Sashe 113
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Zaid, ka koyi hakuri, juriya da dangana, abunda kayi was so wrong, it was inhuman" cike da damuwa Zaid yace "ni mutumin banza ne ko Baba? Maa tayi nadamar haihuwata? Mahaifana sun tsaneni, sun tsani abunda na zama, To wani jin dadi ya rage min a rayuwa? Babu, nagama ta6ewa, na san Allah ba zai yafe min ba, kila ma dan wuta ne ni" da sauri Paapa ya katseshi ta hanyar rufe mai baki da hannu yace "shhh, Zaid, kar ka sake irin wannna maganar, bawa be yanke ranshi daga rahamar Allah, Allahu gaffur rahim, besides ba kayi ma Mamanka komai ba, Yafiyar wanda ka cuta zaka nema, ita Albarkarta zaka nema, in kana son Albarkar, ka saita komai, ka gyara kuskurenka kamar yanda ta ce maka, zaka ci ribar rayuwa, ka daina ma Kanka mummunan zato, duk da kowa yayi nagari ya sani, amma ba ka makara ba, zaka iya gyara komai, You are Zaid Sada Abu, and you are my Son, and i love you".
Fadawa yayi jikin Babanshi ya rungumeshi sosai, da sauri yace "barinje in fara gyara komai, lokaci na kure min" Paapa ya murmusa yace "da yagegen rigar zaka fita? Kana so a ga The whole Zaid Sadam Audu da barkaken riga?" Murmushi Zaid yayi tare da sake rugume Babanshi, ganin yanda yake k'okarin sa shi daria yace "Nagode Baba, ina sonku sosai, i'll make you proud, da yardan Allah" Paapa yace "Ina Alfahari da kai Zaid, Allah ya maka Albarka" amsawa yayi da "Ameen, barinje Baba" be jira cewar Paapa ba ya fita da saurisauri gudugudu ba tare da ya damu da yanda rigarshi take ba.
**
Kuka sosai Maama keyi, Najwa na lallashinta, sai da tsagaita tace "Najwa ban tsani Yayanki ba, ina sonshi fiye da zatonki, amma ya kamata ya san abunda yayi be yi daidai ba, don yana da kudi be kamata yayi abunda yake so ba, Najwa ba zaki fahimci halin da nake ciki ba yanzu, Uwa kadai zata fahimci abunda nayi, ki min Addua, Allah ya sa Yaro na ya tuba, Allah ya sa Allah ya yafe mishi" ka sa magana tayi illa rungumeta da tayi, haka Paapa ya shigo ya iske su, ya hadesu biyu ya rungume.
A dayan dakin ma, Abdulmajeed ne ke karfin halin lallasan kannenshi Hajjo na tayashi, da kyar ya samu sukayi shiru suna ma juna jajen abunda ya faru.
Fadawa yayi Mota Jikinshi har rawa yake, yanda masu tsaronshi suka ganshi sun san cewa ba lafiya, ba wata wata suka shiga motocinsu suka bar Gidan. Wayarshi ya ciro ya latso wayar Idi, muryarshi ta dakushe saboda yaci Kuka, ringing daya yayi Idi ya dauka.
"Hello, Idi, listen to me carefully, Filin nan na Express Way da su Shehu suka rushe Furninshing Company din nan, ka kira Architect @LubnaSufyan yanzu, ta Zana Modernised Building, kayi Order a Italy da Turkey, a kawo kayan Katako, da komai ASAP, ban damu ba in zaa min shipping ni kadai, i need everything done cikin kwana Biyar, Idi Make it happen... Please" Yanda Idi ya ji muryan Oganshi ya san cewa ba lafia, ya san cewa yana cikin tsaka mai wuya, da sauri yace "Oga, angama InshaAllah, yanzun nan zaa fara aiki" da sauri Zaid yace "Thank You" ya kaste wayar ya latso numbern Armstrong.
Yana dauka "Sup Boss?" be da lokacin amsashi yace "Arm listen Carefully, fly down to Kano today, bring me AbdulMajeed's Credentials, and all the documents you collected from him, Arm, Today. (saurareni da kyau arm, ka hawo Jirgin Kano, ka kawo min Credentials din Abdulmajeed, da duk wasu documents din da kuka karba a gunshi)" be tsaya yaji amsar Armstrong ba ya latse wayarshi.
Lokacin da aka zo Gida, da kyar ya shiga ciki, daki ya shige ya fashe da kukan shekarunshi, ya dade yanayi, yana ji Zazzabi na rufeshi, be damu ba ya fada toilet yayi wanka ya doro Alwalan Maghrib.
Saita kanshi yayi ya tattaro natsuwanshi ya dauko wayarshi ya kira wani Alh Bello, bayan sun gaisa yace "DonAllah number din Khalid Mai kudi nake so"mutumin yace "to ranka ya dade barin turo maka" ko minti 2 baayi ba sai ga numbern Khalid an turo, nan take ya latsa mai kira. Sai dai tsinanan matar tace mai wayar kashe take, ya kira ya kai so goma, amma wayar a kashe kamar yayi hauka, ya sake kiran Alhaji Bello, ya tambayeshi ko khalid na da wani layi, ya tabbatar mai da shidai wannan kadai gareshi, amma bari ya tambayar mai wani, haka ya sake kira yace duk wanda aka tambaya, numbern dai da ya turo mai shi kadai ne.
Haka Zaid yayi ta neman layin Khalid amma baya shiga yayi niyyar zuwa Kaduna gobe da asuba.
Cikin dare Massasara mai karfi ya rufe Zaid.
