← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 128

Sashe 75

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Ado yace "Alhaji Abba ka bamu?" Daddy yayi daria yace "na baku" sukayi daria sukace "mun karba kuma mungode, muna so ayi Auren Ran Juma'a me zuwa in Allah ya kaimu" Daddy suka kalli juna da AbdulMajeed, Daddy yace "Alhaji, da wuri haka? Ni ina zaton sai daga baya zaa sa bikin kuma zaa sa a kalla wata 10" Alhaji Ado ya zaro ido yace "Wata Goma dai? Me zaa jira Alhaji tunda yara na san junansu, ka bamu kuma mun karba? Me zaa jira?" Daddy yace "haka ne, amma akwai wata yar matsala da ta auku, ina neman Alfarma a bamu lokaci mu maganceta kafin ayi ma maganar daurin auren yaran" Alhaji Ado yace "nasan kana so kama diyarka kayan daki, nasan kana so nyna bajintarka a matsayinka na Baban yarinya, nasan kana so kamata kayan daki kamar yanda ko wani uba yakr ma diyarsa, amma Ba fin karfi, ba nuna isa ba, ba ma bukatar komai, Yarinya muke so kuma kun bamu, ita ral muke so a daura aure Yaro ya dauki matarshi ya kaita Gidanta" Daddy zaiyi magana Alhaji Ado ya katseshi da cewa" Gatan Marayu na farko ya kan daura ma Yara 100 aure a rana wanda be sani ba fa, ya musu lefe ya musu kayan daki, to me kake tsammamin zai ma Yaronshi in ya tashi aure? Ka na tunanin zai barsu su siya koda kara ne?" Daddy yayi jim kafin ya kalli Abdulmajeed neman shawara, da ido ya gyada mai kai Alamun ya amince, Daddy yace "haka ne, toh Allah ya saka da Alheri, Allah ya kaimu Jumaa din" Alhaji Ado yace "Ameen, ba shishigi ba, amma wata irin matsala ce da kuke son magancewa?" Daddy yace "ba wata damuwa bace, kar ku damu" Alhaji Ado yace "haba Alhaji, tunda ka bamu diya ai an zama daya, ka gaya mana ko menene".

Daddy ya yi shiru kafin yace "Akwai Alhaji Nakowa da muka samu sabani dashi--- tiryan tiryan ya kwashe labarinsu da Alhaji Nakowa zuwa yau" Allahu Akbar, Zaid dai duk wani guiltiness ya kamashi, be taba jin tausayin mutanen nan ba ko kadan amma yau da Daddy ke bada labarin sai yaji wani bangare na zuciyarshi na tausaya musu, da sauri gudan zuciarshi ke mai gargadi da kar ka sake kaji tausayin Azzaluman nan da suka maka katangar karfe da mahaifanka, da sauri ya yakice tausan da ke ranshi, be ankara ba sai ji yayi Alhaji Ado na cewa "Alhaji Abba, tunda yanzu an zama daya zan bada Miliyan 30 din ku biyasu" Daddy yace "gaskia ba zan amince ba, abun ai sai yayi yawa, gaskia ba zan yarda ba, abin da kukayi ma mun gode Allah bada Lada" Alhaji Ado yace "Haba Alhaji Abba, ashe baka yarda an zama dayan ba, to in ba mu ma Zaid ba wa za mu mawa, na gaya maka duk nan ba wanda be ci albarkacin Gatan Marayu ba, duk abunda muka mishi ko danshi bamu fadi ba wallahi" Zaid kamar ya makure Baba Ado, ya sanshi da kafiya, biya musu bashin nan na nufin basu da wata damuwa, meyasa yake da shishigi ne? Tsaki yake ta bugawa a ranshi yana cewa shifa baba adon nan da matsala yake, shi kuwa Daddy ya san cewa in suka rasa tallafin nan ba wanda zai sake tallafa musu, this is the only chance they have, amma be bi san zucianshu ba yace "duk da haka , kuyi hakuri we are not your responsibility, in sunyi aure duk abund zai mata ba me hanashi matarshi ce".

Ganin ba zai amince ba dabara tazo ma Baba Ado, yace "to in ranta maka mana? Da bashi a kan mutane irin Alhaji Nakowa gwara gida ko? Zan ranta maka, in ka samu sai ka biyani" Daddy yace "to ina iya amince ma rance, amma gaskia ba kyauta ba, kuma 25million ne, don mun basu 5, zan dinga biyanka a hankali a hankali" Zaid kamar yayi Ihu don haushi, yasan siyasa Alhaji Ado ya mai, ya san ba zai taba karban kudin ba, shikenan ya yanke musu wahala, kamar yayi kuka, nan dai suka cigaba da tataunawansu cike da mutunta juna, Alhaji Ado yace "gobe zaayi banking a biya Alhaji Nakowa kudinshi, Alhaji Bello yace bayan daurin Aure zaayi gagarumin walima" Alhaji Sani ya ciro rafar 1000 guda uku yace "ga Sadakin Amarya" duk abubuwan da akeyi bakinciki ya turnike Zaid, shifa neman aure yace su zo su mishi ba san iyawa ba, be san lokacin da ya mike ya fita ya bar parlorn ba, ba su damu da shi ba don ba su ma lura da ya fita ba, ba jimawa suka tafi.

