kai nan ba" daria sosai Aliya tayi, tace "aiko ya kai nan, tunda kikayi abunda kikayi, ai Mairo, kwatakwata baki da Imani, hakan kawai ne mafita, in ko ba haka ba, Mutane zasuyi ta surutu har Asirinki ya tonu" Mairo tayi kasak'e tace "yanzu dai meye abun yi?" tace "gobe ki shirya muje gun Mallam sai ya baki maganin da zaki shek'esu" da haka sukayi Sallama suka rabu.
*
聽 聽 "Anya zata iya kisa?" zuciyarta tace "da Asirin ki ya tonu fa?" nan da na Shaidan yayi mata busa, zuciyarta ta bushe ta yanke hukuncin gobe zasu koma gun Mallam.
Jin muryar Abba tayi a Kanta inda yake cewa "Maryam tunanin me kikeyi haka?" a tak'aice tace "tunanin Kashe Sada da Yesmin nikeyi" ya zaburo yace "Saboda mene Maryam? Sun ba mu duk abunda muke da burin samu a rayuwa" tace "hakane, amma zamansu a doron k'asa barazana ce a rayuwata, shiyasa na yanke hukuncin kashe su" da sauri ya rik'o hannunta, "Kiyi Hakuri Maryam, ba sai kin kashe su ba DonAllah, Sada danuwa na ne, kuma ina sonshi sosai" tayi tsuri tana kallonshi, kar fa soyayyar danunwan nan ya bata mata shiri, kar fa Abba ya fara mata musu, a dakile tace "sai ka za6a ko ni ko shi" da sauri yace "ke na za6a uwar 'yayana, ina sonki, kece farincikina, zan iya rabuwa da kowa don in zauna dake, amma Sada danuwana ne, akwai Babba Alaqa tsakaninmu, ina neman Alfarma da ki barshi raye,in bakya bukatar ganinsu zan sa shi su bar garin,amma kar a kashe su donAllah Maryam" tausayin Mijinta ya kamata amma ta dake tace "in kuma hakan zai bani farinciki fa?" yace "da hannuna zan kasheshi don baki farinciki, amma ina rok'onki da kiyi hakuri" shiru tayi tace "zanyi tunani, har k'asa ya durk'usa yana mata godia". A Wannan daren bai runtsa ba, kwana yayi yana kuka, tana sane dashi amma tayi banza ta kyaleshi, ainun ya bata tausayi, nan ta yanke hukuncin da safe zata koma gun Mallam.
*
聽 聽 "Mallam yayi dariya, yace "Mairo, kin raina aikin da na miki, aikin da na miki babban aiki ne, zaki iya sa duk wani mai jinin Mijinki abunda beyi niyya ba, kawai fadan yanda kikeso abun ya kasance ne kawai naki" tace "Mallam, yanzu kana nufin duk abunda na sa Sada da Yesmin zasuyi?" yace "da kikace ya mallaka ma Mijinki komai yayi gardama?" tace "haka ne,yanzu dai da nayi niyyan kashesu, amma na fasa, kawai ina so su shiga duniya, chan k'ololon duniya, kar su sake waiwayen inda muke, suyi nesa da har abada ba zamu sake haduwa ba balle wani ya shaidasu, ina so su zama tamakar mattatu a gun kowa" Mallam yayi daria yace "hakan kawai zaki kallesu kice musu, zaki sha mamaki" tace "naji wannan, amma ina so kaima ka k'ara da naka aikin yanda aikin zaifi ci, ko sunan K'asa Nigeria sukaji gabansu zai fadi balle suyi niyyar zuwa" yace "ki tashi ki tafi, baki da matsala, daga ranar da kika sa su suka bar garin,ki k'addara kamar an sa su a k'abari ne an rufe". Sukayi godia duka suka bar wurin Mallam.
A hanya Aliya ke tambayan Mairo "Shin dansu fa Zaid?" Mairo tace "wannan tsinannen yaron, da yana nan da harda shi duk zaa hada, amma ban iya jira har ya dawo,bari a fara da uwayenshi, ni da hannuna zan murk'ushe shi, ke dai sa min ido". Aliya tace " kai Mairo ba Imani" tayi daria tace "gunki na koya komai".Suka chafe suka saka daria.
Chapter 10 · 0% Book details