← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 128

Sashe 84

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bude mata Gidan aka yi, ta sa kafa tana hararrarsu tana mita, "da kun san ni wacece da baku hanani shiga ba tun farko" ba su ce mata komai ba taji muryan me Napep yana cewa "Hajia,kiyi sauri donAllah" daga hannu tayi daga inda take tace "kar ka min ihu, yanzu zan aiko ma da kudinka" ta shiga fuuu tana rafka Sallama har Parlo ba ta bar Sallama ba, tana shiga ta ji an rungumeta, itama sai ta rungumeta tana farincikin jin dumin diyarta a jikinta, tana fadin "Ziyadata an zama Mace, kinyi gidan kanki, wani abun Allah ma Gidan Ubanki aka kawo ki Cikin Rashin Sani, kila in aka gaya mai ya bamu abun mu, ku kuma ya nema muku wani wurin Zama" Kuka Ziyada ta fashe dashi ta na sake rukunkumeta, Mummy tace "Ya Isa Ziyada, nima nayi missing dinki" da kyar ta samu ta bambare Ziyada daga Jikinta, Kallo daya ta mata tace "Barauban nan" ta zaro ido gami da fadin "Me ya sameki Ziyada? Ciwo kikayi?" dan guntun Murmushi tayi tace "Aa Mummy, ba komai" Mairk ta sake kallonta sama da kasa tace "To wadannan kasusuwan wuyan na uban meye? Kwana 3 kawai kamar shekara uku? Kinga yanda kika zabge kuwa? Kamar ana dibanki ana miya dake? Ba kya cin Abinci ne?" Ziyada ta fashe da kuka tazo fadawa Jikin Mairo, Mairo ta ja baya, tace "ba kuka ba, me ya sameki? Ki min magana, ba ki da lafiya ne?" Ziyada na hawaye tana girgiza kai alamun ba komai, Mairo tace "In baki gaya min damuwarki ba wa za ji gaya ma wa? Kina Missing din gida ko? Kin sa tunanin mu gaba kin hana kanki sukuni, to ai ko wacce mace dole ta bar Gida, ki kwantar da hankalinki, gobe zan sa YaMajinki ya kawo miki su Muhsin da Zinatu, yanzu dai je dauko min kudin Napep, na bar shi a waje, ai ina nan har Dare". Ziyada ta girgiza kai tace "ai banda kudi" Mummy tayi wata 'yar dariya, "Habadai baki da kudi, kice dai baki da chanji"
"0ya je kar6o min wurin Mijinki".

Ziyada na so tace ma Mummy ga Zaid nan fa zaune amma Mummy sai sakin layi take, kamar ance ma Mairo ta kalli chan, Mummy na kallon chan cikin Parlo ta ga Zaid Zaune kan Kujera 3sitter ya hada kafa daya kan daya yana kallonsu, kululu cikinta ya kutsa, haka kurum taji faduwar gaba, kallon Mijin Ziyada da tayi daga nesa sai ta ga ya mata kama da wani kamar Abbanta, wayancewa tayi ta yashe hakora inda ta karasa gunshi tana ashe ga Alhajin nan, zama zatayi yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa "Dakata, kar ki zauna min a kan kujera" Mairo tayi sauran kallonshi ta ga fuskarshi cike da gargadi, Ziyada ta karaso da sauri tace "zo Mummy, zo muje Dakina" Zaid yayi karaf yace "Haba Ziyaaaa, ya zaayi zatayi magana da Sirikinta kice tazo ku shiga daki? Hajia Mairo ai akwai maganar da zamuyi ko?" Mummy ta dara ba tare da damuwan ya kirata da Hajia聽 Mairo ba, ita ko Ziyada taji haushin rashin karan da Zaid ya mata, in be iya kiranta da Mummy ai gwara yace mata Hajia kawai, banda sunanta, Mummy tace "sosai ma, akwai maganganun da nake so muyi" yace "Yauwa Hajia Mairo, fadi matsalolinki in magance miki su".