A GURGUJE
Mairo harda takawa tayi don Dadi da taji sun dangwalo Arziki, har ce ma Ziyada take ta zo ta hau bayanta ta goyata ta share mata hawaye, a zuciyarta take hasko yanda rayuwa zata canza mata, zata fito gari ta taka duk wanda ya tabata, zata gurza ma makiyanta rashin mutunci, Ziyada kam farinciki damke a ranta zata auri farincikin ranta, wai ita zata zama Mrs Zaid Sadam in two days, she cant wait. Bata so yin wani gayya ba, amma Mummy tace sai tayi gayan friends dinta duk da ba wai yawa ne dasu ba, a cewar Mummy ya zaayi ta auri Mutum kamar Zaid amma ba wanda ya sani? Dole ta gayyato kawayenta, haka dai ta hada BC ta tura ma Friends dinta. Itama Mummy aka wuce gidan tsohuwar kawarta hajia Aliya tana bude mata hanci ita zata zama sirikar Zaid Sadam.
Alhaji Nakowa yayi mamakin ganin Cheque da yayi daga account din Ado Mali wai da sunan biya ma Alhaji Abba Bashi wanda daga Kotu aka turo mishi ba haka yaso ba, so yayi ya kuntata ma su Hajia Mairo, amma ya ya iya? Karawa da Alhaji Ado Mali kamar karawar kifi ne da mage.

JUMA'A

Bayan Sallahn Juma'ah ne a babban Masallacin Jumaa na Central Mosque dubbanin Jamaa suka shaida auren Zaid Sadam Audu da Amaryarsa Ziyada Abba Abu a bisa sadaki Naira dubu dari uku.

Wasa farin Girki.

鈥⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€�

Gyara: Dear Bibilicious freaking fans, akwai wani gyara da wata baiwar Allah ta min, attimes ina using Abdulmajeed wasu lokuta kuma Majeed, Malamai suna waazi akan Kiran sunayen Allah hakan Nan batare da sa Abdul din ba, mu kuma mu kan yanke ko don gayu ko don gajeratawa, amma hakan baban kuskure ne, to mu dinga kokari muna cikita sunan AbdulMajeed, from now henceforth zamu dinga karasa sunan, in aka ga akasin haka to kuskure ne da kuma sabo, ina fatab zamu gyara Nagode. .

Yekpa Anyi aure fa, akwai Walima Party anjima, you are all invited.

Akwai gwarama fa, this is the begining of an end, stay tuned, yanda nake kokarin typing haka, kuma dont Forget to Vote and Comment line by line.

#1love
#ADAY
#bibiliciousfreakingfans
#anatare
#nagode

Biebee Isa.
馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱

NA

BIEBEE ISA

庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Wattpad:@biebeeisa

Pg3鈨�1鈨�

Kafin a daura auren ji yayi kamar yaje ya hana wannan daurin auren,聽 ji聽 yayi kamar ya harbe Baba聽 Ado da yafi聽 kowa Zak'ewa a gurin, da aka daura Auren kuwa gabanshi ya tsananta faduwa,聽 wai yau shine aka daura ma aure? Zai rantse yaji girmana da ke shiga kanshi,聽 yaji kulawa da nauyin Ziyada a kanshi,聽 to wayace muku auren聽 zaiyi lasting? Wulakantata kawai zanyi na saketa,聽
Ya聽 san Central Mosque ne na garin Kano,聽 dole ta cika balle sallahr jumaa ce,聽 amma ya tabbata rabi da kwatan mutanen sunzo ne domin daurin auren gatan marayu kuma daga gari daban daban, besan abun ya baza duniya ba sai da ya ga an fito ana tayashi murna,聽 duk wasu abokan babanshi na nesa da na kusa zai rantse daidayyaku ne be gani ba.聽 Kowa burinshi ya gaisa da Zaid ya mai fatan Alheri,聽 a wannan fanin ne yayi nadamar sanar da Baba Ado tun farko,聽 dama zuwa yayi ya hayo Magabantan karya har ya aureta ya sakota Baba Ado be sani ba balle yayi mai tereren jamaa har ana chunkuson nan kamar hawan sallah.

Abdulmajeed聽 kam shima ba laifi Abokanshi na Kano sun hallarta daurin auren, har Khaleed din Zaineema yazo Kano Aliyu ya jawoshi suka zo bikin,聽 gaisawa sukayi kamar ba abunda ya faru tsakaninsu,Khaleed nason tambayarshi Zaineema amma besamu dama ba,聽 sai da suka dunguma sukaje wurin wani Reception da Baba Ado ya hada Khaleed ya samu ya kebe da AbdulMajeed聽 ya tambayeshi Zaineema,聽 Abdulmajeed聽 ya murmusa yace "tana nan lafiya聽 lau" Khaleed yace "Abdul Abba kasan inason Zaineema,聽 ina jin zan Maidota Gidana"Abdulmajeed聽 ya murmusa聽 yace "Kana so ka maidota ne saboda kana sonta? Ko kuma ka bar zarginta ka yarda shes innocent shiyasa聽 zaka maidota?" Khaleed聽 yayi jim yace "Zan maidata saboda ina sonta" Abdulmajeed yace "gaskia bazan yarda ba,聽 duk randa ka bar zarginta ka yarda cewa she was innocent ka zo ka tafi da ita" da sauri Khaleed yace "i saw someone laid on our matrimonial bed?(wani na gani kwance kan gadon aurenmu)" Abdulmajeed聽 yace "did you catch them lying together? Pestle and Motar? Did you?(ka gansu kwance tare? Turmi da tabarya?)" ya girgiza kai zai yi magana Abdulmajeed聽 yace "Khaleed,聽 muna聽 Walimar Aurene,聽 nan ba wurin maganar nan bane,聽 kaidai kawai kaje,聽 sai lokacin da ka yarda da ita". Ya wuce ya cigaba da harkar gabanshi,聽 Alhaji Abba ma sai hulda yake da mutanen shi,聽 Ziyada fa?.
Chapter 75 · 0% Book details