← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 128

Sashe 73

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

A GURGUJE
Mairo harda takawa tayi don Dadi da taji sun dangwalo Arziki, har ce ma Ziyada take ta zo ta hau bayanta ta goyata ta share mata hawaye, a zuciyarta take hasko yanda rayuwa zata canza mata, zata fito gari ta taka duk wanda ya tabata, zata gurza ma makiyanta rashin mutunci, Ziyada kam farinciki damke a ranta zata auri farincikin ranta, wai ita zata zama Mrs Zaid Sadam in two days, she cant wait. Bata so yin wani gayya ba, amma Mummy tace sai tayi gayan friends dinta duk da ba wai yawa ne dasu ba, a cewar Mummy ya zaayi ta auri Mutum kamar Zaid amma ba wanda ya sani? Dole ta gayyato kawayenta, haka dai ta hada BC ta tura ma Friends dinta. Itama Mummy aka wuce gidan tsohuwar kawarta hajia Aliya tana bude mata hanci ita zata zama sirikar Zaid Sadam.
Alhaji Nakowa yayi mamakin ganin Cheque da yayi daga account din Ado Mali wai da sunan biya ma Alhaji Abba Bashi wanda daga Kotu aka turo mishi ba haka yaso ba, so yayi ya kuntata ma su Hajia Mairo, amma ya ya iya? Karawa da Alhaji Ado Mali kamar karawar kifi ne da mage.

JUMA'A

Bayan Sallahn Juma'ah ne a babban Masallacin Jumaa na Central Mosque dubbanin Jamaa suka shaida auren Zaid Sadam Audu da Amaryarsa Ziyada Abba Abu a bisa sadaki Naira dubu dari uku.

Wasa farin Girki.

鈥⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€�

Gyara: Dear Bibilicious freaking fans, akwai wani gyara da wata baiwar Allah ta min, attimes ina using Abdulmajeed wasu lokuta kuma Majeed, Malamai suna waazi akan Kiran sunayen Allah hakan Nan batare da sa Abdul din ba, mu kuma mu kan yanke ko don gayu ko don gajeratawa, amma hakan baban kuskure ne, to mu dinga kokari muna cikita sunan AbdulMajeed, from now henceforth zamu dinga karasa sunan, in aka ga akasin haka to kuskure ne da kuma sabo, ina fatab zamu gyara Nagode. .

Yekpa Anyi aure fa, akwai Walima Party anjima, you are all invited.

Akwai gwarama fa, this is the begining of an end, stay tuned, yanda nake kokarin typing haka, kuma dont Forget to Vote and Comment line by line.

#1love
#ADAY
#bibiliciousfreakingfans
#anatare
#nagode

Biebee Isa. 馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱

NA

BIEBEE ISA

庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Wattpad:@biebeeisa

Pg3鈨�0鈨�

Ta dago rinannun聽 idanunta ta kalleshi,聽 yace "ba zan karba ba,聽 naki ne,聽 kema kina da bukatansu" tace "na sani,聽 amma a yanzu kunfini bukkatarsu,聽 so kawai ka karba" ta tsareshibda idanunta,聽 bata bashi kofar yi mata gardama ba,聽 ajiyar zuciya ya sauke da karfi,聽 yace "Fine,聽 100 dollar kawai zan amsa,聽 kuma shima da Allah ya hore min zan maido miki da kudinki,聽i wont hear more,聽 otherwise forget it(ba zan ji komai ba,聽 in ba haka ba kuma ki manta da maganan kudin)".

聽 Ba ta ce komai ba ya zari 100 dollars,聽 Daddy yace "Najwa Mungode Allah聽 ya biyaki" Murmushi tayi,聽 hawaye yazo mata tayi daku da sauri, Daddy ya kalli Mummy yace "to kin gani聽 Maryam,聽 kina ta kyarar yarinyar nan,聽 gashi ta taimaka mana" Mummy聽 ta tabe baki tace "tunda tazo Gidan,聽 ta taba biyan kudin abinci ko kudin dakin da take kwana ko kudin聽 wani abu? Ai in akayi calculating daga randa tazo zuwa yau in a hotel take zai fi 35000 din,聽 dama duka dollars din aka karba" duk suka bita da kallon how can someone聽 be like this?聽 Daya bayan daya suke sabewa suna shiga daki聽 Mairo ta bisu da ido ta watsa hannayenta sama tace "to me nace?".

