← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 128

Sashe 24

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko a gaban waye Nana ba ta da wurin zama sai jikin Majeed, abun na damunshi ainun, sam Nana bata da kunya, ga jarabar tsiya, Alhaji Abba kauda kai yakeyi don ba ikon Magana, ita kuwa Hajia Mairo in taga Nana na shishige ma Majeed sai ta yashe baki, a cewarta wayewa ce, kuma Nana ce daidai Majeed ita zata bude mai ido, don Majeed wani iri ne.
Nana bata da da'a a kan fita lokacin da taso ta dawo lokacin da taso, ko ta fita da Muhsin da Zinatu ta kaisu wuraren wasan yara, shiyasa yaran ke sonta ita kuma Mairo tana k'ara sonta. Ba ruwanta da Ziyada, a cewarta "she's no fun to be with" gaisuwa ce kawai ke hadasu don kwatakwata halaiyarsu ya banbanta.

K A D U N A

Cika aiki ya kalli Tamfatsetsen gidan da ke gabanshi yace "Barin kira Oga, i'm sure this is the house, address din da Oga ya turo min ne" ya dauko Waya a Aljihu ya latso numbern Oga Zaid sai da wayar ta kutsa tsinkewa kafin Zaid ya daga a dakile yace "Cika Aiki" Cika aiki yace "Oga gani a Unguwan Dosan, na gane Gidan" Zaid yace good, i'll tell you when to go in, i dont want any mistakes cika aiki" Cika aiki yayi daria yace "you can trust me on that.

Amstrong yace "Oga, you are after Hajia Mairo, why arent you getting to her directly? Why are you just hurting her Children" kamar bazaiyi magana ba, sai chan yace "because hurting her Children will hurt her more, she loves them alot, besides i'm just getting started, i'll get her soon". Amstrong ya jinjina kai, shidai ba damuwanshi bane duk me Zaid zaiyi yayi, as long as zai cigaba da cika mai Bank Account dinshi.
Bayan wasu 'yan awanni wanda yake daidai da k'arfe 9;30 na dare, Zaid ya kira cika aiki a waya yace " You can go in now, yana wurin Kawo, remember, bansan a sami matsala" Cika Aiki yace "Yes Sir".
*

Zaineema ta shiga toilet dan yin wanka, yau da wuri zatayi bacci tunda Oga baya nan, yaje Kano gobe zai dawo, ta yi wanka ta shafa mai, kamar yadda aladanta yake ta bi ko ina na jikinta da turare mai k'amshi, yar ficiciyar riga wanda be rufe cinyarta ba ta saka,
Ta kashe wuta tare da hayewa Gado, ta so jin muryan Mijinta amma wayarshi not reachable, adduoin bacci tayi kafin ta rufe ido don yin bacci.
Khaleed ya shigo gidanshi da misalin k'arfe 10:05pm, ya ki gaya ma Matarshi Zaineema dawowan shi don yana son mata Suprise, yau amarci zasu sake, don yayi missing dinta, suka gaisa da Maigadi, ya kwashi ledojin da ya zo dasu ya shiga cikin gidan da Sallama bayan yayi amfani da makulanshi ya bude gidan, beyi mamakin jin gidan shiru ba, dama daga ita sai mai aikinta, ya tabbatar sunyi bacci, kitchen ya shiga ya ajiye ledojin kafin ya shiga dakinshi yayi wanka tare da yin nafila, kayan bacci yasa ya nufi dakin Gimbiyarshi Zaineema. Ya sa hannu ya bude k'ofar, ya lallubo makunnin wuta ya kunna, Bak'in gani Khalid Yayi, idonshi ya sauka kan Zaineema da wani katon gardi kan Gado, da k'arfi ya furta "Inalilahi wa ina ilaihir rajiun". Cikin bacci Zaineema ta yi firgigi ta tashi da salati a bakinta. Tashi tayi da ta lura da wani kwance gefenta, da sauri tayi tsalle ta diro kan gadon, tana cewa " Honey waye wannan?" Hannu ya daga ya kamtseta da mari yace "Ubanki ne" zuwa yayi Kan Gadon ya finciko gardin da tsakanin shi ga Allah bacci yake be san me ke faruwa ba, Khaleed ya kaima wani mugun nushi a fuska ya bude ido tare da cewa , "sweety baki gaji ba kenan" yana bude ido ya ci karo da Khaleed, ya tashi irin a tsoracen nan yace "Sweety ba kice min yau mijinki zai dawo ba da banzo ba" Zaineema da ta kasa gane me ke faruwa tace "wai waye kai? Kuma me kake cewa" Cika aiki yace "Haba Sweety, dan kinga mijinki zakiyi pretending baki sanni ba, bayan na gama biya miki bukkatunki ko?" Khaleed ya kawo mai wani Shak'a ta baya, Cika aiki ya dunk'ule hannu ya guma mai Nushi mai zafi a Ciki, da sauri Khaleed ya sakeshi yayi kasa tare da dafe ciki, Zaineema ta aa Ihu, Cika aiki ya dauki rigarshi ya zura a guje. Da gudu ya bishi amma be cimishi ba har ya fita,ba abunda Zaineema keyi in ba kuka ba, tazo taren Khaleed ya sa hannu ya tureta, yace "Zaineema, na soki tsakani na da Allah, kin haince ni, kin cuceni, ban rage ki da komai ba, kin munafince ni, tsakani na da ke Allah ya isa, na sakeki Zaineema, na sake ki,dare yayi, zan miki uzuri, amma gobe safiyar Allah ki tafi ki bar min gidana, Adultress kawai". Wani irin kuka Zaineema ta sake tare da dafe kai, bata san hawa ba bata san sauka ba, bata san wake shirin rusa mata farinciki ba, tana kallo Khaleed ya sa kai ya bar mata Gidan, sai da taci kukanta ta shiga ciki, ta dauko waya ta kira gida duka basa shiga, da k'yar ta rarrafa dakinta amma bacci ya kaure ma idanunta, haka ta kwana zaune. Washegari da safe ta bi jirgin k'asa zuwa Abuja.

