Sashe 58
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
hurt My Jaan". Afuwan Habibties, nasan cewa an kwan biyu, ku min uzuri, Makaranta ya boyeni, nasan page dinnan yayi kadan kuma sai a hankali, da kunsan yanda nayi typing dinnan ehm, ku fara dashi next page zaizo cikin weekends dinnan Asabar ko Lahadi InshaAllah. Ga Najwa ta gano Nura, ya zata kasance?, A babi na gaba zamu ga Mairo da Nakowa a Kotu. Sorry Sorry. Vote and Comment Please. #1love #ADAY #bibiliciousfreakingfans #anatare #nagode Biebee Isa. DADE ANA YI....sai gaskia馃挱 NA BIEBEE ISA 庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Wattpad:@biebeeisa Pg2鈨�6鈨� Ya san Hajiya Mairo, shes sharp, tana iya yin abubuwanta ta ci Case dinta da Alhaji Nakowa, in kuwa Alhaji Nakowa yayi loosing case dinnan, Zaid is doomed, kawai bari ya sa a zo ayi mai Operation once and for all, ya faki idon Majeed ya fita ya koma BQ. * Waya takeyi da Maama tana jin footsteps tayi saurin ce ma "Mamma i'll call you back" ganin so called Nura ne ya sata 6oyewa a bayan Bishiya, da sauri ya ciro wayarshi ya latso Armstrong, "Hello Arm, get your guys ready, come to the Mansion for Operation" sun dade suna magana ya gaya mishi abubuwan da yake so suyi da daddare, a k'arshe sai taji yana cewa "Yeah use your masterkey, i'll unlock the innerlock for easy passage, and arm i dont want you to fuck up, OK bye". Ya juya da sauri ya koma cikin Gida. Da mamaki Najwa ta bishi da kallo, "This Nura got some nerves" bari taje ta gaya ma Majeed, da sauri ta bi bayanshi, har tana harde kafafunta, to what Evidence gareki? Inji Zuciyarta, Najwa mind your own bussiness, Zuciyarta ta gargadeta, da sauri ta tsaya chak, tana tunanin abunyi. Da Daddare wurin k'arfe 11:30 na dare, Majeed ya latso Najwa a waya, Firan k'auna suke tayi, Majeed harda k'yalk'yalewa da daria yakeyi, Najwa tace "Jaan, ka daina daria da k'arfi, ni ka ga nan Hajjo da Na'ila sunyi bacci kar in tadasu" dariya yayi sosai, yace "ni kuwa zance ni kadai ke dakin, ba kowa bane kusa dani, saboda kurma ke kwance kusa dani, kin ga ko ko loudspeaker zan sa inyi ihu abun ba damunshi zaiyi ba don ba ji yakeyi ba" Nura yayi lamo ya rufe ido kamar me bacci,sai ya samu kanshi da jin haushin furucin da Majeed yayi, wato shine Kurma ko? Sai yaji ma beda wani amfani, wai shin da wa Majeed ke waya? Dama yana da yanmata, a ransa yace "i'll find whoever she is, i'll destroy her, i pledge to destroy your happiness, sai muga ta yanda zakuyi waya har kace ni ba kowa bane". Najwa a ranta tace "ba kurma bane, yana jin duk me kake cewa" a fili tace "still dai ka ga ni ba ni kadai bace, kar in dauki Alhakin su Hajjo" Majeed ya sauke numfashi yace "Shikenan PureHeart, banji bacci amma dole zanyi, Sleep Well Kinji?" ta murmusa kamar yana kallonta tace "You to My Jaan" a tare suka ce "I love you" sukayi daria, yace "sai baki a waya ko? Gobe sai kin fada miin a fili" dariya tayi ta kashe wayan. A bangaren Majeed murmushi yayi a baiyane yace "I love You PureHeart" Zaid ya maimaita kalman "PureHeart" a zuciyarshi, ba