Washegari.

Abdulmajeed be koma bacci ba bayan Asuba,聽 ya hau firdo tarkacen Hajjo na kitchen,聽 ya share kitchen din tas,聽 ya jawo ruwa a rijiya,聽 duk da gabanshi na faduwa,聽 da fargaba da ya leka zurfin rijiyar,聽 be taba jan ruwa a rijiya ba tun da Mumnynsa ta haifeshi, sai da ya cika drum kafin ya wanke kitchen聽 din tas.
Najwa ta fito zata聽 shiga toilet taga Abdulmajeed na ta cin aiki,聽 batace mai komai ba ta shiga toilet ta yi fitsarinta ta fito ta je ta mai tsaye,聽 yaji alamun mutum a tsaye kanshi,聽 ya dago聽 kai be san saada Murmushi聽 ya subuce mai ba,聽 ya ajiye tsintsiyar hannunshi ya mike tsaye yana kallonta,聽 bakinta ta turo ta juya dayan gefen wai ita fushi take dashi,聽 Murmushi聽 yayi sosai,聽 Allah聽 ya san yana son Najwa, har cikin ranshi yake jinta,聽 a hankali ya tako har gabanta,聽 ba tare da yace mata komai ba ya daura hanayenshi biyu kan kunnuwanshi, cikin murya me kama da rada yace mata "i'm sorry pureHearty na,聽 kuma kar kiyi fushi dani" idanuwanta cikin nashi,聽 a ranta tace "how can he be so cute?" a fili kuwa ta k'ara daure fuska tare da juyawa dayan bangaren,聽 be saduda ba ya sake juyowa inda take ya shagwabe fuska kamar dan yaro,聽 sai taga ya mata kama da Muhsin yace "kuma in baki daina fushi dani ba,聽 zanje in hau saman transformer ayi ruwan sama kuma in makale,聽 haka" ya mata alama da hannu,聽 bata san lokacin da ta fashe da dariya ba,聽 shima dariyan yayi yace "there, the smile is all i want purehearty" bata san lokacin聽 da ta sake mai Murmushin da yake matukar so ba,聽 sun dan jima suna exchanging looks,聽 kafin suka ji muryan Ziyada聽 da Zaineema nacewa "Excuse us" firgigit sukayi suna kallon kofan kitchen din,聽 Ziyada tace "YaMaji are we interrupting something?" Kasa magana sukayi sai blushing da suke, Zaineema聽 tace "Ziyada wai are these two inlove?" Ziyada zatayi聽 magana Abdulmajeed聽 yace "Shuttup Zuzu, ni tsaranku ne? " suka fashe da daria,聽 Najwa ina zata sa kanta don kunya,聽 Zaineema tace "zo nan Najwa" Najwa kanta a k'asa zata聽 karasa gun Zaineema聽 Abdulmajeed聽 ya sha gabanta yace "ba inda zaki PureHeart,聽 ku kuma wallahi聽 zanci聽 mutuncinku" sukayi daria duka,聽 Ziyada tace "wai aiki kakeyi?" yace "No ku koma daki" Zaineema tace "wallahi aiki kakeyi,聽 ya kamata a gyara gidan ma" Abdulmajeed聽 yace "ku wuce daki zan gyara" Ziyada tace "Sam sai dai muyi a tare" da kyar ya yarda ya raba musu aiki.

