← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 128

Sashe 7

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

聽 Ran Juma'a yake zuwa Kano ya koma ran Lahadi, sosai yake kula da Matarshi da Hajjonsu, harda Abba, duk abunda zai siyo ma gidanshi sai ya siyan ma Abba, dalilin haka ne Abba yayi relying kan Sada,har ya zama raggon Mutum, zuwa da dawowan da Sada keyi na daga hankalin Hajjo, don ta kanji a Radio Hadarin Motoci daga wannan gari zuwa wannan gari, wannan zuwan da Sada yayi ta mishi magana "Yanzu kai Sada, baka jin wahalan tafiya ko? Baka gudun Sharrin k'arfe?" Yayi murmushi yace "Umma, Allah zai kare, tunda ina daku ai dole nake zuwa ganinku" Hajjo ta jinjina kai, tana son Halaiyar Sada, yana da kula sosai ba kamar Abba ba, shi da yake cikin gari sai yayi kwana 8 ko fi bata dorashi a idonta ba, ta nisa tace "Sada, tunda matarka na hutun Makaranta, ka dauketa ku koma chan gun aikin ka, alabasshi in ta koma Makaranta ta dawo" dadi kamar ya shide shi, dama kunya ce ta hanashi tafiya da Yesmeen, yace "Umma kefa?" tace "in dai ta nine kuyi zamanku chan ka maida hankali gun aikinka, amma na san ba zaka iya ba sai kazo ganina da danuwanka, to ko zuwa bayan wata1 haka sai ka dinga lek'omu" yayi godia yaje ya sanar da Yesmin, itama sosai taji dadi don tana kewan Mijinta.

聽 聽 Zuwa yayi ya gaya ma Abba shawarar da suka yanke, yace "ai dama hakan yafi, zuwa da dawowan nan akwai matsala, gwara ku koma chan" nan suka danyi fira kadan har ya ke gaya mai Mairo na da juna biyu wata 3, murna kamar me gun Sada,ya zaro dari biyar ya ba, yace "ga goron Albishir" Abba ya yi dariya, yace "ai ka shiga ciki kai mata sannu don tana ta kwaikwai, ba don yaso ba suka shiga gidan Abba, kawai shi har yau hankalin shi be kwanta da ita ba, tana zaune ta tara uban miyau a baki, yace "Madam ya jiki?" cike da yatsina tace "da sauk'i" Allah ya k'ara sauk'i" Abba na murmushi yace "Gobe zaya wuce Zaria da Yesmeen" ta dan yi yastina kafin tace "au haka zata tafi bata mana Sallama ba?" Sada yayi adria yace "maida wuk'an zamu biyo da safe kafin mu wuce" bata ce komai ba, din har yanzu bata daina jin wani abu game da Sada ba, haka suka fita, har k'ofar gida Abba ya rakashi yace "to a gaida Umma da Yesmeen".

聽 聽 聽 聽 Bayan Wata Daya

Kwana biyu kenan ta ke jinta wani iri, tashin zuciya da k'warnafi ke damunta, bata yi k'asa a guiwa ba Sada na zuwa ta sanar mai, yace ta shirya suje Asibitin Shika, haka ko akayi, gwajin farko ya nuna tana dauke da juna biyu wata daya, Fadin farincikin Sada bata baki ne, haka ya dinga Addua. Washegari yaje Kano ya sanar ma Hajjo, Hajjo tayi adduan Allah ya raba lafiya, a lokacin Cikin Mairo na da wata huddu, fi'ili da iyayi dai Mairo nayi, ita bata son kaza ba ta cin kaza, kullum sai ta ci tsiren Hansin,shi ko Abba ya ta biye mata.

