← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 128

Sashe 6

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har Girmansu, suna aji 5 na Sakandire Allah ya ma Mallam Abu rasuwa, wannan Mutuwa ta girgiza duk wanda ya sanshi, saboda mutum ne mai Hakuri da iya zama sa mutane. Abba da Sada sunyi Kuka, ya zamana su ma ke lallashin Mamarta su. Kwanaki sun ja, duk cikin Abokan Marigayi, Mallam Iro kadai ne ke taimaka musu, shi yasan sirrin Mallam Abu, yanzu haka Dukiyoyin Mallam abu da duk wani abunda ya bari na wurin Mallam Iro, a cewarshi sai yara sun gama Sakandiri zaa raba musu su kama Sana'a,聽 Kafin nan duk wani ci da sha din gidan Mallam Abu聽 ya koma kanshi, bayan Sun gama Sakandiri ne Mallam Iro ya kira limamai masana rabon gado ya durfanar da komai gabansu yace a raba, haka aka raba mudu Gado kamar yanda addini ya tanada. Cikin Gadon Sada ya dauka wani Fanka yace da Mallam Iro, "baba ga fankan nan ka dinga shan iska" yace "Anya Sada, hakkinka ne" a takaice Sada yace "Na baka" yayi godia Sosai, yace da Hajjo"Hajjo in ba zaki damu ba, ina so in Aureki, ina sonki" fuskar Sada ya nuna farinciki na Abba ya nuna akasin hakan, Jim Hajjo tayi, ba zata k'i Mallam Iro ba saboda kirkinshi ya kuma tsaya musu tun bayan rasuwar Mallam, amma ganin bacin rai kan fuskar Abba ya sata ce mai zatayi shawara. Bayan聽 fitar Mallam Iro, Abba ya bishi da harara yace "Munafikin Baba" Sada yayi saurin cewa "Subhanallah, haba Abba, meye haka? Mutumin da yake kula damu yana bamu ci da sha kai har sutura in Allah ya hore mai, sai ka nuna bacin rai don yana son auren Uwarmu? Abun farinciki ne Abba" cikin聽 tsawa yace"dama ba danAllah yake kula damu ba, bana son wannan Auren, Umma danAllah karki aureshi, bana son ki aura kowa, duk munfukai ne, ni zan kula dake har k'arshen rayuwata, zanyi kudi Umma" ba dan tanaso ba tace "dama ba na son Auren kowa, Mallam shine Mijina na farko kuma ma k'arshe, kune farinciki na, kun isheni" Abba yayi murmushi mun gode Umma, girgiza kai Sada yayi ya fita, da wannan aka bar batun Auren Hajjo.

聽 聽 Hajjo ta musu maganan fara Sana'a, itama zata fara danwake da shinkafa da mai da yajin sayarwa, Abba ya rufe Ido yace "sam bai yarda ba, ya zaayi ace mamarsu tana abincin saidawa, shi gaskia sam, kuma shi kar a takura mai da fara sana'a,zaiyi idan lokaci yayi" Sada yayi mamakin Hajjo da tace ta fasa, da kuma zuba mai ido da tayi. Burinshi yayi karatu kuma InshaAllah sai yayi, ya gaya musu cewa zai ba Mallam Iro gadonshi ya dinga juya mai, Abba yace kai wallahi baka da wayau nan ya kushe hakan, Sada be damu ba tunda Hajjo bata hanashi ba, haka ya kai ma Mallam Iro Gadonshi, Mallam iro ko ya kira shaidu yace "ko bayan ba raina wannan na Sada ne, zan dinga juya mai da ribar da uwar". Sada ya gaya mai yanason ya cigaba da makaranta, Mallam Iro yace "ya jira fitowar takardun shi kafin ya shiga jami'a zai tsaya mai InshaAllah" Mallam Iro ya shiga da Sada wurin Koyan Kayan katako (Carpentry work) da abunda yake samu a gun aikin koyan Kafintan ne ya ke siyo Omo,sugar, ashana, da cingam yana k'uk'k'ulawa a tray yana zagayawa, Allah ya dafa mai ya bude mai kasuwa nan da nan ya ke k'arewa yana siyan wasu, sai kuma ya hada tebiri a gun aiki, yazo yana jera kayan Sana'ar shi a kan tebirin k'ofar gida, Abba ko da kudin gadonshi,sai dai ya siya banza ya siya wofi yana kashe ma abokai kudi,ya zama dan fafa.

