← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 128

Sashe 74

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read

聽 聽 Abdulmajeed聽 da Daddy suna hanyan dawowa Gida daga Masallaci,聽 daga nesa suka ga Motoci kusan聽 guda Biyar a daidai kofar Gidan Hajjo,聽 Daddy ya kalli Abdulmajeed, yace "baki mukayi?" Abdulmajeed yace "da Alama" daga nesa Daddy ya hango Baba Ado,聽 kasancewar Babban mutum Sananne yace "Abdulmajeed聽 kamar Alhaji Ado Mali na GG" Abdulmajeed da mamaki yace "shine Daddy,聽 ko Lafia?" Daddy聽 yace "kace me neman Ziyada dan Marigayi Gatan Marayu ne ko?" Abdulmajeed聽 yace "Eh,聽 Zaid sadam sunanshi" Daddy yace "to ba abun mamaki bane, kowa yasan Alhaji Sadam da Alhaji Ado Aminanna juna ne,聽 kila neman auren Ziyada sukazo" Abdulmajeed ya jinjina kai suka karasa gunsu,聽聽 da Sallama, ta cikin Mota Zaid ke kallonsu cike da tsana,聽 ji yake kamar ya fita ya makure su,聽 a karo na biyu tun bayan da sukazo mai taaziyar Babanshi zasu hadu gaba da gaba,聽 yana jin Daddy da daya daga cikin Abokin Baba Ado suna gaisawa,聽 Abdulmajeed ya gaishesu cikin girmamawa,聽 Baba Ado yace "Alhaji Abba Abu dama wurinka mukazo" Daddy聽 jiki na rawa yace "mu shiga daga ciki".

Abdulmajeed聽 yayi saurin聽 shiga Gida yace "ku koma daki, anyi baki" Mairo tace "su wanene?" Abdulmajeed聽 yayi聽 Murmushi聽 yace "masu neman聽 auren Zuzu ne" dam gaban Ziyada ya fadi,聽 Mummy ta yashe hakori ta na gyara zani tana tura yaran su fita daga palo tana cewa "Gatan Marayun ne?" Abdulmajeed聽 yace "magabatanshi ne" daki suka koma,聽 Ziyada ta rasa me takeji,聽 dadi ne?聽 ko tsoro? Mummy tace "Diyata kwantar da hankalinki mu mun dangwalo arziki" shiru聽 suka mata kowa da tunanin da yake.

Zaune suka a cikin Parlo,聽 ba abunda kakeji sai gaurayen daddan k'amshin turarensu, su 4 ne zaune,聽 sai Daddy na biyar,聽 Abdulmajeed聽 ya fita don siyo musu Lemu, nan suka sake sabon gaisuwa,聽 Baba Ado ya fara magana kamar haka ;
"Da farko muna neman afuwan zuwa ba tare da saninku ba,聽 ko kuma ince izininku ba" Daddy yace "haba bakomai wallahi" Baba Ado ya cigaba da cewa "Alhaji Abba Abu, sunana Alhaji Ado na Mali, Amintakarmu da Marigayi Alhaji聽 Sadam Audullahi ya sa muke jin kanmu kamar yanuwana jini, Yaronshi Zaid wanda ake ma lakabi da gatan Marayu na biyu na neman diyar gurinka Ziyada,聽 be da wanda zai shige mai gaba kamar mu,聽 duk nan da kake ganin mu ba wanda be ci Albarkacin Gatan Marayu ba,聽 ya mana abunda ba zamu taba mantawa ba, ba wannan ba, Yaronmu ya gano fure a Gidanka,聽 kuma yana so a bashi damar tsinka" sukayi dariya gabaki daya.