a dade ba Majeed ya bangas, Nura ya haska fuskar Majeed yaga bacci yake, a hankali ya bude k'ofar, yaje ya zare Sakatan Jikin k'ofar Parlorn,yanda dasu Armstrong sunzo Key kawai zasu sa. Kasa bacci tayi, kowa yayi bacci, ta janyo wayarta taga k'arfe 12 da wani abu, ta ji tabbas an bude k'ofa, abunda ya faru da rana ya fado mata, a hankali ta tako ta dan budo k'ofar dakinsu, ta ga shigewar Nura dakin Majeed, bayan ta tabbatar ya shige ciki, ta fita cikin Sanda, ta saka duka sakatan kofar, harda na sama wanda ba a sakawa, ta koma kasa komawa bacci tayi, har ga Allah ta ji wurin karfe 1, ana ta murda k'ofan Parlor, alamun ana so a bude, amma da yake ta sakata, ko motsi kofar beyi, handle din kawai ke motsi, Armstrong ya ma Nura text, why are we having hardtime opening the Door? Are you sure you unlocked the locks?( Meyasa muke shan wahalan bude k'ofan, ka tabbatar ka cire Sakatan? )" cikin hasala Zaid ya mai reply, "what are you saying? I've unlocked them, just open the goddam door( me kake cewa? Na cire mana, dallah ku bude kofan)" Armstrong ya sake k'okartawa, ya mai reply "Still not opening" Zaid yayi tsaki ya mik'e da niyar zuwa ya zare musu sakatan da ya san ya zare su, Ringing din wayar Majeed ya katse mishi hanzari, da sauri ya koma kan Gado ya kwanta, Majeed cikin bacci ya dauka "Hello PureHeart baki bacci ba?" a ran Zaid tsaki yayi, sai da ya lallasheta kafin ta barshi ya koma bacci, ta kira Majeed ne don ko Nuran zai yi planning yin wani abu in idonshi biyu, gwara Nuran ya ga ba bacci yake ba". Zaid na jin alamhn shigowan Messages din Armstrong, Toilet ya shiga don mishi reply, Cant we just shoot and scare the hell outta them? They'll open up( muyi harbi mana, da munyi harbi zasu ji tsoro su bude mana k'ofa )" cikin dacin rai Zaid ya mai Reply "No dont shoot, abort Mission, go home( aa banda harbi, ku watsar da aikin kawai, ku tafi gida )" Armstrong ya ba yaranshi Umurnin su tafi, Sosai ran Zaid ya baci, waye ya saka Sakata? Ko wani ya ganshi da ya je cirewa? Amma he made sure sai da kowa yayi bacci yaje ya cire sakatan, to ko wani ya san Plan dinshi ne? No impossible, ba zai yiwu ba, tsaki yayi karo na biyu, yana me jin haushin budurwar Majeed, da bata kirashi ba da ya je ya bude musu Kofar, da sun shigo sun ba Mairo tsoro a basu duk wasu Necessary documents din da suke so, kuma ya dau alwashin ko ina take sai ya nemo ta ya wulakanta ta, he'll make sure they dont get eachother. WASHEGARI Ta dade tana tunanin yanda zata sanar musu da batun, ganin zama ba zai mata ba, ya sa ta yin ta maza zuwa inda Daddy da Boy suke, shigarta Parlorn ya janyo hankalinsu gareta, Majeed ya gaida ta fuska sake tare da mik'ewa don basu guri da Daddy. Dakatar dashi tayi ta hanyar cewa "akwai important maganan da nake so muyi Boy" a nutse ya juyo ya samu guri ya zauna tare da bata hankalinsa. Sai da ta kalli Daddy kafin ta fara magana "Dama akan Wannan yar iskar yarinyar nan ne Nana bayan ha'intar mu da tayi, ta salwantar ma Boy Credentials,a zahirin gaskiya ni ban yafe abun da tai