Sashe 13
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaron Ya dade yana aiki, ya shiga nan ya gyara, ya wanke chan, komai sai da ya gyara, Aiki dai yayi ba ha'inci, ya fito ya musu nuni da ya gama, suka lek'a, suka ga komai yana shining, Sada yaji dadi sosai, ya bude Wallet ya ciro 200 rupees ya ba shi,200 rupees daidaid yake da Naira dubu 1 a kudin Nigeria, sosai dan saurayin yaji dadi, daga yanda yakeyi zaka san yaji dadi, be iya cewa komai ba sai "thank you, thank you". Yesmin tayi murmushi tace da Sada "barin ga ko na iya indianci" ta kalli Saurayin tace "Aapka Naam kya hai?(Ya sunanka?)" da Murna yace "Mera Naam Vijhay(Sunana Vijhay)" nan ya shiga rantafo zanttutuka da Indianci, suko sai daria suke tayi.
聽 Vijhay ya rakasu Kasuwa sukayi siyyayan abubuwan bukatarsu, na Abinci, da sauransu.
Washegari Vikash yazo ya tafi da Sada Maaikatansu, cikin ikon Allah aka daukeshi Aiki,Vikash yake tambayar shi, "ita Yesmin ba zata fara aiki ba? Ko su a country dinsu Mata ba sa aiki?" Sada yace "sunayi, in sunyi settling itama zata nemi aiki" yace "me take iya yi?" Sada yace mai "Medical Practitioner ce" Vikash yace "Wow, aikuwa zai kaita wani Private Hospital, idan sun mata Interview zasuyi employing dinta". Ko da ya gaya ma Yesmin yanda sukayi da Vikash taji dadi sosai.
Washegari Vikash yazo ya dauke su suka tafi Indrasptha Appolo Hospital da yake a nan Sarita Vihar. Bayan wani dogon bayani da wasu abubuwa aka dauki Yesmin aiki a Asibitin.
聽 Tun daga ranar da suka dawo Unguwar, kullum Vijhay sai yazo yace "room sweep?" sai dai suyi daria, in akwai wani aiki sai Sada ya bashi ko wanki, ko makamancin haka, har suka fara sabawa duk da ba wani fahintar juna sukeyi ba, in ta dafa Abinci tana zuba mishi yaci. Haka Yesmin da Sada suka fara Sabon rayuwa ba tare da wani damuwa ba ko matsi.
聽聽 BAYAN WATA BIYU
KANO NIGERIA.
聽 聽
聽 聽 Yau Asabar, yau 'yan HIG ke hutu, Alhaji Abba Abu da Matarshi da Zaineema ne suka zo Hassan Gwarzo daukan su AbdulMajid, da gudu suka rugo suka rungume Alhaji Abba, Kafin suka rungume Mairo, Zaid ya dauki Zaineema da take ta tsalle tana fadin Zed Zed ko kallon Abdul batayi ba,abunda ya k'ona ran Mairo kenan,wai don me Zainee zata fi murna da ganin Zaid,ba Yayanta Abdul ba, Alhaji Abba yayi daria yace "Ahh, Zaineema baki manta Zaidunki ba, to ku shiga mota mu tafi gida" bayan sun saka Jakkandu cikin Booth, suka shige mota suka nufi gida.
聽 聽聽 Murna gun Zaid da ya ga an doso Gate din Gidansu, ya k'agara ya ga Maminshi da Babanshi, sosai yayi missing dinsu, Alhaji Abba na parking, Zaid ya bude murfin Motan ya dira ya sa gudu ya na kwala kiran "Maama, Baba, mun dawo" Abdul ma ya rufa mai baya da gudu, gaban Alhaji Abba ya fadi, yana tunanin ta yanda zai sanar da dan k'aramin yaron nan Rasuwar Mahaifanshi,tsayawa yayi yana tunani ya kasa shiga ciki, Mairo ko ta6e baki tayi ta shige ciki.
聽 Ko wani daki da sak'o na cikin Gidan Zaid ya bincika amma wayam, ina Maaman shi, ko suna gidan Kaka Hajjo ne?
