Sashe 93
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kan gado ta koma ta zauna tana juya mishi baya. Tana jin Idanuwanshi akanta, kamun ya tashi ya karasa gefen da take ya zauna. Wani numfashi mai nauyi ya sauke "Yunwa nake ji" a tsawance tace "Sai akace yunwarka ta dame ni?" shagwabe fuska yayi yana ware mata idanuwanshi cikin wani yanayi da bata taba zaton ganin shi ba. Kamun ya kamo hannunta ya dora kan cikin shi "Incase baki fahimta ba, ko kadan banda energy din rikicin ki. Yunwa nake ji" ya sake maimaitawa.
Kwace hannunta tayi tana murza inda ya rike tana jin kaman yabar tambari a jiki. Baice mata komai ba ya mike yana me fita daga dakin. Ta sauke ajiyar zuciya, sam ba zata yarda ta kara fadawa tarkon shi ba. Baifi mintina biyar ba ya dawo, bata kalle shi ba, idanuwanta kafe a kasa.
Bayan Minti 35 da shigowanshi,聽 sai ga room service yayi knocking,聽 Zaid ya fita ya karbo ordern da yaje da kanshi ya musu,聽 don kwadayi irin Dankalin da ta soya Jiya a gida ne,聽 musamman ya fita yaje kitchen din ya musu bayanin yanda yake son dankalin ya kasance.
Kan Carpet ya zube ya tankwashe kafafunshi,聽聽
Yana so yace mata ta sauko su karya amman baida karfin yin gardama, ba kuma yajin zai iya jure ita tai mishi gardama, gabaki daya zuciyarshi ta gama narke mata. Ziyada kam bata san abinda yasa taji tana son ya sake mata magana ba don tunda ya shigo be sake kulata ba, Wata irin kewar muryarshi take ji,聽 ga kuma Yunwar da takeji.
Jin kaman tana kallonshi yasa shi juyawa da fadin "Ki sakko mu karya" duk ya wani canza, abubuwan da yake yi yau kaman bashi ba take gani. Sosai take jin kaman Zaid din ta na farko, kaman Zaid聽 din dayai amfani dashi ya yaudareta, kamun koma menene yake mata magana a zuciyarta ya fara ta sauka daga kan gadon. Shiru suke karyawar har suka gama.
Kallon聽 ta Zaid聽 yayi yana sauke numfashi "Zan fita, may be zan kai karfe biyu ban dawo ba. Akwai Business din da nake son handling. Ki kula da kanki kamun in dawo, can I trust you to do that for me?" bata san lokacin da dariya ta kubce mata ba. "Yaushe ka soma fadamun fitarka ko lokacin da zaka dawo? Yaushe ma ka fara damuwa da halin da nake ciki?" runtsa idanuwanshi yayi yana jin maganganunta na mishi zafi. Mikewa yayi kawai yana kai kofa. "Baka da amsa ko? Ko wannan ma na cikin wata yaudarar taka?" ta fadi a tsawace.
Da wani irin zafin nama ya dawo dakin yana sa hannunshi daya ya dagota dashi kamun ya hada goshin su waje daya yana wani irin sauke numfashi cikin bacin ran da sai da Ziyada聽 ta tsorata, idanuwanshi a runtse yana shakar kamshin da take, murya can kasan makoshi yace "Stop it, ki daina gwada hakurina, bazai mana kyau ba" duk yanda take jin zuciyarta na dokawa bai hanata fadin "Kome zai faru? Me zakai mun wanda bakai mun ba?" bude idanuwanshi yayi cikin nata.
"Sona zan dawo dashi a zuciyarki, sona zan dawo dashi cikin idanuwanki. Batare da izininki ba, saboda zan iya hakan, saboda na gaji da ganin akasin hakan, sabosa nagaji da komai, ke kuma kin ki ganewa, saboda me ba zaki gane hakan ba?" ba abinda take tsammani bane daga bakin shi, dan haka duk wasu kalamai sun tsaya mata, komai ya kwance mata be bi ta kanta ba yace "Please, just,ki kula da kanki" ya karasa yana sakinta hadi da ficewa ya doko kofar kaman ita tai mishi laifin.
Durkushewa ziyada tayi tana fitar da numfashi "Gab kake da dawomun da komai sabo, dan Allah karka mun haka, zuciyata ba zata iya daukar wani betrayal din ba kuma" tai maganar tana jin hawaye masu dumi na taruwa cikin idanuwanta.
BAYAN KWANA BIYU
A kwana biyun nan babu wani shiri a tsakanin su da Zaid , baima kara gwada yi mata magana ba. Asalima duk wani abu dazai hada magana a tsakanin su kauce mishi yake. Ita ke ordern Abincinta,聽 shima yayi na shi,聽 kulleta yayi ya bar tankata,聽 Su biyun yake azabtarwa da hakan. A bangarenta tana kewar muryarshi, har fadan da suke yi kewarshi take yi. Kaman yasan tunanin shi take yi ya shigo dakin.
Kanshi tsaye inda take zaune ya karasa yana zama shima, sosai ya hade space din dake tsakanin su "Look at me" ya umarta ta yanayin da ba zata iya musa mishi ba, fuskarshi ta kalla, ya fada, idanuwanshi sunyi zuru-zuru. "Nagaji...ban taba dauka ina Son聽 zaman lafiya ba... Ban taba dauka zan nemi zaman lafiya a tsakanin mu ba. Kome zance bazai gyara abinda nai ba, bazai gyara abinda ya faru ba" kallon shi take tana son ganin zuciyarshi ta cikin fuskarshi. Tana son ganin duk wani alama dazai nuna mata kalamanshi karya ne, wata yaudarar yake son shirya mata ta kasa.
