← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 128

Sashe 51

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

yace "its Time(lokaci yayi)" Amstrong yace "time to what boss? (lokacin men)" "its time i meet them face to face(lokaci yayi da zamu hadu gaba da gaba)" Kano here i come, cant wait to see my Uncle, my cousins and above all my Evil Uncle's Wife, i'm coming for you all". Amstrong yace "what are you planning? Me kake shirin yi?" How will u meet them face to face?ta ya zaka hadasu da su gaba da gaba?" Zaid ya murmusa ta gefen kumatun shi yace "i'm going to live with them(zan zauna tare da su), in their House(a cikin gidan su), My House(Gidana)". 掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳掳 Bibilicious freaking fans, We have a newest Member in the Family, Who's Excited? Whats Zaid planning? How? Ku biyo ni dai. Shikenan Zaman Nana ya kare? donAllah a mata hakuri a dawo da ita, don nasan akwai 鈩ajeedholics fans, suna so suyi ma Nanarshi snatching, sha ba hope, Mairo ta kasa ta tsare, sai tayi screening Next Matarshi, nasan lot of you are shouting Najwa's name, Najwa-Majeed?? not happening, kuyi zeroing mind dinku, nothing of such will happen lol. Zaid a Kano? Me kuke tunanin zai faru a gidan nan? Theres a fire on the Mountain run run run. Mutane na na Niger, na ji sak'on ku, InshaAllah idan na saka turanci me wuya zan fassara da hausa a bracket, da na iya french da na saka lol. Wattpadians, show me love please. Vote and comment line by line. #1love #ADAY #bibiliciousfreaking 馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱 NA BIEBEE ISA 庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Wattpad:@biebeeisa Pg2鈨�3鈨� * KANO* Kanshi Yayi zafi, ranshi na k'una, ina ma mafarki yakeyi, ya san Nana ba natsatsiya bace, yasan halaiyar Nana tun kafin Aurensu, amma beyi zaton har yanzu tana yi ba, yayi zaton Aurenshi zai sa ta bari, ashe na haka bane, abun nata har ya cigaba, tabi maza tabi mata, kai Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, ya na jin hayaniya a waje, be ma da k'arfin tashi balle ya lek'a wainar da suke toyawa a waje. * Ita Asalinta bata son tashin hankali, tuni ta soma hawaye, bata taba ganin irin tashin hankalin nan ba, garin irin tashin hankalin da Mummy keyi a waje, har 'yan Media sun hallara wuri ya cika, Daddy na hana Mummy wasu abubuwa, su Ziyada hankali tashe, taji ita ba zata iya cigaba da kallo ba, zame jikinta tayi ta koma dakin da Majeed ke kwance, zaune yake, amma kallo daya ta mishi ta san cewa hankalin shi be tare da shi, a hankali ta taka har gaban Gadon da yake zaune, a hankali ta furta "Ya Majeed" kai ya dago firgigit, "pureHeart" ya furta a hankali, ba wai taji abunda yace bane, aa bakinshi kadai ta lura da abunda yace. Girgiza mai kai tayi tace "Dont hold it, cry, kayi Kuka Ya Majeed" kamar ko Umurnin ta yake Jira ya fashe da Kuka, har jikinshi na rawa, tausayinshi ya kamata, tayashi kuka, kusan mintun su 9, kafin Majeed ya tsaida hawayenshi ta hanyar gogewa da bayan hannunshi, ya kalleta yace " PureHeart, kukan ya isa haka" yana k'wak'ulo murmushi, da sauri ta tsaida nata hawayen ta janyo kujera ta kafa kusa da shi gaban Gadon. Ba tare da ta bari sun hada ido ba, cikin sanyi murya ta fara "so da yawa Allah na jarabtar mu da abubuwa kalakala, ba don komai ba, sai don ya gwada imanin mu, ya ga shin zamu rugumi kaddarar da ta zo mana? Zamu yi questioning Allah's Judgement? Or zamu Fawalla ma Allah komai, muyi moving on? I know there are times da zaka ji you want to give up on this life, sometimes zakaji kai komai ya fita a ranka, amma dont give up, Allah yace 'Ku rok'eni, zan amsa muku' so ina so ka dage da Addua, Allah ya baka ikon cin taka Jarabawar, kuma don hakan ta kasance da kai, kace ba zaka k'ara yarda da Mace ba, ko kace ba zaka k'ara aure ba, ba duka aka taru aka zama daya ba, kawai kayi Adduan Allah ya changing ma a better wife". Kur ya kafa mata idanuwanshi, kunnuwanshi na sauraran duk abunda take cewa, zai iya rantsewa kan be taba jin murya me dadin ta Najwa ba, duk da Hausarta be fita duka, sai yaji Hausarta ta mai dadi, kamar ta Yaro me koyon magana, wani abu yakeji game da ita da ba zai iya fassarawa ba, ji tayi yana kallonta, ta gefen ido ta dan kalloshi, karaf suka hada idanuwa, da sauri ta dauke nata idon, cikin wani siga yace " PureHeart,abun is somehow, but i'm fine now tunda daman mun san hakan na iya faruwa, kawai dai mun sama ran mu Positivity ne, amma nagode ma Allah, Allah shine abun godia da ya fiddo halayen Nana a fili, ba kisan kalar Drama din da akasha ba kafin na aureta, sha its in the past, but yanzu ai gwara da Allah ya baiyana mana true