Sanitation sukayi na Gidan gabaki daya duk wasu yana na saman ceiling sai da suka cire, wurin 10 sun聽 gama komai,聽 Zuwa yayi wanka,聽 ya fita yayi changing dollar din,聽 dubu 35,900 ne,聽 ya shiga kasuwa ya musu siyayya,聽 kama da聽 richo,聽 kanazir,聽 kayan shayi, kwalin indomie,聽 bobo da biscuit na yan makaranta,聽 sabulun wanka da na wanki,聽 da dai kayan amfani daidai kudinsu,聽 ya biya ya siyo lantern, ya biya ya bada kudin nepa dubu sha daya,聽 ya siyo bulb na wuta,聽 kudin da ya rage dai dubu bakwai,聽 ya dawo gida a kan adaidaita sahu da kaya nikiniki, kamar wanda ya dawo daga Dubai haka suka tareshi,聽 suka ta yashe baki abun zattausayi,聽 haka suka jera komai inda ya kamata,聽 nan suka ga kyan Gidan,聽 Mumny ta dage ta zira lagwani a jikin risho,聽 aka dura kanazir a risho din,聽 aka daura Abincin Rana.
****聽

聽 Be san meyasa ba ya shiga damuwa,聽 kiran wayarta yayi a karo na kusan ba adadi,聽 wayarta kashe,聽 rabon da yayi waya da ita聽 tun randa tace mishi zasu koma Gidansu, ba wai ya damu bane,聽 yace ma zuciyarshi,聽 kawai ina so in ga ta yanda zan k'untata mata, ban damu da ita ba,聽 ban damu da komanta ba,聽 all i want is revenge, ya buga tsaki,聽 ya dauki keys din motarshi ya fita daga dakin,聽 Guest house din Baba Ado ya nufa, straight ahead Gidan ya shiga, kasancewar an sanshi ba wanda ya tambayeshi ko an san da zuwanshi ,聽 da Sallama ya shiga Parlorn,聽 Baba Ado na zaune kan wat kujera ta alfarma yana karanta wata Jarida,聽 Zaid ya taka cikin takun kasaita har gabanshi ya durkusa ya shafi k'afanshi,聽 shi kuma baba Ado ya dafa kanshi (haka ne gaisuwan yan Mali yake) Jaridar hannunshi ya ajiye,聽 ya mikar da Zaid suna kallon juna,聽 kafin nan ya rungumeshi.聽

Kafin kace komai tuni an cika ma Zaid gaba da kayan motsa baki, sai da ya bata lokaci kafin ya dauka grapes daya ya fara tauna a kasaitance,聽 kasancewar聽 Baba Ado ya san Zaid ciki da bai,聽 ya san halinshi,聽 ya san yanda zai tafiyar dashi, yace mai "Ka sanar dasu zamu zo yau din?" kamar ba zai amsa ba chan yace "Wayarta a kashe yake" Baba Ado ya dago ya kalleshi,聽 yace "kenan basu san zamuzo ba?" dan gajeren tsaki yayi yace "Wayarta kashe yake" Baba Ado yayi jim, kafin yace "to ya zaayi kenan? Na kira abokan babanka biyu sunce mu hadu karfe hudu,聽 Alhaji聽 Hamisu ma musamman ya hau jirgi daga Porthacourt yazo Kano" Zaid yace "Zakuje ai" "ba su san da zuwanmu ba din?" Zaid yace "ai ba wani abu bane,聽 suna Gida" Baba Ado yace聽 "amma dai be kamata聽 ba Zaid" da sauri Zaid yace "Please Baba Ado,聽 banson a samu matsala, banson Auren ya wuce Friday din nan, ka taimakeni" Baba Ado ya murmusa,聽 a zatonshi Zaid na kaunar yarinyar nr da har ba zai iya kara daukan wasu lokuttan ba tare da ya aureta ba, kuma dai abun farincikimsu ne tunda Zaid da bakinsa yace yana son auren,聽 gwara su mishi kafin ya chanza raayi.聽 Baba Ado ya ja numfashi yace "Zamuje Gidan Bayan Laasar".

Bayan Laasar.
Chapter 73 · 0% Book details