Zaman Dirshen tayi a k'asa kamar me rok'on gafara, Ziyada tayi saurin rintse idanu don yanda Mummy ta zube k'asa kamar Marokiya, ta fara magana "Alhaji, kamar yanda ka sani, mun samu karayar Azziki, Akwai wani manafuki Alhaji Nakowa ya kala min sharri wai ya biyoni bashin 30million bayan karya yake, sai da abu ya kaimu ga Kotu, abubuwa da yawa sun faru, har muka saida wannan Gidan da kuke ciki, ashe kai ka siya bamu sani ba, bayan wannan Yarona wato Yayansu Ziyada ba ya aiki, Babansu ma ba yayi, ko mota bamu da, yanzu duk chunkushe muke a gidan kakarsu, inda kuka zo da manyanka, a takaice dai muna cikin wani hali, babu yayi yawa, Amma Allah me share kukan bayinsa ne, ya turo mana kai a cikin Rayuwarmu, me zamu tambaya bayan baiwar da ya mana na sakoka cikin gidan Rayuwarmu?."

Zaid da ke sauraron duk wani zancenta聽 ya Murmusa, abun nema ya samu, yace "Gidan nan na waye kafin ku saida?" da Murmushi tace "Na mu ne" Zaid yace "Ina nufin Mamalakin gidan" tace "Gidan Maigidana nane" Zaid ya ciza hakori "Are you sure?" da sauri tace "Eh, Gidanshi ne bamuyi shekara da dawowa dindindin ba, Abuja da muke zama, saboda rayuwa sai muka saida gidanmu na Abujan muka dawo Gida, ai da yake mun dade a Bariki, gwara a dawo Gida". Ta karashe tana daria. Zaid yace " So wurin wa ku ka聽聽 karbi Gidan, ko ku kuka gina shi, ba ku kashe wasu kun musu haye ba?" Mairo ta kalleshi a firgice, ta girgiza kai baki na rawa tace "Aa, tun asali namu ne".

Zaid da ranshi ya baci amma sai ya danne yace " Yanzu kina so na sama ma Yaronki da Mijinki aiki, kina so na dawo muku da Gidanku, kina so na siya muku Mota, na dawo muku da duk wani abunda kuka rasa, Saboda me?" tayi daria taxe "Sabida ka isa, saboda in kayi haka ba zai taba hakki daga cikin dukikiyoyin da abunda ka tara ba, sabida kafi karfin haka, balle kuma kai Mijin Ziyada ne, zaka fiddo Family dinta daga cikin halin da suke ciki" yayi murmushi yace "kina burgeni Hajia Mairo, kina da wayau" ta fara yashe hak'ora, ya cigaba da cewa "Amma ke wawuya ce" da Ziyada da Mairo suka kalleshi a lokaci guda ido a zare.

Ya cigaba da cewa "Ke Wawuya ce in kikayi tunanin zan taba daukar tsinke
na baku, Ke wawuya ce in kika taba tunanin zan taba taimakon ku ko da dukiyana na zuba kasa sabida yawa, Ke Wawuya ce in dama kin taba daukan Gidan nan a matsayin naku, it was Never Yours, and it will never be yours, none of anything you had was yours, nothing was ever Yours, and you are nothing but a fake manipulating,conniving,hypocritical bi**h (Gidan nan ba naku bane, be taba zama naku ba, ba kuma zai taba zama naku ba, ba wani abunda kuke dashi da da naku ne, ba ku da komai, kema ba kowa bace face Makaryaciya, Munafuka me cin amanar wanda take tare dasu,me zamba cikin aminci)".

