← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 128

Sashe 79

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kasa karantar yanayin da yake ciki,聽 meyasa yake yin haka?聽 Ko gajiar bikin ce be sakeshi ba?聽 Yanda yake wayoyinsa cikin kwanciyar hankali ba tare da ya dago ido ya kalleta bane ya sata mamaki ainun,聽 kamar ba shi ba,聽 kamar ba Zaid dinta ba, bakinta na mata nauyi,聽 da kyar ta samu ta juya harshenta "My Forever" yanda kasan ba da shi takeyi ba,聽 yayi banza da ita,聽 a ranta tace "ko dai be ji ba?" ta sake kiranshi da "Zaid" nan ma shiru yayi mata, wannan shine "hakuri" da Daddynta yake ce mata ta yi? Wannan shine kawar da kai din da ake ta mata magana a kai? Tun baaje ko ina ba? Dama haka maza suke da sunyi aure? Ba haka yake ba da, kamar ba loving and caring Zaid dinta ba,聽 wanda bata taba so ba sai a kanshi,聽 wanda shine ya koya mata yanda zata soshi?聽 Duk ya rikide ya chanza,聽 bata so tayi imagining wani abu is about to go wrong,聽 bata so tayi tunanin chanjin nan da wani manufa,聽 bata so tayi tunanin komai,聽 gwara tayi ta mai uzuri, da sauri zuciyarta tace "ko dai yana da aljanu? Don sharetan da yakeyi ta tabbata ba yin kansa bane,聽聽 Ko moodswing ne? Ai ana haka,聽 wani lokacin kaji baka son yi ma kowa magana,聽 to kila hakan ne,聽 bari ta bashi space,聽 ko anjima zai dawo daidai.

Mikewa tayi zata bar dakin ta tsinkayi muryansa a sama "Ina Wayarki?" da sauri tace "Yana daki" muryarsa cike da umurni yace "dauko" da sauri ta fita Daki ta shiga dakinta ta bude jakkarta ta dauko wayar, komawa tayi dakin da ta bar Zaid ta mika mishi wayan, amsa yayi da karfi kamar fizge, ta kalloshi da sauri, a gaban idonta ya kashe wayar ya jefa cikin aljihunsa ya cigaba da latsar wayarsa da laptop, gabanta ya fadi, me hakan ke nufi? Me Zaid ke nufi? Me yakeyi haka? For how long zata cigaba da mishi uzuri? Bakinta na rawa tace "Meyasa ka kashe min waya? Meyasa ka kawoni Gidan nan? Shin baka san Gidanmu bane nan?" Zaid ya fashe da wani irin dariyan da daga ji kasan cewa bana lafiya bane,聽 kafin yace "thats what you dont know,聽 This is my house,聽 it has always been My house(shine abinda baki sani ba,聽 wannan Gida聽 na ne,聽 dama chan Gida na ne" ta ja baya tana kallonshi, a iya sanninta,聽 ta san wannan gidansu ne,聽 shiyasa suka saida gidansu na Abuja suka dawo Kano,聽 yana nufin da ya siya gidan ne ya zama nashi.

Ita yanzu ba ma wannana ba, Maaurata ne su, burinta ya cika,聽 ta auri Masoyinta abun sonta, be kamata su fara da haka ba, ta sautar da murya tace "My Forever, me ya faru ne?聽 Kana jin yunwa? In dafa maka abinci?" Zaid ya zaro ido yace "Abinci? Abincin diyar Hajiya Mairo? Allah ya tsareni da cin Abincin Mahainta,聽 nasan ko an baki maganin da zaki saka mun inci in mutu聽 ku gaji Dukiyana, No thanks?".聽 Yanzu abun kuma ya fara ba Ziyada tsoro,聽 tsoro fal ranta,聽 ta zaro ido,聽 kanta na juya magananunshi,聽 jikinta yayi sanyi, tace "haba My Forever,聽 wani irin magana kake haka? Ta ya zan samaka magani ka mutu?聽 Ya zaayi in kashe Mijina? DanAllah ka bar irin wannan tunanin" ta karashe cikin sanyin jiki tare da kamo hannunsa,聽 kamar wuta ya tabe shi da sauri ya janye hannunsa tare da mikewa,聽 kar ki sake tunkaro ni,聽 kar ki sake gigin tabani,聽 jinin Hajiya Mairo Najasa ne,聽 ke najasa ce, in kuma shaawar da kika kwaso kike son a rage miki ina da Yara Christians sai in hadaku su zo su biya miki bukkatarki" be karashe maganarshi ba ta sa hannu ta kwashe shi da Mari, Murmushi聽 Zaid yayi tare da shafar fuskarshi,聽 abunda tayi yanzu ya harbi tunaninta,聽 Marinshi tayi, Marin Mijinta ta tayi,聽 kawai聽 sai聽 ta fashe da kuka, "donAllah kayi hakuri, ban san nayi ba" be tanka ta ba ya hau kan gado,聽 da murmushi dauke kan fuskarshi,聽 duk sai ta sha jinin jikinta,聽 rarrafawa tayi kan Gadon tace "ka min magana,聽 ka yafe聽 min, in ba zaka iya ba ka rama,聽 ga fuskata nan,聽 ka rama" banza yayi da ita ya dauko wayarshi da mukuli ya sa a aljihu,聽 fita yayi daga dakin ta bishi saurisauri gudugudu, a tsakar gida ya kwalawa Sule kira,聽 daga dakin Maigadi wani ya fito sanye da kayan uniform,聽 yace "Kar wanda ya sake ya shigo min gida,聽 kar kuma wanda ya sake ya fitar min daga gida,聽 kana jina?" jiki na rawa yace " Eh Oga,聽 nagane" Zaid ya kalleshi sama da kasa yace "Wannan聽 in Mairo tazo ai bugeka zatayi ta shigo,聽 ya latso idi a waya ringing daya ya dauka "Idi,聽 kaje Police Headquater kace nace ina son tsaro a Gida" da fita zaiyi amma ya fasa,聽 ya koma cikin gidan,聽 itama ta bishi,聽 wannan wani irin masifa ne?聽 A ce ko kwana ba tayi a gidanta ba amma ta fara haduwa da bacin rai?".