聽 聽 Haka Sada ya k'ware a harkan Kafinta, yana zuwa gidaje yana gyara musu kujeru da makammancin haka, tradern shi kuwa ta cika mak'il don yanzu ya bar tebiri ya buga Container duk da Abba na shiga na daukan abunda yake so,ko a jikin Sada don a ganinshi abunshi na Abba ne, ya zamana cikin Gida ma Sada ke ciyar dasu. Haka Rayuwa ta cigaba har Sada ya ja raayin Abba suka koma Karatu.

聽 聽 Ko da suke Jami'a ana garin Kano, Sada da kudinshi sosai, don shi yake hidimar makarantansu da ta gida, Abba k'arya ta k'are tunda gado ya k'are, Sada bai da ganin k'yashi ko mai Abba ke so zai mishi, haka suka dinga karatu ba tare da wata matsala ba, har yau Sada bai bar kafinta ba, don yanzu likafa ta ja har kujeru da gadaje yakeyi.
聽 聽 Bayan Shekaru biyu

Ganin shi da kudi da kyaunshi Mairo 'yar mutanen katsinawa ta ganshi,Asalinsu 'yar kamaru ce, tana karatu itama a Kano,sosai take sonshi, ta sha kaimai kanta na ya sota, amma shi san bata mishi ba, ya bata hakuri, ashe idonshi ya k'yallo mai Yesmeen shu'aibu yar mutanen Yola, yarinya ce mai hankali itama nan take karatu fannin lafiya, a lokacin ba ko wani Uba yake barin diyarshi mace zuwa karatu wani gari ba, amma da yake Yesmeen na da kamun kai haka babanta ya barta tazo karatu Kano. Ajinsu daya da Mairo, duk yanda Mairo ta so ta shige ma Yesmeen amma ta k'i yarda, don yanayin Mairo da k'awayenta bai mata ba. Haka su Mairo suke jin haushinta don ta fiye girman kai a cewarsu.
A lokacin da su Sada zasu gama Makaranta,har lokacin Mairo bata bar yi mai Wasik'u ba, don har gida take binshi, a lokacin ne ya baiyyana ma Yesmeen son ta da yakeyi,ba wuya ta amince mai. Wannan kenan.

Ya kuka ga tuna Bayan?

Wattpad : biebeeisa
Please,Biko,donAllah dont forget to Vote, Comments and Share.

#1love
#ADAY
#anatare
#Bibiliciousfreakingfans
#nagode

BiebeeIsa
[11:31, 25/09/2017] 鈥�+234 803 414 9368鈥�: 锟斤拷A DADE ANA YI....sai gaskia锟斤拷

NA

BIEBEE ISA

庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg5鈨�

聽 聽 Ba 6ata lokaci Sada ya sanar ma Mallam Iro ya samu yarinyan da yake so yar mutan Yola ce, yana so ya Aureta kuma,Mallam Iro ya tattara Abokan Mallam Abu su uku suka tafi chan Yola neman aure, ganin Sada ya samu mata, hannu bibbiyu danginsu Yesmin suka karbi Mallam Iro, Baban Yesmin ma yace gwara ayi Auren ta karasa karatun gidan Mijinta, hankalin shi zaifi kwanciya, nan aka Ajiye maganan cewa idan zasu sake dawowa su dawo da Sadaki a daura Aure, Sosai Baba Abba shima ya baza rudun neman mata,Hajjo tace "Abba da ka bari ka fara tara abunda zaka rik'e matar dashi sai kayi auren" ai fa shikenan Hajjo ta gama dashi, don me zata cemai sai ya tara kudi zaiyi aure? Wato shi Sada baa ce mai komai ba da ya tashi Neman Aure, sai shi da ba'aso, dama ya san ta fi son Sada, in banda haka, don me k'aninshi Aure, nan da nan Hajjo ta rude, ta fara lallashin Abba, tace ya samo mata ko diyar wacece zata aura mai shi.

