← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 128

Sashe 105

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Palor suka shiga inda Baba Abba yake,聽 Hajjo sai kallon Sada take tana murmushi jin dadi,聽 shima sai Murmushin suke,聽 Najwa ta shigo da Sallama,聽 Paapa yace "Umma ashe har kuen hadu da Jikarki" Umma ta mika ma Najwa hannu,聽 Najwa ta karasa gareta suka rungumi Juna,聽 tace "Wallahi ganina na farko da ita naji sonta na shiga na a hankali,聽 saidai rashin sani yafi dare duhu,聽 ashe jinin Sadana ne".
Abba ya mika ma Najwa hannu itama,聽 ta bar jikin Hajjo ta karasa inda yake zaune yace "Kin san waye ni?" Murmushi tayi,聽 nan kuma ya bata rai yace "dama ta ya zaki san ko ni waye bayan,聽 Azzaluma bata bada daman Iyayenki su gaya miki kina da Kawu ba" Najwa ta dora kanta kan kafafunshi,聽 tace "hakanbe chanza komai ba,聽 yau na san matsayinka gareni amma ya min kama da na san ka tun asali, abunda yake da muhimmanci yanzu shine,聽 nasan kai waye,聽 nasan matsayinka a gurina,聽 kuma ba wanda zai iya dauke mana hakan kuma" hannu ya daura saman kanta yana shafawa a hankali yace "Allah ya miki Albarka Najwa,聽 tabbas ke diyar Yesmin ce,聽 kina hankali da hangen nesa" Maama tayi murmushi, nan suka fara firan yaushe gamo ba tare da sun sako ma Daddy zancen Mummy ba.
**

Daya bayan daya take kallonsu, kafin tayi jihadin fara magana kamar haka;
"Yarana, ban san ta inda zan fara muku bayani ba,聽 amma ina so ku sani cewa i'm truly sorry, i'm truly sorry for not being a good Mother,聽 ban zame muku Uwa wanda zakuyi Alfahari da ita ba,聽 amma ku sani ina sonku fiye da rayuwa da kanta,聽 kuyi hakuri da Uwar da Allah ya baku,聽 don na san kuna nadamar kasancewa nice Mahaifiyarku,聽 in kunsan abunda nayi a baya,聽 You'd wish you had a different Mother--" Abdulmajeed ya katseta da sauri ta hanyar dafe mata fuska da hanayenshi biyu yana kallonta "Haba Mommy, wani irin magana kike haka? Ki sani,聽 Mu聽 'yayanki ne,聽 bamu damu da abunda kikayi a baya ba, ba zamu taba da nasanin kasancewar ki Uwar聽 mu ba, you are our a Mother and we love you,聽 so ki bar irin wannan maganganun kinji? "