Daddy ya muskuta yace "To Alhamdulilah,聽 nayi farinciki matuk'a da wannan zance,聽 babban abun farinciki聽 shine kasancewar dan Baban Gida kamar dan Gidan Gatan Marayu na neman diyata da aure,聽 ba wanda ba zaiso hada iri da Alhaji Sadam Audu ba,聽 kowa ya sanshi datijjon kirki ne,聽 ban taba ganinshi ba,聽 amma abubuwan Alherin da yayi na isko mu, kuma ko bayan rasuwarshi danshi ya cigaba daga inda ya tsaya,聽 Alhaji Sadam Audu is a legend,聽 he is Dead,聽 but his legacy still lives, so babban abun Alfahari na be wuce ganin diyata ta auri Yaron Baban Mutum kamar Marigayi Alhaji Sadam ba,聽 amma wani hanzari ba gudu ba,聽 duk yanda nake son wannan abu ya kasance,聽 ba zai wuce da Amincewar yarinya ba,聽 in bata amince dashi ba,聽 to ba yanda zaayi sai dai ayi hakuri,聽 don banda niyyar aura ma yarana wanda ba sa so" Alhaji Ado yaji dadin Dattakon Alhaji Abba,聽 yace "haka ne,聽 yi ma yara auren Dole ba fa'ida,聽 amma ina da tabbacin suna son juna, shi dan gurinmu ya tabbatar mana da hakan,聽 yana waje barin kirashi ya sake tabbatar mana da hakan" ya zaro wayarshi ya latsa ma Zaid kira,聽 ringing聽 daya Zaid ya dauka "Eh Hello, ka shigo ciki" be tsaya jiran abunda Zaid zaice ba ya kashe wayar.聽

Zaid yayi jim yana kallan wayar,聽 takaicin Baba Ado yaji,聽 don me zai kirashi? Me zaije ya musu? " Idi yace "Oga ka shiga kawai,聽 Allah ya soka Baba Ado ya baka Manyan kaya kasa, lafiya lau ne, ka shiga kawai,聽 remember聽 gaban sirikin ka kake,聽 banda kallonsu cikin ido,聽 kuma a kasa zaka zauna" tsaki Zaid ya buga da karfi ya bude kofa ya ma su Amrstrong banging da karfi,聽 suko suka fashe da daria,聽 cikin Gidan yayi,聽 gidan ba bakonshi bane, takalmominsu ya gani daga waje,聽 yayi Sallam ya shiga suka amsa mai,聽 a k'asa ya zauna kamar yanda Idi yace, murya cikiciki ya gaida Daddy,聽 Daddy da faraarsa ya amsa.

Baba Ado yace "MashaAllah,聽 Alhaji Abba ga Yaronmu,聽 durfane gabanka, yazo neman auren diyarka,聽 be zo a matsayin Gatan Marayu na biyu ba, yazo ne a matsayin聽 Zaid Sadam me son diyarka Ziyada" kan Zaid a kasa,聽 yanda yake magana sai yake jin wani nauyi na sauka a kansa,聽 anya zai iya kuddirinsa? Kafin Daddy ya bada amsa Abdulmajeed ya shigo dauke da Lemuka su coke fanta mirinda a talauce (waya ce maka suna shan irin wanan? lol).

Alhaji聽 Abba yace "ga Baban dana,聽 yayan Ziyada聽 ne,聽 sunanshi Abdulmajeed" Abdulmajeed聽 ya dirr lemukan a k'asa ya sake gaidasu,聽 suka amsa da faraa,聽 Daddy yace "AbdulMajeed,聽 je ka kira min Mummynku da Ziyada,聽 inshort ka kira min kowa da kowa har Mama" Abdulmajeed聽 ya mike a ladabce ya fita,聽 a dakin Hajjo ya iskesu duka,聽 yace "Mummy kuzo Daddy na kira" jiki na rawa Mummy ta zaro聽 mayafin da bata san ko na waye ba zata fita Abdulmajeed聽 ya tareta,聽 yace "tsaya Mummy,聽 gabaki daya zamuje,聽 Zaineema ku muje,聽 Hajjo har ku" duk聽 suka tashi聽 suna neman mayafin sakawa banda Ziyada da ta takure wuri daya,聽 Abdulmajeed聽 ya kallota ya bude drawer ya ciro wani k'aton gyale ya rufe mata jiki yace "come on zuzu, ba zaki bar surikanki suyi ta jiranki ba ko?" ta mike聽 jiki ba kwari,聽 Abdulmajeed ya ja hannunta suka fita, duk suka rufa musu baya banda Najwa da ta ke聽 gyara inda su Muhsin suka 6ata.