A Parlor ya iske Mairo, ya k'arasa gunta yace "Mama, ina Mamana da Babana?" a tak'aice tace "Sun Mutu" Ido ya fiddo, Zaid na da wayau, haba dan JS1 ai ya san Mutuwa ko? Cikin firgici da tsoro yace "Mama danAllah kiyi hakuri, suna ina? Ko sunyi tafiya ne?" ihu ta datsa mai tace "Ajiyar su ka bani?nace maka sun mutu ko?ko baka san mutuwa ba?" hawaye ke zuba a idonshi, kanshi na juyawa, Mamanshi ta mutu? AbdulMajid ma ya fara kuka, Alhaji Abba ya shigo, da sauri Zaid ya k'arasa gunshi yace "Baba Abba, wai Babana ya mutu?da sauri Alhaji Abba ya kalli Mairo, yace " haba Mairo, yanzu sai da kika gaya mai mutuwar nan? He's just a kid" tsawa ta daka mai tace "yi min shiru, ko basu mutu bane? Boyeboye na meye?gwara a gaya mishi ya sani tun wuri" Alhaji Abba ya fara hawaye, yace "ba dai ta hanyar nan ya kamata ya sani ba" tace "naje na gaya mai, don ma ban gaya mishi ta irin hanyar da suka mutu ba?" tambayar da Zaid ya mata ne ya basu mamaki, ita dai tasan Zaid yasan ba ta sonshi, bata son Yesmin, ta tsanesu duka amma bata taba zaton wayonshi zai kai ga ya mata irin tambayar nan ba Kallonta yayi ido tsaye yace "Ke kika kashe su ko?" tamkar saukar Aradu Mairo taji abun, haka kurum taji tsoro ya kamata, yaro k'arami kamar Zaid ya sa ta fargaba karo na farko. Baba Abba yace "Zaid, kar kace haka, ka bari kaji, nine Babanka Maryam itace mamanka yanzu, AbdulMajid kuma Yayanka, Zaineema kanwarka, kar in k'ara jin maganar nan a bakin ka" Kuka yakeyi sosai, AbdulMajid ya matso kusa dashi yana share mai hawaye, Zaid ya sa duka hannayenshi ya ture AbdulMajid ya fadi kasa warwas,"Mamanka ta kashe min Mama, nima sai na kasheta in na girma, kuma wannan Gida na ne, sai na koreku duka, bana sonku ku fita ku barmin Gidan Babana, Allah sai ya saku a wuta dukanku" Alhaji Abba ya daka mai tsawa yace "Zaid ka min shiru, baka da hankali ne? Wayace maka mu muka kashesu? Baka san kowa zai mutu ba? Lokacinsu ne yayi, nima da na ji rasuwarsu i acted like you did, nasan kai yaro ne, you wont understand, amma Baba Abba is here for you kaji yarona?" da k'arfi Zaid yace "I hate you all" ya ruga da gudu cikin dakinshi ya danna Jamlock ya fada gado yana kuka mai tsuma rai "Maamaaa, Baaabaa, ku dawo, Allah ka dawo dasu, Allah ka dawo musu da ransu, Allah ba zan iya rayuwa ba su ba, Allah nima ka kasheni" haka yake ta fada har bacci mai nauyi ya dauke shi.
Hankalin Mairo yayi k'ololuwa gun tashi, ta rasa ya zatayi, nan da nan ta kira Hajia Aliya ta landline din gidan, tace mata akwai Matsala, Hajia Aliya ta sanar da ita zata zo bayan Laasar.
聽聽 Ba zaman lafiya cikin gidan, gida kamar gidan rainon yara, Kuka Zaineema, da Abdulmajid keyi, tunda suka ga Zaid na kuka suma suke ta kuka,Hankalin Abdulmajid ya tashi, Allah ya daura mai son Zaid, haka ya k'i cin Abinci gashi yana jin yunwa, shi sai an bude kofa ya shiga gurin Zaid, kuka Sosai suke tayi da abun ya ma Mairo yawa sai ta sa chazar fanka ta zane Zaineema da AbdulMajid kafin sukayi shiru, sukayi baccin dole.