Duk yanda ta so shareshi ta kasa,聽 muryarta na rawa tace "Ina tsoro, ina tsoronka, saboda me zan sake yarda dakai?" hannunta ya kamo ya dora kan kirjinshi inda zuciyarshi take.
"Karki yarda dani, karki yarda da kalamaina, ki saurari yanda take bugawa a kan hannunki. Da farko na dauka a lillibe take da son daukar fansa. Saida ta bude naji abin da nake ji daban ne, bance ki yarda dani da wuri ba..." tana jin zuciyarshi na bugawa a tafin hannun ta da sauri da sauri. Itama tata zuciyar bugawa take, hawaye na taruwa a idanuwanta saboda kalamanshi na wargaza mata duk wani bango da take tunanin ta gina na kare zuciyarta daga shi. Runtsa idanuwanta tayi hawayenta na zubowa.
"O. M. G,聽 Ziyaa please karkiyi kuka"聽 rokonta yake, sosai kukan ya kwace mata, saboda tana jin tsoron shi, tana jin tsoron abinda ya faru ya sake faruwa. "Ka daina, dan Allah karka sake hurting dina, zuciyata zata tsaya, zata daina bugawa" girgiza mata kai yake yana janyota jikinshi hadi da rungumeta yana son tai shiru, saboda gabaki daya kukan da take ya birkita mishi lissafi.
"Bazan sake ba, kuskure nayi, bazai sake faruwa ba" yace cike da assurance yana jin kanshi daban. Yana jin mutanen dayai amfani dasu dan cin ma burinshi, Sumbatar goshinta yayi saboda baya son girman laifukanshi su danne shi da wuri haka. Bai shirya ba. Dagowa tai daga jikinshi tana goge hawayen ta. "Kabani wayata..." ta bukata, 6ata fuskarshi yayi cikin rashin fahimta "In har da gaske kake ka bani wayata. Inhar duk abinda ka fada ba yaudara bane kaban wayata" ta karasa maganar tana tsare shi da idanuwanta,聽 ya zata zasu iya rayuwarsu su biyu ba tare da ta bukaci wayarta ba, ya zata zai maye mata gurbin Family dinta,聽 su biyu ba tare da kowa ba,聽 amma in har hakan zai sa su zauna lafia,聽 in hakan zai sa ta yarda dashi zai mata.
Wayarta na kano, "kina son Sabuwar waya? " ya tambaya a takaice, girgiza kai tayi tace "ni nawa nake so" Wayarshi ya zaro ya latso Idi,聽 tana kallon yanda yake waya yana bashi Umurni, ita fa gwadashi takeyi,聽 haka kawai ta ji hawaye na sake zubo mata. Akan me zuciyarta zata sake yarda dashi? Akan me ma zata amince cewar da gaske sonta yake... Juyowa yayi dungurgum kanta,聽 hakan ua katse mata tunanin da take. Dawowa yai inda ya tashi ya zauna "Anjima za'a kawo miki daga Kano" goge fuskarta ta sake yi, cikin sanyin murya tace "Da gaske? Are you for real?" yanayin da tai maganar da fuskarta ya sashi kwashewa da dariya.
Sake ware idanuwa take cikin wani sabon mamakin, dariya yake, da gaske dariya yake, hannu takai ta taba shi "Me ka sha? Ina Zaid聽 yake? Me kayi dashi?" da murmushi a fuskarshi ya kama hannunta yana matsawa dab da ita, yanda tana jin hucin numfashin shi a fuskarta. "Soyayyarki na sha, ga Zaid聽 nan, abin mamaki ko? You tame the beast of in me, kin canza ni"
Gani yai zata lumshe idanuwanta yai saurin hura mata iska a fuskarta "Don't, karki boyemun" warewa idanuwanta sukai batare data shirya ba. Sun jima a hakan tana jin yanda kalamanshi da shirun shi suka hadar mata,suka wargaza duk wani katanga da ta gina a tsakanin su "I will kill you if you betray me again,聽 bansan yanda zanyi ba, I will google and watch how to do it on YouTube but I will, I will kill you (Zan kasheka in ka sake yaudarata) " wannan karon dariya yake daya manta yanda ake irinta. Dariya yake da dukkan zuciyarshi. Ziyada ce ke threatening dinshi wai. Yarinyar dako fada bata iya ba kamun haduwar su. Yarinyar da ko muryarta saika saurara sosai zaka ji tashin ta. Dukkan su sun canza, rayuwa ta canza su. Soyayyarta yake ji a duk wani abu na聽 jikinshi.
Itama abin dariya ya bata kuma, musamman data kalli kirar Zaid聽 da tata, ta kalli yanda ko naushin shi tayi tsaf zata iya targada yatsunta, "Ka canza ni" ta fadi tana kallonshi "Mun canza juna" ya fadi yana kallon cikin idanuwan ta. "Kin yarda mu zauna lafiya? Kin yarda dani? Kin yarda bazan sake hurting dinki ba?" ba sai ya tambaya ba. Amman ba zata mika wuya da sauri haka ba "Bari a kawo mun wayata tukunna" girgiza kai yayi, ta yamutsa fuska "Ka daina yi kaman ba daga wajenka na koyi komai ba" murmushi kawai yayi, tasa shi surutu mai yawa yau din nan. Hannunta kawai ya kamo yana kwantar da ita a jikinshi, bata musa ba, dan su duka suna bukatar comfort din.