Yaken dole tayi tace "ba ku sani ba,聽 Shekaru da suka gabata,聽 Mummy tayi aikin sa6o da yawa, Mummy has wronged too many people聽 in different ways, Mummy bata damu da kowa ba sai kanta,聽聽 kunga wanda suka聽 shigo dazu ai? Uncle dinku ne da Matarshi,聽 Iyayen Najwa,聽 Hardasu a ciki wanda na ma laifi, Sada ya mana komai na rayuwa musamman ma kai boy, ya soka kamar nashi,聽 a School AbdulMajeed Sada kake bearing kafin naje aka ma change of namez duk don So da Kaunarka da yakeyi, amma na sa kafa na shure na saka sun bar k'asar na rabasu da danginsu na raba Sada da Daddynku saboda wani selfish interest dina, but ina so ku sani Mummy tayi nadaman duk abubuwan da tayi, Mummy has regret everything, zatayi duk yanda zatayi don ta gyara laiffukanta, Daddy yayi fushi sosai,聽 na mishi laifi babba,聽 zan tafi,聽 zan bar gidan聽 sai ya huce" Idanuwa suka zare.聽 "No kar ku daga hankalinku, i'll be back for you,聽 i promise,聽 zan tafi for some days, har sai Daddy ya yafe min,聽 zan dawo,聽 bana so kusa kan ku a damuwa,聽 ku kula da junanku,聽 take care of yourselves har sai na dawo,聽 Mummy is going to be fine only if she knows you all are fine, kunji?"聽 rungumeta sukayi banda Abdulmajeed da ya tashi yana share hawaye,聽 daga abunda ya faru daga abunda ta gaya musu duk da ba straight ta fada ba ya gane abubuwan da ta aikata,聽 kuka yake yana tunanin "ya zaayi Mamansa ta kasance cikin irin mutanen nan" lallashinsu take tayi har sai da taga zuciyarta zai kare, itama zata fara nata kukan gaban yara ya sa ta聽 ma Abdul ido,聽 zuwa yayi shima ya fara lallashinsu Muhsin da Zinatu kafin sukayi shiru, ta tashi tsaye ta bude drawer ta dau mayafinta zata fita daidai kofa Zaineema tace "Mummy,聽 DonAllah kar ki tafi" bata juyo ba聽 tace "Daddynku na cike聽 da bacin rai,聽 in ya sauko zan dawo聽 donAllah ku kwantar da hankalin ku kunji?" Ziyada na kuka tace "Mummy to bari muje mu bashi hakuri,聽 zai yafe miki,聽 just dont go" Mummy tace "Aa,聽 ba yanzu ba, please kuyi hakuri,聽 in ba ku barni ba,聽 ba zan tafi ba,聽 kuma Daddy zai cigaba da ganina,聽 ranshi na baci,聽 kun taba ganin bacin ranshi? " AbdulMajeed ya share hawaye yace "Mummy,聽 ki tafi,聽 kije" gyada kai tayi tace "ka kula min daku" da sauri ta fita tana kuka.
Maama na jin fitowar Mairo ta fito itama cikin dabara ba tare da su Daddy聽 sun sani ba,聽 bakinta na nauyi ta bude da kyar tace, "Hajia Mairo Ina Zaid?" kuka mairo ta fara tana girgiza kai,聽 gigirgiza kai me maana Biyu "ko Aa,聽 bansan inda yake ba, ko kuma Aa, ya mutu" ganin bata da abun fada ya sa tayi gaba da sauri ta bar gidan gabaki daya.聽 Zuciyar Mamma ta fara harbawa, Zaid ya mutu, ba rabon su sake haduwa, Allah ya sa mai ceto ne, hawaye masu zafi ne ki fita daga idanunta, ji tayi an rungumeta ta baya, Najwa ce,聽 ba tare da ta kalleta ba聽 tace "He is gone, Zaid baida rai ya mutu" kara rungumar juna sukayi suna kuka,聽 sai da kusan mintuna7 suna tsaye kafin Maama ta karasa gun Pampon da ke gurin ta wanke fuska, atleast yanzun hankalinta zai kwanta,聽 tunda ta san Zaid be raye,聽 ba kamar da da take cikin kokonto ko yana da rai ko babu ba.

Da kyar Abdulmajeed ya samu ya lallabi k'anensa da ban baki, Lek'awa Maama da Najwa sukayi dakin, sukaa musu Sallama,聽 kallon? Maama sukeyi kawai ba su sa wacece ita ba, Maama ta kallesu da Murmushi ta nuna聽 Abdulmajeed da yatsa tace "AbdulMajeed dina, zaka tuna ni?" a sannu ya girgiza kai, ta murmusa tace "ba zaka gane ni ba,聽 its been long" ta gefenshi ta kalla, Ziyada,聽 kallonta takeyi sosai kafin ta dauke idonta ta kalli Zaineema tace "Ga Zaineema nan,聽 na ga kanku daya da wannan beauty din shiyasa nake son gane wacece Zaineen tsakanin ku biyu, well nasan ba zaki gane ni ba kema,聽 coz when i left,聽 you barely talk" kasalaceccen Murmushi Zaineema,聽 Maama ta kalli Zuzu tace "Ya Sunanki?" a hankali tace "Ziyada" beautiful inji Maama,聽 ke kuma fa? ta fada tana kallon Zeenatu,聽 cike da shagwaba tace "Zeenah" Maama tace "inye sunan yan gayu,聽 come here dan yarona,聽 zo inji wa ya taba min kai" Autan Mummy ya taso yana matse hawaye, kiris yake jira ya fashe, ta dauke shi tace "ya sunanka?" turo baki yayi yace "Muhsin" tace "Inye, look at my handsome boy,聽 duk kafisu gaye, yi daria na gani" abunka da yaro ya dare baki yana kyalkyala daria, saukar dashi tayi ta zauna kan bedside drawer.