mana ba,kuma shirun nu na nufin taci bulus, hakan yasa na maka su Court, k'ilan Kotun zasu sa ta fiddo maka da Takardunka, anyi zaman farko last 2weeks, gobe ne zama na biyun kuma ana buk'atar ku da ku halarci zaman dan bada taku shaidar". Daga Daddy har Majeed sauraronta kawai suke, ganin damuwa a fuskokinsu yasa ta Murmushi tace "kar ku damu, nayi amfani da kudaden nan na dauko babban Lawyer, so zamu ci case din". Kai a k'asa Majeed yace " ki janye k'arar" da sauri tace "what?" yace "Mummy ki janye k'aran". Ganin ba wasa fuskan Majeed yasa Mairo matsowa kusa dashi ta hau lallami tana k'okarin nuna masa fa'idar kai k'arar Kotun. Cikin dan fada yace "Haba mummy sai kace wasu Wanda basu san Allah ba, muna musulmai ace mun kasa daukar kaddarar da Allah ya nufo mana? Ni wallahi na hak'ura da Takardun nan, na san su salwanta, da Credentials din na nan da tun kafin ki san da batarsu da Nana ta maido min dashi, abunda kika kasa ganewa, ita karan kanta Nanan ba ta sa wata ba ba, wani ne ya ya yaudareta, wai tsaya ma, wani evidence kike dashi yau in Nana tace ita bata san da zancen credentials dina ba? We are talking about Court here, where everything works only with Evidence (Maganan Kotu muke, komai da Sai da Shaida)". Mairo tace " No Boy, we have Evidence, balle ba zata k'aryata ba, Kotu kadai zata saka ta nemo maka Takaddunka, da kuma cin amanarka da tayi da aurenka a kanta, haba ko da wannan ai an kamata redhanded, saboda ina da Audio din kuma na tura ma Lawyer na Saboda tsaro, ka taimakeni Majeed, kasan ba wanda ya isa Kotu ta kirashi ya k'i zuwa ko? Kotu tace kaje in baka je ba, bansan me zai faru ba, Daddy Please ka sa baki". Daddy kam kai ya jinjina, be san mesa Maryam ke yanke hukunci ba tare da ta nemi shawaran kowa ba, yanzu ta san da wa takeson Ja? Alhaji Nakowa fa? Duk da ya san Cin Case din nan ba k'aramin abu bane, don dai kar ya kadar ma Majeed da hankali ya hau lallashin shi, amma tabbas ran Daddy ya baci yace "AbdulMajid, aikin gama ya gama, Mummynku tayi shirme, babu yadda zamuyi, wuri ya kure mana dole goben mu halarta a zaman, kayi haquri kaji ko? Allah ya ma Albarka". Majeed kai kawai ya iya kad'awa ga mahaifinsa ya mik'e cike da bacin rai ya fita. Tashi tayi zata fita, har ta isa daidai wurin kofar dakinsu kenan ta jiyo daddy cikin kakkausar murya yana cewa "MARYAM DAWO NAN KI ZAUNA" da bata san Muryanshi ba, da ba tace shine ba,cike da mamaki ta juyo tana kalllnshi Galala, ganin Fuskar shi cike da Umurni da rashin wasa ta k'arasa cikin Parlorn ta samu wuri ta zauna, tana me cike da mamaki wai yau ita Abba Abu ke ba umarni har wani tafarfasa yake kamar d'anyar ganda. Daddy yace "nikam Maryam yaushe zakiyi hankali ki gane jiya ba yau bane? Maryam ki ma kanki fada? Kinsan wani irin danyen aiki kika baro mana kuwa? Wa ke takara da Nakowa? Wani me hankalin ne? Wato ke duk abunda ranki ya aiyana miki shi kikeyi ko? Ni da gidan nan bani da ikon sanin meke wakana a ciki? Sai da ta baci nakeji, Wallahi Maryam ki kiyayeni, ki fita idona". Ta inda daddy yake shiga ba