Sallama sukayi suka shiga,聽 suka amsa聽 da faraarsu,聽 duk suka samu wuri suka zauna, kan Ziyada a k'asa,聽 Baba Ado ya nuna ta da yatsa yace "ga Amaryanmu nan" ta sake sadda kanta k'asa,聽 Daddy yace "haka ne, nan Iyalai na ne dukkansu,聽 Wannan itace Mahaifiyata,聽 wannan kuma Mai dakina" ya nuna Mairo da hannu,聽 ita ko sai faraa take watsa musu"聽 wannan kamar yanda na gaya muku shine babban da na AbdulMajeed,聽 sai me bi mishi Zaineema,聽 sannan Ziyada,聽 Zinatu ke bi mata sai auta Muhsin" Alhaji Ado yace "MashaAllah,聽 Allah ya ja kwanan zuria,聽 matuka kun burgeni,聽 ka nuna mana dattako da karamci,聽
Hak'ika hankalin mu zai kwanta ganin gidan da yaronmu ya dauko mata" Daddy yace "haka ne, amma bari mu ji ta bakinsu ko?".

Alhaji Bello yace "Zaid, shin wannan itace ka zaba ta zame maka abokiyar rayuwa har karshen rayuwarka?" be san dalilin da yasashi faduwar gaba ba, yayi shiru gabanshi na dukan chalugude, baba Ado yace "Zaid?" da sauri yace "Eh itace". Daddy ya juyo kan Ziyada yace "Ziyada kin amince in bada aurenki ga Zaid? Kar kiji nauyi ko wani abu in ba kya so, sai in basu hakuri, ki fada min ranki, farincikin ku ya fiye min komai" Ziyada ta sadda kanta kasa, Daddy yayi maganan duniya amma tayi shiru ba tare da ta tanka ba, yace "ko ba kya so?" nan ma shiru tayi, Alhaji Bello yace "Ziyada magana zakiyi kinji? Ba zamu gane me ke cikin ranki ba in ba magana ko alama kika mana ba, kina son sa, ko ba kya sonsa?" shiru tayi har yanzu ba tace komai ba, Mummy ji take kamar ta gwala kan Ziyada da bango, Alhaji Sani yace "kun san dai ma'anar shirun budurwar kirki, yana nufin ta amince kenan" Alhaji Kabir yace "aa kar ayi saurin yanke hukunci, duk tambayar da aka mata shiru tayi, ya kamata musan amsarta, muna iya bata lokaci tayi tunanita gaya mana sirrin da ke ranta".

Abdulmajeed yace "Erhm, in zan dan iya magana da ita, zan samo mana amsar da takasa fada" Daddy yace "Eh Abdulmajeed kuje kuyi magana" hannunta yaja suka fita daga Parlorn, Daddy ya musu alamu da su bisu, su Mummy suka tashi suka tafi, be san meyasa yaji gabanshi na faduwa ba, what if tace bata sonsa? Plan dinshi ya zube kenan? Plan kadai? Cewar zuciyarshi, da sauri yace "eh, plan dina ne kawai, be san mesa ba amma sai ya tsinci kanshi da yin adduan Allah ya sa ta amince.

"Zuzu lookat me, talk to me, kina sonshi? " cewar Abdulmajeed, da sauri ta kallo yayanta tace "YaMaji, a cikin halin da muke ciki, maganar aurena shine karshen abunda ya kamata ayi, muna cikin halin ha'ulai, Ya Maji--" ya katseta da cewa "shhhh, ki amsa ni, kina sonshi?" rungumeshi tayi da sauri tana gyada kanta a jikinshi, yayi daria yace "abunda nake sonji kenan" ya juya ya tafi yayi Parlor, ya rada ma Daddynsu a kunne, Daddy yace "to Alhamdulilah, yarinya ta Amince" duk sukayi hamdala suna faraa, Zaid ya sauke numfashi a hankali yana gode ma Allah.
Chapter 74 · 0% Book details