聽 聽 Lokacin da watan Haihuwan Mairo ya tsaya, lokacin Yesmin suka koma Kano, Yesmeen tayi ja sosai, cikinta na wata biyar yayi dabas a jikinta, ta zama abar shaawa, da taje gidan Mairo kai mata Akwatin da Sada yayi na Jariri, baki Mairo ta bude tana kallon Yesmeen, kasa boye hassadarta tayi, ko murnan ganin kayan batayi ba kamar yanda take mamakin chanzawar Yesmeen.
Don bala'i, saboda da damuwa a ranar ta fara nak'uda, bayan yan wasu awanni ta haifo yaronta dan Jazir dashi,daga Asibiti tace ita a wuce Gidan Hajjo da ita,
Hajjo ta tarbeta sosai. Yesmin ta kama zanin da Mairo ta bata wurin haihua ta wanke su tas.
Haka a ka dinga tarairayar Mairo da Jaririnta.Rago Sada ya Siyo, ran Suna yaro yaci ABDULMAJID.

聽聽 Yesmeen ce Rainon AbdulMajid, Allah ya dora mata son yaron, itace wankin kayan kashin shi,har Abba kance mata Ummin AbdulMajid.
AbdulMajid na da wata 4 Yesmin ta haifo danta Namiji,Farinciki gunsu ba a magana, har Yola Sada yaje ya gaya ma Iyayenta,da zai juyo aka hado shi da tsohuwan da zata kula da ita, Akwati guda Sada ya yi ma Uwar Jego da Jaririnta, harta Mairo sai da ya siyan mata Atamfa da Lifaya na fitar suna, ran Suna Yaro yaci ZAID.

聽 聽 聽聽Jim kadan bayan Haihuwan Zaid Mallam Iro ya rasu, Mutuwar ta girgiza Sada,yayi kuka sosai, Allah sarki tun kafin a rufo shi babban danshi yace akwai dukiyar Sada a gun Mahaifinsu, Sada yace "a bari a gama zaman makoki sai ayi magana" amma shi Dan yace "aa, Baba yace da ya rasu a damka maka Dukiyoyinka" Mukullin Shagon Kasuwa ya ba Sada, kasa karba yayi sai Abba ya karba, haka aka suturce shi aka kaishi gidanshi na gaskia.

聽 聽 Sada ya dauki nauyin gidan Mallam Iro don ba zai taba manta Alherinsa gareshi ba. A na haka ne Sada suka tattara ina su ina su suka koma Zaria, Zaid na da Wata daya, sam ba haka Mairo ta so ba, so tayi su zauna tare tayi ta ganni abubuwan da suke ciki.
聽聽 Bayan 40 ne Sada ya samo ma Yesmeen makarantan Ungozoma(Midwifery),Goggo na nan, Haka suka cigaba da Rainon Zaid.

聽 聽 聽 Bayan Shekara Hudu

聽 Alhaji Abba Abu ya kalli k'aninshi Alhaji Sada Abu yace "Gida yayi kyau sosai, Allah ya sa Alheri, sai ayi Sauka ku tare" Alhaji Sada ya murmusa yace "InshaAllah, yauwa sai maganan Makarantar Abdul dina da Zaid,tunda bakinsu bude yake ya kamata a sakasu a Boko da Islamiya"聽 Alhaji Abba yace "to ai sai a saka sun".

Alhaji Sada ya Gina Gidanshi a Sharadda, Gidane hadadde wanda sai wane da wane ke mallakan irin gidan,yana da motarshi mercedez 190, da ya siya Motar nan ne ya ba Alhaji Abba tsohon Motarshi starlet, bayan ya siya musu gidan da Alhaji Abban ke Haya, duk sun zama Alhazawa, don shekaru biyu da suka wuce Alhaji Sada ya biya musu Makka su 5 har Hajjo, sukaje suka rage farali. Kudi gareshi amma ba su rufe mai ido ba, ba su sa ya dau rawanni tsiya ya daura ma kanshi ba don har Yau yana aikin Kafinta. Yana kamantawa duk abunda yayi a gidanshi yana ma gidan danuwanshi, da Mahaifiyarshi. AbdulMajid kuwa kawai zaa ce Mairo ta haifeshi amma shi dan Yesmeen ne, don ko da yaushe yana gunta, Mairo ta bugeshi ta yi fadan ya bar zuwa amma ina, Alhaji Abba kance "ki rabu dashi kowa ya san AbdulMajid dan Yesmeen ne" zuciyarta sai tayi bak'i.