Yau Tuesday, Mummy tayi Sallama dakin Nana rik'e da Tray din breakfast, Nana ta mik'e tare da karban tray din Mummy tace "good Morning Mother inlaw" Wayewar Nana na burgeta, tace "morning daughter in-law, ga breakfast dinku na kawo muku" "Awwn thats so sweet" Nana ta fada tare da bude Warmers din.
Mummy tace "ina Yaro? Yazo in aikeshi Bank" Nana tuburne fuska tace "haba Mummy daga Aurenmu har zaki fara sashi ya fita, wai yaje wani bank? Tabdijam, to ai be gama hutun ba, besides jiya kwana mukayi muna abu daya so please ki barmu mu shana, in kuma naga zaki matsa mana, zansa Dad dina ya mana processing Visa mu bar k'asan" da sauri Mairo tace "No, no basai kinyi haka ba, sak'on nawa can wait, enjoy your breakfast" Byebye nana tace mata tare da binta a baya tana fita ta danna k'ofa ta sa Makulli tace "ba zai fito din ba" ta matsa wurin toilet tace"My Majeed, breakfast is ready"
*
Bari dai ta shirya ta kai kudadden nan banki, dama jira take komai ya lafa sai akai banki, to gashi Abdulmajeed bai da dama, ita zataje tunda Abba baida lokaci.
Takalma ta zira ta kira Falalu direba a waya. "Ka fito da mota zamu fita". Ta sauko kasa tana kwas kwas, kamar daga sama ta hango Zaineema ta nufo ta a guje, ta rungumeta tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya. In hankalin Hajiya Mairo yayi dubu to ya tashi, jiki har ya fara rawa, Rayuwarta, bata son kukan Yaranta, bata son tashin hankalinu, tana mamakin me ya sa Zaineen ta kuka, tana tunanin irin hukuncin da zata ma duk wanda yayi sanadiyar zuban hawayen diyarta, jikinta har rawa yakeyi, "Zaineema, kiyi shiru ki gaya min waya tabaki, me aka miki?" cikin Kuka Zaineema tace "Mummy, Khaleed ya sakeni"聽 ta sake fashewa da wani kukan.
Mairo ta lailayo ashar ta zuba, tace "da kika mishi uban me? Sai da ya maidaki bazawara zaice ya sakeki? To wallahi ba zaiyiwu ba share hawayenki" hayagagan da Mairo keyi ne ya fito da AbdulMajid da Nana, ganin Zaineema na kuka suka ci birki Gabansu, AbdulMajid ya juyo da ita gabanshi yace "Zaineema meya faru? Me aka miki? Ko wani abun ya samu Khaleed ?" karaf Mairo tace "ai dama wani abu ya samu shegen, wai mu zai tonawa asiri, sakin Zaineema yayi" AbdulMajid ya doka salati, me kika mai Zainee?" Mummy cikin hasala tace "mai ko zata mai? Ya gama cin moriyar ganga mana, wallahi sai naci mutuncin Khaleed, sai na watsa shi, sai na mai abunda zaiyi nadaman furta kalmar Saki ga Zaineema". AbdulMajid yace "Mummy Calm down, ki bari ayi komai a tsanake, ba mu san me ya hada su ba, ke Zaineema, me ya hada ku daga komawanki聽 Kaduna Sunday?" kasa magana tayi, Mairo tace "yo me ko zata mai, ita da ta koma jiya, kuma tace ko da ta zo biki bai gari? Me zata mai? Ko don abokinka ne?" Majeed bai kulata ba ya kalli Nana yace "take her to her room" Nana ta ja k'awarta sukayi daki. Majeed ya bar Mairo sai huci take tayi, ya latso numbern abokinshi Khaleed har ya gama ringing be dauka ba, kafin ya sake wani kiran, wayan Daddy ya shigo wayarshi, a ladabce ya dauka da Sallama, daga bangaren yace;
"Waalaikum Salam, Abdulmajeed, ina Mummynku ne?" AbdulMajid ya sa wayar a handsfree yace "gata tana jinka" yace "Maryam, kudin da Alhaji Nakowa ya kawo shekaranjiya nawa ke ciki?" Mairo cikin damuwa tace "inajin Miliyan 20 ne, ya akayi?" yace "Fanaz Ventures suke so a raba shares din Abba-fanaz Shares, zasu saida ne saboda wani emergency, shine na ga why not mu siya shares din, sai mu zama mallakin joint stocks din duka?" Mairo tace "hakan ma yayi" yace "ai ba a kai ga kai kudadden nan bank ba ko?" tace "da yanzu nake shirin zuwa" yace "good, yanzu AbdulMajid ka kawo min Kudin Office".
Chapter 24 · 0% Book details