Chan wurin 11 Armstrong ya shigo Kano, dauke da takardun da Zaid ya bukata, Zaid na ganinshi ya mike tsaye cike da karfin Hali kar ArArm ya gani halin da yake ciki balle ya hanashi Zuwa Kaduna gobe, haka Zaid ya kwana da masassara, da safe bayan Sallahr Asuba convoy dinsu ya tashi zuwa Kaduna, da kadan 8 ta wuce suka isa Kaduna, straight Maaikatar Khalid suka ma tsinkayi, lokacin GM din Khalid ya iso ya tarbi Zaid cikin mutuntawa, ba watawata Zaid ya tambayi Khalid aka ce mai Khalid na America, yaje yin wani course, Zaid ya dafe kanshi, kanshi na barazanar barewa ya kalli Hafiz yace "Get all the Information about Khalid" ya fita.
Armstrong ya bishi a baya.
Be da lokacin jiran Khalid ya dawo daga America, be da wannan lakacin, kwana biyar Maa ta dibar mishi, be da wani zabin da ya wuce bin Khalid America, Ganin bata lokacinshi zaiyi wurin neman Visa da komai ya yanke hukuncin bin Khalid America.
Umurni ya ba Drivers da zasu wuce Abuja inda Private Jets dinshi suke, Armstrong ya kalleshi yace "We no fit Fly Today, Fog they, and we need to get a pilot to take us off, coz them Ben dey Newyear Holidays, me sef i had to cut mu jolly coz na u callme(ba zamu iya tashi yau ba, garin akwai Hazo, kuma sai an kirawo Matukin Jirgi, Ben na hutun sabon shekara, nima don dai kai ka kirani ne, shisa na taho)" Zaid yace "Armstrong, i dont care just get me Someone to fly me to America, or i swear to you i'll fly mhself to America i dont know how but trust me i will (ban damu ba, ka nemo wanda zai kaimu, in ba haka zan kai kaina wallahi, bansan ta yaya ba, amma zan tafi)" Armstrong ya bude baki yace "Haa, e no reach that make i call Ben, we go payam double(Ahh, be kai nan ba, bari na kira Ben, sai a biyasu Double". Tak Zaid be ce ba, illa kiran Idi da yayi don jin ya progress din Ginin.
A M E R I C A 2pm
Khalid na zaune a Aji, Zaid ya shigo Ajin, Khalid na ganinshi ya mike tsaye cike da faraa, ai kowa dai in dai dan Nigeria ne, da wasu kasashen k'etare sun san Gatan Marayu, Zaid ya tunkareshi sukayi musabaha, Khalid ya murmusa yace "A iya sanina Gatan Marayu ya wuce shigowa Aji da niyyar karatu" Zaid ya danyi gajeren Murmushi yace "Aiko ku shugaban Kasa be wuce ya shigo Aji a koya mai ba" Khalid yayi daria yace "Shugaban k'asa? Ai ka fishi, kaine fa Zaid Sadam Audu, Gatan Marayu, The Youngest Multi Billionaire" Zaid ya sake musabaha dashi yana daria yace "Khalid na taso tun daga Nigeria don nazo gunka" Khalid yace "Ina fatan lafiya dai?" Zaid yace "Mu samu wuri muyi magana ko?" Khalid yace "just a minute" ya ma abokan shi Sallama ya bi bayan Zaid.
Wani Coffee shop suka samu suka zauna, Zaid ya fara magana.
"Khalid mai kudi, na san zakayi mamaki da nace na zo America dominka ko? To ba abun mamaki bane, Khalid na san ba ka sanni ba, amma ni na sanka, na san duk wasu moves dinka, saboda kana Auren k'anwata Zaineema" da mamaki Khalid ya kalleshi, Zaid yace"ka daina mamaki, Zaineema cousin dita ce, zuciyata cike da bakinciki, da nadama zan sanar da kai wani abu me rikitarwa, Khalid, nine sanadiyar rabuwarka da Zaineema" a firgice Khalid ya kalloshi, yace "bangane ba" Zaid yace "Khalid, nine na tura wani ya darsa Zargi a zuciyanka tsakaninka da Zaineema" dan karamin tsaki Khalid yayi yace "Ahh Mr Zaid, ba sai kun fito ta haka zan Maida Zaineema ba, na riga na gano framing Zaineema akayi, na san its not her fault, wasu Masu sharri ne wanda ba sa son zamana da ita suka hada mu, idona ya rufe shisa na kasa gane hakan tun a lokacin na sauwake mata, amma wallahi ina da niyyan in na koma Nigeria inje in maido matata, So Mr Zaid ba sai ka dauka laifin da ba naka ba zan maidata".
Zaid ya jinjina kai yace "Mallam Khalid, naji dadin wannan batu da kayi, amma ina so ka sani, ba wai don ka maidata na ke son daukan laifin da ba nawa ba, ina daukan laifin ne saboda laifi na ne, Khalid, nayi abubuwa da yawa na sabo, akwai wani abu da ya taba shiga tsakanina da Family dinsu gabaki daya, so na ma kaina Alkawarin maida rayuwarsu abar kwatance, na dinga binsu one by one ina tarwatsa farincikinsu, na taba Zaineema, na taba AbdulMajeed, na taba zinatu, na taba Ziyada, kai harta Yayan Babana Babansu Zaineema na taba, saboda wani abu da nayi ma mummunar fahimta, so yanzu ina gyara laifuka na, shine nace sai na zo na sanar maka da gaskian lamari" Mikewa yayi yace "ina zuwa donAllah, minti biyu" fita yayi da sauri, jim kadan sai gashi ya dawo da Armstrong.