colors dinta ko?" shiru tayi saboda irin yanda ya kafeta da idanuwa yana jiran ta bashi amsa. Bata ce komai ba, yace "Ehen, gaya min, kince in rok'i Allah Allah ya chanza min Mata kamar PureHeart kikace ko?" da sauri ta zaro ido tace "ni bance kamar ni ba" ya dan dara yace "kin yarda kece PureHeart dina?" kunya ya rufeta, abunka da fara mace nan da nan kumatun ta suka danyi Ja saboda dadi wanda ya hade mata da kunya. Murmushi yayi yace "Someone is Blushing" da sauri ta sa hannu ta rufe fuskarta tana Murmushi me sauti. Banko dakin Mummy tayi Kamar wata zararra, gadan gadan ta yo kan Gadon Majeed, Najwa na ganin haka tayi saurin tashi, Fadawa kan Majeed Mummy tayi ta rungumeshi, tana shafan kanshi, Najwa tayi hanyan fita k'ofar ta ba ma Mummy Baya, don Majeed ke kallonta, Mummy na kallon dayan barayin, yana rungume Jikin Mummy, ya furta "*PureHeart* " a hankali ta juyo, da baki yace mata "I love you" daburcewa tayi lokaci daya, bata taba zaton hakan daga gareshi ba, kamar dazun fuskarta ya fara blushing, har kumatun ta sunfi dazun ja, cike da kunya ta fita waje, inda ta ci karo da su Ziyada da sukayi tsuru, shikuwa sake Rungume Mummy yayi tare da kwantar da kanshi kan kafadunta. Jin yace "i love you" Mummy ta fara magana, a zaton ta da ita yakeyi, kamar zatayi kuka "Boy, I'm sorry, ka yafe min, na maka zabin tumin dare, kayi hak'uri, we are getting yout Credentials back, na kira Dr, yanzu zaizo ya maka test din HIV, boy my son are you Alright?". Murmushi yayi, ya rik'o duka hannayenta, yace " I'm Fine Mummy, I'm totally fine" still dai sai anyi Test dinnan, saboda tsaro, yasan ba amfanin gardama da ita, sai ya chanza magana yace "da anyi Test din zaa sallameni, nagaji wallahi" tace "No, sai ka k'ara kwana, bakayi 1week din da Dr yace ba ai" yace "Noo Mummy, so kike dan kudadden da suka rage mana su k'are a gadon Asibiti? Duk kwana 25,000 fa, haba Mummy, kar ki manta, Monday Zuzu zata soma zuwa School, akwai abubuwan da nake son siya mata, in ina kwance a nan me kike tunanin zai faru? Zamu kwana mu tashi sisin Kobo ba mu dashi, so please kice ma Dr naji sauk'i ya sallameni" ta kalleshi cike da So da k'auna, me tayi Allah ya bata d'a kamar Majeed? Majeed Yaro ne da ko wacce Uwa zata so Danta ya kasance kamar shi, ka sa hakuri tayi sai da ta sake rungumeshi tace "I love you too" dariya yayi a ranshi yace "that one wasnt actually for you tho" a fili yace "and i love you More, Mummyn Majeed". ***** 'PureHeart I love you' sune kalmomi hudu da kanta ke nanata mata, tayi murmushi a karo na ba adadi, tayi lamo jikin bayan Motan da Fallalu ke maidasu Gida, itama tana jin wani abu game dashi, "but is this love?" sai Murmushi take tayi har suka isa Gida, sai da Hajjo ta tanka tace "Najwa, ko dai bushara aka miki da Gidan Aljanna, wannan faraa haka?" sai ta sa hannu ta rufe fuska saboda kunya. Cikin ikon Allah da aka gwada Majeed ba a samu komai ba, he's HIV-, hankalin Mairo ya kwanta, aka sallameshi Washegari, suka dawo Gida, hankalin kowa a kwance ganin Majeed ya samu sauk'i, yanzu burinta ta maka Nana Kotu, don ba zataci bulus ba akan cutar mata da Da da tayi, ba ubam da ya isa ya taba danta ya kwana lafiya, kuma duk inda Takardun Majeed suke sai an fiddo su ko da komai da ta tara zai k'are, ba ta sanar da kowa k'uddirinta ba ta fara gudanar da burinta, ragowan Kudadden da ya rage musu harda wanda Hajia Aynarh ta hada ta samo Lawyer, ta dangana da Kotu Washegari aka kai Sammaci Gidan Alhaji Nakowa Abuja. A B U J A Kwance take kan Cinyar Mom dinta tana kuka mai taba zuciya, Dad dinta safa da marwa yake, ranshi in yayi dubu ya baci, ya rasa me ke mai dadi, cikin hargowa yace "Ni Hajia Mairo zata ma haka? Ni? Ni zata tozarta, wulakanta diyata da tayi be isheta ba, har sai da ta makani kotu? Lallai Hajiya Mairo da Iyalanta zasu gane shayi ruwa ne, zan tona musu asiri, zan wulakantasu, zan tozartasu" Hajiya Sayluba rai 6ace tace "bayan duk hallacin da Nana ta musu, ta so dansu tsakani da Allah, ta zabi zama dashi duk da tasan basuda komai, ta rabu damu ta bar daula ta bisu ta zauna da su cikin talauci, amma itace abun k'ulla ma sharri da mata k'azafi, bayan a yad'ata a social media, yanzu kuma an kawo mana Sammacin Kotu, kai cin fuskan yayi yawa, Daddyn Nana kar ka barsu duka". Nana na shasheka tace "Mom, Dad, ba ruwan My Majeed, Mummyn sa ne, please kar ku mai komai, ku bashi hakuri ya dawo dani, i cant live without him" ta fashe da kuka, lallashinta suka hau yi, suna bata hakurin cewa ta hakura da Majeed, ba za su iya dawo mata dashi ba, kawai suyi focusing kan Case dinsu na court kuma by all means sai sunci, don daga Lagos Alhaji
Chapter 51 · 0% Book details