Kan Kujera ya zauna ya kira Gidan Marayu na Kaduna yana waya,聽 tana zaune dan nesa dashi tana karantar halaiyarshi,聽 komai nashi yayi聽 ne,聽 ji yanda yake magana cike da isa,聽 ta kasa gane me yake nufi da ita,聽 amma ai ta ji labarin yanda angwaye ke rawan jiki a kan Amarensu,聽 ita meyasa nata ya sha bambam? Suna zaune Idi ya kira Zaid ya ce mishi ga Police聽 nan da Civil defense, kamar ta sani ta bi bayanshi聽 da ta ga ya mike ya fita tsakar gida,聽 nan ta ga garada sun kai sha biyu da uniform din tsaro,聽 duk suka shiga kwasan gaisuwa be karba musu ba ya shiga basu umurni kamar haka;
"Ban yarda a shigo min Gida ba,聽 ban yarda na ciki su fita ba,聽 i mean ko waye kar a barshi ya shiga,聽 i want tight security here".聽 A tare suka ansa da "Yes Sir".
Nan take ya kira Armstrong, ringing daya ya dauka "book our tickets,聽 we are leaving for Porthacourt聽 now" Zaid ya wuce ta ya shige ciki,聽 da gudu ta bi bayanshi, ta bishi har daki inda yake hada Naurarshi cikin jakka, baki na rawa tace "Porthacourt? Chan zamu?" banza yayi ya kyaleta,聽 tace "kayi wa darajan manzonAllah ka min magana" ya dago ya kalleta, zaiyi magana kuma ya fasa,聽 tace "please, You are not leaving me here are you?" nan ma shiru ya mata,聽 tace "ka ban wayata ina so nayi magana da Yayana" nan ma shiru,聽 da sauri tace "Don girman Allah ka kaini Gida wurin Mummy na,聽 ka kaini wurin iyayena" tsaki yayi a k'arshe ma ya finciki jakarshi me kama da school bag ya rataya ya fita ya bar mata daki.

A guje ta kwasa ta bishi,聽 a tsakiyar farlo ta cimma shi,聽 ta rungumoshi tare da fashewa da kuka,聽 jimmm yayi yana tsintar kanshi cikin kunan rai,聽 be san聽 dalili ba,聽 kukanta ne ya sashi kuka?聽 Ko haushin ta taba shi?聽 Sosai ta rungumeshi,聽 ta matse shi ta baya, tana kuka har hawayenta na zuba akan farar rigar bodyhug dinshi,聽 cikin kuka take cewa聽 "me ya faru damu?聽 Me ya samu soyayar mu?聽 Me na maka? Meyasa kake min haka? A iya sanina banyi maka wani abu ba, all i did was to love you,聽 i didnt do anything wrong,聽 Sonka kawai nakeyi,聽 shin So dama laifi ne? Ina Alkawarin Soyayyar da ka min?" zaiyi karya in yace Jikinshi be mutu ba,聽 zaiyi karya in yace be jin duk wani kalamanta, murya dishidishi yace "ki sakeni" kara matseshi tayi tana girgiza kanta a jikinshi tana cewa "ba zan sake ka ba, sai ka gaya min聽 what change,聽 sai ka gaya min what happened聽 to us" da kyar ya tattaro wani courage ya daka mata tsawa yace "Ziyaaaaaa,聽 Let Go" lumshe idanunta tayi,聽 daidai da saukowan hawaye masu dumi,聽 duk聽 da tana cikin tashin hankali,聽 wallahi taji聽 kiran nan da yayi mata da wani suna da ba wani mahalukin da ya taba kiranta dashi "Ziyaaaa" sake kwantawa tayi a bayanshi ta girgiza kai tace "No,聽 i wont let go,聽 Never (ba zan barka ba,聽 ba zan taba barinka ba)".
Shikenan ta gama kashe jiki,聽 be so be so ya yarda,聽 amma tausayinta yaji,聽 karo na farko聽 da tausayin wani abu ya darshe shi.

"Your Plans,聽 dont let het ruin it" Sashen zuciyarshi ta tunasarshe shi,聽 da karfi ya banbareta daga jikinshi ya yasar da ita a kasa yace "kar ki sake tabani,聽 kina so kisan what changed? Zan gaya miki,聽 ban taba sonki ba,聽 i cant love you" dariya me hade da kuka takeyi tace "karya kakeyi,聽 biglie,聽 ban yarda ba ba zan kuma yarda ba,聽 kana sona,聽 shiyasa ka sa akayi bikinmu cikin kurarren lokaci,聽 you聽 cant wait to have me,聽 shiyasa aka aura maka ni cikin kwana biyu,聽 kana sona, so mai yawa, you love me that much" Zaid ya girgiza kai irin na tausaya makin nan yace "You are even more stupid than i thought, dont you get it? Ko da yake diyar Mamanki ce ke, bakwa ganewa, to barin gaya miki Na aureki ne don na Wulakanta ki, na tozarta ki, na Aureki ne don na dau fansa, wanda so far ina ganin da kyau, na Aureki ne don na kuntata miki da mahaifanki, baki fara ganin wulakancin ba? Na kawo ki Gidan da kuke takama naku ne a da, it was never yours, i took back whats rightfully mine".
Chapter 79 · 0% Book details