Cikin Zafin nama Ziyada ta ruga da gudu kicin,wuka ta dauko tayo kan Zaid da gudu zata chaka mai, har ta daga hannu zata chaka mai ya kama hannun ya murde mata shi da sauri ta sake wukan tare da kara, ya murde mata hannu ta baya ya sako kanshi kan wuyanta.
Hajia Mairo ta rugo gunta yace "kika matso nan sai na sa an harbeki wallahi" hankalinta tashe,聽 takasa fahintar maganganun Mijin Diyarta,聽 tsakani ga Allah bata san inda ya dosa ba, idonshi ta kalla taga ya kada yayi jazur,聽 rashin imani tagani kwance a idonshi,聽 tsaf zai iya sa a harbeta, ta daga hanayenta sama tace "ba zan zo ba,聽 amma please dont hurt her".

Be bi ta kan Mummy ba ya fisge dankwalin kan Ziyada yayi cilli dashi聽 yana shishinar kanta,yana mata magana a kunne "Kina so ki kasheni? Don na fadi gaskia?聽 Don ina tona ma Uwarki Asiri? ba zaki iya ji ba ko My Forever? Ba zaki iya jin gaskian wacece Hajia Mairo ba, saboda you cant take it, but wallahi sai kinji, Your Mom is a Monster,聽 zata iya yin komai don Kudi da Shahara,聽 she can kill for money wealth and fame,聽 No she already Did, she's a Killer,聽 she's a murderer,聽 zata iya Kashe Yaro sa'an Zinatu,聽 or maybe Muhsin".聽 Tashin hankalin da tunda uwata take ciki bata taba shiga irinshi ba ta shiga yau,聽 ba zata iya dauka ba.

Luuu Ziyada ta fadi kasa a jikin Zaid,聽 sakinta yayi ya ruga Fridge da sauri ya dauko ruwan sanyi,聽 kafa ya sa ya hambare Mairo da ke kan Ziyada tana kuka da k'arfi. Ya kwarara ma Ziyada ruwan Sanyi a jiki,聽 Ajiyar zuciya ta sake da karfi kafin ta daura da kuka me sauti,聽 dagata yayi ya na girgiza kai "No,聽 No My Forever, no, ki tashi ki gaya mata dalilin聽 da ya sa na aureki,聽 tashi ki gaya mata" Ziyada kuka takeyi ta kasa magana,聽 sake ta yayi ta fadi k'asa.

Ya kalli Mummy yace "Hajia Mairo,聽 barin gaya miki dalilin da ya sa na auri Ziyadarki, na aureta ne聽 Saboda na k'untata mata,聽 na kuntata maku gabaki daya,聽 na aureta ne saboda na mata wulakanci, wulakanci nake mata,聽 ran da aka kawo min ita rannan na tafi Porthacourt,聽 bayan na karbe wayarta,聽聽 am sure kin kirata kinji wayar kashe,聽 kafin na tafi na saka securities,聽 inda na bada Umurnin kar wanda ya shigo min gida,聽 itama kar a barta ta fita,聽 ki tambayeta gata nan,na san hurting your kids means hurting you, and hurting聽 you gives me Joy and Happiness (na san in an taba yaranki kamar an tabaki ne, ganin cikin聽 wuya da rinsti na sani farinciki da annashuwa)聽 babban farincikina shine na ganki ke da Iyalenki cikin Bakinciki da kunci,聽 everything that has happened聽 to you,聽 i enjoyed every聽 bit of it(duk abubuwan聽 da suka faru da ku,聽 naji dadin ko wanne daga ciki)".

Mairo tace "Meyasa kake haka?聽 Me na maka?聽 Me muka maka? In laifi muka maka,聽 dan Adam Ajizi ne, sai mu rokeka gafara,聽 me yayi zafi haka Zaid?聽 Babanka Marigayi Sadam mutumin kirki ne,聽 meyasa kake haka?".
Pillow ya dauka ya wurga mata a fuska ya nunata da hannu,聽 "kar na sake jin kin furta babana da dattin bakinki, baki san komai game dashi ba"
Zaid ya kalli Ziyada yace "Na sani,聽 Ahap i knew it,聽 Mamanki Dakikiya ce, ta ya zaayi ta san me ta min bayan聽 shes the dumbest person that ever lived(tafi kowa dakikanci a duniyar聽 nan) .
Chapter 84 · 0% Book details