Sashe 65
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read
umurnin kudi kaza ayi kaza dashi, to meyasa yake yin haka? Ko wani laifi suka mishi yake son daukar fansa? Haka dai tayi lamo tana ta sakawa da kwancewa, babban burinta ta dauko package dinnan ta ga ko menene. Ba zata iya shiga dakin ba, saboda dakin kulle yake, tana wannan zantutuka har aka kira Azahar tayi Sallah, Jim kadan taji Nura na waya, da Alamu da me Gadi yake waya, don da sauri Nura ya shige dakin Majeed, kila sanar mai yayi Madam ta dawo. Mummy na dawowa dakinta ta bude ta shiga, chan ta fito ta shiga kitchen don daura musu Abinci. STORY CONTINU Start from the beginning "This my only Chance" cewar Najwa da sauri ta bude kofar ta lek'a window taga Mummy a kitchen tayi wuf ta shige dakin, ta fara neme neme a drawer ta duba har cikin wardrob bata ga komai ba, ta saka stool ta duba saman wardrob bakomai, hankalinta ya kai kan karkashin Gado, ta na dubawa kuwa ta ga Package din, ta zaroshi da kyar, taji alamun tafian Mummy, ta san halinta, zata iya cewa itace ma ta kawo ko me ke ciki, da sauri ta bude Window ta wurga abun, ya fadi ta baya, ta rufe da sauri tayi hanyar fita sukayi kicibus da Mommyn, gaban Najwa ya yanke ya fadi, Mommy ta bita da kallon tuhuma, tace "Me kike yi a dakin nan?" Najwa tace "zuwa nayi na gyara muku ashe a gyare yake" Mommy ta bita da kallon rashin yarda tace "in na duba abuna ban gani ba kece" Najwa tace "Nayarda" Mommy tace wuce ki ban wuri "Munafuka" Najwa tayi sauri zata wuce, Mairo ta sake mata rankwashi a tsakiyar Kai, Najwa ta danyi kara tare da guntun hawaye ta fita da sauri ta fada daki, tana luluya kanta saboda azaba. Saida ta gama kukan zafin kanta kafin ta tashi ta zagaya bayan window din dakinsu Mummy, daukan package din tayi ta zagaya baya, chan BQ, a hankali ta bude package din, wasu Garin powder ne kusan leda biyar anyi sealing dinshi, ko ma meye ne tasan ba abu me kyau bane, pit toilet din wurin ta bude ta shiga, ta bude masai din, ta jefa chan cikin shadda ta rufe ta fito, ta wanke hannuwanta ta koma cikin Gida. Wannan Kenan. ************* Murmushi tayi a ranta tace "atleast na rage ma Jaan wani bacin rai, ashe dama Cocaine ne?Allah ka shiga tsakanin mu da mugaye, ta gyara kwanciyarta ta koma baccinta. Bacin rai ya hana Zaid bacci, jira yake safiya tayi ya gano waye ke mishi abubuwan da yake mai. Kamar Kullum su 3 sun fita, Zaid ya fita wurin Maigadi rai a bace, "Kai, bayan su AbdulMajeed akwai wani a Gidan nan ne?" Maigadi ya girgiza kai alamun aa, yace ka tabbata yaran gabaki daya aka tafi dasu?" Maigadi yace "eh, akan idona naga Hajjo, Ziyada, Zaineema, Muhsin da Zinatu suka bi Hajia Ainau, duk sun tafi" Zaid yace "kai, Akwai wani a tare damu, ya zaayi sai nayi shiri, sai a bata min shiri, ko Aljani ne yau sai ya bar Gidan nan" a hankali Maigadi yace "Najwa" Zaid ya Kallo shi yace "wa?" "Najwa na cikin Gidan nan tabbas, na kan ganta tayi hanyar BQ" Zaid yayi murmushin takaici, itace ta san sirrinshi, itace ta ke rusa mai plan, fuska daure yace"wacece ita?" Maigadi yace "Bakuwar Majeed ce, Hajia bata sonta dai" cikin bacin rai Zaid yace "Ko ma wacece sai tayi nadamar shiga Gonata" yayi cikin gidan a Fusace. "Maama i miss you sosai wallahi" bam taji an bugo k'ofarta, gabanta ya yanke ya fadi, ganin Nura gabanta, ranshi 6ace, kallon juna suke ido cikin ido, tsanar junansu a zuciyoyinsu, duk da ta tsorata da lamarinshi, don shi din abun tsoro ne, Handsfree ta saka ta cigaba da cewa "Maama, idan an ma mutum laifi, ko an zalunceshi, ko an kwareshi me ya kamata yayi?" Maama tace "Sai Yayi hak'uri, sai ya bude zuciyarshi, sai Allah ya saka mai" Kan Zaid ya sara