聽 聽 Tunda ya tashi bacci yake jin yunwa, rabonshi da Abinci tun wanda yaci a School karfe 9 na safe, gashu yanzu past 4, bude k'ofar dakin yayi zaije kitchen yaji magana K'asa k'asa dakin Mamanshi, cikin sando ya karasa yaji me ake cewa,
"Yanda Allah ya rufa min Asiri, don uban yaron nan so yake ya tona min Asiri, inshaAllah I got rid of Yesmin and Sada for good, sun tafi kenan" Aliya tace "Amma da mamaki, wai haka kurum ya tambayeki ke kika kashesu? Ko kin taba gwada kashesun ne a gabanshi?" "Wallahi Aliya, yanda kikaji haka, nima haka naji, ban taba ba, nima ya ban mamaki" Aliya tace "gaskia akwai matsala, yaron nan zai baki matsala nan gaba,tunda kinji ya fara claiming in ya girma zai kasheku, nan Gidan Babanshi ne,waye-waye, wata rana Allura zai tono garma, gwara tun wuri ki san nayi" Mairo tace "Wallahi na tsorata,yaro ya hargitsa min gida, sai da na zane su Abdul kafin suka shafa min lafiya sukayi bacvin dole, Abba ko tausayin yaron ya sashi fita, bansan ya zanyi ba, Aliya ya zanyi?" tace kawai "ki murkushe shege cikin dare, ko kuma muje gun Mallam ya baki maganin da zai shek'eshi"
Be tsaya karasa jin me suke cewa ba ya fara ja da baya-baya, duk da wasu kalmomin sun mai girma, hakan be hana shi fahintar komai ba, wato sun kashe Iyayenshi, shima zasu kashe shi ko, dile ya ceci kanshi?" a hankali ya shiga dakin Baba Abba, ya ko ci saa Wallet dinshi na kan dressing mirror, budewa yayi ya cire kudin da ke ciki duka ya sa a Aljihu, da sauri ya fice daga gidan a guje, yana gudu yana waigen Bayanshi, Yanayin unguwan shiru, kowa na cikin gidanshi sai da yayi gudu mai nisa kafin ya samu machine, mai machine ya kalleshi yace "ina zaka?" inda zan bar gari, Mai machine din Yace kana da kudi? Zaid ya bude Aljihunshi yace "gasu nan" ganin yawan kudin ne mai machine ya waiga gefe ya ga ba me kallonshi ya fizge duk kudin ya burka machine dinshi yace "yaro koma Gida" Zaid na kallo mai machine ya gudu, Zaid ya sake fashewa da kuka, mutane ba Imani, haka ya cigaba da tafia yana kuka, be sanin inda yake jefa kafanshi, ga Wani Uban yunwa yanaji,har ya fito bakin titi har bayan Sallahn Maghrib, Zaid na tafia, da yaga jiri na dibanshi ya samu wuri ya zauna, daga nesa ya hangi wani Mutum mai kama da Babanshi, ya fito daga wani Supermarket din da a zahiri na Babanshi ne, sai yanzu ya ga nisan tafiar da yayi, cikin zafin nama ya tunkari Mutumin da ke k'okarin sa Ledoji cikin Mota, Zaid ya fada kan K'afan Mutumin, a firgice Mutumin ya dago yana cewa "lafiya yaro?" baki bushe Zaid yace "Babana.." daidai da digowar hawayen mutumin, a ranshi ya maimaita kalmar 'Babana', Zaid ya karasa maganar da ta sark'e mai a baki "ka taimakeni" luuu jiri ya dibi Zaid ya fadi k'asa sumamme....
Wanene wannan Mutumin?
One word for Mairo,
And Zaid's journey begins...
Hello lovers show some love, Vote, Comment and share..
#1love
#ADAY
#bibiliciousfreakingfans
#anatare
#nagode
Biebee Isa
[12:01, 25/09/2017] 鈥�+234 803 414 9368鈥�: 锟斤拷A DADE ANA YI....sai gaskia锟斤拷
NA
BIEBEE ISA
庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg9鈨