聽 聽聽 Soyyayar Sada da Yesmeen ya zagaye ko ina, da Mairo taji labarin dangin Sada sunje Yola neman auren Yesmin komai ya kwance mata, ta shiga damuwa sosai don sosai take son Sada, Abba ko Allah ya daura mai son Mairo, don Mairo na da kyan jiki, dirin ta na fizgar Maza, ya nuna mata So amma ta nuna mai ita Sada take so, kadan kadan yake jin kishin Sada, amma da yaga cewa bata gaban Sadan sai hankalinta ya dan kwanta, da Mairo taga ba sarki sai Allah, soyayyar Yesmin da Sada sai gaba yake k'arawa, ta maida wuk'aken Har Abba ya samu ya dinga chusa kanshi gunta har ta fara bashi hadin kai ba don ta hak'ura da Sada ba, sai dai don kar tayi biyu babu,a yanda take cema k'awayenta "gwara dan Abu daya, da ace na rasa su duka" har wa yau tsanar Yesmin dank'are a ranta.

聽 聽 聽 聽 Bayan Shekara 1

聽聽 Wata 4 kenan da Aurensu duka, Sada na zaune da Yesmin a nan gidan Hajjo, inda ya buge Soro da dakinsa ya gina musu Ciki da Parlo wadattace, Abba ko Hayan ciki da parlo聽 Hajjo ta kama mai a sharadda, a cewar shi nan Gidansu ya musu kadan ga Sada sa Iyalinshi, amma a zahirin gaskia Mairo ce tace ita ba zata iya zama da Uwar Miji ba, da yake yana sonta sai ya biyo ma Hajjo ta haka.
聽 Duk hidima da shagalin da akayi da biki Sada ya dauki nauyin, harta lefen Mairo shi yayi, abunda ya ma Yesmeen, shi ya ma Mairo, be nuna bambancin ba. Hajjo suna zaune lafiya da Yesmin, yesmin tana girmamata don har wanki take mata, hakan kuwa na faranta ran Sada, yana son Mai kyautata ma Uwashi.
聽 A haka bayan sun gama Makarnata,k'offofukan Alherin Sada sai budewa sukeyi, Don yanzu Provision Stores dinshi Guda Biyu,ya Mallaka ma Abba na K'ofar Gida,a Kasuwa kuwa yana da Shagon Saida Yankunne masu daraja,聽 Aikin Kafinta kuma be bari ba, don ya zama Ogan kanshi yara ne dashi. Kasancewar ya gama karatu da Matsayi mai kyau, wani Mallamin su ya bashi shawarar zuwa Zaria neman aiki don ya gani a Newspaper ana Neman wanda suka gama Makaranta,ya samu Abba yace "suje Zaria neman Aiki" Abba yace "Wallahi Sada baka da Godian Allah, Aikin me zakaje nema? Kana da Sana'oinka, yo ko ni da Shago na daya a ba zanje neman wani aiki ba, balle kai,Mallam kawai ka zauna tare da matarka, nima hakan zanyi" Sada yace "ai ba laifi idan aka k'ara hanyar Samu" a tak'aice Abba yace "to ba yanzu ba nidai Allah ya baka Saa". Fir ya k'i bin Sada Zaria, Sada ya tafi da takaddunshi, cikin ikon Allah, aka dauki Sada Aiki, kuma zaa dinga bashi Albashi mai tsoka.
Chapter 6 · 0% Book details