ya buga, ya san me muryar nan, definitely ya san voice dinnan, Najwa ta cigaba da cewa "Maama daukan fansa fa?" Maama tace "ai baa so mutum ya dau hukunci a hannunshi, is either ya kai kara gurin hukuma su bi mai hakkinshi, ko kuma ya bar ma Allah, shine kadai baya zalunci, shi kadai ne adali me Adalci" Najwa tace "Maama, misali Daukar Fansa ya maida ni abun tsoro fa?" Muryan Maama ya chanza tace "Najwa, ba zan yafe miki ba in Daukar fansa ya chanzaki for any reason, i pray ba wani abunda zai saki chanzawa daga halayenki da na sanki dashi, duk da na san tambaya kawai kike don neman ilimi, maaff karane ke lie seekhana (ki koyi yafe ma mutane)". Ba zai cigaba da jin Maganganun nan masu kama da saukar aradu a tsakiyar kanshi ba, ba zai jure jin Maganganun su ba wanda ya tsargu da shi suke, da sauri ya fizge wayar hannunta tare dNasoyana, yana huci, Najwa ta samu karfin guiwa tace " Ka fadi ranka, i know you can talk" da mamaki ya kalleta, "how long have you been stalking me?(tun yaushe kike bibiyata)" murmushi tayi tace "Tun randa kazo Gidan nan" "what happened yesterday was you right?" tace "Mummy na ne kaji muke waya da ita, kaji abunda ya kamata kayi, in laifi aka maka, ba ta haka ya kamata ka biyo ba, ka barsu da Allah, ko kai kara wurin hukuma, Allah ba Azzalumin kowa bane", So yayi ya mata lagalaga ya nuna mishi kalar Asarar da ta mai wurin mata jinajina, saidai ranshi ba zai bari ba, saboda me? Saboda mace ce, cewar ranshi, in ma yace zai buge ta me zaiji? Tsaki ya buga yace"stay away from me" da karfin hali tayi daria sosai tace "ka fara tsoro na ne? Too early, ai duk wani shirin da kayi nike warware maka, duk shirin da zakayi nan gaba zan warware maka, as long as ba zaka gaji da hada mugunta ba, nima ba zan gaji da warware maka muguntanka ba har sai asirin ka ya tonu". Hannu ya sa ya kwasheta da Mari, ya sake marinta ta dayan bangaren, tare da nunata da dan yatsa, " Stay the f*ck away from me, kika sake shiga harkata, I will Kill you, Believe That". Ya fita a fusace tare da buga k'ofar, Najwa ta zube kan Gado tare da fashewa da kuka mai taba zuciya. ******* Assalam Alaikum Masoyan ADAY, nasan kun dade kuna jiran Post dinnan, hakurin nan dai zan cigaba da baku, shi zakuma ku cigaba dayi, da kunsan tun yaushe nake typing page dinnan da kun sha mamaki, sai yau Allah ya sa na gama page din. Dalili daya ne na rashin samun Post akai akai, MAKARANTA, makaranta ya samu gaba wallahi, Semester yazo gangara, abubuwa sunyi zafi, nakusa fara Jarabawa, in kuma nace zan cigaba da muku typing zan shiga Hakkina, kuma Karatuna gaskia shine a gaba, hakan yasa zan saka Aya a wannan Page din, bayan Hutun Makaranta, zuwa Decemeber, zan cigaba daga inda na tsaya In Allah ya kaimu rai da lafiya, a lokacin ne zaku samu post a kai akai cikin kwanciyan hankali ba tare da wani excuse ba da Yardan Allah. So ina fatana zaku fahimce ni, kuma ku kasance tare dani, tare da adduoin samun nasarar da saar Jarabawa, don shi kadai ne son da zaku nuna min. Nagode Allah ya kaimu lokacin.... R anar da muke Jira tazo, Najwa da Zaid Ido da Ido Zaid zai auri Ziyada? Ya rayuwar su zata kasance bayan sun koma Gidan Hajjo? Kamar Mairo zata fara k'osan saidawa, lol, idk. Me zai faru in Paapa da Maama suka dawo Nigeria? Ya Zaid zaiji in ya san Mahaifanshi na da rai? Maama zata yafe ma Zaid in ta san abubuwan rashin imanin da yayi da sunan rashinsu? Najwa kuwa zata cigaba da son Majeed in ta gano abunda Mommynsa ta ma Iyayenta? Tambayoyi da yawa wanda amsar su kadai zaizo ne bayan Kun kasance tare dani. Remember Patience is a virtue. I heart you all. #1love #ADAY 馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