Da doki Alhaji Abba ya shiga gidan shi yana k'walawa ma Hajia Mairo kira, da sauri ta fito da tulelen cikinta, tace "Abba Lafiya?" cikin Zumudi yace "daga Sharadda muke, baki ga gini ba, ba kiga Gidan Sada ba, yanda kika san gidan kansila, gida ya hadu wallahi" ya karashe cikin d'oki, "tsuut" ta buga tsaki, da mamaki ya kalleta yace "ya akayi?" tamau ta daure fuska tace "Ya fa? Kai yanzu baka jin kunya? Ace k'aninka na da gidan kanshi kai baka dashi?" shima fuskan ya daure yace "Wannan gidan naki ne?" tace "aa naka ne, amma waya siyan maka?" yace "Sada, kuma lokacin da ya siyan min ya zama mallakina ko shi bai da iko akanshi" "hmm, haka dai kace, amma abun kunya ne ace k'aninka shine Ja Gaba a kan komai, Sada ya maka Fintink'au, kai kana nan zaune gida kamar hoto sai an dauko an baka, kaine fa babba ya kamata ace kai ne Gaba yana bin ka baya, amma ya maida ka sakarai, sai abunda ya dauko ya baka, gashi da Manyan Shaguna har da na saida gwal, gashi da shagin kafintoci, ga Aikin gwamnati yanayi, kai ka k'are a teaching" ran Alhaji Abba yayi matuk'a gun baci, yace "Ke Mairam, ki fita ido na, ai Arzikki na Allah ne, kuma da ni da Sada duk daya ne, tunda Allah ya bashi, kamar ni yaba, ba wani abu kuma zan cigaba da gode mai, ai naga da Arzikkin Sadan ne muke takama ko? Naga har Makka ya kaiki, kuma yake kula da danki kamar nashi, to kinga bansan Sakarcin banza da na wofi, ina sane da duk abubuwan da kikeyi cikin gidan nan, ki kiyayeni, So kike ki samin bak'ar Hassadanku ta Mata, to Allah ya tsareni da yin hassadan danuwana" yana kaiwa nan ya wuce fuuuu ya barta ranta na k'una, kawai dai ta fashe da kuka bakin ciki, jin Zafi da kishin Yesmin ya turniketa, yanzu ya zatayi??..

Wattpad:biebeeisa
Toh wannan pagen sai aslow, ban samu nayi editting ba, nevertheless Dont forget to Vote, Comment and Recommend.

#1love
#ADAY
#anatare
#Bibiliciousfreakingfans
#nagode

Biebee Isa
[11:32, 25/09/2017] 鈥�+234 803 414 9368鈥�: 锟斤拷A DADE ANA YI....sai gaskia锟斤拷

NA

BIEBEE ISA

庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg6鈨�

聽 聽 聽 Alhaji Sada ya dauki AbdulMajid da Zaid ya kai su wani IMAN Nursery and Primary School nan k'asan Sharrada phase 2, Makarantar mai hade da Islamiyya ne, a wurin interview "Whats your name?" Headmaster ya tambayesu, AbdulMajid yayi wuf yace "My name is AbdulMajid Sada Abu" Zaid ko yace "My name is Zaid Sada Abu" Headmaster yace "Wow ashe twins ne" shidai Alhaji Sada bece komai ba, don ba yau ya fara jin Abdul na amfani da Abdulmajid Sada ba, burgeshi yakeyi shiyasa yake sonshi kamar Zaid.聽 Makarantar mai hade da Islamiyya ne hazak'ar su da basirar su ya sa aka basu Aji biyu(Nursery 2), nan take Ya biya kudin makarantan duka, ya kwashe su ya zube su a Mota suka wuce gidan Baba Abba. Tijara sosai Mairo tayi, wai don me AbdulMajid zaiyi using sunan Sada bayan Ubanshi na da rai, ita sai taje ta chanza mai suna, Wulakanci Sosai Alhaji Abba ya mata, k'ila da ba don cikin da ke jikinta ba da ya maketa. Wannan Kenan.

聽 聽 聽 聽 聽 聽 聽 聽 Bayan wasu shekaru
Chapter 7 · 0% Book details