"Sunana Aunty Yesmin, Maama zaku dinga ce min kunji ai?" duk suka gyada kai, "Ni Matar Uncle Sada dinku ne,聽 kunsan shi?" nan ma suka gyada kai, ta cigaba da cewa "Uncle Sada shine Autan Umma Hajjo,聽 Kannin Babanku ne,聽 Immediate Brother dinshi,聽 lokacin聽 da muka bar gari,聽 Abdulmajeed da Zaineema kawai aka haifa, its been long,聽 ba zasu tuna mu ba,聽聽 so bana tunanin ko hoton mu kun gani,聽 So This is Najwa,聽 Our聽 Only Daughter,聽 cikin ikon Allah ta zo Gidansu ma ba tare da sanin kowa ba,聽 Rashin Sani yafi dare duhu,聽 nidai na san ta na gidansu Abdulmajeed da Ziyada, coz labarin su kawai ake ban,聽 haha,聽 ta ban labarin yanda kuke kula da ita, unknown to you kuna kula da jininku, Mungode Allah muku Albarka" da Amin suka amsa,聽 yanda sukeyi ya sa ta gane suna cikin Alhinin tafiyar Uwarsu,聽 sai ta lura da akwai shakuwa mai girma a tsakaninsu da Uwarsu hakan taji tausayinsu,聽 ta murza hanayenta biyu tace "kunsan me?" bata jira amsarsu ba tace "Hajia Mairo na burgeni sosai wurin yanda take so 'Yayanta,聽 tana sonsu fiye da komai,聽 lokacin in Abdulmajeed ke聽 Zaineema basu da lafia,聽 to zaka ganta cike n damuwa,聽 har kuka zaku ga tanayi,聽 in ko Abdul ya dawo Gida yana kuka wai wani yaro ya bugeshi,聽 to nan fa ake yinta,聽 nan zata sabi gyale taje gidansu yaron ta bugi uwarshi wai danta ya bugan mata da" daria suka saka gabaki dayansu,聽 ba su taba kokonta a son da Mummynsu ke musu ba. Ganin sun washe yasa Mummy tace musu "Oya ku tashi muje Kuyi聽 introducing kanku da Paapa" tashi suka yi suka nufa Parlo inda su Daddy suke.
***

AMERICA
Zuciyarsa ke tunzura shi ya bar Course dinna ya koma Nigeria gun Matarshi, ya fi yarda da Sharri aka k'ulla mata,聽 yafi yarda da Yan Hassada ke son shiga tsakaninsu,聽 to in ba haka ba,聽 sunyi waya fa da ita randa ya iso Kaduna,聽 ya sanar da ita zuwanshi Gida kawai zai karaso,聽 yana a daidai Kawo sukayi waya, shi da Gidansu ke Unguwan Dosa, amma聽 don tabewar basira sai ta kawo kwarto dakin? Is not possible,聽 Kuma in ya tuna clearly, kwarton ya gani kwance kan gado,聽 ita kuma ta fito daga toilet da alama Wanka tayi, yasan Zaineema tana da Zafi,聽 amma tana sonshi sosai kamar me,聽 ba zata ha'inceshi ba,聽 ba zata ci amanar Aurensu ba,聽 meyasa be mata uzuri ba? Meyasa ya zabi da ya saketa? Kai Inallilahi聽 wa ina ilaihir rajiun, she's Innocent Wallahi,聽 yanzu haka wasu da ba sa son aurensu ne suka shiga tsakaninsu,聽 yayi da nasanin yanke hukunci da sauri,American Friend dinshi ya dan zungureshi yayi firgigit ya dawo daga tunani,聽 "Khaleed,聽 whats wrong ?聽 you are lost deep in your thoughts" Khaleed ya sauke numfashi,聽 a hankali ya ba Abokinshi dan Amerika labarinshi ya karashe yana ganin laifin kanshi,聽 Abokin ya jinjina kai yace "I'm so sorry, dont blame your self, its not your fault, when this is over,聽 go back to Nigeria and get your wife back,聽 i'm sure she's waiting for you".聽 Kansa khaleed ya jinjina tare da kudurin yana isa lagos,聽 Jirgin Kano zai siya ya wuce ya dauko matarsa.
Chapter 105 · 0% Book details